NOVELSUncategorized

DIYAM 48

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forty Eight: When The Going Gets Tough

Bature yace “when the going gets tough, only the tough gets going” hakane?
It is either you get tough ko kuma kana ji kana gani a tafi a barka.


“Mr Abatcha? Menene hadin Sadauki da Mr Abatcha?” Na dafa bango na mike ina kallonsa kawai. Babu abinda zance masa a yanzu, dama kokari na shine inyi preventing dinsa from finding out kuma ya riga yayi. So magana ta kare kuma. 

Ya zuba min ido, “magana nake miki Diyam? Sadauki kike texting ko Mr Abatcha” kallon da nake masa yasa ya tsaya shima yana kallona and then the realization hits him. I saw lokacin da yanayin fuskarsa gaba-daya ya chanza, ya saki wayoyin duk guda biyun suka zube a kasa. His whole world came crashing down on him. 

“Mr Abatcha? Mr Abatcha shine Sadauki? When? How?” Ya saka hannayensa duk biyun acikin kansa ya fara zagaya palon da sauri har wani gumi ne yake karyo masa. Idonsa ya ciko da kwalla. Ya taho da sauri ya tsaya a gaba na “you? You were playing me all these years? All these years kina tare dashi dama? My God!” Ya sake dora hannu aka jikinsa har rawa yake sai ya dafa kujera yana mayar da numfashi. Ya jima a haka sannan ya juyo yana kallona sannan yace “ke kika saka shi ya bani aiki ko? I remember ke kika ce inje in nemi aiki. Ke kika saka ya dauke ni without even looking at my credentials saboda ku kasance tare ko? Saboda kuyi controlling dina ko? Is that it?” Na girgiza kai kawai amma kafin inyi magana yace “kar kice min komai, ko inzo in babballaki anan. My God, wannan wanne irin cin amana ne, hatta sunan da zan sakawa yata shi ya zaba min” sai ya fara dukan kansa da hannunsa yana cewa “wawa, dolo, soko, dakiki”.

Sai kuma ya zauna akan kujera ya dafe kansa da hannayensa yana girgiza kai. Yace “wato tare kukayi planning din abinda aka yiwa Alhaji ko? Shi yasa ya tura ni tafiya a lokacin. Da aka gayamin sharadan daya saka sai da nayi tunanin me yasa a ciki bai ce in sake ki ya aura ba, ashe baya bukatar wannan tunda already yana tare da ke”.

Kamar wuka haka maganganun Saghir suke huda ni. Wannan accusations din yana daya daga cikin abinda na kasa mantawa har yau. Komai zan gaya masa ba zai fahimta ba, amma duk da haka zan gaya masa ruwansa ne kuma in ya dauka in kuma bai dauka ba matsalar sa. I was beyond caring a lokacin.

Nace “sanda Sadauki ya dauke ka aiki bansan shi bane ba, bai taba contacting dina ba, I had no idea yana ina ma har sai ranar da kuka shirya masa party, a ranar nasan shine oganka. Bansan dalilin sa na daukan ka aiki ba, zata iya yiwuwa ya dauke kane kamar kowa, wannan shi yasa ban gaya maka ba tunda ina ganin fadin bashi da amfani. Bamu taba magana ni da Sadauki ba in banda sanda Alhaji ya tura ni gurinsa, a lokacin ma yayi shutting dina out dan haka babu maganar da muka yi sai wadda takaini. Bamu taba waya da Sadauki ba. Texts din da ka gani sune a tsakanin mu. Wannan shine gaskiyar magana” na juya zan bar gurin naji kafafuwana sun rike tun daga cinyoyi na zuwa marata suna min wata irin suka. Nace “Saghir?” Bai amsa ba sai cewa yayi “karki gaya min karyar banza. Wallahi bai isa ba. Baku isa ba daga ke har shi kuyi min wannan cin mutuncin. Sai na nuna masa dukiyar sa ta banza ce wallahi sai ya raina kansa. I will destroy him ko zan rasa raina wallahi.” Sai ya shiga daki ya dauko key din mota, zai wuce ni na rike rigarsa nace “Saghir bani da lafiya” ya kwace rigarsa yace “zaki warke ne ma, munafuka” ya fice ya barni without another look at my side.

Na daga rigata naga jini yana bin kafata a dai dai lokacin dana ji tashin motarsa. And I realized something, na rasa cikin jikina kamar yadda na rasa twins dina. And there and then na yanke shawara, na gama auren Saghir.

Nayi kokarin motsawa daga gurin na kasa. Ina so in taimaki kaina kuma ina son in warning Sadauki dan ban san me Saghir zaiyi ba daya fita amma na kasa zuwa ina waya ta take yashe a kofar dakin Saghir. Kafafuwana tamkar sun daina aiki haka nake jinsu sai jini ne yake biyo su zuwa kan tiles. Option dina daya, Fauziyya. Na fara kiranta da dan abinda ya sauwaka daga murya ta. “Fauziyya, Fauziyya” amma shiru, ban tabbatar ta jini ba ko a’a saboda nasan kallo takeyi. Na jima a haka sannan na jiyo hawowarta sama. Tana shigowa palon ta tsaya tana kallo na yadda na hada gumi ga busashshen jini a hancina ga kuma jinin da yake kwance a kasa na sai ta saki purse din hannunta ta taho da sauri “Halima? Me ya same ki haka?” Cikina kawai na iya na nuna mata, ta kama ni ta kwantar a gurin sannan ta koma ta dauko jakarta data yar ta dauko wayarta ta fara kira. Jikina ya bani Saghir take kira sai kuwa mukaji wayar tasa tana kara a kusa da tawa. Ta ajiye wayar tace min “ina ya tafi?” Kaina kawai na girgiza mata, sai tace “ko miscarriage kike yi ne? Ko asibiti zamu je?” Na gyada mata kai sai ta kama ni zuwa toilet dina, ta taimaka min na wanke jiki na amma fa jini zuba yake dan pad ma ba zata rike shiba sai face towel ta bani na saka muka tafi. She half carried my down the stairs sannan ta saka mai gadi ya samo mana abin hawa muka tafi asibiti. Wannan yasa ba zan taba mantawa da Fauziyya ba.

Bayan fitar Saghir daga gidansa ya shiga motarsa ransa a mugun bace, bai taba jin bacin rai irin na ranar ba danji yake kamar ya hada ni da Sadauki ya saka mana wuta mu kone. Sai kawai ya bude aljihun motarsa ya dauko wata tsohuwar ajjiyar sa da kullum in ya dauko zai sha sai ya tuna yayi wa Diyam alkawarin ya daina sha. But yau Diyam din ce da kanta ta bata masa dan haka with vengeance ya shanye kwalbar gabaki dayan ta sannan ya kunna motar ya fita daga gidan ya tunkari kamfanin Abatcha Motors.

Sadauki yana cikin meeting da ma’aikatan sa, meeting din da ba’a ko gayyaci Saghir ba sai assistant dinsa. Sadauki yana tsaka da yin bayanin sababbin dokokin da yake kafawa saboda ma’aikatan da suke incompetent da irin hukuncin da za’a ke dauka akan duk mai karya doka sai ga Saghir ya banko kofa ya shigo, duk suka juya suna kallonsa ya taho yana tangadi ya nuna Sadauki yace “munafiki. Allah ya tona asirin ka yau” gaba-daya gurin suka mike, wasu daga ciki suka mike suka yo kan Saghir amma sai Sadauki ya dakatar dasu da hannu yace “ku rabu dashi” ya gyara zama ya kalli Saghir yace “menene yake tafe da kai?” Saghir ya nuna Sadauki yana kallon mutanen gurin yace 

“wannan da kuke gani is not who he is saying he is. Ba sunan shi Abatcha ba sunan shi Sadauki kuma Sadauki shine Mr Abatcha kuma shine saurayin Diyam kuma Diyam kullum sai ta fadi sunan Sadauki ashe shine Mr Abatcha. Shine kuma ya bani aiki sannan ya saka wa yata suna ya siya mata ragon suna. Yazo kuma ya kai Alhaji kara ya karbi rabin gidan sa yayi gidan gona. Sai yau na ga message din sa a wayarta sannan na gane ashe shine” 

Wani a gurin yace “do you understand cewa baka making sense kwata kwata?” Sauran mutanen suka kwashe da dariya. Sadauki yayi ajjiyar zuciya ya nuna Saghir yace “Ladies and gentlemen, this is an example of one of the effects of shaye shaye” sai ya kalli security yace “get him out of my sight”.

A asibiti akayi confirming fitar cikina. Amma suka ce bai gama fita ba. Sai suka bani wani tablet suka ce zai fitar da sauran. Muna can lokacin tashin su Subay’a daga school yayi, Fauziyya ta koma gida ta dauko ta ta kai makotan mu sannan ta dawo gurina. 

Har muka koma gida gurin magrib Saghir bai dawo ba. Na sha tablet din sannan na kwanta, Subay’a tana ta jera min sannu. Na sake trying number din Sadauki bata shiga, duk da dai nasan koma menene zai faru ya riga ya faru. Na kwanta ina ta jiran shigowar Saghir amma shiru har bacci ya dauke ni banji ya shigo gidan ba. Cikin dare wani azababben ciwon mara ya tashe ni, ji nayi kamar raina zai fita gashi daga ni sai Subay’a a daki. Jini guda guda haka ya rinka fita daga jikina. Ban yi bacci ba sai da aka fara kiraye kirayen sallah.

Cikin bacci naji Fauziyya ta shigo dakin tana tashin Subay’a, sai kuma tace min “Daddy fa bai kwana gidan nan ba. Ga wayarsa kuma tana nan. Na kira Kabiru kuma yace basa tare. Ko zaki kira gidan Alhaji kiji ko yana can?” Nace mata to kawai, amma ba wanda na kira. Ita ta shirya Subay’a ta mika ta school sannan ta dawo ta kawo min tea. 

Zuwa 12 na dan warware, sai dai weakness sannan kana kallona zaka ga nayi pale saboda ba karamin jini na zubar ba. Na tashi nayi wanka, na fito na shirya sai na tsaya ina kallon kaina a mirror. Na dora hannuna akan marata ina tabbatar wa kaina cewa it is gone. It is dead before it even begins living. It is going to be the last thing da zanyi loosing a sanadiyar auren Saghir. Ina saka kaya na sai na jawo akwati na fara zuba kayana dana Subay’a. Ina cikin zubawa Fauziyya ta shigo, yanayin ta kamar a rude tace “Halima, kizo inji Kabiru” ta fita na saka hijab dina na bita a baya. Yana tsaye a bakin kofa ya kalle mu yace “Saghir yana station tun jiya. Bansan me ya faru ba amma ance security din gurin aikinsa ne suka kama shi suka damka shi a hannun police. Ban san menene charges din ba. Nayi kokarin yin bail dinsa sun hana ni, sunce order ce direct from the commissioner of police cewa kar a bayar da bail dinsa”.

Fauziyya ta zame ta zauna. Ni kuma sai na juya nayi hanyar sama. Kabir yace “Diyam ki kira gida ki fada. Maybe Alhaji yana da wani a sama wanda zai saka a fito dashi” na gyada masa kai kawai na wuce. Ina zuwa daki na karasa hada kayana na fito na wuce Fauziyya a palo ta zabga tagumi na je na dauko Subay’a na dawo na sake wuceta. Na shirya Subay’a sannan muka sauko tare da akwatin kayan mu. Fauziyya ta tashi tsaye tana kallon mu tace “ina zuwa haka?” Nace “gida” bata kuma cewa komai ba har muka fita. Mai gadi yayi min sannu da jiki sannan ya taya mu da kaya muka tari abin hawa muka tafi.

Inna tana ganina da akwati tace “lafiya” na ajiye kayan hannu na sannan na gaishe ta, bata amsa ba tace “lfy nace? Lafiya na ganki da tsakar ranar nan da akwati?” Na sunkuyar da kaina nace “Inna na gama auren Saghir” ta saka salati, “shi Saghir din ne ya turo ki gida ko kuma ke kika yi ra’ayin kin gama aurensa kika taho gida? Dama igiyar auren a hannun ki take?” Na girgiza kai nace “Inna Saghir fa….” Tace “Saghir me? Saghir din yanzu ai bana da bane ba. Kika zauna da wancan Saghir din ma ballantana wannan da kowa ya tabbatar ya chanja. Dama tun randa Sadauki yazo nan da maganar aurensa naga yadda kikayi nasan in ba sa’a akayi ba sai kin fito da wata maganar kuma” naji hawaye ya fara bin fuskata, nace “Inna ba a kan Sadauki na taho gida ba, tsakani na da Saghir ne, ni ba zan koma gidan sa ba Inna. Dan Allah karki mayar dani” tace “ina Saghir din?” Na share hawaye na nace “yana police station” ta sake wani salatin “me ya faru? Me yake yi a can?” Nace “Sadauki ne ya rufe shi.” Ta mike tace “kuma kika ce ba’a kan Sadauki bane ba. kira min Sadauki yanzu yanzun nan” nace “na baro wayata a can gidan. Kuma ma ba daukan wayata yake yi ba” ta kwalla kiran Asma’u. Tana zuwa tace mata “kira min Sadauki da wayarki” Asma’u tana kallo na da alamar tambaya ta dauko wayarta ta danna kira ta saka a speaker. Har ta gama ringing bai dauka ba sannan ta sake kira shima shiru. Sai kuma gashi ya kira. Ta dauka tasa a speaker naji muryar sa yace “Yar Asama ya akayi?” Tace “Inna ce tace in kira ka. Gata” Inna tace “Sadauki me ya hada ka da mijin Diyam har ka rufe shi?” Yayi shiru, ni kaina sai da nayi mamakin karfin halin Inna. Sai ta ce “tazo gida yanzu tace wai ka kama Saghir ka rufe shi” ya sake yin shiru sannan yace “ita Diyam din ce ta kawo kara ta akan na rufe mata miji?” Nayi saurin girgiza kai zanyi magana Inna ta harare ni tace “eh fa, shine nayi mamaki nace me ya hada ku?” Yace “a ce wa Diyam tayi hakuri, za’a fito mata da mijinta gobe in Allah ya kai mu” sai ya katse wayar.

Na saka sabon kuka “Inna yanzu haushi na fa zaiji yace na kawo kararsa” Inna tace “na sani ai. Haka nake so saboda ki fita harkarsa ki barshi yayi aurensa kema ki zauna ki rike naki auren”.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button