NOVELSUncategorized

WA ZAI FURTA 25

???? *WA ZAI FURTA?*????
              2⃣5⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri’a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.**KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki…… beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

????????????????????  *RUKAYYA  BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*????????????.

    ******************
*ABUJA NIGERIA*
…. Na rantse da Allah ban aminta ba, sai dai kaima ka dawo nan mu gama tare …. What do you take me for?
Bilkisu…… Da su mufeeda a school Zan Barka acan bana nan?…. Ya zaro ido…
Ta rike kugu billahil azim tare zamu koma FUDMA…. Abinda nake so ki fahimta….. I’ll never understand you, amma ka mayar dani shashasha…. Wallahi bazan aminta ba,
Ya harde hannuwa a kirji ji yakeyi kamar ya kamota ya rungume….
Ta banka mishi harara, yanda kake da kishi nima haka nake dashi, dole ka zaba ko nan ko dutsinma Amma kafa ta kafarka……. Ya kyalkyace da dariya…
  Ikon Allah Bilkisu ta dawo….. Ta banka mishi harara, Shi yasa ka daina kula ni ka kaurace mun?
Kana son proving meye?, Wannan ne prove? Ai prove shine gani ga ka ba Ina can kana can ba….. Naji maida wukar yanzu zauna ya kike so madam…..
Ta galla mishi harara kaje ka yo cancelling din komai mu koma FUDMA…. Ya maganar Sanya nikaf???? Wannan ce damuwar ka?
Zan saka…… Ya kura mata ido…. Sai Kuma kunya ta kamata ta sunkuyar da Kai….. Ya yi murmushi yace *Akwai chakwakiya*……. 
Tayi shiru….. Watau kina son gani gaki ko?
Ni Zaki kure Bilkisu????
  Kome zakace sai dai kace amma wallahi ba school din da zance ba tare da Kai ba, idan Kuma ka dage na rantse da Allah sai dai a warware….. Dal!.. ya buge bakin da yatsa… Mutu ka raba yarinya duk yanda kike so haka zanyi what next?
Ta zumbure baki shikenan….
Yayi murmushi yace *nawaoooo* 
   Har na siya Miki mota wallahi gata can awaje don bana son wani driver kawai da akwai masu binki a baya da tsaronki Koda yaushe….. Sai ka koma da abinka su Kuma ka canza masu aiki…. Ya tuntsure da dariya…. Anya Baki fini kishi ba???? 
Ta Dan harareshi cikin kunya.
 Ya Kama dariya, Watau bazaki yarda gani ga mufeeda bakya Nan ba ko?
Ta rufe fuska nidai ya Isa, 
Ya Kara dariya anya wannan semester din Babu damuwa????
Ba wata damuwa,
Ba Kya Jin tsoron anything can happen bayan nasan ke matata ce Bilkisu?
Ta harareshi ashe baza ka iya ba daddyn mamaki ba…… Yayi murmushi Zan iya Mana.
To Kuma.
Ya bi ta da kallo, ya zuki iska ya fesar tare da sakin ajiyar zuciya.
   Gaskiya rigimar ki tafi tawa… Ta dan harareshi, but I’ll try my best ya karasa maganar Yana murmushi.
  Ta Dan sunkuyar da Kai, ya Mike Amma bazaki koma gobe ba sai next week ki fadawa daddy Zan Aiko a daukeki Zaki hau private jet na from Abuja direct to katsina zamu tare ki a can kinji ko?
 Ta daga Kai kawai.
  Yana Isa gida ya tarar da sadeeq a basket ball ground, ya chabe ball din …. Malam ya akayi ? Ya rike kugu,
    Wai kasan nayi wa yarinyar nan transfer taki yarda?
  Ka mayar da ita Ina?
Wallahi nan Abuja , ya danyi dariya, could you imagine kishi ke damunta??…. Sadeeq ya kyalkyace da dariya na fada ma miskilanci ke hana Bilkisu nuna maka so amma wallahi zaka Sha wahalar ta idan ta goge …Amma fa ta birgeni.
  Kai ta birge ko Ni sadeeq kasan dai akwai rigima ko?
Babba ma kuwa suka kyalkyace da dariya tare da tafawa.
Ya wurga mishi ball din suka Fara bugawa cikin nishadi.
  Yanzu ya zakayi kenan?
  Zan siyi gidan nan Wanda naga angama sabo na darawa ko nawane yayi Masa kudin bala’i Zan biya Mata,sai ta zauna ita da Aisha da Maryam Amma banda khausar don bana son yarinyar… Daddy zai yarda?
Dolen sa ma, Zan Sanya Mata masu gadi sosai Nima na siya Mana gida bayan gidan redio zamu bar hostel…… Sadeeq ya buga tsalle amma ka gama birgeni nawan suka tafa suna dariya…
  Na Kira VC na fada mishi ayi meeting wallahi duk lecturer din da ya Kara Kira mun Mata Zan daure Shi….. Sadeeq ya zaro ido ai FUDMA sun gama shiga uku Yanzu…… Suleiman Kuma na mishi text na fada mishi na auri Bilkisu kallonta idan yayi ya gama Jin dadi har abada don zai Kare rayuwar sa a prison….. Anwar kada ka firgita makarantar can…. Yayi dariya kawai.
  Da mota zamu koma yanzu?
 Ya kyalkyace da dariya Kai mota ce dakuwar ka Wai?
To motoci ba mota ba, Zan fito musu a mutum sak!
   Nawaoooo… Sadeeq ya fada.
    Bilkisu kuwa, Miskilancin ta da zurfin ciki ya hana ta fada wa mommy abinda ya faru ba.
  Haka suka taru sukayi Mata nasiha cikin hikima na duk darasin maganar bai wuce ta kiyaye tarayya da shi Kuma ta kula.
    
    
   *******************
*Federal University dutsinma*

   Aisha da Maryam abun ya daure musu Kai, gidan tsoro ma yake Basu, har basa son fita saboda kattin da gewaye da gidan, komai an saka gida abinda ke gida ga masu aikin abinci da gyaran gida…..
 Da yake sun rigata komawa da kwana biyu shine yakai su ya masu bayanin anan zasu zauna tare da Bilkisu ranar duk da suka gayyato wata kawa ko namiji wallahi sai yayi maganin su….
Su Kam sunyi tsuru tsuru gashi har yau basuyi waya da Bilkisu ba.
  Misalain karfe shidda na marece jirgin ya ajiyeta motoci hudu an musu layi Yana tsaye ya goya hannu a kirji ta Fara saukowa da zumbuleliyar hijab har kasa ya kura Mata ido tun kafin ta karaso ya bude Mata kofa….
  Tana shiga ya shiga suka rufe kofa aka fizgesu sai dutsinma…..
Ya kalleta ba gaisuwa hajia?
Ta danyi murmushi, 
Kin gaji ko?
Ta ce hmm kawai,
Ya makarantar?
Ta tambayeshi tana kallon fuskar Wayarta,
Lafiya Lau, Amma fa ban shiga ba har yau sai gobe nima Zan Fara zuwa lecture… Ta Dan kalleshi saboda me?
Ya Dan yamutsa fuska haka kawai…. Sai tayi dariya.
Dariyar me kikeyi?
Naga kana mun karairaya kamar mace… Ya kyalkyace da dariya Wai Ina son in birgeki…. Ta dalla mishi harara…. Ya Kara dariya.
Su Aisha sun kagara ki dawo…
 Kai meye hadin ka da Aisha???…. Ya zaro ido ya watsa hannuwa ba komai fa….
Sai tayi murmushi, 
Anya Bilkisu???, Ya leka fuskar ta.
Ta rufe tana Yar dariya.
 Kin iya mota?
Um.
Good, to na ajiye Miki tana nan, zaku zauna keda su Maryam, nima nabar hostel muna bayan gidan redio nida sadeeq, idan daddy ya Miki magana kice ninayi Haka, akwai masu gadi da ma’aikata Amma fa ki sani idan zakiyi mun abinci kada kisa kowa naki nake so kin gane ko?
  Ta mishi banza.
Ko bakiji ba?
Karatu nazo ko girki?
Komai ma kinzo yi, kin sani cewa akwai Aure na akanki ko?
Gabanta ya bada ras!
   A bakin gate ya fita yabar su suka shiga gidan driver ya fito yabar Mata motar tare da Mika Mata key, ta zaro ido Wai wannan motar ce tawa?
Ya sunya eh Hajia, ta amsa kawai tayi ciki….. Su Aisha suka kwaso da gudu tana ganin su ta fasa ihu itama sukayi ciki suna Murna………Suka tsareta da tambaya Wai ya Haka?
Ta fada masu ya tura iyayen sa neman Aure Bata sanar dasu akwai Aure akanta ba.
Mufeeda kuwa hauka kadai ke batayi ba da taji Anwar ya siya ma Bilkisu gida ba.
Zuwanta biyu Amma ko layin gidan Bata iya kaiwa saboda body guard, shima ta gano nashi gidan cikin Daren Nan ma securities ne gewaye unguwar…..

Ta dunga kunduma ashar tare da Shan alwashin gobe sai ta ji dalili.
   Bakwai suke da lecture ta munafuki Richard, akayi sa’a Aisha ma nada 7am
Suka fito abin mamaki har an goge motar…
Ta kalli Aisha wallahi kunyar hawan motar Nan nakeji Aisha….. Meye na kunya?
Kuma ba ga nikaf kin saka ba?
Kai nasan yau na gama shiga uku makarantar Nan….. Ke muje ni ki ajiye ni kada na makara ta bude motar ta shiga … Ko Zaki ja mu….??? …. Ni??? Ta daki kirji.
Anwar yau ya mayar dani kauyen mu kike so ko?
  Ba yanda ta iya dole ta shiga tare da bata wuta suma suka tayar da mota suna jiran ta fita su bita ( securities biyu ),, ta fita gate din a hankali tana Hawa titi ta chilla da gudu saboda sun kusa makara. Suma suka rufa Mata baya.
Duk da safiya ce duk tsiraren mutanen da wuce sai sunbi motar da kallo…..
Kai Anwar karshe ne, shida sadeeq kasa suka tako, a bakin gate ta wuce su, ya kyalkyace da dariya Sadeeq yarinyar can gudu take da mota fa…
Dan ubanka mu ba ka hana mu dauko ba?
Ya Kara dariya suna ta sauri….
  Ta tsaya Aisha ta sauka saboda ba hanyar su daya ba ita ciki zataje Aisha Kuma nan farko farko.
  Tana zuwa kowa yayo ma motar chaaaaaa….. Chinayye ta gane ta da gudu ta makale tana fadin Bilkisu oyoyo…..
  Ya akayi Kika ganeni?
Ta fada a hankali , haba ya bazan gane ki ba?
Wai kinyi Aure?
Inji waye?
Eh Mana ance you are married woman now….no, not yet. But am engaged… With Anwar??…. Shigowar sa yasa ta Kyaleta, ya rufe idanun sa da facing cap abin mamaki kawai ya wuce baya yaki Zama kusa da ita.
  Suleiman ya shigo sai kawai ya chanza layi ya koma can baya saitin Anwar din.
  Sai mazurai yakeyi cikin facing cap.
 Mugun na shigowa sai cewa yayi test… Hankalin kowa ya tashi, ko ajikin Anwar, 
Nan da Nan Bilkisu ta Fara kyarma…..
Question biyu ce, ba Wanda ya sani Anwar kadai ya amsa da kyar Bilkisu tayi attempting ta biyun sai kuwa su chinayye.
  Yana fita ya taso da sauri… Kin amsa?
Ta zumburo Baki Ina na sani?
Bakiyi ba kenan?
To me Zan rubuta?
Ya buga tsoki this man .
  Nan da nan Yan class suka Fara kallon kallo.
Shi kuwa Suleiman Richard na fita shima yabar ajin.
  Ya zauna bisa table Yana kallonta, budo in Miki bayani ya saboda gaba… Ta Mika mishi book din, duk nikaf din ta ishe ta ba yarda zatayi ne.
  Ya Fara Mata bayani a hankali ya lura sai mutsu mutsu takeyi yace Wai ya akayi?
Nikaf din nan ta isheni wallahi Dan Allah in cire?
Ya danyi dariya cire Mana .
Ta kalleshi da sauri da gaske ko gatse?
Sai kawai yasa hannu ya cire mata….. Dai dai shigowar mufeeda…. Ta tabbata wallahi, kutumar uba… Anwar da gaske An daura muku Aure da wannan banzar….. Ji kake tasssssssss! Fassss…..ratssssss duk illahirin hankalinta ya bace ta gigice ta kidime shima ya razana ainun ganin Bilkisu tsaye tana wanka Mata wadannan marukan………….na rantse da Allah Akan *Anwar Zan iya kisa* don Haka ki kiyaye… Body guards suka gani cirko cirko nan da nan Yan ajin suka fara direwa ta taga saboda firgici…….✍???? Ayi hakuri da kadan.

*maman Abdallah*????

*uwa Mai bada mama mom ( Maryam adamu tikau maman amannas) mom you are the best I love you so much Mom*

Wadanda ke cewa ba ni ke rubutawa ba a fada wa Mai rubutawa ta ci gaba da kokari Nima Zan dage wajen sharing…..????✍????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button