NOVELSUncategorized

DIYAM 53

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Fifty Three : Check up

Sai naji tunani na ya tsaya. I just want to make a sense of wannan abin but na kasa believing abinda nake thinking. Is Saghir helping himself out of Sadauki’s money? Ko kuma yana blackmailing Sadauki ne akan wannan maganar? But anya Sadauki zaiyi paying Saghir irin wannan kudin saboda empty
threats dinsa? Tun sanda yayi threat din ni ban ji ko alamar tsoro a voice din Sadauki ba. Menene ma kuma dalilin da yasa Sadauki ya mayar wa da Saghir aikinsa? In dai kuwa har Saghir kudin Sadauki yake dauka then he is dumber than I thought.

Koma dai menene ni abinda na sani shine ya kamata inyi warning Sadauki akan ya kula da kudinsa tun kafin Saghir ya debi wanda zai kassara Sadauki ko kuma shi wanda ba zai iya biya ba. Kamar yadda na tabbatar zan mutu haka na tabbatar Sadauki ba zai bar masa ba.

Wayar Asma’u na nemo na dauki number din da naga Sadauki ya kira ta rannan na saka a tawa wayar nayi dialing amma sai taki shiga, naji kamar in jefar da wayar saboda bakin ciki, wato a wannan number din ma sai da yayi blocking dina? Wai me yake tunanin kansa ne? Ni ma na damu, sai sune suyi tayi ai daga shi har Saghir din.

Washegari Saghir yazo gidan. Ya ci kwalliya fiye da yadda yake da sai sheki yake yi kamar tarwada. Sai naga rashin kunyarsa da har zai iya shigowa palon Inna bayan duk abinda yayi mata da kuma sakinna da yayi a gabanta. Subay’a ta tafi da gudu ta rungume shi ya daga ta sama yana juya ta kamar yadda yake yi mata sanda muna gidansa. Asma’u tayi tsaki ta fita. Sai ya dan rissina ya gaida Inna ta amsa masa ba yabo ba fallasa. Sai ta dauki mayafinta tace min zata je unguwa. Ya zauna yana kallona yace “babu gaisuwa gimbiya” na kalle shi nace “yaushe babana ya zama sarki ballantana ni in zama gimbiya?” Yace “ai ba gimbiyar gari bace ba, gimbiya tace ni kadai. Kinsan cewa an bani kyautar budurwa naki karba saboda ke? Ke kinsan wanne irin so nake miki kuwa Diyam?” Nayi shiru ina tunanin irin maganganun daya fada a nan palon a gaban Sadauki, is that his version of love? 

Yace “wata biyun nan yayi min yawa please. Ki rage. Ko kuma ince na rage miki da kaina. Na sayi sabon gida, you are going to like it. Zanyi tafiya zanyi two weeks kafin nan komai na gidan ya kammala ina dawowa zamu tare. So, I want you to get ready kafin nan kafin lokacin dan har dake din zamu tare a lokaci daya. Kinga da kin koma ma da dake zamuyi tafiyar nan. Am taking Fauziyya to the honeymoon I promised her, but in kin koma kema sai muyi fixing time ki zabi kasar da kike so mu tafi” na gyada masa kai kawai a raina ina jin haushin Sadauki da yace ince da Saghir zan koma. I don’t like this idea at all.

Ya fara duba kayan jikin Subay’a “wannan kayan duk sun tsufa a zubar dasu Diyam. Ga kaya nan na taho mata dasu suna mota sai ta cigaba da amfani dasu” sai ya dora ta akan cinyarta tana ta zuba masa surutu yana dariya, ina jinsu ya fada mata zaiyi tafiya ita kuma ta fara lissafo masa kayan da zai siyo mata. Sannan tace “Daddy dan Allah ka dawo da wuri mu koma gidan mu ni nafi son zama tarr da kai da Mommy” yayi pecking dinta a cheeks yace “ina dawowa zamu koma kinji princess? It is going to be sabuwar rayuwa for us”.

Sai naji a raina cewa tunda har yanzu ni matarsa ce then it is my responsibility inji source din kudinsa. Sai nace “kudi ka samu ne masu yawa haka? A ina?” Sai ya watso min wani mugun kallo yace “matse ni sai in gaya miki, kinsan dai tunda kika sanni da arziki na kika san ni ko? Ko kin taba gani na ina gyaran matattun motoci? Wanda ya samu dukiya sama ta ka shi ake yiwa tambayar inda ya samu dan zata iya yiwuwa yankan kai ko fashi da makami yake yi”. 

Sai da yasa na raka shi har bakin kofa, ya fito da kayan Subay’a jaka guda ya mika min sannan yace “I will be seeing you soon, sweet pie”.

Washegari jirginsu ya daga shi da Fauziyya, I didn’t even know ina suka tafi sai ya suka sauka ya kira ni yace min sun sauka a Miami, yace in ajiye number din saboda zai ke kira na da ita. 

Bayan tafiyar Saghir ne Asma’u ta kammala jarabawarta, tayi candy, sannan kuma hakan yazo dai dai dayin saukar Alqur’anin ta. Wannan yasa ta shirya walima a nan gidan mu ita da kawayenta. Inna ta aika wa duk yan’uwa aka gayyato su kuma ga mamakin mu sai gasu sunzo, sai dai abinda muka lura dashi shine babu jituwa tsakanin iyalin Alhaji Babba da kawu Isa. Aka gabatar musu da abinci iri iri wanda su kansu sai da sukayi mamaki, daga abincin da aka ci har zuwa sutturar da muka saka daga mu har Inna duk sun nuna cewa ba a cikin kunci muke ba. Su Murja sai tambayata suke yi “yaushe zaki koma gidan hamma?” Murja ta jani gefe “dan Allah Diyam in baki koma bama kiyi masa magana ko zaiji maganar ki. Kinga maganar auren nan fa ta tsaya duk uban kudin da yake samu kwanan nan amma yace ba zaiyi ba. Shi kuma kawu isa da muke tunanin tura masa samarin mu shi kuma gashi yanzu ko magana basa yi da Alhaji” nace “wai me ya hadasu ne?” Ta rufe baki tace “ba za’aji a baki na ba”.

Kwana biyu da yin walimar Asma’u sai ga Kawu Isa a gidan mu. Mamaki ya ishe ni na tuna ranar da yace sun cire mu a cikin zuri’a ranar da sagjir ya sake ni a gabansu amma yanzu gashi few months after ya dawo da kafafuwansa. Muka gaishe shi ni da Asma’u muka fita muka basu guri da inna. Sun jima suna maganganu kafin muji ya fita sannan muka dawo dakin. Asma’u ta saka Inna a gaba da tambaya “me yace? Me ya faru” Inna tace “ina ruwanki? Suda mai bakin magana” 

Sai da Asma’u ta tafi islamiyya sannan inna ta bani labari. “Zuwa yayi yace min wai dan Allah duk yadda za’ayi kar mu mayar dake gidan Saghir. Ashe abinda Yalwati take fada min rannan gaskiya ne, Suwaiba dai har da cikin Saghir a jikinta. Alhaji Babba yace shi lallai sharri aka yiwa dansa, shi ma kuma Saghir din yace ba nashi vane ba kuma yama fasa aurenta ke zai mayar. Shine shi kuma hamma Isa yazo yace kar mu mayar masa da ke in yaso yayi biyu babu kenan. Su yanzu likitan da zai cire cikin suke nema”. Nayi shiru ina jin hawaye yana bin fuskata. Na tuno zafin da naji sanda Saghir yayi min sharri a gaban yan’uwan mahaifina amma duk babu wanda yayi komai a kai. Ga zina nan ta kare a gabansu, yanzu sai su ware ni da Saghir waye mazinaci.

Bayan sati ya kuma zagayowa sai ga malam iliya maigadin gidan Saghir ya kirani hankali a tashe. Na tambayeshi sai yace “yan NDLE ne suka zo gidan, sun yi filla filla da komai na gidan wai suna neman kayan maye” cikin tashin hankali na tambayeshi sun samu sai yace “sun samu, a dakin mai gidan sukayi ta fitowa dasu sannan suka samu wasu kuma a motarsa. Yanzu tafiyarsu kenan nima guduwa nayi da ina jin dani zasu hada. Shine na kira ki tunda su basa nan in gaya miki halin da ake ciki” nayi masa godiya na kashe wayar, ina kokarin bawa inna labari sai ga kira ya shigo wayarta daga Hajiya Yalwati tana ta kuka “Amina mun shiga uku. Wai yan drugs ne suka zo zasu tafi da Alhaji. Alhaji Babba fa? Me ya hada shi da shaye shaye?”. Nan take Inna ta rikirkice ta saka mu muka shirya muka tafi gidan gaba daya, muna zuwa muka tarar har an tafi dashi ga yan gidan nan sun fito sunyi chirko cirko masu kuka nayi masu salati nayi, yan unguwa kuma ana tsaye ana kallo. Mukayi ta basu baki muna mayar dasu cikin gida har muka samu suka koma ciki sannan aka fara tunanin ta inda za’a bullowa lamarin. Ni dai na fada musu abinda mai gadin gidan Saghir ya fada, dan haka sai muka fahimci cewa neman Saghir suke yi shi yasa suka kama Alhaji. Aka kira Kawu Isa aka gaya masa amma yace shi babu ruwansa “tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka”.

Dan abin kunya sai surukan gidan aka nema, ciki harda wanda yake neman auren Murja, su sukayi ta zirga zirga Inna kuma ta saka Asma’u taje ta ciro kudi a account a bawa wancan cin hanci a bawa wancan amma sai da Alhaji Babba ya kwana biyu a garkame sannan suka sake shi da yarjejeniyar Saghir yana shigowa kasar zai danka musu shi a hannun su.

Ranar da Alhaji ya dawo gida haka ya zauna yana ta kuka kamar karamin yaro “ban taba ganin cin mutumci irin wannan ba, wannan yaro mai ya janyo min haka ni Muhammadu. Ankwa hannu da kafa haka aka saka min ana jana a titi kamar wanda yayi kisan kai” sai kuma ya fara yiwa Inna godiya a kan kokarin ta da karfin ta da kudinta gurin ganin an fito dashi. Yana ta kuka har ciwonsa yana kokarin tashi dan haka akayi masa allurar bacci mu kuma muka tafi gida.

What remains a mystery shine yadda akayi yan drugs suka yi suspecting Saghir yana ta’ammali da kayan maye har suka kaiwa gidansa ziyara.

Two weeks after tafiyar Saghir sadauki ya dawo. A gurin Asma’u naji zancen dawowar tasa sai kuwa gashi nan yazo gidan. Ina jin shigowarsa na shige cikin daki na lulluba kamar mai bacci. Ina jin su suna ta hirar su a palo, ya kawowa Asma’u graduation gift na wata desighner handbag da takalmi, ya kawo wa Subay’a yar karamar computer ta yara mai kyau. Ta shigo da murna tana nuna min “Mommy kinga abinda wannan yayan naki ya kawo min, amma ke yace bai siyo miki komai ba” na karba ina dubawa nace “to kije kice kin gode madallah” ta fita na koma na kwanta. 

Ina ta so dai inyi masa maganar kudin companyn sa, amma bana son ganinsa dan haka bayan ya bar gidan sai na kara dauko waya ta ban kirashi ba dan nasan ba shiga zata yi ba amma sai na rubuta masa message. “Ka sa ido a kudaden kamfanin ka. I might be wrong. Just taking precautions”. Na tura masa. Na zauna da wayar a hannu ina jiran reply, shiru shiru babu. Har na gaji na ajiye ta na tashi na cigaba da harkoki na. Aka jima na sake dubawa babu reply, nayi tsaki a raina nace “ku kuka sani” Sai kuma nake jin haushin kaina for caring a inda ni ba’a damu dani ba. 

Saghir yakan kira ni sometimes, in ya kira sai in bawa Subay’a suyi magana. Ko da wasa ban bashi labarin case din drugs ba dan nasan ba karamin aikinsa bane ba yaki dawowa dan ba damuwa yayi da abinda za’ayiwa Alhaji in bai dawo din ba. Ranar nan ya kira na bawa Subay’a suka gama maganganun su sai yace ta bani, na karba yace min “jibi zamu dawo. Ina son ki kawo Subay’a airport ta tare mu. Tace tana son zuwa” nace “okay Allah ya kaimu jibin. Allah ya kawo ku lfy” yace “ameen. Hope kin gama shiryawa dan daga airport sabon gidazamu zarce” na sake cewa “Allah ya kaimu” na kashe. I didn’t have the energy or the patient to argue.

Muna gama wayar sai naga Asma’u ta dauki tata wayar tayi kira sannan tace “jibi zai dawo” ta kashe. Ta kalleta nace “what was that?” Tace “Hamma yace in gaya masa ranar da Saghir zai dawo” na saki baki kawai ina kallonta. What was that about?

Ranar dawowarsu na shirya Subay’a tana ta murna muka tafi malam Aminu Kano international airport. Muka tsaya a gurin da aka tanada dan taryar matafiya. Subay’a tana ta tsalle ta kasa tsayawa a guri daya yayin da ni kuma nake ta lissafe lissafen halin da nake ciki. Ni har yanzu ban gama fahimtar kudurin Sadauki na mayar da Saghir aiki sannan da kuma hanani gaya masa cewa ni ba zan koma gidansa ba. Na fahimci kamar yana buying time ne but for what? Me yasa kuma yake son jin lokacin dawowar Saghir?

Muna tsaye akayi announcing saukar jirgin su Saghir, muna tsaye kuma har suka gama checking out suka fito. Na hango shi, as handsome as ever, hannunsa cikin na Fauziyya suna fitowa daga revolving door din gurin. Subay’a ta fara murna “Daddy, Daddy” ya dago mata hannu yana murmushi. 

And then as he steps his feet out of the door, police surrounded him. Police, not NDLE officers. Fauziyya ta matsa baya da sauri tana ihu, Subay’a ma ta fara ihun kiran Daddy yayinda shi kuma ya fara demanding dalilin kamashi. Na daga Subay’a na rungume ta a kirjina, muna kallo daga inda muke tsaye aka garkamawa Saghir ankwa a hannayensa aka wuce dashi police car da take gefe tana jira. 

Subay’a ta fara jera min tambayoyi “me yasa yan sanda suka tafi da Daddy na? Ina zasu kai shi?” A lokacin naji karar shigowar text cikin wayata. Na dauko ta na duba naga number din Sadauki. Sai yanzu yayi replying message dina. Na karanta “check up” it said.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button