NOVELSUncategorized

WA ZAI FURTA 7

???? *WA ZAI FURTA?*????
              0⃣7⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri’a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.**KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki…… beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

*Ina alfahari daku kawayen yarinta:*
*Rakiya Amadu m/bread da badiyya Amadu m/bread*

        ***************

*Federal University dutsinma*
 Aisha, sumayya da khausar sune kawayen Bilkisu na kut da kut!, Tare suka zo makarantar secondary school daya sukayi watan federal Bakori dake shiyyar funtua ta jihar katsina.
Aisha da sumayya political science sukeyi, khausar na micro biology sai ita Bilkisu dake Economics.
Su ukun dakin su daya, Bilkisu kadai ke nata dakin.
Mafi yawa su ne suka fi zuwa dakinta ko a secondary ana tare Amma ita komai nata daban ne.
Tana yawan yin girki baka raba ta da ko miya ce Shi yasa Mafi yawa sune ke zuwa wurinta neman abincin musamman irin lokacin da semester ta raba tsakiya komai yayi zafi.
Khausar na bala’in son Anwar Amma tun lokacin da ya dizga ta daga magana taji ya fita ranta.
Aisha ce ta shigo dakin tana ta kokarin yanka carrot da zata Sanya cikin farar hinkafar Daman tun safe kafin ta fita tayi miyar kifinta.
Ke yunwa fa nakeji har bana gani.
Tayi murmushi to gashi Bata karasa tsanewa ba ko zakiyi tsame yau ma?
Mtsew tayi guntun tsoki, tare da kwanciya bisa lumtsetsiyar katifarta, wannan uwar shinkafar Kuma fa ko yau kin tabbatar zamu zo kwaraka ne?
Ta dan tabe baki Anwar ne Mana da rigimar sa nace zanyi girki Wai zaici na tafin mishi dashi class 4 idan zamuyi tutorial.
Hmmm, kawai tace.
Ta Dan waigo Fadi kada ta kasheki. 
Ta kyalkyace da dariya keji Kama Kai ai bandai *furta* ba ko?
Murmushi tayi kawai,
Daga Nan Bata kara mata magana ba.
    Yar madaidaiciyar cooler ta samu ta zuba mishi miyar Kuma tayi amfani da Yar roba Mai marfi.
  Saboda kurewar lokaci a daki tayi sallah tun kafin ta sallame yayi mata missed call biyu.
A gurguje ta shirya ta fito.
A bakin gate ta kirawo shi, bugu daya ya dauka.
Malama kinfa shanyani,
Ya hankuri gani na shigo school kana Ina?
Lecture room 2, ya fada.
Okay I’m coming……ta kashe wayar.
Sanye take da doguwar riga ta lace coffee brown, hijqbinta kalar flowers lace din maroon.
Tana saka kafa wayar ta na Kara *Daddy ne ke mata video call* ta karasa da sauri tana murmushi.
Ya hangota Amma sai yayi kaman bai ganta ba har ta zauna kusa dashi dai dai kuma lokacin da ta ajiye mishi ledar abincin sannan ta latsa wayar…..Hello daddy. Ta fada tare da fadada murmushinta zuwa Yar dariya.
Yabi fuskar ta ta da kallo Yana masifar son tayi dariya Shi kadai yake ganin abinda yake gani.
Bilkisu ya kike?
Kina class ne?
Eh daddy kaga nazo karatu ne wurin Anwar ta kanga fuskar wayar saitin Anwar din.
Yayi saurin sunkuyar da Kai…… yarinyar nan nada hankali kuwa?
Anwar?…….ya dago ido da sauri….barka da wuni Daddy ya fada da sauri tare da rusunawa Yana Dan murmushi.
Dariya yayi ……Kaine Anwar? Yau ba’ayi fadan ba kenan? 
Ya zaro ido kadan kunya ta baibayeshi yayi saurin kallon Bilkisu atuhumce.
Ta janye wayar…..mun shirya daddy yaban hakuri ta fada tana dariya.
To yayi kyau. Allah ya taimaka a kula dai kada amanta Allah Yana tare da kowa a zahiri ko badini. 
Na sani daddy.
Ta zaro ido Wai daddy kana sokoto ne???
Eh mun zo nida mommy bikin saifullahi ko?
Ta zumburo Baki daddy……ke sai anjima kuyi karatu kada lokaci ya shige……
Daddy zakuzo din ko? 
Eh in shaa Allah zamu shigo jibi……yeeeeeee ta fasa Kara yayi saurin latse wayar Yana dariya.
Ta kalli Anwar su daddy zasu zo jibi……ya dalla mata harara. Ya akayi yasan  muna fada?
Ta danyi guntun tsoki…. Ai sun Sanka Ina Basu labarinka sosai…..kina cewa me?
Tayi murmushi.
Kinji?
Hmmm kawai tace.
Magana zakiyi meye kike fada ne?
Ka gane sun San wajen ka nake daukar karatu to ya kirane yace yau bamuje karatu ba nace munyi fada dakai shine……..yaushe mukayi fada?
Me yasa zakiyi karya? Sai kice fushi nakeyi dashi ba kice muna fada ba…….naji sorry oya muje ta bude littafin.
Ko sai kaci abincin zamuyi?
No, Zan tafi dashi hostel ne.
Okay.
Lafiya lau sukeyi tana ganewa sosai, yana magana tana satar kallonsa idan taga ya maida hankali ga littafin sai ta daddage kuwa ta Kura mishi ido.
Yana da kyau, natsuwa da Kuma kamala problem dinsa kawai miskilanci…..da yazo zai kalleta sai tayi saurin kawar da ido….haka..haka….sunyi nisa sosai sai taji an kwada mishi Kira “`ANWAR“`…..
Dukkansu suka kalli wajen… Mufeeda ce.
Gaban Bilkisu yayi mummunan faduwa.
Saboda, mufeeda ana raderadin budurwar Anwar ce physics department take yarinyar ta hadu karshe saboda iya daukar wanka, Bata fi Bilkisu kyau ba Amma saboda iya gayun ta yasa idan tana wajen baza’a taba ganin kyan Bilkisu ba da kullum cikin hijabi.
Sanye take da wani material dinkin Riga da skirt, tayi kyau matuka fuskarta sanye da kwamemen glass ya mata kyau sosai. 
 ……… Ta tsaya daga jikin taga alamar ganinsa take sonyi.
Kawayen ta Kuma na gefe suna jiranta.
Ya kalli Bilkisu please Ina zuwa, ya mike.
Wani abu ya taso mata ya tokare a makogoro tunda ta yi kasa da Kai bata dago ba.
Tana ta latsa waya ta ma kasa gane inane take shiga tana fita.
Agogo kawai take dubawa.
Mufeeda nada daukar hankali, kafin kace me…..Anwar ya fara shafa’a.
Ai nayi tunanin bazaka taso ba tunda ance tsoron ta kake ji.
Yayi murmushi sai kuma na taso Kika gane hakan ba gaskiya bane ko?
Wai meye tsakanin ka da yarinyar can da kullum baka tashi koya mata sai da marece Kuma ku biyu kawai?.
Yanzu dai gani. Ya fada Yana murmushi…..
Ta dalla mishi harara minti nawa ta baka ne?
Ni kamar baka cikin natsuwa ma wallahi. Baka daukar waya baka amsa gayyata idan ma an iske ka….. Ikon Allah mufeeda ki Bari zamuyi waya anjima Kinga Babu dadi……babu dadi ka barota kazo wurina?
Bai San lokacin da ya kyalkyace da dariya ba ……dai dai lokacin da Bilkisu ta dago Kai, kutumar bala’i….
Yana mamakin yanda yanmata ke tuhumar Shi akan Bilkisu.
Mikewa tayi ta hada litattafan sannan ta dauki ledar abincin kawai ta fito……
Ba karamin razana yayi ba don yasan kwanan zancen….. *Bilkisu*………. *Bilkisu*…. *Bilkisu*!!!……. Amma Ina! Ko waige….
Duka yaushe ya samu suka daidaita, mtseww.
Please zamuyi waya ya fada tare da Dan rugawa *Bilkisu*…….
    Sauri takeyi sosai, ya cimmata da kyar…Dan Allah kiyi hakuri.
KO kallonsa batayi ba.
Wallahi ban manta dake ba Ina cikin kwatanta mata naga kin fito……… Nace ka manta Dani ne? Ko kaji nace nayi fushi ne? Kaje ka gama da ita ni lokacin da kake free Zan dawo tunda nice nake nema a wurinka……kiyi hakuri Dan Allah.
Ta tsaya cak tare da kallonsa….. Banyi fushi ba, kamar yanda ba haushi naji ba, ai kana da damar ka ko?
Wannan bin da kakeyi mun Shi zai hasalani don haka ka koma ka kyaleni…….ya daga hannuwa sama, naji Amma kiban abincin Mana……wallahi bazaka ci Shi ba. Ta fada tare da wurga mishi kallon da yafi komai tsana sannan ta tafi tabar Shi tsaye.
  Wai me yasa bazai kyale yarinyar nan ba?
Duk Yan mata na shakkar sa me yasa ita bata tsoron yi mishi gadara?
Ko ya ayyana zaiyi fushi da ita Shima me yasa baya iyawa?
Yaja wani dogon tsoki……. Ya wuce a fusace.

      *******************
*KADUNA RIGASA*
Wannan ba shawara bace, kasan su mata shaidanin su babba ne, Basu da hankali ko kadan.
Idan nayi haka mun Zama daya dasu kenan.
Abinda nake gani ka dawo gobe da safe kawai Bari na shiga masallaci na kwanta.
Amma yarinyar nan akwai Yar iska….. Ya dafa kafadar idanun sa kamar garwashi kada ka damu, mu zauna da safen…… shikenan Zan taho dasu hajia……noooo kada ka Kira kowa please.
Dole ya hakura ya tafi ba don ya so hakan ba ….. Abin Babu dadi hakan yake ta nanatawa a cikin Rai domin yasan kawaici ne yakeyi mishi saboda kada abotar su tayi rauni.
Ya girgiza Kai……zata ci ubanta goben.
Ina Kai Yara school 7:30 gidan Zan yi ma tsinke.
Hakan kuwa akayi, 
Kamar kullum karfe bakwai Yara suka fito Yana hangosu ya fito masallacin saboda Babu Wanda ya gane a can ya kwana daga cikin masu aikin gidan sai Mai gadi.
Ya ce Ahmad je ka karbo mun mukullin motar mamar ka.
Da gudu ya juya, tana kitchen tana gyaggyara inda tayi aikin kayan break din yaran domin ( Amira tana da masifar tsafta Sam da yawa Bata jiran masu aiki musamman bangaren da ya shafi dahuwar abinci)…..Kai lafiya ko jakar ce ka manta?
Abba yace ki bashi makullin mota.
Ta kalleshi sosai Ina Abban?
Gashi can ya fito daga masallaci….gabanta ya Fadi. Kamar zata Kuma tambayar Shi sai ta fasa ta tafi daki don dauko mishi.
Ya kura ma kofar ido ya kalli agogon wayar sa har da kwata tayi Yana mamakin dadewar da Ahmad din yayi sai gashi ya fito da gudu.
Ya Dan saki ajiyar zuciya har Almustapha ya Dan kalleshi abinka ga yaro bai hasaso komai ba saboda Babu kwalwar tunanin.
Duk abin nan tana tsaye jikin taga tana kallon su, Yana fita da motar ko layin bai shanye ba ta fito da sauri don komawa bangarenta,  maimakon tabi ta hanyar baya kamar kullum sai ta fito ta kofar gaba, abinka ga babban gida kuwa tana mikewa zata Sha kwana Yana shigowa da mota.
Gabanta yayi mummunan faduwa ta tsorata ainun sim…sim …sim …zata wuce ya fito. Wurinki nazo daman.
Ta yi zuru zuru da ido alamar rashin gaskiya Yaya Ina kwana ta Dan rusuna, ya wuce gaba muje daga ciki…….
Mai aikinta har tazo tana ta goge goge, saboda tana da nata makullin.
Yana shiga yace ke fita ki jira a waje….. Tayi saurin ajiye mop kuwa.
  Tana bayan sa zugum tayi tsuru tsuru tsaye….waigowar nan da zaiyi kuwa sai kauuuuu ya wanka mata Mari ta gigice kafin ta saka hannu ya Kara wanka mata……sai kawai ta zukunne don girman Allah Yaya na tuba……ta fada cikin karaji tana kuka….
Dan ubanki kina tunanin kin wuce duka har Yanzu? Ke har Zaki rufe ma miji kofa Kuma nazo nayi magana kinji muryata saboda ki nuna bamu Baki tarbiyya ba shine Kika yi shiru. Ya daga hannu zai Kara Kai mata bugu yaji an rike hannun……..Kana da hankali zaka Dakar mun Mata?……. Ya fincike hannun cikin bacin Rai….Dan ubanta ta wuce a dake ta ne?
Ya janye Shi, malam ba haka ake sasanci ba….Ni kiranka nayi ka sasanta ni da matata ba ka rikita man ita ba…….. Sasanci? Kishin nata na hauka shine zaisa a sasanta ku? Sai dai in Mata rauni in karairayata Dan ubanta…kizo ki iske Shi da matar Shi da yaranshi ki nuna Baki kaunar su don Kina mahaukaciya har kiyi tunanin zakiyi daraja da kima?
Duk suka zauna lokaci guda…… Saurara malam.
Matsalar Ummi daya tsageranchi da wannan mugun kishin na kwatanta Mata Amira Bata da matsala……ko tana da matsala ba dole tayi hakuri ba tunda ta Aure Mata miji don ubanta…..
 Dan Allah ka daina hargitsa lamarin nan.
Ummi koma can ki zauna…..ya nuna Mata kujera…ba gardama ta tashi fuskar har tayi fushi.
    Wallahi tallahi ban auri Ummi don in mayar da ita zawara ba. Amma Ina Mai tabbatar maka da cewa muddin ta Kara kuskuren da tayi jiya na rantse da Allah sai na rabu da ita Koda zata kawo karshen alakar mu……saboda tun farko ita ce ta hada mu?
Noooo….
Then, what do you mean, wannan idiot din ta Isa ta rabamu ne? Daga alfarmar Dan ubanta?……Dan Allah ya Isa.
Ummi …..Ummi…ummi.
Ya Kira sunanta sau uku.
Ga Dan uwanki zan maki magana ta karshe daga yau.
Kina son Zama Dani?
Tayi shiruuuuuuuuu,
Ki bude Baki kiyi magana yau zanyi wa tubkar hanci.
Kin shirya Zama Dani?
Da kyar ta daga Kai alamar eh.
Good, to saurara.
Muddin kina son Zama dani sai kinbi wadannan dokokin wallahi tallahi inba haka ba Zan sawwake Miki Yanzu matukar kikaji sunyi Miki tsauri.
Idan kuwa Zaki iya to ki sani Koda wasa Kika kuskure Nan gaba daga gone har shekara dari Nan gaba kada ki taba tunanin ban iya rabuwa da mace don na haihu da ita ba wallahi ko duniyar Kika safke mun sai na sallameki.
Na farko Amira wacce ta zame Miki damuwa tun kafin ki shigo gidan Nan. Matukar kina son Zama Dani sai kin Mata biyayya da kyautatawa, na biyu maganar abinci ya Zama wajibi kiba kowa hakkin sa lokacin da kike da dama. Na karshe Yan aikin gidan nan ki sani ba bauta suka zo ba neman abinci suka zo yi to ya Zama wajibi a kyautata ma nemansa ta ko wace hanya. Cin fuska ,izza da gadara bazan Kara dauka ba.
Allah ya gani naso in biki ta ruwan sanyi to maganar gaskiya yau na kafa shaida da yayanki akan kadan daga cikin wautar da kikeyi gidan Nan. Maganar iyaye na Kuma ko na Amira kice ma Baki sansu ba wannan kanki kikayi mawa domin duk Wanda ya kashe uwarshi to Shima baza ‘a mishi kani ba…..
Wannan kenan shawara Kuma Yanzu ta rage daga wurin ki………….
           *************
*Federal University dutsinma*

Idanun sa jawur kamar garwashi ….dakin a cike Amma ana ganin yanayin sa kowa ya Fara zarewa one by one. Ko takalmi bai cire ba ya fada bisa katifa ruf da ciki.
Anas ma fita yayi sadeeq kadai ya rage.
Anwar……ya Kira sunan sa.
Bai amsa ba Amma ya dago Kai.
Lafiya dai ko?
Kamar jira yakeyi…… sadeeq bana tsoron yarinyar nan wannan Zan biye Mata fa.
Bilkisu?
Ya buga tsoki who else?
Me Kuma ya hada ku?
Simply useless girl din nan mufeeda tazo muna karatu she couldn’t even understand abinda nake undergoing a wurin yarinyar nan ta fito a fusace, nayi Kiran duniya tayi burus Dani na bita Ina Bata hakuri shine ta barni a wurin ta wuce abinta, Kuma tana fada mun Bata ji haushi ba idan bataji haushi ba zata ce in daina binta?
In don Bilkisu zuwa safe za’a ga tana ma magana……. A da ko? Yanzu fa ko itace tamun laifi sai nine Zan Bata hakuri I called her on ma way here for more than seven times she refused to pick up the call.
Nawaoooo….sadeeq ya fada Yana murmushi. 
To Wai meye ke kawo yawan fadan Nan naku? Ya kamata ku zauna ku gano Shi ……itace keda problem din buh I’ll soon leave her and rest.
Are you sure?
Mtsew abeg leave me alone. Ya juya abinsa.
Waje sadeeq ya fita Yana kyalkyatar dariya. Zai so yaga ranar da ko wane zai ajiye girman Kai ya bayyana zuciyar sa, sun tsaya sai ba juna wahala sukeyi.
Bilkisu kuwa harda Yan kwallanta. Ko da mommy ta kirata ma bayan isha’i maganar batayi tsayi ba karyar kanta ke Mata ciwo.
Washe gari sai 11 suke da lecture.
Ta riga Shi zuwa, tasan cewa ya tsani Zama gaba sai Sami gefe kusa da Ruth ta zauna.
Lokacin da ya shigo har an Fara lecture.
Idanunsa na kanta har aka gama, malamin na juyawa zai fita ya Mike don yau lecture daya garesu gobe ma free ce idan ta fita shida ita sai jibi.
Can karshe take jikin bango Yana zuwa yace masu Ruth duk su fito zai zauna yasha bakin glass Yana sanye da shirt Fara Mai ratsin light blue haka da blue jeans.
Ta Kara tsuke fuska ta Mike itama zata fita kawai ya hawo bisa table din ya tsallaka ya zauna. Dole ta koma ta zauna. Sadeeq na can baya Yana kallon drama.
Ina zakije bayan kin San don in zauna nace su tashi?
Ina da aikin yi ne.
Yayi murmushi na sani. Har Yanzu fushi akeyi dani?
Fushi ta kalleshi up and down ta watsar kallon da ya gwammace duka dashi kafin tace fushi akan meye? Kamun laifi ne?
A’a ya girgiza Kai.
To bani wuri in wuce ta mike tsaye, ya daga Kai me yasa kike son mun wulakanci gaban jama’a?
Kamar ta kurma ihu don takaici, ta dalla mishi idanu wulakanci? Simply don nace kabani wuri in wuce shine na maka wulakanci?
To jiya fa da…….. Anwar na tsani tariyo duk abinda ya wuce a rayuwata kullum Ina hangen abinda gaba zatayi. Ban wuri in wuce jiya Kuma Kai ta shafa bani ba.
Amma ai na Baki hakuri ko? 
Ikon Allah nace ban hakura bane? To idan kin hakura ki zauna mu Kara abinda muka Fara jiyan…..tayi murmushi Mai Kama da kuka Allah ya albarkaci abinda mukayi din ya wadatar wallahi bana so na yafe.
Ya kife Kai bisa table….shikai yasan yanda zuciyar sa ke mishi.
Kai nake jira.
Ya dago Kai har Yanzu taki yarda su hada ido, me kike so Yanzu in Miki?
Ka bani wuri in wuce. Ta fada fuska chunkushe.
    Anya yarinyar ba zafin kishi ke addabar ta ba? Me yasa bazata fito tace tana sonsa ba kamar yanda sauran Yan Mata keyi Masa?.
Zan Baki wuri ki wuce Amma sai kin mun alkawari Zaki dauki wayata anjima…..banyi ba Kuma bazanyi ba ka bani wuri in wuce Wai Ina dalili?.
Ya Mike tare da say hannu duka biyu aljihu Yana gaba tana bite kamar zata tureshi Yana fita sit din tayi hanyar waje da sauri ya bita da ido har ta yi nisa ta taga.
Sadeeq na can baya kansa bisa littafi kamar Mai karatun gaskiya. Ya ce su tafi library din.
Ita kuwa daki ta koma.
   Tana sallar azahar barci yayi awon gaba da ita, sai biyar ma ta wuce ta tashi. Ga wayarta silent missed calls kusan goma shaa biyu. Khausar biyu, mommy biyu, hudu sabuwar lamba sauran Anwar.
Sai da ta Dan watsa ruwa tayi sallah sannan ta bi Kiran, khausar abinci zata Mata tayi, mommy Kuma zata fada Mata gobe zasu shigo Murna tsalle.
Alamar shigowar sako ta gani tana budewa taga wata number.
“`i’m guilty I knew, please accept my apologies it will never happen again I promised“` 
  Hmmm, tace kafin ta ci gaba da magana a fili.
Bana iyawa Yan matanka nesa nesan zaifi gaskiya don haka ka gaji ka kyaleni.
Washe gari karfe biyu su daddy sunka iso. Cikin wata Hummer Jeep bullet proof. Duk inda motar ta gitta binta akeyi da kallo. A bakin hanya ta taro su tunda sukayi waya ita da khausar, su Aisha sunje test. Murna, tsalle, da ihu kawai takeyi.
Hankalin Yan compound din ya dawo kansu *lallai Bilkisu ba diyar kananan mutane bace* Nan da Nan kallo ya dawo gunsu musamman lokacin da sukaga irin kayan da ake shiga dasu ciki.
Har dakinta Shima daddy.
Ta rasa inda zata sa kanta tana makale jikin kafar mommy ana shagwaba. Kayan ciye ciye baje na gani na fada. Daman sunce ko ruwan zafi kada ta dafa.
   Kawaye aka Fara shigowa da makwabta ana gaisuwa abin ya birge kowa……
Daddy ya kalleta Ina *Anwar* ki kirashi mu gaisa da abokin fadan naki……mutanen dake cikin dakin duk aka Kama dariya.
Gabanta ya Fadi.
Wannan karon fa fadan na gaskene ……mommy tayi karaf, ai dole mu ga Anwar yau Kam maza kirashi a waya kice gamu munzo………..


Ayi hakuri da kadan. Wallahi nayi typing 7 dinnan kawai mistakenly na gogeshi Shi yasa na rasa ta inda Kuma Zan Fara .
Afuwan???????????????????????????????? zainab wowo ce????✍????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button