NOVELSUncategorized

DIYAM 40

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forty: The Masked Man

“Madam?” Na maimaita cikin kokonton abinda kunnena yaji min. Sai ya dauke idonsa daga cikin nawa ya wuce mu ya tafi gaban taron ya daga murya yace “Thank you, all of you. I really appreciate this surprise party and I am really surprised” ya Indanyi dariya, “but I am sorry I can not stay, I have something really
emergency that I need to do. You guys should go ahead and enjoy yourselves. Thank you ones again” sai na juya da sauri yayi hanyar waje, abd without even a second glance at me ya fice daga building din. Da sauri organizers din partyn suka bishi a baya, ciki har da Saghir, nima sai na samu kaina da binsu a baya, hoping to see him again, to talk to him even dan in tabbatar cewa da gaske shi dinne kuma da gaske bai gane ni ba. “Can it be? Ace Sadauki bai gane ni ba ni Diyam?”

Ina fita kofa yana tayar da mota, yaci taya ya bar gurin a guje ba tare da ko ya tsaya ya saurari ma’aikatan sa da suka biyo shi a baya ba. Nabi motar da kallo har ya fita daga gate, sai kuma na zame na durkusa a gaban wata flower bed na jingina kaina a jiki ba tare da ko damuwa da menene zai iya fitowa daga ciki ya cutar dani ba. I only wanted to wake up, wake up from this nightmare where Sadauki doesn’t know me.

Ina jin su Saghir suka wuce suka koma ciki suna ta maganganu babu wanda ya lura dani, bayan mintina kadan kuma sai aka fara watsewa kowa yana fitowa yana neman shiga motarsa. A lokacin ne kuma naji muryar Saghir ya na nemana “Diyam! Diyam!” Amma na gaza bude baki ballantana in amsa masa har yazo inda nake sannan cikin whisper yace “what the hell are you doing here?” Maimakon in bashi amsa sai hawaye ya fara kwarara daga idona kamar an bude pampo, ya fincike ni ya tayar dani tsaye yana grinning at mutanen da suke wucewa sannan ya kaini mota ya cusa ni ya rufe kofar muma muka fita.

Ba wanda yayi magana har muka je gida, yana packing ya zagayo ya bude inda nake ya fige ni zuwa cikin gida ya jefa ni a kan kujera yace “me kike tunanin zakiyi archiving ne by embarrassing me a cikin mutane? By trying to destroy my carrier? Oga na yana miki magana ki wani tsaya kina kallonsa kamar statue? Sannan kuma ki fito ki zauna a cikin flowers are you nuts?” Na dafe kaina da hannuna, ni ihun da yake min ji nake kamar zai tsaga min kaina gida biyu. Har yanzu kaina yaki budewa balle in yi tunani. Farkon abinda nake so in fahimta shine me Sadauki yake yi a gurin aikin su Saghir? Kuma har nani suna addressing dinsa as if shine manager dinsu daya dawo daga karatu suka shirya masa party. Can it really be? In kuma har ya kasance haka ne to how comes? Ni dai Sadaukin dana sani sanda muka rabu seven years ago bashi da komai, kuma shekaru biyu bayan rabuwar mu Saghir ya samu wannan aikin then how comes Sadauki yayi kudin da har zai bude companyn motoci a cikin shekara biyu? Bayan wannan kuma shin sun gane juna ni suke playing ko kuma suma kansu basu gane ba? Anya kuwa Saghir zai karbi aiki a gurin Sadauki in har yasan shine? Sai wani tunani yazo min, as we were growing up ni da Sadauki, bazan iya tuna ranar da Saghir yaje gidan mu ba, lokacin ma shi kusan kullum baya kasar. And Sadauki was never allowed to enter gidan Alhaji Babba tun yana dan karamin sa har sai sanda naje nake shigo dashi a boye and even then basu taba haduwa ba. So what I was sure of shine basu san faces din juna ba. 

But, me yasa Sadauki zai yi acting kamar bai sanni ba? He did looked surprised akan party din but he did not act surprised to see me there, meaning yasan dangantaka ta da Saghir. And then many things started to become clear to me, sunan subay’a, aikin Saghir. Tabbas Sadauki ya gane Saghir bayan yayi masa tambayoyi a gurin interview wannan shi yasa ya dauke shi aiki even with his pass certificate and lack of experience, kuma shi yasa har yanzu ba’a kori Saghir ba daga aiki duk da negligence dinsa. But why? Ina son insan me yasa Sadauki yayi haka? Is my Sadauki still behind the mask of Mr Abatcha?

Sai bayan na dawo daga tunani na nayi realizing har lokacin Saghir fada yake yi. Na tsaya ina kallon sa ina realizing cewa he had no idea mai ya faru a gurin nan. Shi kawai fada yake na wulakanta ogansa. Nayi gyaran murya nace “Allah ya baka hakuri. Ni ba’a saba cemin Madam bane ba shi yasa na kasa amsa masa. Amma kayi hakuri, nan gaba in ance min madam zan amsa” na mike zan hau sama yace “ina jakarki?” Sai lokacin na lura bata hannuna nace “ta fadi a gurin” nan kuma sai ya koma fadan yar da jaka “tunda bake kika siya da kudin ki ba ai dole ki yar” ni dai nayi wucewa ta sama na barshi a nan.

Ranar yadda naga rana haka naga dare. All I wanted to do is to see Sadauki again and ask him tons of questions da suke zuciyata.

Exactly a week after that. Muna palo ni da Subay’a ina kokawar yi mata kitso tana ta zillo tana kuka Saghir ya sauko daga sama. Ya saka hannu ya dauke ta daga cinyata ya suka hau kujera yana warware mata kitso dayan da da kyar na samu nayi mata shi. “Tunda bata so sai a rabu da ita, ke waye yake takura miki yanayi miki kitso in bakya so?” Ban ce komai ba danni yanzu bana cikin mood na musu da Saghir. Yace “wato idan Allah ya yi mutum shi mai sa’a ne a duniya to bashi da wani sauran stress kuma a duniya. Kinga a office dinmu tun daga dawowar oga yadda ake ta rububi ana shishshige masa kowa yana so ya kafa kansa, ni kuwa babu abinda ya dame ni dasu aikin gaba na kawai nake yi. Amma kinsan ina daki kawai yayi kirana a waya, wai dan Allah in an jima inje airport in dauko shi zai dawo daga Maiduguri, kinsan dan can ne ai, babarbare ne” na cigaba da harkokin gabana looking uninterested, Amma kirjina lugude kawai yake yi nace “hmmm, Allah ya taimaka” ya danyi shiru sai kuma yace “I have an idea, tunda kowa neman shiga yake a gurin oga why not me? Nima ai ina son promotion din. Idan na dauko shi daga airport nan gidan zan kawo shi, you prepare dinner for him tunda dama bashi da aure kuma bashi da gida a hotel yake zama, nasan zaiji dadi, in ya ci abinci anan sai in kaishi hotel din da take zama” na yi saurin juyo wa ina kallon sa, sai na samu kaina da girgiza kaina nace “no” no matter how much zuciyata take son ganin Sadauki nasan ba dai dai bane ba, shigowar sa cikin gidan aure na ba abu ne mai alfanu ba “Please ka zarce dashi inda zai sauka kar ka kawo shi nan” ya mike tsaye yana kwantar da Subay’a da tayi bacci a hannunsa yace “yes, nan zan kawo shi first. Zan fita in yo miki cefane and you cook something nice for him, abincin da kika san mutane irin sa zasu ci” kafin in sake retaliating ya fita. Na zauna a gurin na dafe kaina kirjina yana bugawa da karfi, wata zuciyar tana gaya min cewa in gaya wa Saghir waye ogan sa wata kuma tana hanani har sai na samu Sadauki munyi magana na fahimci inda yasa gaba tukunna. But yaushe zan same shi? Ni a matsayina na matar ma’aikacin sa? Ni a matsayina na wadda yayi addressing as Madam?

Ina nan zaune har Saghir ya dawo da ledoji niki niki ya shiga kitchen ya ajiye, ya fito yace “ga nama can da kayan miya da fruits, akwai wani abu da kike bukata kuma?” Na langwabar da kai “ni yanzu mai zan dafa masa?” Yace “think of something, nima ban sani ba”. Daga haka ya fita ya barni. 

Sai dana kai Subay’a islamiyya sannan na dawo na shiga kitchen, na saka ledojin a gaba ina kallo, me zan dafa? Kuma wai Sadauki zan dafa wa abinci a matsayin sa na ogan mijina. Lallai life is full of twists and turns. 

Sai na tuno da tuwon Ummah da take yi mana muna yara ni da Sadauki. Tuwon laushi miyar yauki sai ta dagargaza kaza a ciki ta cire kashin gaba daya. Sadauki yana so sosai dan har cewa yake yi ayi dan haka na nutsu na fara shirya masa. Na gyara fruit din nayi smoothie na saka a fridge. Zuwa magrib na gama na shirya komai a dining table sannan na fita na dauko Subay’a sai kuma na sake gyara gidan na saka turaren wuta naja subay’a muka hau sama. 

A sama nayi wanka nayi mata wanka itama muka yi sallah tare sannan ta kwanta ina yi mata kitson da taki tsayawa ayi dazu, a haka har tayi bacci sannan naji shigowar mota, gabana ya yanke ya fadi na kalli window amma wani barin na zuciyata yace “kul kika leka kallon haramun” sai na kwanta na dunkule a guri daya kamar mai zazzaɓi, naji an tsayar da motar an kuma bude an fito sai dai ba’a rufe ba, naji ina son in san me yasa ba’a rufe din ba. Na jawo pillow na dora a kaina na danne da hannayena amma the next second sai gani na nayi a bakin window a bayan labule ina leka waje.

Saghir na hango a tsaye a bakin mota yana magana dana cikin motar wanda shi bai fito ba, sun jima suna magana a haka, kamar na cikin baya son fito wa yayin da Saghir yake ta insisting akan sai ya fito. Sai kuma naga ya zuro kafafuwansa ya fito Saghir ya rufe masa kofar sai suka jero a tare suka doso cikin gida, yayinda fitilar gaban gidan ta haske min su.

Two men; one fair and the other one dark, fair one din shine mijina amma ni zuciyata dark one din take so; one taller than the other ni kuma tall one din nake so, one younger than the other ni kuma younger one din nake so, one frowning the other one smiling ni kuma me frowning din nake so, one employer the other one employee ni kuma employer din nake so. But the other one is my husband. That was how cruel my was.

 For a split second, Sadauki smiled, a smile that went straight to my heart, nayi saurin sakin labulen naja da baya kamar wadda ta taba wuta. Ji nayi kamar an debo wani tarin sonsa cikin trailer an zuba min a zuciyata sai naji tayi min nauyi dan haka na ruke kirjina na zauna akan gado ina ambaton sunan Allah da niyyar ya kawo min dauki a cikin lamari na tun kafin inyi tabewar da zata kaini ga halaka.

Waya ta ta fara ringing, da kyar nayi karfin halin dauka na kara a kunnena Saghir yace ina whisper “mun shigo. Ki zo ki kawo masa abinci” nace “dan Allah Saghir ka bashi kawai, bana jin dadi wallahi” nasan banyi rantsuwa akan karya ba saboda yadda nake jin jikina tabbas nasan akwai zazzaɓi a tare dani, yayi tsaki ya katse wayar. Na koma na kwanta na jawo Subay’a jikina na lullube mu, amma muna fikin kunnena sai yake kokarin zuko min maganganun da ake a palo, wishing to hear muryar Sadauki. 

Ina nan kwance kawai naji an hawo saman sai aka bude dakin, Saghir ya shigo fuskarsa kamar zaiyi kuka “Diyam? Me yasa ne wai ke kullum burinki kiga na tozarta a duniya, why?” Na tashi zaune ina girgiza kaina nace “me nayi kuma?” Yace “tuwo. For God’s sake tuwo Diyam zaki yi wa wannan mutumin da bana jin ya taba cin sa? Ko ni ba cin tuwo nake yi ba kuma kin sani” nace “cewa yayi ba zai ci ba?” Yace “to ni ina zan iya bashi? Kin san da yadda nayi convincing dinsa ya shigo kuwa kuma kawai sai inkai masa tuwo?” Na tashi na zura jihab dina na fita ya biyo ni a baya. 

Yana facing stairs, wannan yasa ina fara sauka na ganshi amma shi kansa yana kasa yana daddanna wayar hannunsa. Na dauke ido na daga fuskarta ina kallon gefe nace cikin wata muryar da naji kamar ba tawa ba “Barka da zuwa” ya dago kai, kallo daya sannan ya mayar da ganinsa kan wayarsa yace “Barka kadai Madam. Ya gida?” Still with the Madam, na fada a raina and my heart hurts. Ban amsa ba na mike naje dining na duba na tabbatar komai yana nan yadda ya kamata sannan na dawo na tsaya ina kallon Saghir da yake ta kokarin yi masa hira nace “ga abinci a table Ko nan za’a kawo muku?” Sadauki ya mike da sauri yace “thank you, zamu ci a can din. Ni am fine ma really, maigidan ki yace sai nazo naci, so I guess I will just have a taste and go” sai kuma ya tafi dining area da sauri Saghir ya bishi a baya, yana zuwa ya dauki plate zaiyi serving kansa sai plate din ya zame daga hannunsa ya fado ya tarwatse, and I noticed that his hand was shaking. Saghir ya kwalla min kira “zo da sauri ki gyara gurin nan” amma kafin in karasa Sadauki ya bar gurin da sauri yayi hanyar waje, Saghir ya kalleni da alamar tambaya na daga masa kafada, sai kuma ya bishi wajen. 

Na tsaya da tarin abinci a gaba na ina kallon kofa, so the mask has fallen, my Sadauki is still in there kawai duk pretence ne.

Ina tsaye Saghir ya dawo yace “get a basket ki zuva warmers din a ciki, he is taking it away” naje na dauko na hada masa komai har drink din na rufe, Saghir ya karba yana cewa “Allah yasa ma yaci, wannan mutumi kamar aljanu ne dashi”.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button