Labarai

Wallahi Aure Nakeso Na Gaji Da Kwana Ni Kaɗai Acikin Sanyin nan Cewar Wata Budurwa

Wallahi Aure Nake So, Na Gaji Da Kwana NiKadai”. Cewar Wata Budurwa Dake Neman Miji Ruwa-Ajallo Daga Zaharaddeen Gand.

Wata kyakkyawar budurwa ta koka, kan
yadda take matukar son aure amma babu
wanda ya fito, ta dauki takaitaccen bidiyo ta wallafa a shafinta tana kukan takaicin rashin mijin aure.

A wani bidiyo da jaridar Labarun Hausa taci karo da shi dake yawo a shafukan sadarwa, ya nuna yadda wata budurwa ke rusa kuka tana bayyana irin yadda take son aure.

Bidiyon mai tsawon dakika 15 ya nuno
budurwar mai suna dinaoumal a shafintiktok cikin hijabi tana kuka tana cewa:Wallahi aure nake so, na gaji da kwana nikadai”.

Wannan bidiyo ya dauki hankula da yawa
inda mutane da dama suka dinga yadawaa
shafukansu, a cikin mutanen da suka wallafa wannan bidiyo a shafikansu na sadarwa akwai, tsohon Sanatan jihar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani. Sai kuma wani mai suna Muhammad T. Shehu, wanda ya wallafa yayi rubutua kasa kamar haka:

jama’a dan Allah a samu wani ya auri wannan baiwar Allah mana.”.

Kamar yadda kowa ya sani yanzu mun shigo
wani zamani da rayuwa tayi wahala, haka
abubuwa na addini da al’ada na cigaba da
canja waa kowacce rana, hakan ya sanya
allumma da dama ke shiga cikin wani hali
idan suka bukaci wani abu da zai sanya su jin dadin rayuwa suka rasa.Samari da ‘yan mata da yawa a wannan zamani na bukatar aure, sai dai kuma wasudalilai da dama na hana su ganin sun cimma
burinsu.

Budurwa na neman aure a lokuta da dama,samari na samun matsalar aure sakamakonrashin aikin yi, rashin kudi da sauran su, yayin da su kuma mata a nasu bangaren sukan samu matsala sakamakon rashin hali, wasu kuma saboda ruwan ido da wani burina abin duniya.

Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Rohoto, Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button