Labaran Kannywood

Wani Ya Shawarci Maryam Yahaya ta nemi Malamin da Zai ringa Koya Mata turanci Saboda gaba

Wani Ya Shawarci Maryam Yahaya ta nemi Malamin da Zai ringa Koya Mata turanci Saboda gaba.

An bawa jaruma maryam yahaya shawara kan ta nemi malaminda zai ringa zuwa har gida yana koya mata turanci duk sati saboda ta gujewa irin Kalubalenda take Fuskanta na cin Mutunci da akeyi mata a Shafukan Sada Zumunta.

Kamar dai yadda wasu suka sani a kwanakin da suka gabata ne Akaita yawo da wata faifan vedio a Shafukan Sada Zumunta musamman ma TikTok inda wani yayiwa jarumar turanci Saita bashi amsa sabanin abinda yace ta fada.

Hakan yasa akaita yawo da faifan vedion inda yawancin mutane kowa keta tofa albarkacin bakinsa akan abinda ya faru.

Wasu masu Sharhi akan al’amuran Yau da Kullum sun bayyana cewa rashin iya turanci fa bawai wani abun kunya bane domin duk kasashen duniya da sukaci gaba toda yaren kasarsu suke amfani. sannan kuma turanci ba wani abu bane illa yare Kamar dai yadda harshen hausa yake.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button