Labarai

Wannan shine Ɗan Takarar da ya sami ƙuria 1 tal dukda yana da Iyalai 19 a India 

Wani ɗan asalin Jihar Gujarat a ƙasar Indiya mai suna Santosh Halpati, wanda ya tsaya takara a ƙauyensa a zaɓen Ƙananan Hukumomi da aka gudanar a watan jiya, tabbas ya bar abin tarihi.

Zaɓen ya zama abin magana a kafafen yaɗa labarai na duniya, saboda yadda ya samu ƙuri’a ɗaya kacal duk da cewa yana da aƙalla mutum 12 da suka cancanci kaɗa kuri’a a gidansa.

Santosh ya tsaya takarar neman shugabancin kauyensa (Sarpanch ) a

kauyen Chharwala na Gundumar Vapi,

kuma duk da bai sa ran samun nasara ba, amma bai yi tsammanin samun kuri’a ɗaya kacal ba.

Ɗan takarar mai matsakaicin shekaru, ya yi mamaki lokacin da ake ƙirga ƙuri’u a mazaɓarsa aka ce ƙuri’a ɗaya da ya jefa wa kansa kawai ya samu, inda ya shaida wa manema labarai cewa yana da ’yan uwa na ƙut-da-ƙut su 12, waɗanda suka cancanci ƙada kuri’a a gareni, don haka ko dai ba su damu da jefa ƙuri’a ba ko kuma sun zaɓi wani daban, kamar yadda jaridar Aminya ta rawaito.

Santosh ya bayyana cewa, “zaɓe yana zuwa ya tafi, amma na samu kuri’a daya kawai.. ko iyalina ba su zabe ni ba a wannan takarar.” inji shi.

Irin wannan lamari ya faru shekarun da suka gabata, lokacin da wani ɗan-takara mai zaman kansa daga Jihar Punjab a Indiya ya fashe da kuka, yayin da yake shaida wa wani ɗan-jarida cewa, kuri’u biyar kawai ya samu duk da cewa yana da ’yan uwa 9 da suka cancanci kaɗa masa kuri’a.

Saide, al’amarin Santosh ya ma fi zafi, domin bai samu kuri’a ɗaya ba daga wurin iyalansa sai tasa da ya jefa, kodayake ya ce, mutane da dama sun tabbatar masa da ƙuri’unsu.

Daga Zaharaddeen Gandu

 

 

 

 

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button