Labarai

Wata mata ta sake haifar ‘yaya biyar ‘yan tagwaye

Wasu mutane a jihar Katsina dake Arewa maso yammacin Najeriya sun fara kiran wata mata mai suna “Hajara Shu’aibu” da cewa, ita ce mace mafi haihuwa a kasar sabida yawan ‘yayan da ta haifa inda ta haifi ‘yan biyar a baya-bayan nan.

Matar ta haifi tagwaye sau biyu sannan ta haifi dai-dai sau tara sannan kuma a yanzu ta haifi ‘yan biyar, jumulla ‘yaya 18 kenan.

A tattaunawarta da BBC kan haihuwar da tayi ta ‘yan biyar a karshen nan tace, babu wani sauyi data ji ko tsammanin cewa zata haifi abin da ya fice da daya.

Tace, ko awon ciki bata taba zuwa ba haka tahaife su a gida da taimakon ungozoma, inda bayan ta sauka ne sai aka tafi dasu babbar asibitin Funtua domin a duba lafiyarta da jariran.

Zuwan su asibitin ne tace, sai aka kara mata jini aka ce mata ta samu ta huta tana mai karin bayani da cewa, dukkanin sauran haihuwar da tayi a baya bata taba zuwa asibiti ba a gida ta yi, kuma ba tare da an yi mata tiyata ba.

Hajara wadda tace, ita matar aure ce dake zaman gida kawai ba wani aiki ko sana’a da take yi, tace ba wani abinci na daban ko wani abu na daban da take yi dake sa ta haihuwa da yawa irin wannan ba.

Tace, ikon Allah ne kawai ba wani abu nake ci bana musamman dake sani haihuwa da yawa, matar tayi roko ga gwamnati da sauran jama’a dasu taimaka musu kan yadda zasu kula da ‘yayan.

Sai dai kuma mijin wannan mata wato mahaifin wadannan jarirai mai suna “Shu’aibu Umar” ya gaya wa BBC cewa, biyu daga cikin jariran sun rasu washe gari bayan haihuwarsu ranar Laraba.

Amma ragowar ukun suna nan da ransu, sai dai an kai su babbar asibitin tarayya ta Katsina tare da mahaifiyar domin kula dasu yadda ya kamata.

Sannan yace, a babbar asibitin na Funtua babu kwalba da za’a sa jariran sabida haka ne aka turasu zuwa cibiyar gwamnatin tarayyar ta Katsinainda yanzu suke samun kulawar da suke bukata.

Shu’aibu wanda manomi ne a kauyen Doma na jihar ta Katsina yace, ya dauki ‘yayan a matsayin wata baiwa da rahama daga Allah.

Umar Hussaini wanda shi ne mahaifin Hajara yace, ya aurar da ‘yar tasa tun shekara 21 data gabata, yace Shekarar Hajara 35 kuma tayi aure tun shekara 21 data gabata, a dangane da yawan haihuwarta sai in ce wata baiwa ce daga Allah.

Da BBC ta tambayi Hajara ko zata sake haihuwa nan gaba sai tace, lamarin ba’a hannunta yake ba Allah ne yake da komai, idan ya kaddara zan sake haihuwa zan haihu.

Rahoto daga???? BBC Hausa

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button