NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 17

NO. 17_*
  ………….Sai da yagama komansa hankali kwance sannan ya fito sanye cikin wando 3quarter da ta t-sheat baƙa, sai slipper baƙaƙe masu taushi a ƙafarsa. Ko kaɗan fuskarsa babu fara’a, hannayensa duka suna cikin aljihun wandon.

      Ƙamshin turarensa ne ya fargar da Bukky dake kwance a kujera kamar tasamu gidanta.
       Ta tashi zaune da hanzari tana faɗin “Babie!”.
      Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke idonsa batareda ya amsata ba, ya zauna saman kujera 1seat ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tareda ɗora dukan hannanyensa a hannun kujerar.
       Cikin muryarnan tasa mai cike da miskilancin gwarzantaka yace, “Miya kawoki gidana?”.
       Mamaki ƙarara a fuskar Bukky, ta miƙe tareda nufoshi, amma saiya ɗaga mata hannu alamar dakatarwa da maimaita maganarsa akausashe.
     “Bukky nace miya kawoki gidana?!”.
     Jatai ta tsaya zuciyarta na fara hasala da salon wulaƙancinsa, murya a dasashe tace, “Ajiwa miyasa kake sha’awar wulaƙantani a duk sanda nazo gidanka?”.
      Lumshe idanunsa yay ya buɗe akanta, wani kallon banza yay mata daga sama zuwa ƙasa ya taɓe baki da ɗage kafaɗa alamar oho miki, kafin ya ɗauki wayarsa ya hau dannawa hankali kwance.
       Dai-dai nan kuma Ummukulsoom ta fito dan duk azatonta baƙuwar tama tafi, amma saita ganta tsaye kamar mai shirin danbe, yayinda boss Amaan ke zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya yana danna waya .
        Juyawa Ummu tai da sauri da nufin komawa, amma sai Bukky ta katse hanzarinta ta hanyar nunata tana faɗin “Ita kuma wacece wannan?”.
        Banza yay mata, yaƙi ɗagowa balle yaga wacece ɗin, dukda dai zuciyarsa na basa yarinyar da aka kawo gidance amatsayin matarsa, danyaji ƙamshin munafikin turarentan nan dayake gab da hanata sakawa.
        “Ajiwa! magana fa nake maka”.
     Tamkar bazai ɗagoba sai kuma ya ɗago ɗin, kallo ɗaya yaymata itada  Ummukulsoom ya ɗauke kansa yamaida kan waya yana faɗin, “Kunne keji, kuma yajiki, sanin ita wacece kuma ba matsalarki bace”.
       “Tabbas ba matsalata bace ba, amma kai zata zama taka, Ajiwa kenan, ai bai kamata ka ɓoyemin ka kawo mace gidakaba, koka manta zancenka Na karshe kafin rabuwarmu?”.
         Wani banzan kallo yamata yana juya manyan idanunsa dake kunshe da tsanarta, yaja wani siririn tsaki, kansa ya maida jikin kujera ya kwantar yana lumshe idanunsa, dan zuciyarsa tafara zuwa maƙoshi.
      Haushi yakai Bukky Bango da dizgatan dayake agaban Ummu da A’i data hango a makale, dukda kuwa tanada tabbacin bajin turancin sukeba, cikin shirmensu Na yarabawa da tsantsar gogewa a bala’i ta tafara girgiza jikinta, “Ajiwa kasanifa zan iya tada barrack dinnan tsaf da jama’ar dake cikinta inhar abinda aka sanarmin akanka ya tabbata, Dan alkawarine inhar bazaka aureniba to Baka Isa zama da wata maceba kuwa ko ita wacece a matsayin mata” ta kalli Ummu dake tsaye har yanzu, “Ke kiramin ƴar iskar yayarki dan yau koni ko ita a gidanan”. 
      Bakomai Ummu take fahimta a zancen nasuba, saboda duk wannan bala’in da turanci akeyinsa, sai dai kiran yayarta datace tayi yabata mamaki, wato ita batakai akirata maceba ashe, karon farko arayuwarta dataji wani fushi da sha’awar tsiwar rashin ragi, dan haka ta zubama Bukky harara ta ɗauke kanta”.
      “Heeey” tafaɗa cikin dirga tsalle tana nuna Ummukulsoom da dafe baki, “Ajiwa ni wannan yarinyar take harara danna aiketa?”….
       Kansa daya fara masa nauyi saboda hayaniyata ya dafe, kafin ya dago a zafafe ya nunata, “Wlhy Bukky idan kika bari naje bango akanki zan ragargaza ƙasusuwanki ne a gidannan, halan kin mance dawa kike magana ko? wane Warning nai miki akan zuwa gidana last time?”.
         Tsalle takuma dirgawa ta dire tana nuna Ummu, “Warning ɗinka na banza, da kace karna sake zuwa maka gida baka bukatar mace, su kuma waɗan nanfa? wai inama banzar matar takane? Tafito inba tsoroba”. ‘taƙare maganar a gadarance, tana hararar Ummu tamkar wata kashi’. 
       Idanunsa ya lumshe ya bude a kanta, yayinda tuni suka canja launinsu Na farare tas zuwa Dan jan hasala, Sai dai bakinsa yagaza cemata Uffan…
       Itama Ummu tana buƙatar taji amsar dazai bata akan matarsa da taketa ambata. 
        A’i ma dake a labe har yanzun ko gajiya bataiba, burinta taji amsar dazai bama Bukky, taga kuma zai nuna Ummu amatsayin matar tasane?, dan bakaramin dadi tajiba da jarabar Bukky ta dawo kan Ummu, babban fatanta Bukky ta naɗama Ummu dukama danta kula akwai alaƙa mai ƙarfi tsakaninta da mai gidan, dukda shi sai basarwa yakeyi.
       
        Sosai Bukky ta hango wata wutar bala’i daga idanunsa, tasan wanene Ajiwa akan zuciya da tsantsar rashin daukar raini, saidai kuma sam baya son hukunci cikin fushi, da wannan damar take amfani a yanzu take zuba iskancinta a gidan,  amma hakan bazaisa ta tafiba sai taga wacece matar tasa? dan kuwa tana zamanta a Abuja wajen sister ɗinta aka kirata ana sanar mata yayi aure, shiyyasa tazo lagos babu shiri, saidai kuma ita bataga matarba……..
      Tunaninta ya katse ganin ya tashi zai koma dakisa, hartana kokarin taune harshe wajen azamar dakatar dashi,
        “Waini ko kana nufinma wannan abarce matar auren taka?”. Tai maganar da nuna Ummu.
        Cak ya tsaya, sai dai bai juyoba, bayason hasala kansa da yawane gudun karya karya yarinyarnan, amma tai wasa daga gidannan saidai a wuce da ita asibiti.
     Yunkurawa yay zai cigaba da tafiya tasha gabansa cikin tsantsar cika bakinsu Na yarabawa, “Ajiwa maganar nake, nace wacece matarka?”.
         Ɗan yatsansa yasa ya shafi girarsa da lumshe idanunsa ya bude a manta, “Bukky inaga kin manta wanene Ajiwa ko? Ina ɗaga miki kafane bisa wani dalilina………”
       Saurin katseshi tayi, “Bana bukatar ɗaga kafarka Ajiwa, inkaga nabar gidannan sai ka sanarmin wace banzar yarinyace wanan ɗin?”.
          “Banza? Matar tawa ta aure kike kira banza?”.
         “heeeeey!! Matarka!!? A hakan!?, Wannan jinjirarce kake kira matarka a gabana Ajiwa? Lallai yau na sake tabbatar da halin hausawa, dama anfada min naki ji”.
       “Ko kina bukatar tabbatarwa ne Yoruba girl?”. 
     Wata banzar dariya ta tuntsure da ita tana kamo hannun Ummu zuwa gabansa,  ta fincike rigar Seawater din jikinta tana fadin, “kalleni da kyau banga abinda banfi wannan jaririyar yarinyarba da har bakinka ke iya kiranta matarka a gabana”.
          Raɓasu yay zai shige ɗaki batareda ya kalli ko ɗaya a cikinsuba “Kin makaro, dan abun ba’a jiki bane wawuya kawai”. Yay maganar tamkar bashine yayba.
      Hankaɗa Ummu tayi, tai baya kamar zata faɗi amma saita faɗo jikinsa.
     Tasss!! sukaji Saukar ƙarar mari a fuskar Bukky batareda kowa yaga ya akai yayishiba.
      Tuni gani dajin Bukky ya tsaya, yayinda falon yay tsitt saboda firgicin da suka shiga har A’i.
     Babu shiri Ummu da jikinta yahau mazari takuma shigewa jikinsa tare da ƙanƙamesa tamkar ita aka mara.
     Wutar kan Bukky data ɗauke na wucin gadi bata gama dawowa aikiba Amaan ya finciko Ummu datai shirin barin jikinsa zata gudu ya maidota ya matseta a kirjinsa tareda Dora bakinsa akan nata batareda tunanin komaiba…..
      “Eeeeeeehyyyyyy Me!!! Ajiwa!!!” Bukky tafaɗa cikin kwala ihu tareda buga wani uban tsalle ta zube ƙasa irin zaman ƴan bori.
    Daga canma A’i hannu ta aza bisa kai da fadin “Ni jikar Haƙilu, kajimin tantirin yaro zai kashemin sauran ganina”.
    Ihunsune ya fiddo Desmond daga kicin a guje, ya waro ido shima yana komawa da sauri ya labe bayan kofa yana wani mazari da jiki irinna iya shege ganin Boss da kansa yana cika aiki.
        Bukky dai saijuye-juye take a ƙasan tiles tana ɗora hannu aka da yarfarwa, ga hawaye na kwarara da majina a fuska, yayinda idonta yakasa daina kallon Yaa Amaan dake kissing ɗin Ummu a salon daya fara canjawa daga bata haushi zuwa wani yanayin daban, tun tanayi da yarabanci da turanci harta koma Igbo, catake Chiiii!!!, Chineke God woooooh!!!…..
      Oga Amaan dake shagulgula ai ko motsi baiyiba, tuni ma shi yabar duniyar dasu Bukky suke, ya lula sabuwar duniya dabai taba lekawaba a rayuwarsa sai a mafarki, Ummu kam da jikinta ke bari cikin tsantsar rudanin abinda batai zatoba, baikuma taba faruwa a kantaba sai hawaye takeyi, tsoronsa ya hanata yunkurin yin koda mitsi na nufin kwatar kai……
         Bukky ganinfa zata halaka akan bugun zuciya saitay Kansu ta fara jan Ummu daga jikinsa….
       Sai a lokacin Amaan ya dawo hayyacinsa,  hannu ɗaya yasa ya hankaɗa Bukky baya, kafin ya janye Ummukulsoom daga jikinsa itama yaykan Bukky yana fincike belt ɗin wandonsa, idonsa yay jajur duk farinnan ya bace, gashi sun wani zama kanana saboda tsantsar fusata.
     Ba Bukky da yake dukaba hatta da Ummu kuka take, A’i kanta jikinta yafara mazari…
     Desmond ma dayasan halinsa baƙaramin ruɗani ya shigaba, dan bai taɓa tunanin haukar bukky ɗin zai hasala boss irin hakaba yau.
         Dai-dai nan Attahir yashigo falon hannunsa dauke da briefcase ya kawoma Amaan daya manta a wajensa, kuma takardune masu amfani aciki, yasan zai iya nemesu a yanzuma saboda akansu aka turasu Abuja.
        Ihun dayake jiyowa tunkan ya shigo ya tada masa hankali, badai ƴar mutane Ajiwa kema wani abuba, har tuntuɓe yake wajen shigowa falon, turus ya tsaya ganin Bukky ce, sakin briefcase din yayi yay azamar shan gaban Amaan tareda ƙoƙarin riƙe belt ɗin hannunsa.
       Hankaɗe Attahir yay cikin daka tsawa yace, “kabarni na koyama wannan dabbar yarinyar hankali, yau saita faɗamin idan niɗin sa’antane dan ubanta”.
          Tsantsar fitina kawai Attahir ya karanto a idon Amaan, daƙyar ya riƙe belt ɗin daga hannunsa yana faɗin, “A’a Ajiwa Please, dan ALLAH kayi haƙuri kabarta haka, idan ita batada hankali kai kana dashi ai”.
         Amaan ya zubama Bukky harara da sakin belt ɗin da Attahir ya rike, ya nunata da yatsa cikin kakkausar murya da fushi yace, “yanzu kin kuma tabbatar dani din jinin hausawan ne? Kinkuma tabbatar da cewa itadin tafiki komai ko? Wawuya kawai, minti 3 kacal nabaki kibarmin gidana kafin naimiki abinda sai an kwasheki a Ambulance wlhy”. ‘yay maganar dakuma yin kanta tamkar zai sake duka, amma sai Attahir ya taresa da azama.
      Ƙwafa yay kawai ya fice daga falon.
      
      Kuka Bukky take tana faɗin saita halaka Ummu wlhy, yau saita ƙona Barrack ɗin gaba ɗaya sannan ta kashe kanta dashi kansa kowama ya rasa.
     Yanda take kuka haka Ummu ke kukan dabatasan daliliba, dan batajin abinda Bukky ke faɗa saboda da yarabanci takeyi.
      Da ƙyar Attahir ya fidda Bukky daga gidan, tanata rantsuwar saita halaka Ummu ayau tunda ta rabata da Amaan.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

*_KD_*

         Da sauri Suhailat ta fisge wayar hannunsa tana fadin Maci amana kai da wa?”.
         A matukar firgice Baseer dake rigin-gine ya juyo tareda wantsalowa daga gadon, muryarsa har zuga take wajen fadin “Banason shashanci Suhailat, Lukman n……..”.
         Tuni takai wayar kunnenta, batareda ta saurareshiba, “Ai sainaji wace jakace kake waya?. Hello! Wace ƴar iskace ke mai waya da mijina”.
     Jin ba’a amsataba ne yasata saurin Ciro wayar daga kunnenta ta kalla, Ashe tama katse kiran wajen hanzarin amsa, sai dai kuma ganin ansa Lukman Dilau ne yasata sauke numfashi da maida kallonta ga Baseer daya hangame baki alamar ya sadakar tashi ta Kare.
      “Love sorry please, wlhy nazata da mace kake wayane”.
    Wata irin ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke jin ALLAH ya rufa masa asiri a karo Na biyu, yay azamar canja launin fuskarsa zuwa fishi, “Wlhy Love ban taba zaton waɗannan halayyar daga garekiba? Dama yardar da kikaimin kafin aure ta karyace?…….”
       Da sauri ta saka hannu ta rude masa baki tana faɗin, “Nacefa kayi hakuri Dan ALLAH”.
        Tureta yay yatashi irin a fusace ɗinnan yafito daga dakin, yayinda itakuma tabiyoshi da gudu tana kwala masa kira.
      Duk yanda taso ya saurareta yaƙi, saida ya garata son ransa sannan ya saurareta
      “Suhailat tsakanina da ALLAH bazan ɓoye mikiba nagaji, miyasa kika ɓoyemin halayenki ne kafin aurenmu? Wace irin rayuwar aure mukene tamkar kece mata nice miji?…….”
        “Laifinkane Baseer”.
 “Laifina kuma? Miyasa yazama laifina Suhailat?”.
        “Katashi kanema aiki, duk namijin dazai zauna gida mace ke masa komai duk soyayyar dake tsakaninsu dolene darajarsa ta zube, badan naci zarafinka na faɗaba, shawara na baka, saboda a yau anjefeni da gori akanka wanda ya sosa zuciyata, bakomaine ya jawo hakanba kuma sai soyayyarka dake raina, a kullum dangina kallo suke tsakanina dakai *Wutsiyar raƙumi tai nesa da ƙasa*, soyayyar danake maka nikuma ta hana idona ganin hakan, duk abinda kaga ina maka inayinsane dankasan ciwon kanka, nagama maka babban yaƙi tunda har muka mallaki juna matsayin miji da mata”.
      Baseer dake tunani da amsar maganarta hundred percent ya jinjina kansa, “Lallai gaskiya kika faɗa Suhailat, kuma na gamsu da jawabinki wlhy, nakuma miki alƙawarin kawo canji nan bada daɗewa ba”.
    Farin cikine ya kamata, dan tana sonsane tsakaninta ga ALLAH saɓanin shi daya saka taura biyu a bakinsa.
  
     Tun daga wannan zama sai rayuwar gidansu Baseer tafara canjawa, dan a washe garin da hakan tafaru ya shirya yaje ɗilau.
       Iyayensa sunyi mamakin ganinsa, amma sai babu wanda ya nuna hakan, suka shiga tambayarsa iyali.
        Ko kaɗan rashin hankalinsa bai barsa fahimtar iyayensa fushi suke dashiba, baimayi wani zaman minti talatin a gidanba yafice zuwa ƙauyen da malaminsa yake anan kusa da garinsu.
     Har yamma lis bai baro garinba, dan duk w
[1/28, 1:18 PM] ????Noorinnissa????: ani ƙula-ƙula saida ya tabbatar anyi akan Suhailat da mahaifinta dama duk ƴan uwanta sannan yataho.
    Dole a ɗilau ya kwana, washegari tunda farar safiya yafar garin tamkar korarre.

★★★★

      Ya iske Suhailat bata gida, dan ita babu tsarin tambayar fita agareta, hakan sai ya bashi damar yin ƴan binne-binnan sa da barbaɗe-barbaɗe.
       Ance tsafi gaskiyar maishi, to lallai Baseer ya gazgata hakan, dan kuwa yasamu yanda yakeso akan Suhailat da ahalinta, zuwa yanzu kam shike juya gidansa da ƙarfin iko na mazajen ƙwarai, yayinda tuni mahaifinta yabasa babban matsayi a kamfaninsa wanda kowa yay mamakin hakan, amma saninsa matsayin surukinsane mijin tilon ƴarsa sai babu wanda ya iya tankawa.
      Lallai duniya ta samu ga Baseer, yakuma cika da ƙara ƙyau, sai mulki yake zubama Suhailat, ga laulayin ciki data fara batareda ta shirya hakanba. Sai dai kuma koda wasa batai yunƙurin zubdawa ba, saboda tana son babynta.
     Haka tacigaba da karatunta ga laulayi, Baseer kam ya manta dawani cigaba da karatu, aganinsa duk abinda zaiyi karatun a kansa yariga ya samu, kasancewarsa mai kaifin basira saigashi yagama fahimtar abubuwa mafiya yawa na kamfanin daddyn Suhailat.
      Yakan zagaya ɗilau ya gaishesu lokaci-lokaci…………✍????


Kuyi haƙuri babu editing dai, banda lafiyane????????????‍♀

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button