NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 16

*_NO. 16_*

……….Matan Barrack ɗin sunata shigowa ganin Ummukulsoom amarya, Hausawa da ƙabila, waɗanda basajin hausa iyakarta dasu gaisuwa, saikuma taita murmushi.

       Da yawansu sukan ƙunshi gulmar mamaki a ransu, basu taɓa zaton ganin matar Ajiwa yarinya irin hakaba, sun zata zasu gata wata babba irin sa’arsa ɗinnan.
       Ummu dai bama tadan sunaiba, damuwar gida da tabon da Baseer ya barmata arai sune maƙale a ranta, duk da dai tana ƙoƙarin cire Baseer ɗin da ƙarfin tsiya.

         Yau ma dai bayan ta tashi barci ta kimtsa ɗakinta da jikinta, fes ta fito cikin doguwar riga ta shadda ruwan gwaiduwar ƙwai, kayan sun mata ƙyau dukda babu wata kwalliya atare da ita, daga fauda sai lipsgloss data saka, sai ƙamshinta mai daɗi dake tashi a jikinta.
     A falo ta iske A’i na faman Morping, suka gaisa cikin girmama juna tamkar gaske, Ummu dai batada matsala da A’i, saima yabon halayenta da takeyi, girmamata kuma takeyi sosai kasancewar a haifema zata iya haihuwar kamarta.
     Bata zaunaba ta wuce dani danta karya. A’i tabita da ido tana wani taɓe baki, itafa harma tafara tsarawa kanta ƴarta zata kawo gidan itama a dama da ita, idan da rabo sai aci wannan daular duniyar da ita tazama matar soja. dan tun randa tazo gidan tai tozali da Amaan taji a ranta sun dace da ƴarta, dan Aina’un tata ƙyaƙyƙyawace san kowa ƙin wanda bai samuba.
      Ummukulsoom dai batasan hidimar da A’i keyiba ma ita, anutse tai breakfast ɗinta ta taso tadawo falon da A’i kesa turaren wuta. Kasancewar babu nepa saita kwanta cikin kujera tana tunanin rayuwa da sauyin da take zuwa dashi akowacce rana.
        Cike da salon iya bariki A’i tazo ta zauna a falon ƙasan carpet, “Uwar ɗakina barci ake?”.
     Ɗago ido Ummu tai ta kalleta tana murmushi, “A’a baba, idona biyu wlhy, natafi tunanin duniyane kawai”.
      A’i tai ƴar dariya da gyara zamanta, “hakanma yanada ƙyau Uwar ɗakina, amma nikan idan ban shiga hurumin daba nawaba da munyi wata magana”.
     Zaune Ummu ta tashi sosai, cike da girmamawa tace, “Baba ke uwace a gareni, duk abinda kikaga yadace kimin magana na gyara ko nayi karkiji komai kimin”.
     “Gaskiyane Uwar ɗakina, ALLAH dai yay miki albarka. Dama akan mijinki ne wlhy, nakula kamar babu wata shaƙuwa a tsakaninku, sai kace ba auren soyayya kukaiba?”.
       Murmushin takaici Ummu tayi idonta akan A’i, “Humm Baba kenan, kusan hakane gaskiya, dan saida aka kawonima mukasan juna”.
      “Irin auren mutan da kenan, muma ai duk shi akai mana kuwa uwar ɗakina, irin wannan auren ai anbar yinsa yanzu saboda zamani ya canja, amma karki damu, duk shawarar data dace zan baki yanda zaki kama mijinki kuwa yamafi waɗanda sukai auren soyayyar”.
      Ƙasa Ummu tayi da kanta saboda kunyar A’i.
     “Barjin kunyata Uwar ɗakina, sosai zan karantar dake indai nice, sai daifa na lura waccan uwar mijin taki ba mutuniyar kirki bace ba”.
      Da sauri Ummu ta ɗago ta kalleta, kafin ta fara waige-waige a falon cike da tsoron kar wani yaji maganar da A’i tayi, ganin babu kowa yasata maida kallonta gareta, murya ƙasa-ƙasa tace, “Baba wannan maganar mubarta dan ALLAH, Momcy uwace a gareni kuma ni bata taɓa min wani abu mara ƙyauba”. 
       Ji A’i tai kamar ta make Ummukulsoom, dan recoding take a wayarta, sotai Ummu ta saki baki suyi gulmar Hajiya Jamila, amma takula wanna yarinyar shegen wayone da ita, sai tayi da gaske zata ɗorata a network, a fili kuwa saita washe jajayen haƙoranta tana muskuta zamanta kusada Ummu, “Uwar ɗakina ai maganar gaskiya dolene ayita, amma tunda baƙya buƙata anbar zancen, yanzu maganar miskilin mijinnan naki akwai hanyar dazan miki a bidashi ta ƙasa kisameshi ram a hannu”.
      Wani irin tsargawa cikin Ummukulsoom yayi na tsoro, dan kuwa A’i na rufe baki Yaa Amaan na shigowa cikin falon.
       Duk sai sukai tsiru-tsiru alamar rashin gaskiya.
     Shikam ma bai kula da suba, dan waya ya shigo yanayi, hakanne yasaka Ummukulsoom sauke ajiyar zuciya ta miƙe zuciyarta na addu’ar ALLAH yasa baiji zancen nasuba.
     Taɗan saci kallonsa tana gyara tsayuwa, sanye yake da wandon Uniform sai farar t-sheat data kamasa sosai, hakanne yasaka ƙirar dirarren jikinsa bayyana fili.
      Kallon Ummu yay sau ɗaya shima ya janye idonsa yana cigaba da wayar da yake cikin harshen turanci.
      A’i kuwa tuni ta miƙe tabar falon jikinta na ɓari kamar gaske, a ƙasan ranta kuwa taso ma Amaan ɗin yajisu, danya fara zargin Ummukulsoom.
      Ganin A’i tabar falon saiya zauna yana cigaba da wayar.
     Desmond kuku ne yafito hannunsa ɗauke da ƙaramin tire ya ɗoro ruwa da glasscup.
     A table ɗin gefen kujerar da yake zaune ya ɗora tiren, yana ƙoƙarin ɗaukar ruwan ya buɗe Ummukulsoom tai masa alamar daya barshi, dan ta tuno nasihar kakarta Gwaggo hinde da tace *_Umma karki zama cikin mata masu yima miji rowar ruwa, a duk sanda mijinki yashigo gida kifara tarbarsa da sannu sai ruwa ya biyo baya, hakan zaisa aduk lokacin dayaji ƙishi koda yana a wajene saiya tunoki, wannan ma mallakace mai daraja da mace zataima mijinta babu boka babu malam, balleke da akai muku auren haɗi_*.
       Babu musu Desmond ya miƙa mata ruwan cikin rissinawa irin ta girmamawa, dai-dai lokacin da Amaan ya ajiye wayar yana kuma ɓata fuska.
     Gaisheshi desmond yayi, kafin yabar wajen da hanzari gudunma Boss laifi.
        Ummukulsoom kam ida buɗe ruwan tayi ta tsiyaya a cup ɗin, har ƙasa ta durƙusa ta bashi tana faɗin “Sannu da zuwa, ya hanya?”.
      Manyan idanunsa Farare tas ya ɗago daga kallon wayar ya sauke a kanta, kafin yaɗan lumshesu ya kuma buɗewa akanta. Batare daya amsaba ya ɗaga mata kansa kawai da miƙa hannu zai karɓi ruwan data miƙo masa.
      Tattausan hannusa ya ɗora akan nata batareda yay niyyar hakanba, da sauri Ummu ta ɗago idanunta ta kallesa,  shima dai-dai ya ɗago nasan akanta.
     Kallon ido cikin ido sukaima juna, ya janye nasa idon cike da basarwa tamkar ba ai komaiba, dukda kuwa har yanzun hannun nasa nakan nata.
     Ita ta fara yunƙurin janyewa a kasalance, kafin shima ya janye yana ƙara haɗe fuska sosai, yakai ruwan bakinsa ya fara sha sukaji ana ƙwanƙwasa ƙofa.
      Ita kaɗai ta waiga ta kalli ƙofar, shiko ko motsi baiyiba, saima kofin ruwan daya ajiye ya miƙe zai nufi ɗakinsa.
         A’i dake laɓe tana kallonsu ce ta fito har tana tuntuɓe tanufi ƙofar ta buɗe, ƙyaƙyƙyawar mace fara tas ce a tsaye.
     A yatsine ta kalli A’i kafin tai mata nuni da hannu alamar ta matsa mata a hanya.
    Matsawa A’i tai numfashinta na fita da go slow, “wannan kuma wacece haka?”. Tai tambayar a zuciyarta.
      Duk wannan abun dake faruwa a idon Ummukulsoom ne dake tsaye itama a inda Yaa Amaan ya barta.
     “Hi babie”. ‘Budurwar ta faɗa tana ɗagama Yaa Amaan dake ƙokarin ida shigewa ɗakinsa hannu’.
      Sai dai harya shige abinsama.
    Ummukulsoom dai da A’i na tsaye suna kallon ikon ALLAH, dan ita shigar dake jikin matarma take ƙarema kallo.
    Sanye take da dogon wando jeans da jar t-sheat, ta cusa rigar a cikin wandon, sai siririn belt ɗin da aka tsuke wandon dashi kalar jaa, sai sweater wadda da alama tasakane dan gayu ba sanyi ba, gashin da Ummu ke ƙyautata zaton na dokine ta ɗauresa a tsakkiya yana reto ta yana gyale siriri…….
      Maganarta ta kuma katse Ummukulsoom daga kallon head to toe ɗin da take mata.
       Desmond take ƙwalama kira alamar dai ita ƴar gidace.
     Cikin hanzari desmond ya fito yana amsawa da “Ma”. Amma sai yay turus ganin mai kiran nasa, a wani yanayi na firgici yake baza idanu  a falon da leƙe-leƙe.
       Ranta a ɓace take magana cikin harshen turanci da nuna Ummu, “Waɗannan fa?”.
      Dukda Ummu batajin turancin sosai taji wannan, dan haka tai shiru taji amsar dazai bata.
     Jikin desmond na ɗan rawa yace, “yi haƙuri Ma, banida hurumin baki wannan amsar, sai dai Boss”.
       Harara ta zuba masa tana jan ƙwafa, kafin tace, “Jeka kawomin abinsha kaje ka sanar masa zuwana”.
    “Ok Ma”. ‘Ya faɗa cikin risinawa’.
    Ba komai Ummu ta fahimta ba a zancen nasu, bare kuma A’i da ba’asan komai ba, amma hakan yamata daɗi, addu’a ma take a ranta ALLAH yasa karuwar mai gidance, sai dai koda hakan ta kasance sai ƴarta ta shigo gidannan, dan zuwa yanzu kam ta fahimci ALLAH ya kawota gidanne danta sama ma ƴarta matsuguni badan taima Hajiya Jamila leƙen asiriba.
        Gaba ɗaya itako Ummukulsoom ranta a dagule yake, tasan ba kishi baneba, abune mai kama da tsoro ke shigarta, dan itadai ba sonsa takeba balle taji kishinsa, ko zataji zafi sai dai taji akan darajar igiyar aure dake a tsakaninsu, dakuma takaicinsa na ɗan musulmai mai aikata zina inhar hakanne tsakaninsa da matar, dankan wannan ai sai dai ta kirata mata, tunda ko a ido kasan zasuyi sa’anni da Yaa Amaan ɗin…….
     Dawowar desmond ce takuma katse tunaninta.
     Matarkam dako kallon su Ummu batayi ta amshi lemon da Desmond ya bata tana cigaba da danna faskekiyar wayarta.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button