NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 18

_NO. 18_*


……….Bayan Barin Bukky gidan Attahir yashiga neman inda Amaan yake, dan yasan yana cikin barrack ɗin babu inda yaje.

       Saida yaɗansha wahala kafin ya samoshi can wani waje inda babu kowa zaune a saman farar kujera idonu a lumshe ya ɗora ƙafafunsa a tebir ɗin gaban kujerar yana kaɗasu alamar har yanzu a sama yake can ƙololuwa, har Attahir ya iso wajen bai motsaba, dukda kuwa yaji motsinsa, kuma yanada tabbacin shine saboda wajen bama kowa ke zuwansa ba sai irinsu, shi kansa Attahir ɗin sanin idan ransa na a ɓace yafison waje mara hayaniya yas yay tunanin zuwa wajen dubashi.
      Tsawon mintuna uku yana tsaye akansa amma baida alamar nuna yasan da zuwan nasa.
    Attahir yaɗan girgiza kansa yana guntun murmushi, Ajiwa mai abin mamaki, ubangiji mai hikimane daya halicci bayinsa iri-iri mabanbanta halayya, da a labari akace masa akwai masu irin kalar halin Ajiwa saiya ƙaryata, saboda baitaɓa ganin mutum miskili mai zuciya irinsa ba, ko mahaifinsa da ake ganin taurinsa Ajiwa ya takashi ya shanye…….
      “Malam ka tashimin aka”. 
       Murmushi Attahir yay yanajan kujera shima ya zauna, ”Oh dama kasan da zuwan nawa amma ka shareni?”.
     Banza Amaan yay masa yaƙi bashi amsa. Sai dai hakan bai damu Attahir ba, saima numfashi daya sauke yana kuma kallonsa sosai, “Ajiwa miyasa ka daki Bukky? Bayan na sanka da tsanar wannan halayyar ta dukan mace?”.
      Shiru yay tamkar bazai tankaba yanzuma, harma Attahir ɗin ya fidda tsammani sai yaga ya buɗe idonsa dasukai jazur akansa.
    Kallo ɗaya yayma Attahir ɗin ya maidasu ya rufe, sai da yaja wasu seconds kafin yace, “Miyasa baka tambayeta ba ita?”.
      “Kasan bazata faɗamin gaskiya ba ai, ni namayi mamakin ganinta  musamman idan na tuna irin rabuwar da kukayi”.
      Nanma shiru bai tankaba, shima kuma Attahir ɗin bai sake maganaba har tsawon wani lokaci, saikuma ya cigaba da faɗin, “Ajiwa Bukky ba karamin so take makaba wlhy, ni dama nasan dawuya ta iya rabuwa dakai, wancan lokacinma fushin da tayine yasata nisantarka, mizai hana kawai ka cire komai a ranka ka aureta kodan gudun karta cutar da matarka ta hanyar da bamu zataba”.
      Cikeda wata irin fusata ya buɗe idonsa akan Attahir, “Amma bakada hankali, Attahir harkai kake faɗamin na auri yarinyar data nemi yimin fyaɗe, tadawo tana roƙona akan nai divergent ɗinta babu igiyar aure a tsakanina da ita saboda ita dabbace karya. Idan wannan maganar banzarce ta kawoka wajen tashi barnan”.
      “Yi haƙuri nabar maganar, to amma miyasa ita Ummukulsoom bazaka karɓeta a matsayin mataba kamar yanda ka karɓa a gaban Dad”.
     Wata banzar harara yaa Amaan ya zubama Attahir yana jan tsaki, kafin yamiƙe da nufin bar masa wajen. Saurin riƙosa Attahir yayi yana faɗin “Ajiwa ka tsaya muyi magana mana”.
      “Dalla malam sakeni, nakula yau hankalinka baya cikin kanka”.
      “Ni wlhy garau nake, kaima kuma kasani tunda ba shaye-shaye kataɓa gani inaiba, nakan rasa gane halinka wani lokacin wlhy Ajiwa, halayyar Bukky yasaka jin bazaka aureta ba dukda ɗumbin son da take maka, tun kana shareta harka karɓeta, yanzu kuma yarinyar nan da Dad ya aura maka ni banga aibunta ba, kanada damar ɗorata aduk makarantar da kakeso inma kasancewarta ƙaramane batai makaba ko rashin zurfin ilimi, kaga nanda shekara biyu zuwa uku sai kaga anwuce wajen tamaka yanda kake buƙata, dan girman ƴa mace baida wahala musamman idan tanasamun kulawa mai ƙyau da kwanciyar hankali, wlhy kai kanka idan ka kusanta zamanka da mace zaka rage wannan baƙar zuciyar taka, kasamu nutsuwa fiye da zatonka, ka kai age ɗin da kake buƙatar mace ƙololuwa, amma kake azabtar da kanka akan wani ra’ayi naka mara dalili……”
      Fisge jikinsa yayi tareda jan tsaki da harar Attahir ɗin yana faɗin, “Banza kawai, kai yaushe nataɓa cemaka ina buƙatar macen? To bana sonta kuma bataiminba, amincewa Dad dakake magana kuma kaima kasan bana taɓa jayayya dashi, karɓa daban, hakama amincewa daban, karka sake sakomin yarinyarnan a shirmenka”.
      “Idan baka amince da itaba miyasa ka daki Bukky akanta yau?”.
     “Shaƙeni na faɗa maka mana”. Yana gama faɗa ya canja wajen zama zuwacan nesa da Attahir.
     Dariya Attahir yayi yana binsa da kallo, a fili yace, “Ajiwa kana raina wacece mace, namaka alƙawarin inhar ina cikin masu tsawon rai saina sakaka kaso zaɓin Dad fiyeda tunanin duk wanda ya sanka, kwanannan zamu fara wasan kuma”.

       Shidai Amaan baisan alwashin da Attahir ke dauka a kansaba, dukda kuwa yaji dariyar da yayi da buga table alamar tabbatar da alwashinsa.
       Attahir bai bisaba, sai waya daya ɗauka yakira Abbas akan ya sanarma Desmond yabashi ya kawowa Amaan ɗin abinci inda suke, danya fahimci baici abinciba.

★★
     Koda Attahir ya fita da Bukky sai Ummu ma tanufi ɗakinta tana sharar ƙwalla, itafa harga ALLAH tausayi Bukky tabata, sannan tana son sanin mike tsakaninsu haka?.
      Kwanciyarta ta gyara akan gadon zuciyarta nakuma tsorata da lamarinsa, yanzukam taƙara fahimtar miyasa ƙannensa ke shakkarsa, idan har zai iya buɗe ƙwanji ya lakaɗama budurwa da suke soyayya duka irin haka inaga ƙannensa ko ita da aka cusamawa akan dole?.
      Laɓɓanta ta shafa da tuna abinda yay mata, wani abu takeji na sauka a zuciyarta mai kama da shakku da tsoro, tasan yayi hakanne dukdan yabama baƙuwarsa haushi, amma harga ALLAH batai zatoba. “Ya ALLAH kasaka sanyi da salama a zuciyar mutuminnan, idan har a haka zanyi rayuwa dashi nashiga uku kenan wlhy” ‘tai maganar tana sharce hawayen dake gangaroma fuskarta’.
     Har yamma takasa fitowa, salla kawai ke tashinta da tayi sai ta koma ta kwanta, koda wasa bata fatan haɗuwarsu, dan yau abu biyune a tsakaninsu, kunya da tsantsar tsoronsa.

       A’i kanta wannan lamari ya firgitata, yo ashe Alhaji Mahmud ga babban magaji daya zartasa nan, wannan jarababben yaron ai zai iya halaka mutum idan ya shigar masa hanci, itako ina ita ina kawo Aina’u wannan gidan, yanda take da shegen rawar kantanan yaje ya halaka mata ɗiya, to amma kuma harga ALLAH fa burinta na ƴarta ta auresa yana nan zaune daram a ranta, dan dama a kullum burinta ƴarta ta auri miji na kece raini kamar yanda ƴar kishiyarta ta aura, to ga damar kuma tasamu sai dai wannan jarababben mutum haɗa inuwa dashi  haɗarine…….
    Wayarta datai ring ce ta dawo da ita hayyacinta, ganin Momcy ce saita ɗauka da hanzarinta. Cike da girmamawa ta gaidata.
    Daga can Momcy tace, ”A’i yau najiki shirune, bayan kuma Fodio yacemin yadawo tun ɗazun”.
     “Ki gafarceni hajiya, ai yau abin faɗarne akwai ban takaici wlhy….”
    Cikin katseta Momcy tace, “baruwanki da takaicinsa, kamar yanda na faɗa miki koma miye akayi ki sanarmin”.
    “ALLAH ya huci zuciyarki to, dama dai watace tazo bayan dawowarsa………..”
    Tsaf ta kwashe komai ta sanarma Momcy hatta da kissing ɗin Ummukulsoom da kaɗan ya hana zuciyar Momcy bugawa, tashiga zabga masifa akan dolene tasaka Fodio sakin Ummu kwanannan, dan wlhy baza’a haifa mata jika daga tsatson ƴar aikiba kuma ƴar ƙauye, ai garama ya auri Bukky ɗin koba komai ɗiyar manyace mai aji da ƴanci…..
           Ummayya da Aneesa da suka shigo suka isketa suka shiga tambayarta, jin abinda ya farune sai suka shiga tunzurata suma suna cewa asiri Ummu taima yayansu, taya za’ai wannan ƙazamar yarinyar harta birgesa yace zaiyi mata kiss?. Ummayya harda ƙaƙaro amai wai ƙyaƙyamin haɗa baki da yayansu yay da Ummu.
      Suma kansu da ba’ai a gabansuba gulmar A’i tasakasu yini da takaici, gashi Momcy nata kiran yaa Amaan yaki ya ɗaga.


ALLAH ya rabamu da sa kai a uku.
⛹‍♀⛹‍♀, surukai da dangin miji kuma kanku faɗa akan sakama ƴaƴanku ido da matansu, babu abinda ke janyowa sai hana sukunin zukata wlhy.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

          Yayinda Suhailat ke fama da karatu da laulayin ciki, Baseer nacan soyayya tai ƙarfi tsakaninsa da Lubna, sam Suhailat batasan mike faruwa ba, koda ta sani a yanzu batada wata fawa ɗin ɗaukar mataki, dankuwa asirin da yay mata yay masifar yin tasiri a jikinta, saboda sakacin addu’a dayin ibada akan lokacinta, ga azabar laulayima dake addabarta, sauƙintama ƴan aiki daya kawo ya tile a gidan, wanda ba son zamansu takeba saboda kishinsa, sai dai batada baki yin magana a halin yanzu.   
         Maganar Baseer hartaje gidansu Lubna, nanfa saiya ƙara haukacewa saboda ganin mahaifin Lubna yafi na Suhailat kuɗi nesa ba kusaba, gidan da sukema kawai abin kallone, dan wata duniyace guda mai zaman kanta.
      Dayake saida yayma Lubna da mahaifinta shiri na musamman sai babu wata jayyaya family ɗinta suka karɓesa hannu biyu,  dukda sun tabbatar sun fisa komai na game da dukiya da alfarma.
        *Alhaji Wada barma* ya bama Baseer damar turo iyayensa, dan acewarsa so yake ya aurar da Lubna kasancewar ta kammala karatunta, shikuma mutumne dake riƙo da aƙida tasa, da ƙyarma ya amince Lubna tafara jami’a a gida, sauran yayyenta duk iyarsu secondary yay musu aure, agidajensu suka cigaba da karatunsu.
        Sai da ya gama tanadar iyayensa na bogi kamar aurensa na farko sannan ya shirya yaje ɗilau ya sanar musu zai ƙara aure.
    Tsantsar mamaki ne da al’ajab suka bayyana a fuskar iyayensa da ƴar uwarsa talatuwa, baba yashiga masa faɗa akan hakan, dan aganinsa yin fushi da Basiru yanzu ba nasu bane, garama sujawosa a jiki da masa nasiha ƙila ya dawo hayyacinsa.
    Tsare-tsaren gaskiya da ƙarya ya zauna yayta musu har suka amince, tareda masa addu’ar fatan alkairi, ba komai yasa sukai hakanba sai masa talala akan canja salon dawo dashi hanya idan yanada rabon hakan.
      A wannan karon iyayensa bama suje ɗaurin aurenba, dan kaf garin ɗilau bayansu babuma wanda yasan Basirun zaiyi aure, su baba sunƙi sanarma kowa.
     
      Ba tareda Suhailat tasan komaiba aka shiga shagalin bikin Baseer da amaryarsa Lubna.
     Abinda Suhailat kawai ta lura dashi shine canja mata daya farayi, datai magana kuma ya hau kanta da masifa dacewar shifa babu lallai babu tilas saisu rabu.
     Baƙaramar girgizata zancen rabuwarnan tasu yakeba. Tun tana ɗaukar lamarin wasa harya fara taɓa rayuwarta. Shiko ko’a jikinsa, dan ta amaryarsa Lubna yake.
     Haka akasha bikinsa da Lubna, tareda raƙwashewa da ƙwallewa batareda dangin Suhailat ko ɗaya ya saniba, abokansa na su Najeeb kansu abun basu saniba tunda a kano amarya take.
       Dama tun ana saura sati a ɗaura aurenne Baseer yayma Suhailat ƙaryar zaije lagos wani aiki daya shafi kamfani, amma ko daddynta bayason ya sani har sai ya kammala.
     Son da take masane yasata aminta dashi, tai masa addu’ar dawowa lafiya harda rakkiya zuwa mota dukda tana fama da kanta kuwa.
       Koda yabaro gidan saiya hau tuntsura dariya da faɗin “Kai anya a duniya akwai wawaye irin mata kuwa? Da anyi magana suce sun fika wayo, to shidai baiga wayonba, dan gasu yana garawa tamkar sitiyarin motarsa a hannu, shiko lallai ƙyau yamasa rana, dan gashi yazama jarin tara dukiya ta hanya mai sauƙi batareda shan wahala ba” wata dariya yakuma bushewa da ita “Lubna kema kin shigo tarkon Baseer, ALLAH ya kawo wata mai tsautsayin a next target”.
     Harya ƙarasa kano aranar yanata haukarsa a mota shikaɗai.

    Bayan biki aka kai masa amaryarsa gidansa daya saya da kuɗin Daddyn Suhailat.


⛹‍♀⛹‍♀Humm su Baseer samarin shaho.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

             Hankalin mahaifiyar Bukky ya matuƙar tashi saboda a yanda ta dawo gida.
       A ruɗe suka shiga tambayarta abinda ya sameta?.
     Tsaf ta zauna ta zayyane musu komai akan auren Amaan da dukanta dayay akan matarsa.
      Cikeda masifa yayanta ya miƙe, “Yanzu kingane mi muke sanar miki akan halin Hausawa, kin zauna kin mutu akan akansa saikace shine kaɗai namiji a duniya, idan ƙyawunsa ke ruɗarki acikin yarenmu akwai waɗanda suka fishi komai, idan dan yana sojane akwai waɗanda suka fisa komai a gidan soja wanda Dady zai iya samo miki, ƙilama asiri yay miki, dan hausawan nan sun iyayi dama, mutanen da babu abinda suka iya sai auren mata suna sakinsu……..”
     “Bolaji ya isheka haka, ƴar uwarka nacikin damuwa maimakon ka taimaketa saikaita cimata mutunci?”.
     “Niba mutuncinta nake ciba Mom, gaskiya nake faɗa mata tunda ita takasa ganowa kanta”.
      “To anji, jeka kawai”.
 Baki ya taɓe ya fice daga falon haushin ƴar uwarsa nacinsa a rai, shi dama can yatsani wancan guy ɗin, dan ƙiri-ƙiri aka hanashi wani gurbi a gidan soja saboda shi.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button