WUTSIYAR RAKUMI 18

Yana fita Maman Bukky ta kalleta tana faɗin “Kinga dear bar Bolaji kinji, indai har akan Amaan ne bar zubar da hawayenki, dagashi har matar tasa zasu gane kuransu, kamar yanda bai aurekiba itama bazai zauna da itaba”.
“Mom da gaske kike?”.
“Yes dear da gaske nakeyi, daddynku ma yana dawowa zan sanar masa komai, nasan zai ɗauki mataki a wannan karon, dama kece kika hana a faɗa masa abinda yay miki wancan lokacin, amma a wannan time ɗin tunda haukarsu na sojoji ya ɗebesa harya dakeki saiyayi dana sani kuwa”.
Rungumeta Bukky tayi tana dariyar jin daɗi, “Nagode mommyna, shiyyasa nake sonki, komi ranki yabaki kima shegiyar matarsa, nikuma inason ya mutu akan sona duk abinda yamin harna baya saina ramashi”.
“Duk za’ai masa, gobenan zanje wajen babalawo na Obada”.
Daɗi sosai ya kama Bukky hardasu rawa, dan tatsani Ummu sosai a ranta, dama saboda ƴar yarinyarnan yaketa mata wulaƙanci ashe tuni, ai yanzu kam saiya zauna da ita tagani.
????????????
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Yaa Amaan bai dawo gidanba sai kusan 10 na dare, babu kowa a falon sai tv da keta aiki, daga A’i har Ummukulsoom tsoro ya hanasu fitowa, abincin darema sai ɗiba Desmond yay yakai mata ɗaki.
Wayarsa daya manta a falon ya ɗauka a saman table ɗin dake gefen kujerar, babu wanda ya motsata duk da ya lura an sake gyara falon, a falon ya zauna yana danna wayar, kira yagani rututu a kuma duk na Momcy yafi yawa, daga ƙarshe yaga harda saƙonta.
Cikin dafe kai ya buɗe massege ɗin nata.
_Fodio nakiraka kaƙi ɗagamin waya saboda ka maidani ƙawarka ko?, kokuma mace ta rufe maka ido._
Rumtse idonsa yayi sosai, zuciyarsa na wani bugawa da sauri-sauri saboda ƙarin wani sabon ɓacin rai da yaji, harma shi Momcy kecema mace ta tsonema ido, yaushe yarinyar takai ajin zama mace dahar zata makantar dashi su, datasan yanda ya tsani aurennan ma da ko a mafarki bazatai wannan tunaninba, ya karɓetane saboda bazai taɓa iya jayayya da mahaifinsa ba, zamanta kuwa a gidan akwai gaɓar da yake jira ta barsa, dan a tsarinsa bayason auren ƙaramar yarinyar dako 20years bata cikaba, haba wannan ai solon jan rainine, ya zauna da sa’ar ƙaninsa Bassam matsayin matar da zata iya ganin ƙarshen girmansa, ko a mafarki baya fatan wannan mummunan al’amarin. tsakaninsa da ita *Wutsiyar raƙumi tai nesa da ƙasa* wlhy.
Wani takaici yakuma taso masa saboda tuna abinda yay mata ɗazu a dalilin waccan jakar yarinyar Bukky, saidaga baya yamafi jin zafin kissing ɗinta da yayi akan haukarda Bukky tazo tai masa a gidan………✍????
*_Baseer yace karku sake ku samasa ido shida amaryarsa????????????????⛹♀⛹♀⛹♀_*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*