WUTSIYAR RAKUMI 21
*_NO. 21_*
…………Sosai hankalin maman Ahmad ya tashi jin bayanin desmond, dan haka ta kirayi Attahir ta sanar masa tana hawaye, harga ALLAH tana
ƙaunar Ummukulsoom, amma lallai ta jajantama Amaan bisaga wannan gangancin da yay.
Kasa magana Attahir yayi gaba ɗayasa, tsawon mintuna biyu kafin ya yaneke wayar yana haɗiye wani ƙududun takaicin Ajiwa a maƙoshinsa.
Kiran Maman Ahmad yay yace ta haɗashi da desmond.
Bayan desmond ya karɓa yay masa tanbayoyi akan direban daya ɗauki su Ummu, duk bayanan da yake buƙata ya sameshi garesa, dan haka ya kashe wayar tareda neman Abbas daya kawo direban, shine yabama Attahir Number ya kirasa.
Bayan sun gama tattaunawa ya yanke yana nazarin akan tarar Alhaji Mahmud da zancen tareda abinda yake shiryawa, baisan yaya zai fahimcesaba, tunda yana tunanin anya Amaan zai iya faɗa masa?.
Ganin bai samu mafitaba sai kawai yakoma Office.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Yini guda yau Dad yana gida bai fitaba, sai dai ya kaɗaice kansa acan baya daga harabar gidan yana harkar business ɗinsa ta lap-top, ya daɗe a wajen kafin ya tattaro kayan ya dawo cikin gida.
Gidan shiru babu kowa, yaran duk suna makaranta, dan Bassam ma yacigaba da karatu tun tafiyar Ummu babu daɗewa.
A falon ƙasa ya zauna danya ɗan huta, wayarsa dake gefe tai ɗan wani motsi alamar shigowar saƙo ya kalla, ganin sunan Fodio yasashi ɗauka ya buɗe saƙon.
Ƙurama wayar ido yay yakasa koda motsi saboda firgici da saƙon ya ƙunsa, tare da tsantsar al’ajabi da tsaurin ido irinna Fodio, ya maimaita saƙon yafi a ƙirga kafin ya adanashi inda wanima bazai ganiba.
Ana haka Momcy ta sakko cikin kwalliya, yanayin fuskarsa yasata faɗin “Abban Fodio lafiya kuwa?”.
Wani kallo yamata tareda ɗauke kansa kawai, yasan tasan komai dake faruwa, dan yanaji a jikinsa itace ta saka Fodio a wannan hanyar, dan haka ya shirya binta ta inda bata zata ba.
Duk iya bin kwakwkwafi na Momcy bataji abinda takeson jinba, saima ta fara zargin ko fodio ƙarya yay mata bai saki yarinyarnan ba, tashi tai tabar falon takoma sama tana neman wayarsa, sai dai kuma bai ɗagaba kusan kira uku, haushi yakuma hasalata, dan ta ɗauki alwashin a wannan karon inhar Fodio ya bijirema umarninta saita janye son da take masa gefe ta saɓa masa.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Lokacin da su Ummu suka iso cikin kaduna ƙarfe ɗaya na dare ya wuce, linƙis take da zazzafan zazzaɓi a jikinta, dan hannunta da tajima ciwo ya mata nauyi sosai, ga ciwon kai saboda kuka da tasha.
Tasha mamaki sosai ganin Attahir ya taresu, sai dai ƙala kasa cemasa tayi, sai idanu da takebinsa dashi, idan san samuntane daganan kawai su wuce ɗilau, dan ko sha’awar zama gidan inna harira batayi itakam a wannan karon, ƙauyen can da ake cin zarafinta a kansa take sha’war komawa da burin yin rayuwa.
Attahir ne yay musu jagora zuwa wani katafaren gida da Ummukulsoom ta gaza fahimtar inane, sai dai gidan shiru babu hayaniya alamun jama’ar cikinsa sunyi barci, amma a mamakinta saiga kusan mutum uku sun fito tarbarsu, babbar mace mai tsananin kama da Attahir sai matashiyar budurwa da zasu iya zama sa’anni da Ummu, sai saurayi wanda kallo ɗaya zakai masa kasan ƙanin Attahir ɗinne.
Tarba sukai musu ta mutunci da girmamawa, harda A’i uwar gulma.
Matar da kanta ta kama hannun Ummu sukayi cikin gida, sai jera mata sannu da zuwa takeyi.
Ummu nata mamakin kirkin mutanen gidan, ko kaɗan basuda wulaƙanci, lallai ga inda Attahir ya gado ƙyaƙyƙyawan hali ashe, sai dama-dama ake da ita babu wani ƙyanƙyami ko nuna isar su wasune, ta tuna gidansu yaa Amaan iyayen alfahari da tunƙaho.
A ɗakin budurwar akaima Ummu masauki, dandanan ta haɗa mata ruwa mai zafi dan tayi wanka.
Godiya Ummu tai mata sannan tashiga wankan, tana wanka tana kuka, haka dai ta gasa jikinta sannan ta fito.
Tun fitowarta Bilkisu ta lura da hannun Ummu.
“Amma kamar hannunki da ciwo ko?”.
Kallonta Ummu tayi kafin ta kalli hannun tareda yin guntun murmushin takaici, “karki damu, bawani ciwo bane mai yawa”.
Hannun takamo tana kallonsa da faɗin, “Wannan kam ya wuce ƙaramin ciwo, kallifa yanda tafin hannunki ya yayyanke, kinga ga kayan barcinan ki saka bara na dawo”.
Ummu bata iya cewa komaiba, sai binta da kallo datai harta fice, ajiyar zuciya taɗan sauke kafin ta ɗauki kayan barcin wando da riga masu ɗan kauri ta saka, tana ƙoƙarin saka hula taji sallamar yarinyar tareda Attahir. saurin jan ɗan kwalin kayan data cire tayi ta yafa a jikinta, dukda kayan ba matseta sukaiba kuwa.
Kallo ɗaya yay mata shima ya kauda kansa, yayinda budurwar kuma ta ajiye ƙarmin tire mai ɗaukeda kofin shayi da madai-daicin cake a gefe.
“Yaya bara na akarɓo maganin wajen Ummy”.
Kansa ya ɗaga ɗaga mata kawai ya zauna a kujerar data kasance guda ɗaya a ɗakin.
Ummu dai na tsaye tana saurarensu, sai dai kallo ɗaya zakaima fuskarta ka fahimci bata tareda walwala.
Attahir ya furzar da huci yana faɗin, “Bismilla ki zauna mana”.
Bata musa masaba ta zauna a bakin gadon tana haɗiye hawayenta, maganarsa ta sata ɗago ido taɗan kallesa.
“Shine ya jimiki ciwo a hannu ko?”.
Kanta ta girgiza masa tana juya idanunta saboda hana hawayen da suka tara zubowa, amma hakan bai hanasu fitowarba, bakin gyalen tasa ta goge, “Bashi ya jimin ciwoba Abban Ahmad”.
Kansa ya iya girgizawa kawai, yace, “Ok, kiyi haƙuri Ummukulsoom, ki ɗauki hakan a matsayin ƙaddara, dare yayi yanzun, zuwa da safe zamu tattauna insha ALLAH, kisha wannan tea ɗin bilkisu zata kawo miki magani, dan ALLAH ki fidda komai a ranki, ki kuma saki jikinki a gidannan, domin ke ba bare baceba”.
Kanta ta ɗaga masa tana kuma share ƙwallarta, “Nagode sosai Abban Ahmad, amma kayi haƙuri, zuwa yanzu babu inda nake kwaɗayin zama irin ƙauyenmu, kuma yadace mahaifina yasan matsayin aurena a yanzun”.
“Wannan tilas ne ai Ummukulsoom, dolene baba yasan komai, maganar ina zaki zauna kuma duk zamuyi magana daga baya”.
Nanma kanta ta jinjina masa.
Bai bar ɗakinba har Bily takawo maganin, suka saka Ummu tasha tea ɗin dukda taƙii cin cake ɗin, magani tasha yay musu sallama ya fice.
Gajiyar datai a hanya ce tasaka barci saurin ɗauketa, dukda sunsha kokawa tsakaninsa da damuwarta kafin barcin yaci nasara akan damuwar tata.
A washe gari da safe saida Ummu ta makara sallar asuba, bily kuma taƙi tashinta.
A gaggauce tayo alwala tafito, dan ƙarfe takwas saura, bayan ta gabatar da sallar tai addu’a tana kuma tariyo abinda ya faru a jiya, kusan iyanzu duk sun baro cikin Barrack ɗin.
Ganin dukkan kayanta a ɗakin sai mamaki ya kamata, ta kasa fahimtar ma’anar hakan, ita duk tunaninta gari na wayewa zasu ɗauki hanyar ɗilau, kallonta ta maida ga Bily dake ƙudundune a bargo tana barci, Ummu ta sauke nannauyar ajiyar zuciya kawai.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
“Honey wai meke damunkane kwana biyunnan?”.
Baseer dake kwance ɗai-ɗai a gado yana danna waya ya ɗago idanu ya kalli Lubna mai maganar.
“Mikika gani?”.
“Ba komai, kawai dai naga kamar kacika maida kanka busy a kwana biyunnan, bakason zama a gida, idanma ka zauna kata danne-dannen waya kenan”.
Idanunsa ya janye a kanta ya maida kan wayarsa, “Kece dai kikaga hakan, amma ni nasan babu wata canjawa danai”.
Shiru tai kawai tana kallonsa, tama kasa cewa uffan.
Tsawon mintuna suna a haka kafin ta miƙe tabar bedroom ɗin.
Bayanta ya raka da harara yana taɓe bakinsa, a yanzu kam ko kaɗan bata birgesa, bakaramin haushinta da takaici yakeba idan ya kalli ƙaton cikin gabansa, ya tunano zabgegiyar yarinya jinin kanuri Fannah ɗinsa, yarinya mai zamani mai lokaci a zuciyarsa, tuni soyayya tai ƙarfi a tsakaninsu, harma mahaifinta yace ya fito, burinsa ƙarshen watannan ya tura kuɗin aure, dan bayason bikin ya wuce nanda wata biyu, hotonta dake wayarsa ya latso yana kallo, wata nutsuwa da ƙaunarta tareda sha’awa wadda itace ƙarfin son na rinjayar zuciyarta, yarinyar komai yaji kam, dan akwai halitta mai ƙyau.
Tsawon lokaci yana kare mata kallo lungu da saƙo ta hoton, kafin ya rufe yana zamewa ya kwanta.
Lubna kam bata sake shigowa ɗakinba, kwanciyarta taje tayi a ɗayan ɗakinsu kodan ta hutama ranta.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Sai da su Ummukulsoom sukazo yin breakfast sannan takejin ashe A’i ta wuce gida tun ɗazun, ita kaɗaice a gidan yanzun, suna cin abinci amma banda ita, sai tsakura take kaɗan-kaɗan.
Lura da hakanne yasaka Ummi mahaifiyar su Attahir janta da hira tareda lallashinta akan taci, duk sai kunya ta isheta, dan haka taɗanci abincin.
Kammalawarsu babu jimawa Attahir ya fice akan zaije ya dawo yanzun.
Addu’ar dawowa lafiya sukai masa, itama Ummi ta shirya tafita wajen aiki kasancewar ita likita ce.
Daga Ummu sai Bily aka bari a gidan, Zaid ma yafice wajen nasa aikin.
Kamar yanda Attahir yacema Bily ta ɗaukema Ummu kewa haka ta dake taita janta hira, dukda bata amsawa iyakarta murmushi ko e ko a’a.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Koda Attahir ya fita gidan su Fodio ya nufa, a falon baƙi akai masa masauki, dan haka hajiya jamila batasan wanene baƙonba, Jud ya kawomasa ruwa da lemo. Babu daɗewa da fitarsa saiga Dad dayasan da zuwansa ya shigo, fuskarnan babu fara’a tamkar kullum.
Zamowa Attahir yay daga kujera ya koma saman Carpet yana gaidashi. Cike da kulawa Dad ya amsa da tambayarsa wajen aiki.
Attahir yace, “Alhmdllh Dad”.
Kujera ya nuna masa alamar ya koma ya zauna, amma sai Attahir ɗin yace, “A’a Dad nanma ya isa”.
Attahir sai juya maganar da zaiyi yake a ransa, amma ya kasa, saikace shine Fodio ɗin, lura da hakanne ya saka Dad gyara zamansa, “Attahir bakinka da magana, sai dai bansan mikake son ɓoye minba? Inhar maganar abokinkace karkaji komai, yama rubutomin text massege a jiyan, ina tsumayen isowar Ummu ɗinne kawai, ɗazun da safe tsohuwar dataje ta tayata zama ta iso gidannan tareda driver, shine yame sanarmin dama tana tare dakai, Saƙo ɗaya zan baka kabama abokinka Attahiru, yayi yanda yakeso, nima saiya jira lokacin dazan masa yanda nakeso, duk duniya ban haifi ɗan dazai jayayya daniba wlhy, ni nafisa tsaurin ido dagashi har uwar tasa data sakashi, idanma shine ya aikoka ka sanar masa bana buƙatar kowa akan wannan maganar”.
jikin Attahir sai tsuma yakeyi jin Dad a matukar fusace yake magana, yakuma kasa da kai yana kwantar da murya, “Wlhy Dad ba Amaan bane ya turoni, hasalima baisan nabaro legas ba a yammacin jiya, amma amin afuwa bisa yin gaban kaina da nayi, nayi hakanne gudun kartace zata wuce garinsu a daren dan bansan shiyama sanar mukuba”.
“Babu komai Attahiru, hakan dakai ba laifi baneba, yanzu ina ita Ummukulsoom ɗin?”.
“Tana gidanmu na barota, dama nafara zuwane akan wata shawara”.
“To to ina saurarenka wace irin shawarace?”.
Shiru Attahir yay yana juya zancen, kafin yace, “Dad dan ALLAH kayi hakuri akan abinda Amaan yayi, karka nunamasa fushinka dan zai taɓa rayuwarsa sosai, mubi ta hanya mai sauƙi wajen nuna masa kuskurensa kawai, sannan mizai hana Ummu ta koma makaranta ita kuma”.
Shiru Dad yay yana kallon Attahir tareda nazarin maganarsa, yaɗan nisa yana kaɗa kansa, “Shawararka mai ƙyauce Attahiru, shikam dama ai bazan taɓa masa maganarba daman, maganar karatunta kuwa zan zauna da mahaifinta muyi magana, dan dama naso takomane tana ɗakinta, a yanzu kam bamuda hurumin hakan tunda bata a ƙarƙashin ikonmu”.
“Eh gaskiyane Dad, sai kuma maganar zamanta a gidan namu”.
“Eh to wannan kam ka bani lokaci, dan nafison tadawo kusa dani kam, amma zuwa anjima zanzo gidan itama na ganta insha ALLAH ”.
“To Dad nagode sosai, ALLAH ya ƙara girma da lafiya mai amfani”.
“Amin ya rabbi Attaru, nine da godiya ai basa zamowarka aboki na ƙwarai, ALLAH yay muku albarka, shima ALLAH ya shiryesa”.
“Amin Dad mun gode, ALLAH ya huci zuciyarka, bara naje ni, shima Amaan ɗin a satinnan zaizo kd ɗin ai”.
“Ok babu damuwa”.
Attahir ya koma gida zuciyarsa na cigaba da takaicin Amaan, sai dai a ransa yanajin cewar yanzune za’a fara wasan, fatansa ALLAH yabasu tsawon rai na dawowa lafiya daga inda zasuje kawai, ALLAH yasa ita kuma Ummukulsoom karta basu kunya………✍????
*_Ayi haƙuri da jina shiru, dan lafiya uwar jikice, babu mai fushi da ita????????????_*
Duk wanda yamin saƙo ta pc daga ranar alhamis yay hakuri zaiga ban amsaba, by mistek komaina ya goge.
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????