NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 23

*_NO. 23_*


………..Yau kam sunsha shargallensu agidan inna harira, dama Aziza yaya lafiyar giwace itama, har dare suna gidan, baba yazo suka gaisa bayan sallar magrib.

      Da zai tafi saita bisa soro dansu ɗan tattauna.
          “Baba dan ALLAH ku amince naje Ɗilau, wlhy ina kewarsu sosai”.
      Baba dake zaune a tabarma yay ƴar dariyarsu ta manya, “Ummukulsoom kenan, indai ɗilau ce zakije, kibari su Alhaji sugama shirin karatun naku, dan dama munyi dashi sai kin kammala iddarki, tunda dai yanzu kin kammala nasan da kansa zaimace kije ɗin”.
     “Hakane baba, amma ya jikin Gwaggo hinde ɗin?”.
      “A jikin Gwaggo kam Alhmdllhi wlhy, ta murmure dan talatar satin can data wuce mun haɗu da ita wai zataje tsinkar gyaɗa gonar babanki Ayuba, harma naita faɗa akan bai kamataba, amma sai tacemin itace tace zataje saboda likita yace take ɗan motsa jikinta”.
       “ALLAH sarki gwaggo, to ALLAH ya ƙara musu lafiya, amma baba ai batasan aurena ya mutuba ko?”.
      “Haba Ummukulsoom, ya za’ai a sanar mata da wannan maganar banda dai wautarki ta ƙuruciya, ai ba abune na daɗiba kinga, balle ita dake fama da jikin tsufa”.
       “Hakane kuma baba, ALLAH yasa mudace”. ‘Ummu tai maganar cikin share hawaye’.
       “A’a Ummukulsoom, nifa wannan kukan bana sonshi, idan akai haƙuri komai mai wucewane, saikiga yazama labari tamkar baima faruba, a rayuwa kowanne bawa da tasa ƙaddarar, ki ɗauka keɗin taki kenan, idanma kikaji ta wani saikiga ai ke takin ba komai baceba”.
      “Hakane baba, insha ALLAHU zan kiyaye”.
    “Yauwa ko kefa ƴar albarka, ni bara natashi naje, dan gobe idan munkai da rai asubanci zanyi”.
     “To baba ALLAH ya tsare hanya, a gaishe mana da kowa”.
     “Amin dai Ummukulsoom, duk zasuji ”.
     
     Har baba yay musu sallama ya tafi Yaya Zaid bai ƙarasoba, sai wajen tara saura yazo, ko shiga gidan baiyiba, waya yayma Bily akan su fito waje.
        Aziza ta rakosu har ƙofar gida, bayan su. gaisa da yaya Zaid suka ɗau hanya, itakuma ta koma gida abinta.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

              Lubna shiru zaune a falo ita kaɗai sai masu aikinta, ta zuba tagumi tana tunanin wai ina Baseer yake zuwane ne, a ƴan kwanakinnan takan rasa ina yake zuwa duk bayan kwana biyu, na farkoma saida yay kwana tara, ita dai a saninta sai kanada kishiyane kowa gidansa daban miji ke wannan asha ruwan tsuntsayen, itako ba kishiyace da itaba balle tace…..
       Motsin da taɗanjine ya sata waigowa da sauri, shine sanye cikin ƙananun kaya tamkar yanda ya saba, cike da zumuɗi tai masa sannu da zuwa.
     Amsawa yay tare da tambayarta jikinta da gida, tai murmushin yaƙe da amsa masa, hakan da yake mata yake sakata samun nutsuwa koda zuciyarta ta fara mata rawa a kansa.
      Da kanta ta taimaka masa yay wanka dukda ƙaton cikin dake gabanta kuwa, bayan sun dawo falo suka baje suna ƴar hirarsu.
    Kiran da ya shigo wayarsane ya saka Baseer saurin ɗaukar wayar ya danne ƙarar, Lubna ta ɗan tsura masa idanun tuhuma, “Babie ka ɗaga mana”.
      Murmushin yake yay mata, “Lah karki damu Hafiz nefa”.
     Murmushi tai tareda ɗauke kanta, shima haka, kusan minti biyu sai aka sake kira, nanma yay azamar danne ƙarar. miƙewa Lubna tai ta bar masa falon, dan ta lura bayason ɗaga wayar a gabanta.
     Da yake baseer ɗan barikine na gasken gaske sai yama kashe wayar gaba ɗaya, Lubna dake laɓe taga kozaiyi wayar harta gaji da tsaiwa ta dawo falon suka cigaba da zamansu, da zaije masallacima a gida yabar wayar yanda zata kuma yarda dashi ɗari bisa ɗari.
    Sosai kam hakan yay tasiri a zuciyar Lubna.

    Shikam yana fita ya ciro ƙaramar wayarsa ya kira fannah, “Oh babie sorry kinata kirana wlhy barci yaɗan kwashenine, kinsan matafiyi”.
      “ALLAH sarki babie na ya gajiyarka ya aikin?”.
       “Alhmdllh babie na, sai daifa kewarki tareda kewar lallausan jikinki da ƙamshinki”.
      “Karka damu, indai wan nanne nakane ai dear, bara na barka ka huta anjima mayi waya mijina abin alfaharina”.
      “Ok amaryar ƙamshi ki huta lafiya kinji”.
      “Insha ALLAH” Ta faɗa tana kissing wayar.
    Murmushi yayi ransa fes, duniya sabuwa yake jinsa, yasan da Lubna ta fahimci yayi auren nan da sai anyi uwarwatsi, dan ya gama lura tafi Suhailat kishin masifa, shiko baya buƙatar rabuwa da Lubna a yanzu, dan yana amfanuwa da mahaifinta fiye dana Suhailat, zaitabin hanya mai ɓullewa da wani bazai taɓa fahimtar yayi aureba balle har wani a family ɗin Lubna ya sani.


★★★★★
  
    Kwansa biyu a gidan Lubna ya ballaƙa mata karyar zuwa gaida iyayensa a kaduna, bata damuba, dan dama yana irin hakan, kuma tasan iyayensa acan suke, tunda itama kanta acan ɗin suka fara haɗuwa.
      Yana barin nan sai gidan daya kamawa amaryarsa Fannah haya, wadda duka-duka auren nasu bai wuci sati ukuba kacal.
     Yanda su Suhailat suka mutu akan son Baseer haka Fannah ma ta mutu, sosai take bashi kulawa da tattali, banbancinta dasu Lubna ita mahaifinta ba mai kuɗi bane sosai, amma gwargwado sunada rufin asiri, ƙarfin soyayyarta a zuciyar Baseer kam sha’awa ce, dan Fannah mace ce har mace, akwai diri ɗan gaske dako wanne irin namiji zaiso samun matarsa haka, ga uwa uba ƙyaƙyƙyawace jinin shuwa ɗan asali.
        Tarba tai masa ta musamman, kasancewar tunda sukai aure wannan ne karo na biyu dayay tafiyar kwana huɗu, iyakacinsa kwana dayane a matsayin aikin Office, nanko gidan Lubna yake zagayawa itama yaɗan kare yawa.

       Haka rayuwar tasu taci gaba da tafiya batareda sun fahimci wa suka auraba, garama Fannah idan taga abinda bai mataba takan tanka, wataranma har suyi faɗa da baseer ɗin, daga baya kuma yadawo su shirya.
      A haka har ALLAH ya sauki Lubna lafiya ta haifi ƴarta mace ƙyaƙyƙyawa mai tsananin kama da baseer, sosai yay farin ciki da wannan babie, sai dai abinda zai baka takaici babu ko mutum ɗaya daga dangimsa na jini, sai iyayensa na bogi dayay amfani dasu wajen aurensa, sukansu su Inna sai a hoto sukaga ƴar, amma hakan bai hanasu saka mata albarkaba da addu’a, dansu har yanzu bama susan ba Suhailat bace uwar ƴar, a tunaninsu har yanzu itace matar tasa, lamarin baseer yabar ɓata musu rai, sun zubamasa idone kawai.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

            Ummukulsoom ce farkon fita a motar, tai gaba tabarsu, shi Zaid ma dariya ta bashi, yasan duk dan karsu kasance su biyune take wannan abun.
           A falo ta iske su Ummi da suma basu wani jima da dawowar ba, Ahmad yazo yana mata oyoyo ta ɗaukesa tana shillawa.
     “Ku yanzu dama haka ake yini?”. Cewar maman Ahmad.
     Dariya Ummu tayi itama tana zama gefenta, “Kai aunty, kuma da alama fa yanzune kuka dawo, muma dan yaya Zaid baije da wuri baneba, Ummi fa?”.
        “Ummi tanada baƙo, suna falon Abba”.
     Kafin Ummu tayi magana su Bily ma suka shigo. Yaya Zaid dake kallon Ummukulsoom yace, “Hajiya bamu ɓataba, muma man gane hanya”.
     Murmushi kawai Ummu tayi ta ɗauke kanta, yayinda maman Ahmad take binsu da kallo baki buɗe, dan itakama tafara fahimtar akwai wata a ƙasa. Bily kam data saba gani dariya kawai tayi tana zama ɗauke da Ahmad.
      “Wai Aunty Hafsat kallon mi kike mana hakane?” cewar yaya Zaid.
      “Babu ko ɗaya Uncle, sai daifa ina bada shawarar abi a sannu kar ai karo da muruci, dan ramin damisa ba wajen wasan yara baneba”.
      “An samu matsala Aunty Hafsat, kinsanfa ni bawani gane wannan hausa cikin hausar nakeba”.
     Bily tace, “To balleni kuma yaya Zaid”.
      Ummukulsoom dai kam tsaf ta fahimci maman Ahmad, shiyyasa ta miƙe tama bar falon, a ganinta bada wannan amsarma ɓata lokacine, tarasa yanda zata hana mamana Ahmad dangantata da Yaya Amaan, mafi yawancin lokacima itace ke tuna mata sunansa, dan itakam tama manta da har sunan nasa, kamar yanda takeda tabbacin ita dama baima san natanba.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
       
      *_Gidan Alhaji Mahmud_*

        “Mun shiga uku Momcy, mike damun Dad ne, ina zamu samo mazan aure a wata biyu kacal? Wlhy Momcy kaf samarina babu maimin zancen aure”.
       “Toke kinama da Samarin Aneesa, ni nace mi, banda Huzaifa wanene ke zuwa wajena, Huzaifa kam iyayensa wlhy bazasu masa aure yanzuba”.
     Momcy na zaune ta zuba tagumi tareda zubama ƴaƴan nata idanu, abin duniya duk ya isheta, tarasa gane kan Abban Fodio a kwanakinnan, sai fito mata da salon abubuwa yake waɗanda ita kaɗaice ke fahimtarsu, yanzu daga Aunty Nurse ta samu miji shine yace Ummayya da Aneesa ma su fidda gaba ɗaya zai haɗasu ya aurar…….
     “Momcy magana mukefa”. ‘Aneesa tafaɗa cikin girgizata’.
      Cikin sauke ajiyar zuciya ta dawo hayyacinta, “To ni Ummayya mikukeson nace muku? Kunsan dai wanene mahaifinku da abinda duk ma zai iyayi, amma kubari zan gwada, ina zuwa”.
       Fatan samun nasara sukai mata, ta miƙe ta fita zuwa falon Dad.
    
      Zaune yake a falo yana danna Lap-top, yana waya kuma, hajiya jamila taji daɗin samunsa cikin walwala, gefensa ta zauna harya kammala wayar yana faɗin Alhmdllh, ALLAH kabani tsawon ran sauke wannan nauyin”.
     Da “Amin” hajiya jamila ta amsa, duk da bata fahimci komaiba a zancen nasa.
     Juyowa yay ya kalleta yana gyara zamansa, “Lafiya dai ko?”.
      “Lafiya lau Abban Fodio, dama dai akan maganar yaran nanne”.
     Ɗaure fuska ya kumayi sosai, “Waɗanne yara kenan?”.
     Tuni zuciyarta ta fara hautsinawa ganin yanda ya koma mata, cikin in ina tace, “Su su Ummayya, kayi haƙuri ka kara musu lokaci”.
      “To, to, saboda ga mijin hajiya Jamila ko? Jamila wlhy ki kiyayeni, ina tarakine kawai, idan kika bari nakai bangon da zan amayoki bazakiji da daɗiba, wlhy kinji na rantse duk wadda bata kawo mijiba a watanni biyunnan danace saina aura mata duk wanda yaymin, har shima Ameer ɗin, niba shashasha bane dazan zauna naita tara ƴaƴa a gida manya-manya babu aure, ko Buhayyah ta samu miji bayan kammala secondary ɗinta aure zan mata, dan haka wannan shine gargaɗi na farko, kuma na ƙarshe tsakanina dake, karki sake zuwamin da wannan batun, ina buƙatar ɗakunan da suke ciki dan mai zama cikinsu tana gab da shigowa”.
     Wani irin duka ƙirjinta yayi, ta waro idanu waje cikin tsantsar firgici, “Abban Fodio ban gane maganarka ta ƙarsheba wlhy”.
     Miƙewa yay tsaye tareda kwasar tarkacensa yana faɗin, “Ai bazaki taɓa ganewaba tunda kinacin kan kifi”.
      Tamkar sha katafi haka tabisa da kallo, manyan idanun nan da Amaan yay gado tamkar zasu zubo ƙasan carpet ne, jinta yay wani diimm, hakama ƙwaƙwalwarta tai jingim bata aiki gaba ɗaya, sam saita daina fahimtar komai, dukda wani gefe na zuciyarta na faɗa mata bafa abinda take tunani baneba.

        Sam a kwana biyunnan gidan ya sauya, saika ɗauka ko Amaan ne yazo, amma ba hakan baneba, dafin umarnin Dad ne kecin kowa a zuciya, idan ka ɗauke Aunty Nurse dake cikin farin ciki da shirin Dad ɗin, dan itace tabasa wata shawarar a cikin shirin nasa, bama tai zaton zai ɗaukaba ashe ya amsa.

       Ana cikin wannan yanayin a gidan saiga admission ɗin su Ummukulsoom ya samu, sai dai kuma a Rivers state ne, University of port harcourt suka samu, hakan bai damu Alhaji Mahmud ba kam, dan a ganinsama canne Ummukulsoom zatafi samun wayewar kai kasancewarta cikin ƙabilu daban-daban, zata samu ilimin zamantakewa da jama’arda koda ba kabilartaba.
       A ranar yakira Abban Attahir ya sanar masa, shima yayi matuƙar murna da hakan.
     Babu ɓata lokaci aka hau yima Ummukulsoom da Bily shirin tafiya port, duk da ita a ranta tana tunanin yaya zasu rayu a inda basusan kowaba, gashi ita koɗan turancinma bawani iyawa tayiba, danma Bily na nuna mata wasu abubuwan a zamanta gidan, sai karatunta na islamiyya, tana bukatarsa matuka, dan babu wani ilimi dazai tasiri ga rayuwar ɗan musulmi idan babu na addini a cikinsa.
    Kasa daurewa tai taima Bily tsokacin maganar, Bily kuwa ta samu Ummi da zancen ba tareda Ummukulsoom ta saniba.
    Murmushi Ummi tayi tanajin ƙarin ƙaunar Ummukulsoom a ranta, haka takeson mutum ya kasance mai sananin ciwon kansa da martabar addininsa.
      “Karku damu Bilkisu, zanyi magana da Abbanku saimuga yanda za’ai gameda islamiyyar taku, idanma wani malami za’a samu sai a sama muku acan, dan namaji kamar bacikin makaranta zamu zaunaba”.
     “Tofa, ba cikin makarantaba Ummi, to wajenwa muda ba dangi garemuba acan ɗin?”.
     “In banda shirmenki Bilkisu ko babu dangi ai akwai abokan arziki ko, mudai jira muji yanda za’ayi ɗin, kudai yanzu ku kammala shirin tafiyar taku ɗilau ɗin”.
     “Aini Ummi kinma tunamin, kinsan kuwa yanda na ƙagu muje garin nan nasu Ummukulsoom? A rayuwata inason naganni a inda ban saniba, musamman ma ƙauye wlhy”.
         Dariya Ummi tayi tana girgiza kai, “Hajiyar zumuɗi kenan, koda yake Ummu mafa na lura tana cikin tsantsar farin ciki, tana dai dannewane kawai, yarinyar tanada nutsuwa sosai wlhy, shiyyasa a kullum take sake shigemin rai, narasa miyasa Abbanku yace karna kaita wajen Hajiya yaya?”.
      “Wlhy nima Ummi abinnan na bani mamaki, nasan kuma Hajiya yaya batada matsala, tanada son jama’a zakuma taso Ummukulsoom sosai”.
       “Karmu damu, na tabbata akwai nashi dalilin shima ai”.
      “Hakane kuma Ummi, yanzu dai bamu kuɗin mutafi wankin kan kar rana tayi, nadsan Ummukulsoom ma tagama wankan yanzu”.
      “Duba a bag ɗincan da nadawo aiki ɗazun ki ɗaukar muku dubu biyar, sai ai muku har ƙunshi ko, dan sonake taje tsaf”.
      “Hakane Ummin mu, shiyyasa nake ji dake barci da ido biyu”.
       “ALLAH shirya minke Bilkisu, kindai maidani kakarki wlhy”.
      Dariya Bily ta fita tanayi da faɗin “Ni na isa Ummina.

         Ummukulsoom na zaune gaban Mirror tana rolling gyalen doguwar rigarta Bily ta shigo.
        “Hummm kaga ƴammatan yaya Zaid, irin wannan ƙyau haka”.
     Harara Ummu ta ɗago ta zabga mata, amma batace komaiba, Bily ta kwashe da dariya tana jingina da mirror ɗin, “Miye na hararata to? Kin zata ban harbo jirginku baneba shin?”.
      “Bakida man kai wlhy Bily, a’a garinmu kika harbo ba jirginmuba, idan kin shirya muje, idan kuma bazaki jeba nai gaba”.
       “Oh ga maganata ta fito, bama kwaso na biku dama ai, to duk tsiyarku sai naje”.
    Dariya Ummukulsoom tayi, ta ɗauki bag ɗinta tana faɗin “Ki sameni wajen Ummi parrot”.
       “Nice parrot ɗin?”.
“Kinmafi Parrot ai Bily”.         
          Bayan Bily ta gama shiryawa ta samu Ummukulsoom a wajen Ummi suna hoto, shiga tai itama akayi da ita sannan suka fita zuwa sashen maman Ahmad da itama taketa shirin komawa legas, amma anan zatabar Ahmad wajen Ummi, tare suka tafi wankin kan.
      Sai yamma lis suka dawo gidan, ammafa sunyi ƙyau sosai, barema Ummu datai kitso, sai fuskar ta ƙara fitowa fes da ita, dukda baza’ace takuma zama wata cikakkiyar maceba amma jikinta ya murje sosai, fatarta tayi wani irin ƙyau da kwanciya saboda bawani yawo takeba, kallo ɗaya zakai mata ka gamsu hankalinta a kwance yake, batada wata damuwa sai wadda ba’a rasaba.
     Hankalin Ummi saiya sake kwanciya dataga yanda Ummukulsoom ɗin tai ɗas, koba komai ƴan garin nasu bazasu taɓa samun hanyar yin ƙananun maganaba, dan babu wanda zai kalleta bai sake kalloba.

*_Washe gari_*

            Washe gari saiga Aziza itama, dan tare zasuyi tafiyar zuwa Ɗilau.
       Tsaf suka fito kamar ka sacesu ka gudu, haka kawai Ummukulsoom saita tsinci zuciyarta da fargaba, amma saita danne dan a yanzu bata buƙatar halin tsoro a rayuwarta, burinta akomanta ta zama jaruma, su ukune kaɗai zasuyi tafiyar, sai yaya Zaid dazai kaisu ya dawo, dan 1week zasuyi su dawo.
     Sunyi sallama da maman Ahmad, itama insha ALLAH gobe zata wuce Lagos ɗin.

         tunda suka tafi a motar Aziza da Bily ne kawai ke fira, sai Yaya Zaid dakan ɗan saka musu baki idan yaso, amma sam Ummukulsoom kamar bata ma a motar, sai kallon hanya take abinta, shirun natane dai kan ɗan saka yaya Zaid janta da hira lokaci-lokaci shima, a haka har suka isa Zaria, tsaraba ya ƙara musu ta kayan marmari sannan suka hau hanyar ɗilau bisa jagorancin Ummukulsoom………✍????

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button