NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 22

*_NO. 22_*


…………A falo Attahir ya iske Ummukulsoom da Bily suna hira, dukda dai bily ce mai firar Ummu tana dai tayata da murmushi da e ko a’a ne, dan tunani gaba ɗaya ya hana
zuciyarta sukuni.
      Sannu sukai masa ya zauna cikin kujera yana amsawa, da ido yayma Bily alamar ta tashi. Murmushi kawai tayi ta miƙe zuwa kicin.
      Attahir ya tattara dukkan hankalinsa akan Ummu da kanta ke ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, “Ummu ina fatandai komai lafiya? Gidan namu yana miki daɗi?”.
       Murmushin da baikai cikiba tai masa, kafin tace, “Komai Alhmdllh, kuma gidannan namin daɗi, musamman dattakon jama’ar gidan da ƙyawawan halinsu abin alfahari da koyi, sai dai kayi haƙuri, ina bukatar tafiya gida kodan iyayena susan halin danake ciki”.
     “Hakane, kema kinzo da magana mai ƙyau, amma kiyi haƙuri kiɗan bamu lokaci, dan Dad ma yace zaizo anjima. Dan ALLAH in tambayeki mana”.
      Kaɗan ta ɗago kai ta kallesa ta maida, “Ina saurarrenka”.
       “Please iya ina karatunki ya tsaya?”.
       “Secondary ne kawai”.
    Da tsantsar mamaki yake kallonta, “Wai Ummukulsoom dama kinyi karatu har zuwa secondary?”.
      “Eh Abban Ahmad ”.
Wani daɗine ya kama Attahir, danshi duk zatonsa Ummukulsoom bata wuce primary ba, a lallai aikin nasu mai sauƙine, cike da zumuɗi yace, “Kin amshi result nakine?”.
        “A’a gaskiya bankai ga karɓaba”.
     “Wannan mai sauƙine ai amaryarmu”.
    Karan farko da wannan sunan ya sosa zuciyarta har fuskarta ta nuna, Attahir dayaga yanda ta ɓata fuska sai yay murmushi yana miƙewa.
     Babu zato Ummu taji yace, “Ayi haƙuri bazan sake faɗaba, daga yau Ummukulsoom kawai”.
       Kunyace ta kama Ummu, dan batai zaton fuskarta ta tona asirin zuciyarta baneba.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

               Cikeda farin ciki ta shigo gidan nasu, dan daga kano take, turus taja ta tsaya a bakin ƙofar tana sauraren labarin da A’i kebama Momcy, wasu hawaye masu zafi suka gangaroma fuskarta batareda ta shiryama hakanba.
      “Momcy lallai kinyi kuskure mai girma”.
     Daga A’i har Momcy da basusan da shigowar aunty Nurse ba suka juyo  da sauri suna kallonta. Da hannu Momcy taima A’i alamar ta tashi taje, miƙewar kuwa tayi ta fito, amma saita maƙale jin gulma.
    Aunty Nurse taci gaba da takowa cikin ɗakin tana share hawayenta, “Yanzunan Momcy rayuwar ƴarki bata zama isharar kiyaye ƴaƴan wasuba kenan? Momcy da kanki kika saka Yaa Amaan sakin matarsa, miyasa? Mita tare miki ne? Kin manta raɗaɗi da ɗacin da kikaji a lokacin da Muzaffar ya sakeni bisa tursasawar mahaifiyarsa? Kin mance kukan da mukayi ni da ke da ƴan uwana? Zamana a gida matsayin bazawara baisa zuciyarki raunin tausayama yarinyar da bata tsare miki komaiba Momcy, acikin ƴaƴanki mata kaf ɗinmu Aunty Ummi ce kawai zaune gidan miji, gani ga Ummayya ga Aneesa ga Buhayyah dako yanzu aka mata aure saita zauna amma har kikaba shaiɗan damar ingizaki maida ƙaramar yarinya Bazawara, Momcy nasan kinyi amfani da ƙarfin ikonkine akan Yaa Amaan saboda kinsan bazai taɓa bijire mikiba, amma lallai shima ya tabbata saiyayi dana sani wlhy, kuma yayi asarar mace wadda inada yaƙini a raina bazai taɓa samun koda kwatankwacintaba…….”
      A zafafe Momcy ta daka mata tsawa, “Jalilah! Wane irin banzar fatane wannan, wlhy ki kiyayeni”.
       Ƙin amsawa Aunty Nurse tayi tama juya ta fice daga ɗakin, ko kallon A’i dake laɓe bataiba dukda kuwa ta ganta, akwatinta taja ta fice takoma motarta tabar gidan, dan yau tamaji gidan nasu gaba ɗaya ya fice mata a rai, duk kayan farin cikin data kwaso sai taji bata sha’awar juyesa anan kwata-kwata, gidan kakanninta ta tafi waɗanda suka haifi Momcy, saidai ƙin faɗa musu abinda ya faru tayi.

      Dukda jikin Momcy yayi sanyi da kalaman Aunty Nurse hakan baisa taji zata iya barin Ummukulsoom ta rayu da ɗantaba.

 ★★★★

     Duk abinda ke faruwa tsakanin Aunty Nurse da Momcy Dad na jinsu daga falonsa, murmushi kawai yayi wanda yakan daɗe arayuwarsa bai yisaba, musamman irin wannan dahar hakoransa farare tas suka bayyana, koda ya fito domin tafiya zuwa gidansu Attahir baiko kalli hanyar ɗakin matar tasa ba ya fice abinsa, su kansu yaran wasu a ciki suna falo zaune wasu kuma na ɗakunansu. Hannu kawai ya iya ɗaga musu koda suka gaisheshi.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

             Gidansu Attahir Isa direba ya kaisa, dukda kuwa yasan mahaifin su Attahir ɗin baya ƙasarma, amma ya kirasa sun tattauna akan batun Ummu kasancewarsa abokinsa tun barowarsa Ajiwa, kasuwanci ma tare sukeyi abinsu.
        A falon Alhaji Abubakar akai masa masauki, kasancewarsa ba baƙo bane a gidan.
       Ummi ta fara shiga suka gaisa, tareda tattaunawa itama akan batun Ummu ɗin, kafin atura masa Ummukulsoom.
      Tunda ta shigo falon sai kawai taji wasu hawaye na neman ɓalle mata, a gaban Dad ta zube a ƙasan carpet ta fara gaidashi cikin rawar murya.
     Shima tunda ta shigo idonsa na kanta, wani tausayinta na ratsasa.
     Yay ɗan gyaran murya yana kuma maida hankalinsa a kanta sosai, “Ummukulsoom badai kuka ba?”.
      ƙasa tai saurin yi da kanta hawayen na sakkowa.
     Nannauyan numfashi Alhaji Mahmud ya sauke, kafin yace, “Yanzu ba lokacin kuka baneba ɗiyata, lokacin sanin ciwon kaine, ni na haifi Fodio amma bazan taɓa hanaki damarkiba domin maida masa murtani, bana buƙatar jin abinda ya rabaku a yanzu, fatana kizama jaruma wajen neman abinda yake tunanin kin rasa kinji”.
         kanta ta ɗaga masa alamar amsawa tana share kwallar data zubo mata, “Baba to dan ALLAH inason komawa gida, kodan su baba susan halin da ake ciki suma”.
         “Ummukulsoom kenan, bazance miki a’a ba, bakuma zance miki eh ba, sai dai albishir dazan miki shine, Babanki yasan komai, dan ɗazun da rana mun haɗu dashi agidan innarki mun tattauna”.
      Cike da mamaki ummu ta kalleshi, cikin suɓucewar harshe tace, “Amma baba shine baice na koma gidaba”.
       Sosai ya kalleta shima yanzu, “Ummukulsoom ba komawarki gidane matsalarba, mutuncinki shine abin dubawa, kindai san miya faru kafin aurenki da Fodio, idan kin koma a matsayin bazawara wace kalar dariya kike tunanin za’ai miki da mahaifinki a wannan ƙauyen? Dama akwai masu jiran irin wannan ranar a gareki, waɗanda a kullum suke jifar babanki da kalmar saidaki yay gamasu kuɗi, ke yarinyace, sai nan gaba zaki fahimci abinda muka hango miki, ki kwantar da hankalinki kicigaba da zama anan gidan, yanzu haka an fara bincika miki makaranta”.
       Wani ɓangare na zuciyar Ummu a ƙuntace yake, wani gefen kuma yayi farin ciki da komawarta karatu, dan aganinta shine farkon tsanin nasara a alwashinta. Godiya ta shiga yima Alhaji Mahmud, yayinda kaunarsa keta ratsa ranta, samun irin waɗannan a cikin al’umma abune mai matuƙar wahala, irinsu Dad  sune jagororin masu kishin ƙasa da al’ummarsu na gaskiya, da ace irinsune suka yawaita a yankinmu da bamuyi kuka da attajiraiba da shugabanni.
       Dad yaji matuƙar daɗi ganin Ummu tabasu haɗinkai, ya saka mata albarka sosai kafin yay musu sallama ya tafi bayan yabata kwalin waya sabuwa fil da wasu ƴan kuɗi.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

           *_SABUWAR DUNIYA_*

       Dole mu kira wannan ƙaddara ta Ummukulsoom da suna sabuwar duniya, dan kuwa tazo mata da sauye-sauye na haƙiƙa, a sati ɗaya kacal datai gidansu Attahir harta fara canjawa, dan kowa a gidan ƙoƙarin canja damuwarta yake da farin ciki, Ummi tajata a jikinta sosai tamkar uwa mahaifiya, Bily kam amsa suna biyu takeyi, ƙawa kuma ƴar uwa, Attahir ya zama yaya hakama Zaid, saiko Uwa Uba Dad da Abba mahaifin su Attahir da tun dawowarsa gidan yaji wata tsantsar ƙaunar Ummukulsoom, tareda girgizar zuciya dayaji ainahin sunan garin da Ummukulsoom ta fito, ya daɗe yana maimaita sunan garin *ɗilau* a ransa, sai dai kuma ya haɗiye komai batareda yabar kowa ya fahimtaba.
        Abinda yakuma saka Ummu sakin jikinta da gidan shine zuwan Maman Ahmad, dan Attahir ya kawosu gida har sai an koma yajin aiki, sai kuma ga Aziza da Inna harira sunzo gidan ganin Ummu, daɗi ya kama Ummu matuƙa, harda kukanta kuwa, yini sukai a gidan ranar, Ummi tace a bar Aziza ta kwana biyu.
    Hakan yakuma sakama Ummu ƙaunar Ummi da ahalin gidan su Attahir gaba ɗaya.
     Haka suke haɗuwa ɓangaren maman Ahmad susha hirarsu idan Ummi ta wuce wajen aiki, Abba dama bai cika zamaba saboda yanayin business ɗimsa, hakama Zaid aiki kan hanashi sukuni, Attahir kuma tunda sukazo yanata cuku-cukun amso takardun Ummukulsoom a Zaria, dan so suke itada Bily su wuce makaranta, itama shekararta ɗaya da kammala secondary, saidai result ɗinta baiyi ƙyauba saida ta gyara a wannan shekarar.
        Yaa Amaan har gidan yazo ya gaida Ummi kamar yanda ya saba, dan shima yazo yin sallama gida akan tafiyarsu.
        Har yazo yatafi ma Ummu na barci a ranar, saida ta tashine Maman Ahmad ke sanar mata da Bily, baki ta taɓe tai tamkarma bata jisuba, dan ita a halin yanzu baya gabanta.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

              Tunda Amaan yazo kd yake samun gata ga Momcy kamar yanda ta saba a duk lokacin da yazo garin, inda sukuma su Bassam suka shiga tsantsar takura hatta da Ameer, ko kaɗan babu mai ƙwaƙwƙwaran motsi na jin daɗi, sai rayuwar gidanma ta canja, ƴan aiki suka sami ƴancin kansu dan babu mai musu kallon banza hatta da Momcy.
      Ko a fuska Dad bai nunama Yaa Amaan abinda yayba na sakin Ummukulsoom, baima bashi fuskar tado masa zancenba, abinka ga ɗan gado, shima saiya basar tamkar bai aikata komaiba, saima Momcy dake zungurarsa da zance, amma sam yaƙi biye mata, ko sau ɗaya yaƙi cewa komai game da zaman Ummu gidansa balle sakin nata.
      Momcy tasan zaimayi abinda yafi haka, dan hallayar Fodio sai dai du’ai kawai.
     Kwanansa goma a kd shida Attahir suka koma legos cikeda addu’ar ƴan uwansu da iyayensu.
      Ranar saboda jin daɗin tafiyarsa su Aneesa har ƙaramin perty suka haɗa, dama ga Dad baya nan yana Ajiwa shida Ameer, shi kansa Fodio saida yaje, dan yana matuƙar ƙaunar garin sosai.
      Momcy ce kawai taji kewar tafiyar ɗan nata mafi soyuwa a gareta, dan ranar yini tayi a gidan tamkar mai zazzaɓi.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

        Komai da ake buƙata na takardun Ummukulsoom Attahir bai tafiba saida ya kammalasu, yabarma Dad neman makarantar dasu Ummu ɗin zasu tafi.
         
*_BAYAN GAMA IDDAR UMMU_*

           Rayuwa mai juyi da sauyi, akwana a tashi kuma baida wahala a wajen ubangiji, musamman a wannan zamanin da babu abinda yakai lokaci gudu da sauri, zuwa yanzu tabon dake cin zuciyar Ummukulsoom yafara dasashewa, a da kam kullum dare sai tayi kuka,  ahankali tafara sabawa da sabuwar rayuwa tareda janye duk wani ƙududun mazaje biyu dake ranta tamkar rubutu bisa dutse.
       Rayuwar Ummu agidansu Attahir abin birgewa, hankalinta saiya kuma zama waje ɗaya bayan ta gama idda taje gidan Inna Harira ta kwana biyu sun gana da babanta, nasiha yay mata mai ratsa jiki tareda ƙarfafa mata gwiwa akan burin Alhaji Mahmud na tayi karatu, dan shima da farko bai yardaba, saida Dad yay masa bayani na gamsuwa sannan ya fahimci lallai a yanzu karatu shine gatanta, dan haka ya amince hundred percent.
       Ummukulsoom ta murmure sosai, jikinta ya fara dawowa, zuwa yanzu batada zumuɗin daya wuce su fara karatunsu, dan Islamiyyar data shiga inda Bily keyi saita kuma zaburar da ita amfanin ilimi, tareda jin ƙarfin gwiwar cikar burinta tunna farko tana ɗilau.
       gaba ɗaya ta shafe babin Amaan balle wani Baseer a ranta, takuma dunƙule maza tamusu kuɗin goro a yanzu, Dad da mahaifinta da Abba sai ko Attahir ne kawai sukaciri tuta mai girma a ranta.

       
★★★★★★

          Yau ta kasance asabar, shiyyasa kowa yana gida, maman Ahmad ma bata koma legas ba saboda makarantarsu basu koma yajin aiki ba har yanzun, su kansu su Ummu can ake jira su koma a samar musu, kasancewar Ummi batada ƴan aiki sai wata dattijuwa mai wanke-wanke kawai sai suka zage suka gyara ko ina tamkar yanda suka saba.
      Bily dake Morping ta riƙe ƙugu tana faɗin wash ALLAH na, ALLAH bayana kamar zai cire”.
     Baki Buɗe Ummukulsoom take kallonta, kafin tace, “Oni Ummu, wai Bily ke wace iriyar raguwace? Morping kawai kikema raki irin haka?”.
     Hararan wasa Bily ta mata tana zama a hannun kujera, “ALLAH bazaki ganeba Kulsoom, kefa shaidace akan wahalar da muka shawo jiya a kasuwa”.
       “Kai babie nan kina bani pepe wlhy, yanzu nan har ɗan yawon jiya yakai a kirashi wahala? ALLAH ya bama Yaya Zaid haƙuri dayayta yawo da kayan nauyi a hannu, kinga muyi sauri wlhy time ɗin islamiyya zai ƙure”.
       “Kai nifa yauma kamar karmuje islamiyyar nan wlhy, dama Ummi ta yarda muje gidan su Aziza musha weekend ma……..”
       “Mu kuma kubarmu shiru a gidan dagani sai Hafsat ko? Anƙi wayon”.
    Da sauri suka juyo jin maganar Ummi dake fitowa daga ɗakinta.
      Dariya sukayi suna durƙusawa suka gaisheta, ta amsa cike da fara’a tana kallon yaran nata tamkar tagwaye, ita badan karta zula ƙaryaba da tace har kama tame gani Ummukulsoom nayi da Bily da maigidan…..
     Bily ce ta katse tunanin Ummi da faɗin “Please Ummin mu, kingafa ga yaya Zaid ma yana gidafa, muma muɗan miƙe ƙafa muga gari dan ALLAH”.
       “Bily duk daɗin bakinki ƙyayi ki barni, indama yinine sainace kuje, muma sai muyi tafiyarmu gidan Hajiya yaya”.
      Da sauri Bily tace, “Mun yarda koma yini ɗinne ko Ummukulsoom ”.
       Murmushi Ummu tayi tana gyaɗa kai alamar amsawa.
      Ummi tayi dariya tana faɗin “Ok, saiku shirya Zaid ya kaiku, amma islamiyya fa? Bilkisu banason baƙin yawonki yasaki faramin wasa da karatun yarinya”.
     “Kai Ummi ALLAH a’a, itamafa tanason zuwa”.
      Cike da tsokana Ummu tace, “Nidai a’a banaso Ummi, muje islamiyyar mu kawa……”
    Cikin wani tsalle Bily ta isa gaban Ummu tareda rufe mata baki da hannu alamar karta ƙarasa.
     Dariya Ummi da Yaya Zaid dake shigowa suka sanya musu.
      Yaya Zaid ya ƙarasa wajen cin abinci yana faɗin “ALLAH Ummi karki bari Bily ta koyama Ummukhoolsum baƙin yawonta da tamkar anmata ƙauri da ƙafafun kare”.
      Baki bily ta turo gaba tana kallon Ummu, “Yanzu kin yarda ashiga tsakaninmu kenan?”.
      Dariya Ummu da Ummi sukayi, Ummu tace, “Inafa zan yarda, ai ko saɓani haka ya ganmu ya barmu tawajena”.
       “To aiko saidai kufita anguwar a Napep” cewar yaya zaid yana musu harar wasa.
      Ummi dake ƙarawa inda yake tace, “A’a ba ayi hakaba Yaya Zaid, gwiwar autocina bisa ƙasa, sun tuba”.
      “Ummi karki nemar musu alfarma, gara kibarsu su ɗana suji, dama ni inada gun zuwa”.
      Ummukulsoom tai saurin cewa, “Yi haƙuri Yaya Zaid, karmuje a sake irin ta wancan karon muka ɓata”.
       “Ai hakan shine dai-dai daku ma”.
      Haka suka cigaba da hirarsu suna shirin yin breakfast har maman Ahmad ta shigo itama, da gudu Ahmad ya nufi Ummi kasan cewar kakar tasa na matuƙar sonsa.
         Itama zama tai suka cigaba da breakfast ɗin har suka kammala Ummu da Bily suka gyara wajen, kafin kowa yanufi ɗaki ya shirya.
         Ummi da maman Ahmad ne suka fara tafiya gidan hajiya yaya suka bar su Bily na jiran fitowar yaya zaid a harabar gidan. 
    Tunda ya fito idonsa nakan Ummukulsoom da tai ƙyau cikin sket da riga na shadda pink, sai dai kuma ta saka hijjab mai hannu, dukda babu kwalliya a fuskarta sai tayi ƙyau sosai.
    Ɗauke kanta tayi dan batason yana mata wannan kalon, shima sai yay murmushi kawai yana musu nuni dasu shiga mota.
      Da sauri Bily ta shige baya ta kulle, hararta Ummu tayi ta buɗe gaban ta shiga badan tasoba.
      Ta mirror bily tai mata gwalo, dan tasan ta tsani zaman gaban mota dama.
        Yaya Zaid na tafiya yana jan Ummu da hira, itako iyakarta murmushi, dama bata sakin jiki dashi inba taga Ummi a wajenba, har ƙofar gidan su Aziza ya kaisu, daɗi ya kama Aziza sosai da inna harira. Bayan Zaid ya shiga sun gaisa komawa yay ya barsu nan………✍????




*_Nagode da addu’oinku gareni ALLAH yabar zuminci_*????????????????



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button