NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 24

*_NO. 24_*


……….Babu abinda ya sauya mata a garin a kusan shekara ɗaya da bata ciki, sai dai gine-gine da aka ƙara na jar ƙasa alamun dai matasan garin
sunsha aurarraki, sanin babanta na gida yasata nunama Zaid hanyar da zata kaisu babban gida, yara saibin motar suke da gudu dukda basusan wanene a cikiba.
       Sai suka bama Ummu tausayi, duk wanda ya rayu a ƙauye yasamu wani cigaba dolene ya tausayama waɗanda suke a ciki, bawai dan suna cikin ƙunciba ko koma baya na rayuwa, a’a sai dan kawai suna rayuwane tamkar shugabanni sun manta dasune, ka shekara goma bakaje ƙauyenkuba idan kaje saika tarar babu wani canji da aka samu, idan kayi wasama saikaga ankuma samun taɓarɓarewane.
        Tunda Ummukulsoom suka fito yaran dake binsu sukai cirko-cirko suna kallonsu, hakama manya dake cikin inuwoyi zaune ana zaman gulmar mata sai duk suka zubo musu ido.
     Mariya ce data dawo daga ɗibar ruwa rafi tai tozali da Ummukulsoom, cikin ƙaraji tace, “La’ila, yaya Umma”.
       Hakan da tayine ya fargar da waɗanda basu gane Ummu ba, Ummu na kiranta amma tuni tayi cikin gida kai rahoto.
     Kafin kace mi an zagaye su Ummukulsoom har mata na leƙe ta katanga kowa burinsa yaga Ummukulsoom yata komane.
    Itako sai zuba musu murmushi takeyi, fuskarta a washe take tarbar kowa.
     Duk sun ɗauka Zaid ne mijinta, dan danan aka bashi masauki, Ummu tashiga matuƙar mamakin tarbar da suka samu gasu baba yalwa, kafin kacemi ƙauyen ya ɗauki zuwan Ummukulsoom. Ƴan gidan kam sai kawo musu abinci ake da fura, sunci iya abinda zasu iya ci, Bily sai daɗi takeji, harga ALLAH garin yamata sosai.
      Da yawan ƴan gidansu Ummu jikinsu yayi sanyi da ganin yanda Ummukulsoom ɗin takuma canjawa, ta murje tayi ras da ita, saidai fa dukda hakan sunata ƙananun gulma wai babu komai (Ciki????).
         
     Lokacin da Ummu ta fito zasuma yaya Zaid rakkiya gidan Gwaggo hinde ya gaisheta sai mata ke leƙensu ta katanga, oho sudai basusan anaiba, gashi abindama zai ƙara ɗaukar hankalinka, da Ummu suka tafi jere da Zaid ɗin, Bily kuwa da Aziza suna gabansu, duk Aziza ce da shirinnan, dan fatanta karsu bada wata ɓaraka da wani zai fahimci Ummukulsoom batada aure yanzu.
     Shiko Zaid da hakan yay masa daɗi sai jan Ummukulsoom yake da hira akan mizai shirya musu kafin su dawo na tafiya makaranta, wannan ne yasata biye masa harda murmushin dake narkar da mazan garin.

      Gwaggo hinde na tsakar gida a garken dabbobi tana basu ruwan tsari su Ummu sukai sallama, dukda an sanar mata da zuwansu saida taji wani irin daɗi, sai dai kuma a lokacin da take ma su Ummukulsoom lalale marhabun sai idonta ya sauka akan Zaid dake shigowa a ƙarshe, gabantane yay tsananin faɗuwa, tai kasaƙe tana kallonsa baki a hangame.
       Daga Bily har Ummu har Aziza duk juyawa sukai suma suna kallon abinda Gwaggo hinden ke kallo,  ganin Zaid sai duk suka juyo gareta.
        Ummukulsoom ta karasa inda take taɗan girgiza hannunta, ”Gwaggo! Kin ko baƙya murna da zuwan nawa na koma?”.
     Ajiyar zuciya Gwaggo hinde ta sauke, kafin tai murmushi tana canja zancen da faɗin, “Sannunku da zuwa amarya, kumuje ciki mana, angona lalale marhabun (tazata Zaid ne mijin Ummu itama).
         Zaid da duk yasha jinin jikinsa da kallon Gwaggo hinde yay murmushin yaƙe yana amsata.
      Koda suka zauna a tabarmar da Gwaggo hinde ta samusu gindin bishshiyar mangwaro dake gidan sai bin Bily da Zaid take da yawan kallo a sace, Ummu da Zaid ne kawai suka lura da hakan, amma dai basuce komaiba duk da shima Zaid mamakin kamannin Gwaggo yake da Abbansu, sai dai ita tsufa daya kamata.
      Bayan an gaggaisa sukasha ruwan da Gwaggo ta ajiye musu sai aka hau ƴar hira, musamman tsokanar Ummu da gwaggon keyi akan ina zatakai jiki?, watanni kaɗan hartayi irin wannan canjawar, Mi Zaid ke batane? Itama a kawo mata nata kar kishiya tafita a wajensa.
      Dariya kawai Zaid kema Gwaggo dajin wani nishaɗi a ransa, inama ace zancen Gwaggo zai tabbata daya zama cikin masu sa’a, saidai gefen zuciyarsa na mamakin shin Ummu ta taɓa aurene? Dansu babu wanda yama taɓa sanar musu komai akan dalilin zaman Ummukulsoom gidansu shi da Bily, dukda ita bily takanji maman Ahmad na ambatar sunan Amaan ɗin bata taɓa sanin matsayinsaba a wajen Ummu, bama ta zata yaya Amaan na gidansu Buhayyah ba.
        Sunsha har zuwa biyar na yamma Zaid yayma gwaggo alkairi suka rakoshi har mota tanata saka masa albarka da fatan saukarsa lafiya, anan aka sauke kayan su Ummu tareda tsarabar gwaggo yatafi cikeda kewar Ummu da Bily, tareda alwashin dawowa ya kwana garin dan yamasa daɗi sosai.
     Su Ummu kuwa nan suka dawo suka cigaba dashan hirarsu, sai dare taje babban gida itada Aziza, dan Bily maƙalewa tai wai ita tana gidan Gwaggo suje su dawo.
      Acan su Ummu sukasha hirarsu da baba saida suka farajin barcine suka dawo gidan Gwaggo, dan baba cayay su kwana acan safi samun sakewa.
       Gwaggo kuwa tanata jan Bily da hira cikin hikima, dan ganin Zaid ya tada mata wani tsohon tabonta, hakama kamannin Ummu da Bily wanda saika daɗe tare dasu zaka fahimci hakan.
      Bily batasan dawan garinba, duk tambayar da Gwaggo tai mata itadai kai tsaye take amsa mata harsu Ummukulsoom suka dawo gidan.  


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

          “Wow ga wata kaya fa alhaji tana tunkaromu”.
       Baseer dake zaune a mota yana latsa waya ya ɗago ido a sace yana kallon zankaɗeɗiyar yarinyar fara tas, motar da aka buɗe mata ta fitoma kawai abar kalloce.
    Karon farko a rayuwar Baseer dayaji son mace na gaskiya a ransa bayan Ummukulsoom, ya cije leɓe da ƙarfi yana binta da kallo harta shige wajen hutawar.
       Hafez sabon abokinsa da shima yake binta da kallo sake da baki ya sauke sassanyar ajiyar zuciya yana maido kallonsa ga baseer daketa kokawa da busashshen yawu a maƙoshi.
       “Bas abari ya hucefa”.
      Da ƙyar Baseer ya iya faɗin “Abokina shike kawo rabon wani, amma muja aji”.
     “Aji kuma? Yo kai mace ne? Ai irin waɗannan ina faɗa maka idan bakai ka tayaba saika ƙaraci haɗiyar yawunka ko kallo baka ishesuba, kaidai tashi muje kawai”.
      Fitowa Baseer yayi bayan yakuma fesa turare tun a mota ya goge fuskarsa sosai, nufar wajen sukai shida Hafiz suna tafiya ɗai-ɗai tareda basarwa dan shima Hafiz ɗin masha ALLAH ƙyaƙyƙyawane.
       Tunda suka shigo wajen suke baje ido amma ko alamarta basu ganiba, nanfa suka shiga zagaye-zagaye amma babu ita, fitowa sukayi waje sai sukaga motar tatama babu.
      Kowannensu yay tsirmai-tsirmai da idanu sunma rasa a yanda zasu fassara abun, kamar ance Baseer ya ɗaga ido saiya hango motarsu can saman titi, da sauri ya bugi kafaɗar Hafiz ya nuna masa motar.
      Ido Hafiz yaɗan zaro, “Bas wai yaushema ta shiga  motar to?”.
        “Ƴar dariya Baseer yay, “Wato kasan mina fahimta kuwa?, ba wajennan ta shigaba, wancan shagon ɗinkin ta shiga kasan akwai ƙofa tacan baya, wannan kuma kamar ba kowa yasan da itaba”.
       “Kumafa maganarka gaskiyace wlhy Bas, yanzu yaya za’ai kenan?”.
        “Wai kai tsayama dai, sonta kake komi?”.
       “Sosaima ko” cewar Hafiz.
      Wata banzar harara Baseer yay masa yana faɗin “bakada mankai wlhy, kwana nawa bikinka ya rage da Aysha, wannan kayanace”.
           Hafiz yace, “Babu komai saina barmaka, amma wlhy nakamu fa”.

       Tun wannan gani da Baseer sukaima wannan budurwa hankalinsa ya kasa kwanciya, kullum cikin tunanin ina zai ganta yake, ahaka suka shiga shagalin bikin Hafiz.
        Ranar Dinner ana tsaka da raƙwashewa saiga yarinyarnan yagani, itama kuma tun shigowarta wajen da Baseer ta fara tozali dake zaune kusa da ango.
        “Meenal wai mikike kallone haka?”.
     Sassanyan murmushi tayi tareda juyowa ta kalli mai maganar, “Zakiyya na macene, dan ALLAH kalla guy ɗincan”.
     Kallon tsaf Zakiyya tamasa tana jinjina kanta, banga laifinkiba babie, komai yaji kama, sai dai irin waɗannanfa mata bazasu barki ki hutaba saboda bibiyarsa”.
      “Karki damu Zakiyya, indai nasamu zan adana yazama nawa ni kaɗai”.
      “Nasan zaki iya kam, amma batun rashin son zama 9ja fa?”.
      “Saina fara bincike a kansa, idan mai bine saimu tafi, idan kuma sai an bisa babu matsala zanyi manage”. 
      “ALLAH ya taimaka ƙawata, batun ƙulla alaƙa fa?”.
      “Ga katina ki bashi, idan yazo da wulaƙanci to lallai ɗan manyane, idan ya karɓa da hannu biyu zamu sama masa ajin karatu”.
      Dariya zakiyya tayi kafin ta maida kallonta ga Baseer, ita kanta badan ƙawarta tayi shigar sauriba data shiga daga ciki, amma babu komai, ai akwai bayan katanga.
        A wajen liƙine Baseer da Meenal suka haɗu, sunama amarya da ango sai suka koma yima junansu kowanne na jifan ɗan uwansa da murmushi, tun a wajen alaƙa tafara ƙulluwa, musamman da amaryar Baseer ta gabatar musu da Meenal matsayin yaya.
      An tashi taron biki lafiya tareda alaƙa mai ƙarfi tsakanin Baseer da Meenal.⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡.

             Sosai su Ummukulsoom kejin daɗin ɗilau, sai faman zaga gari suke suna yawo, gidan murja kam ai nanne gidan hutawarsu, tai musu wannan tai musu wannan, Ummu na ƙaunar Murja sosai, dan zumincinsu akwai shaƙuwa acikinsa na haƙiƙa.
       Kwanansu huɗu a ɗilau sukaje wajen Nusaiba itama, hakama Azima, bakaramin rikicewa da sauyar Ummu sukaiba, sukam duk sun fara zama wasu mama, musamman ma Azima daba jin daɗin zaman takeba yanzu saboda kishiya, tausayinsu saiya cika zuciyar Ummu, takaraji. ƙarfin gwiwa akan nutsuwa taci gaba da karatunta.

       Gaba ɗaya kwanansu takwas a ɗilau Yaya Zaid yaje ya kwasosu suka dawo kaduna.
       Ummi tayi murna da ganin yaran nata, dama tanata kewarsu, ga maman Ahmad itama ta wuce tuni.
     Suma dai dawowar tasu duksai ta kasance ta shirye-shirye, duk abinda zasu buƙata angama kimtsa musu shi, Ummi duk sai taji kamarma ta hanasu tafiyar, amma dai tanason babies ɗinta suyi karatu kuma ai.
        Ana gobe zasu tafi Dad yazo gidan, haɗuwa sukai shida Abba sukai musu nasiha mai ratsa jiki akan su kare mutunci su, karsuyi wasa da addininsu dansunje ciki. kabilun da addini ya banbantasu, su zama ƴaƴa nagari, suje suyi abinda yakaisu shine abinda aka turasu.
       Sosai su Ummukulsoom sukaita share hawaye, danda kallon abun sukeyi kamar wasan yara, ashedai tafiyar ta gaskece..
     Da daddare yaya Zaid yakaisu gidan inna harira sukai mata sallama, canma kamar karsu rabu da Aziza sukaji, sai kusan 11 suka dawo gida……….✍????
Kuyi manage da wannan Please????????⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀ 
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button