NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 25

_NO. 25_*


        ………..“Abba fodio wai dan ALLAH har yanzu kana akan bakanka gameda aurensu Ummayya?”.
      Yi yay tamkarma bai jitaba, hankalinsa kwance yake kallon labarai a NTA.

     Ta sake maimaita maganar a karo na biyu.
      Wata lalatacciyar harara ya zabga mata yana kuma tamke fuska, “Jamila! Amma dai kinsan halina ko? Kinsan banason rainin arziki ko? Tom kici gaba”. Yay kwafa yana miƙewa yabarta a falon.
     Tsan tsar tashin hankaline yakuma bayyana a fuskarta, a gaba ɗaya kwanakin nan batada wani dogon sukuni, ba auren su Ummayya bane kawai damuwarta harda maganar buƙatar ɗakunansu daya tofa, tama rasa a yanda zata fassara zancen nasa, dan tunaninta da fassararta mugun abu yake bata, wato Alhaji Mahmud zai ƙara aure. Zabura tai tsaye tana faɗin, “kai ina bama haka baneba, da zaiyi dayayi tun munada ƙuruciya”. Gaba ɗaya ta susuce. Mansura ƙanwarta ta kira, amma saitace mata ta jirayi zuwanta ƙarshen satin sama, dan yanzu maigidanta yana gari.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

       Su Ummu sai shartar hawaye ake itada Bily, sunbi sun kanainaye jikin Ummi suna mata shagwaɓa, Abba da suka bashi dariya saiya murmusa yana faɗin, “Autocin Ummi ayi hakuri, wannan shine ake kira da neman ilimin ko a birnin sin, fatanmu dai ku kasance masu nasara, nanda wasu shekaru muga lauya da ma’aikaciyar banki a gidanmu”.
     Murmushi duk sukayi masa, suna ɗaga kawunansu da share hawaye.
      Yaya Zaid dake musu dariya ya miƙe yana faɗin, “ALLAH yabamu haƙuri muda aka tura wata ƙasa tsawon shekaru, ALLAH Abba kubar ƙara shagwaɓasu ma, dan tafiya port dolene yau, muna dawowa muci daɗinmu dagani sai my Ahmadi na, ko my boy”. Yaƙare maganar da jawo Ahmad jikinsa.
     Hararsa Ummi tayi tana nuna masa hanya, Ummukulsoom da Bily kuwa suka kumburo baki suna kuma matso hawaye, hakan saiya saka Abba dariya, ya kama hanyar fita yana faɗin, “Kunga kufito jirgin da zamubifa ya kusa tashi”.
      Miƙewa sukai har Ummi suka fito, dayake duk gidan zasuyi musu rakkiya, Abba ya kama hannun Ahmad da shima yay laƙe yana kallonsu dukda bai fahimci miza’ayiba.
    ko a mota yaya zaid sai tsokanarsu yake, amma sunƙi kulashi, suna lafe a jikin Ummi abinsu.

★★★★★

        Karo na biyu Ummukulsoom a jirgi, saidai wannan lokaci yazo da cigaba, dan zuciyarta tsaye take babu wani ƙauyanci ko tsoro a ranta, hirarsu ma sukeyi itada Bily a hankali.

      Jirginsu na sauka suka sami tarba ta musamman daga abokin Abba Mrs Alabo, ɗan asalin Abiloma L.G. ne, yaren Calaberi ne na asali.
     Tare yake da iyalansa, matarsa mai suna Miss Ibiso, sai ƴaƴansa Uku, akwai babbar budurwa mai suna Blessing, sai mai bimata namiji Dakubo, sai kuma matashiya budurwa kamarsu Ummu mai suna Peace.
           Kwasarsu sukai zuwa anguwarsu dake Bony street hausa line, anguwar ta burge su Ummukulsoom, babu wata hayaniya, gata tsaf, gidane madaidaici mai ƙyau da ƙayatarwa, dankuwa daka gansa kasan an kashe ƴan canji, komai abin birgewa, dan danan aka cikama su Ummu gabansu da abinci da kayan ciye-ciye.
     Yanda Abba ke fira da Mrs Alabo Zai tabbatar maka da akwai sanayya mai ƙarfi a tsakaninsu, hakan saiya birge Ummukulsoom da bily, tuni suma suka saki jikinsu da yaran, sai daifa Bily ce mai maganar, Ummu bakomai take fahimtaba kasancewar turanci sukeyi.

           Bayan sun huta sai suka shirya zuwa makarantar, duk abinda ya dace akuma yimusu Abba saida yayi, kafin su dawo gidan Mrs Alabo akan ranar Monday su Ummu zasu fara lectures, Ummukulsoom dai kallon abun take tamkar wani mafarki ko almara, sai dai tana ƙarfafa zuciyarta bisaga raunin dataga tana neman faɗawa.
        A ranar Abba da Ummi da yaya Zaid da Ahmad suka juya, har airport suka sake rakasu, saida sukaga tashinsu suka dawo gidan.
       A ranar dai kam su Bily sunyi baƙunta kasancewar akwai rashin sabo, amma yanda Peace taketa shige musu a jiki sai suka fara sakewa, gashi kuma duk jama’ar gidan basuda matsala, duk da kasancewarsu ba musulmai ba hakan bai hana su Ummukulsoom yin ibadarsu cikin kwanciyar hankali ba.

        A kwanaki Uku kacal su Ummu suka gama zama ƴan gida, sun saki jikinsu sosai, yin komai suke tamkar gidansu.
       A ranar Monday kuwa tunda wuri sukai shirin tafiya makaranta, kasancewar itama Peace Can takeyi bama ta daɗe da farawaba sai suka samu ƙwarin gwiwar tafiya hankali kwance.
      Daga Bily har Ummukulsoom shigar dogayen ruguna Arabian gown sukai, ta bily baƙa da adon stones honey color, ta Ummukulsoom ma baƙa da adon fararen stones, sosai sukai ƙyau, saikace tagwaye, haske kawai Bily zata gwadama Ummukulsoom.
      Peace data fito cikin dogon wando da t-sheat sai taita kallonsu, dansun birgeta sosai, hakanma saiya sata komawa ta ɗakko siririn gyale ta kawo wai itama sumata irin rolling ɗin dasukayi da gyalen jallabiyarsu.
      Ummukulsoom ta karɓa tamata, dama ita tama bily ma.
        Dakubo Yayan Peace Shine ya ɗaukesu amota zuwa school, dama shima canɗin dai yakeyi, yanama shekarar ƙarshene shi.
     Suna tafiya Peace Na nuna musu abubuwa, suko sai ware ido suke suna kallo da haddacewa.

      *_BABU NAKASASHSHE SAI KASASHSHE_* Cewar Ummukulsoom data tsinci kanta a gaban lecturer cikin hall yana zuba musu lecture, ba abu ɗaya zasu karanta ba itada Bily, dan kowa akwai burinsa, a ganinsu kuma hakanne zai basu damar maida hankali akan abinda ya kawosu.
      A ranar sai 5pm sukabar school suka koma gida, tun a mota kowa kebama ɗan uwansa labarin abunda akayi peace nata musu dariya musamman yanda Ummukulsoom ta dage tana haɗo turanci, dan acewarta ahakane zata iya har tayi kamar kowa wataran.
     Sun iske gidan babu kowa, Mom da Blessing Sunje Choch, Daddy kuma bai dawo aikiba.
      Kai tsaye ɗakinsu suka nufa, kowa yashiga warware gyalen kansa, kafin Ummukulsoom tai saurin shigewa bathroom tana dariya akan zata rigasu yin wanka.
        Suma cikin dariyar suke faɗa mata zasu ramane, ta ɗauka yau ranartace.
        Gaba ɗaya yau cikin nishaɗi Ummukulsoom take, kallo ɗaya zakai mata kuma ka fahimci hakan, koda sukai waya da Ummi bayan sun idar da sallar magriba saida ta fahimci haka, shiyyasa itama sai taji zuciyarta takuma sanyaya akan kewarsu.
          Suna ajiyewa Yaya Zaid shima ya kira yay musu fatan alkairin farawa a sa’a, Abba dai bama ya kasar.
    Saiga Maman Ahmad ma takira, hira da itane yajasu tsawon lokaci, dan sunata bata labari daki-daki, yayinda take kuma ƙarfafa musu gwiwa musamman Ummukulsoom dakeda tabo a zuci.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

            Cikin wani murmushin iya bariki Meenal take kallon Baseer dake gabanta, ta juya idanunta cike da salo tana tauna cingam yana bada ƙara ƙass! Ƙasss!!, “My Boo kenan, aini duk abinda naso bana masa ruƙon sakainar kashi, karkasha mamaki akan son danake maka, sai daifa a aurenmu akwai sharaɗi mai girman gaske”.
     Cikin faɗaɗa murmushinsa yace, “Minene sharaɗin?”.
       “Banason zama da kishiya, banason yaudara, banason ƙarya, banason ha’inci, idan harka kiyaye wannan zan mallaka maka dukkan kaina da dukiyata harda ragamar iko dani”.
       Saida ya jinjina maganar sosai kafin yay murmushi, “indai wannan ne bakida matsala dani, dukna ɗauka kuma insha ALLAHU zaki sameni yanda kikeso”.
      “To Alhmdllhi my Boo, abu nagaba shine karabu da dukkan ƴammatanka, sannan bayan munyi aure bazamu zauna a Nigeria ba, yanzu haka bikin Aysha ne ya kawoni dole, sai kuma haɗuwa dakai daya riƙeni gam, kamar yanda nasar maka Abbana shine Ambassador na Nigeria a ƙasar Frace, so kuma dama can acan kusan muke gaskiya tunkan hakan ta faru, amma idan baka ra’ayin zama can nimai haƙurice mu rayu anan ɗin….”
      Da sauri Baseer yace, “Haba dear, mizai hana nabi zaɓinki, wlhy ni na amince koma inane muyita tafiya kawai”.
      Wani tsadajjen murmushi tai masa tana faɗin, “Ok, kayi ƙyan kai kuwa, sai dai gaskiya zamanmu bazai wuce shekaru biyu ba zamu dawo Nigeria kawai, badan komaiba sai dan cikar wani buri na mahaifina, dan yanason neman takarar gwamna”.
     Wani daɗine yakuma ratsa ransa, dan haka ya murmusa tareda cewa “ALLAH ya tabbatar mana da hakan”.
     “Amin My Boo, so yanzu dai nabaka dama akan ka tsara yanda komai zai kasance, nima insha ALLAH zan tsara na turama Abbana dukkan bayanan”.
        Nanma murmushi yayi, kafin su mike tayo masa rakki har mota, bayan ta buɗe masa ya shiga ta manna masa kiss a kumatu.
     Idanu ya lumshe wani daɗi na ratsa ransa, lallai yanzune aka dace ashe, dakam kansa a tukunya.

        Gaba ɗaya Baseer ya susuce akan Meenal, babu abinda yake sai tunani akan ya sanar mata gaskiyane kokuwa ya ɓoye? gaba ɗaya Lubna da Fannah sun gaza gane kansa, ita Lubna ma ana tsaka da wannan sauyawar ta Baseer babban tashin hankalin rasuwar mahaifinsu ya risketa.
     Wannan yasakata tattara komansa ta watsar, rashin mahaifinta ya taɓa dukkan rayuwarta.
     Zuwan Baseer biyu gidan yabar zuwa, danshi a yanzu ta matsalarsa da Meenal yake, yagama yanke hukuncin sanar mata da komai gameda asalinsa, maybe hakan zaisa tafi sakin jiki dashi da ƙaunarsa, danshi harga ALLAH son gaskiya yake mata babu nufin yaudara ko kaɗan a ransa.

      A haɗuwar da sukai ta yau ya zauna yasanar mata komai gameda asalinsa, saidaifa baice mata ya taɓa aureba.
     Ta jinjina zancen ƙwarai da gaske a ranta, amma saitaji tama samu ƙwarin gwiwar aurensa.
     A washe gari Baseer yakama hanyar Ɗilau.
      Babu wanda yay mamakin zuwansa a cikin iyayensa, dansu yanzu kam lamarinsa sun maidashi gefe.
       Bai samu zama dasuba sai dare, dukkan abinda yazo dashi gameda aurensa da meenal ya fayyace musu, sannan ya sanar musu ya rabu da Suhailat saboda yaga danginta ba mutanen arziki bane, yakuma roki su yafe masa bazai sake aikata kuskuren da yayba a farko na wofantar dasu, a yanzu tsakaninsa ga ALLAH yakeson meenal take sonsa, shiyyasama ya sanar mata gaskiyar shiɗin wanene.
      Duk da baba bai aminta dashiba ya jinjina zancesa sosai a rai, dan haka yace indai hakane to ya tattaro ya dawo gida, sannan zai tura da kansa zuwa nan auren meenal din, inhar aka wulakantasu to lallai yasani wlhy bazai auretaba, idan kuma ya bijire musu a wannan karon to zasu sallamasa gaba ɗaya.
      Duk da jikinsu yay sanyi da kalamansu ya amince da hakan, dan wlhy a wannan karon jiyake idan basu aminceba zai iya barin duniyarma gaba ɗaya.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

           Ummayya da Aneesa sun kawoma Dad miji kamar yanda ya umarta, shiko ya amsa tareda shiga yin bincike akan mazajen nasu, shidai baiga wata matsalaba a wajen samarin nasu, dan haka yabasu damar turowa.
     Cikin ƙankanin lokaci komai ya kammala, aka tsaida ranar biki dai-dai da ɗaurin auren Aunty Nurse.

     Momcy na murna zata aurar da ƴaƴanta, sannan tana fargabar kalmar dad ta jiran daki, danma dai Mansura nata dannarta da nuna mata tabisa ta makirci.
     Dad duk yana lura da halin da take ciki, amma yay biris da ita yashiga hidimar fita kunyar ƴaƴansa.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

          Su Ummukulsoom ƴan jami’a, karatu ake babu kama hannun yaro, yayinda suke ƙara samun ilimin zaman duniya da zama da jama’a. Zuwa yanzu kam turanci yafara zama bakinta, dayake akwai kaifin ƙwaƙwalwa ga burin na neman cikar alwashinta, kasancewarta mace mai murjajjen jiki saita kuma ƙara ɗan buɗewa, tai wata ƴar kuɓul-kuɓul da ita, kayan da Yaa Amaan yakira na ƙwaila suka fara cikowa ɗas.
     Koda yaushe tana waya da kowanta, Babanta, Aziza, inna harira, Gwaggo hinde idan baba yaje ɗilau, hakama ƴan uwanta inhar baba na ɗilau, Ummi, Maman Ahmad, yaya zaid danma shi bata wani sakar masa jiki saboda a salon da yake zuwa mata.

     
 ⛹????‍♀️ Ummukulsoom ɗinmu ta mutunci acigaba da gashi????????????


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

         Shagalin biki a gidan Dad ya kankama, dankuwa nanda kwanaki Huɗu za’a ɗaura auren yaya Ameer, Ummayya, Aneesa da aunty Nurse.
     Kowa kagani yana tare da farin ciki, sai dai Hajiya Jamila nata kam akwai rauni, tanata dai yaƙe a fuska.
       Duk wani abun ƴan gata shi ake musu, hakanne yasakasu jinsu a sama.
        Duk wasu bidi’oi anyisu, kasancewar su Momcy ƴan abama bidi’a haƙintane babu algus????.
         Ummi ma duk tana halartar bikin, hakama yaya zaid daya kasance abokin Yaya Ameer.
       Ranar ɗaurin aure aka ɗaura na aunty Nurse sannan Ummayya sai Aneesa. Zuwa sallar zuhur aka ɗauro na Ameer shima da tasa amaryar.
        Aranar aka kai amare ɗakunansu bayan an halarci dinner ɗin da Yaa Amaan ya ɗauki nauyin yi dukda baya ƙasar, wayama saiya shari wata biyu basuyi da waniba saboda yanayin da suke ciki a ƙasar Syria, sunata fama da ƴan ta’adda abin babu sauki.
        Aunty Nurse ce dai bata tareba sai bayan kwanaki biyar da gama nasu Ummayya, batawani yi taroba, mijinta Abdul-hakeem yazo ya ɗauketa bayan Dad yay musu nasiha mai ratsa jiki da addu’ar zaman lafiya, sannan yayma ƴarsa rakkiya har gidanta itada mijinta a garin Abuja.

     Zuwa yanzu dai gida yadawo tsitt, daga Momcy sai Dad da Buhayyah, Bassam ma ana gama biki yakoma Kano makaranta.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

         Ɓangaren Baseer ma zamu iya cewa burinsa ya cika, dan kuwa a wannan karon iyayen Meenal sunsha banban da sauran surukansa, tarba ta girmamawa sukaima su baba da sukaje masa neman aure, hakanne yasaka zukatansu kwanciya waje ɗaya har aka tsaida ranar ɗaurin aure.
          Wata ɗaya da Sati biyu na cika aka ɗaura masa aure da Meenal ɗinsa ƴar mutan katsinawa, wadda acan aka ɗauro auren.
        Lubna da Fannah da basusan abinda ke faruwaba saidai sukai karo da text massege nashi kowacce da zanen saki biyu.
     Lallai sun tsinci kansu a matuƙar tashin hankali, dan aranar Fannah a asibiti ta kwana, Lubna kam ai ba’a magana, ga tabon rashin mahaifi gana Baseer, duk Number sa data sani saida aka nema, amma dukya karya layukan, tashin hankalin rashin mahaifinsune ya hana yayyenta maida hankali ga matsalar Baseer ɗin, kowa yayta lallashinta, ga yarsu daya barmata.

        An ɗaura aure da kwanaki biyu Baseer suka ɗage paris shida amaryarsa Meenal.
      A wannan karon kam hankali baba da inna yaɗan kwanta, hakanne yasa basu damu da tafiyar ta baseer ba, fatansu dai ALLAH yasa dattakon iyayen Meenal yazama silar nitsuwarsa waje ɗaya kawai…………✍????


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button