NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 29

_NO. 29_*


……….“Bestie wai duk gajiyarce haka?”.
          Guntun Murmushi Ummukulsoom dake kwance a kan gado tun ɗazun tayima bily mai maganar tareda miƙewa zaune tana ɗan sauke numfashi.

       “Wlhy Bily kin ganninan kaina kemin ciwo kaɗan-kaɗan, nasan dai bai wuci wannan hayaniyarba, kina ganin yanda Aziza ta baje”. Tai maganar tana kallon Aziza da tuni tai barci.
       “A kwaifa gajiya, yaukam ansha bidiri, yanzu danaje ɗakin Ummi take cemin Yaya Amaan ma ya aiko mana da ƙyautar kuɗi dubu ɗari mu raba”.
      Duk da Ummukulsoom ta fahimci wa bily take nufi saita ɗan yatsine fuska, “Waye kuma haka?”.
          “O ashefa kina buƙatar ƙarin bayani, wanda ya bamu ƙyaututtuka shida yaya Attahir, shima yayanmune ai, ɗan gidan Dad”.
       “ALLAH sarki, to kin gode. Kinga bara na haɗo ko tea nasha yunwa ta fara gallabar rayuwata”.
      “Maganinki kenan ai, tunfa ɗazu nakawo tuwo da zafinsa amma kikace kin ƙoshi, kuma kikace na gode ke baki godeba kenan?”.
       “Indai kin gode nima kamar na godene kinji bestie, bara dai naga mike a kicin ɗin, dan sai yanzu nake dana sani, yanzu kuma idan nace zanci zai takuraminne dan dare yayi”.
        “Gara dai kisha tea ɗin kawai, saiki haɗa dako wani abune”.
     ”Ok ina zuwa”.
 Gyale ta ɗauka ta yafa akan riga da wandon kayan barcinta ta fice, ba kowa a falon kowa gajiya ta sakashi yin tiɓis, dama duk baƙi sun kama gabansu tunda ba wani taron biki bane ko suna. Tea ɗinta ta haɗo ta dawo ɗaki tasha kafin tasha magani su kwanta.

         Washe gari ma haka suka tashi a matuƙar gajiye, amma haka suka daure suka gyara gidan tsaf ko ina ya ɗauki haske da ƙamshi.
      Kafin su kuma komawa ɗaki susha barcinsu yanda ya kamata.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

               “Fodio ya maganar mu ne? Ina muka kwana ina muka yini?”.
        Ci gaba yay da yin breakfast ɗinsa hankali kwance, kafin ya ɗago manyan idanunsa ya harari Buhayyah da itama tame breakfast ɗin, dan a dining suke su uku, Dad ne kawai babu.
       Fahimtar dalilin harar tata da yayne yasata miƙewa ta kwashi kayan break ɗinta tabar musu Dining ɗin, dama duk zamansa ya takuta.
      Momcy batace komaiba, dan shifa dama ƙa idarsace wannan, ko hira bayason yi gaban ƙannensa, garama Aunty Nurse taci wannan darajar.
        “Tunda ka koreta saika bani amsa”.
       Shiru yay nanma bai tankaba, sai laɓɓansa da sukaɗan motsa alamar yanason maganar fitarta ce wahala a garesa, saida yaja wasu seconds kafin yay ɗan gyaran murya da cirar tishu ya goge bakinsa, “Momcy kenan, nifa ban ganiba har yanzu?”.
      Kallon mamaki ta tsaya masa tana kurɓar tea, “Ban gane baka ganiba? Ita matar auren film ce da har saika gani?”.
        Alamar gajiyawa da maganar ya nuna a fuskarsa kafin ya lumshe idanunsa ya buɗe a kanta, “Momcy Please bar wannan batun, ni yauma zan koma?”.
       “Barin batu kam ai baima tasoba Fodio, dan aure dolene kayisa nan kusa, Dad ɗinku fa zuba mana ido yay yaga yanda zamu kwashe, kaga ko ai yakamata muba mara ɗa kunya ko. A ganina yarannan biyu na gidan Alhaji Abubakar mizai hana ka zaɓi ɗaya”.
      Baƙaramin waro mata manyan idanunsa yayiba, tareda kafeta dasu batareda ya fargaba.
      “Nidai ɗauke waɗannan idanun naka a kaina kaji”.
     Karan farko data bashi dariya, dan haka fuskarsa taɗan nuna alamar sakewa, amma fa ba murmushi yayba, saikace ba gunta ya gajesuba.
       “Bakace Komaiba?”.
“To Momcy banida abin faɗar ne, kibani lokaci zan duba na gani to”.
      “Zaka duba ko zaka zaɓa”.
         Tashi yay tsaye yana faɗin, “To zan zaɓa” dan shikam yagaji da surutun.
        Da kallo ta bisa tana maijin ƙarin ƙaunar ɗanta har cikin ranta, wataran halayyarsa ta bata haushi wataran kuma tai mata daɗi.


 ★★★★

          Koda ya koma sashensa sabon shafin tunani ya buɗe, dama a cikin yanayin ya kwana, haka kawai ya tsinci zuciyarsa da daskarewar harbawa, baisan minene daliliba, abinda kawai ya iya fahimta shine yawan tuno kalmarta ta *“Shikuma wannan dangin tsakar daga ina? Waya bashi lasisin taɓani ma?”* da karfi ya rumtse idanumsa, furucinta na sukarsa, yarasa miyasa yarinya ƙarama irin wannan kalamanta sukai tasiri a ransa?, hararar da tai masa bayan bazar gyalenta ta maƙale masa ya mugun tsaya masa a rai itama, dolene ya ɗauki mataki akan yarinyar, dan zuciyarsa bazata iya ɗaukar raini daga kowaba.
     Haka yayta saƙawa da kwancewa shi kaɗai, tareda juya zancen Momcy.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


            “Yaya Attahir wai dan ALLAH da gaske kake mu shirya?”.
       “Oh Bily kin rainani wlhy, na taɓa muku irin wannan wasanne? Ina Ummukulsoom?”.
         “Tana ɗaki kwance, amma ba barci takeba”.
      “Ok, tom kuyi maza ku shirya, Dan hafsat ta shirya tuni”.
          “Kai godiya cikin kd babban yaya”.
      Murmushi kawai yay yana girgiza kai, baisan randa Bily zata bar rawar kaiba shikam, halin autanci sosai yake tasiri a jikinta.
       “Madam tashi ki shirya”.
      Ummukulsoom da barci ya fara ɗauka ta ture hannun Bily dake bugunta tana faɗin, “Dalla malama ki bari, wai miyasa kekam a rayuwarki kike baƙin ciki kiga mutum na hutawa”.
        “Hhhhh yarinya zakiga baƙin ciki, Yaya Attahir ne yace mu shirya ya kaimu wani waje muga gari”.
         Buɗe ido Ummukulsoom tai tana kallonta, “Dan ALLAH da gaske kikeyi?”.
     “ALLAH kuwa karkiji wasa”.
     Tashi Ummukulsoom tai cike da jin daɗi, dama zaman gidan ya isheta, sun saba da yawon fita makaranta.
       Shiryawa tai cikin siket da riga na atanfa, kasancewarta mace mai cikar halitta sai sukai mata ɗas, tai ɗaurinta ture kaga tsiya, wanda ya bayyana gashinta dake a tsaka tsakin tsawo, baƙi siɗik saboda gyaran da yake samu, yanzu haka babu kitso, amma a gyare yake  tsaf,ga ƙamshi mai daɗi na tashi saboda kayan ƙamshin da ake turareshi dashi a koda yaushe. Bata cika son kwalliyar shirmeba a fuska tunma tana ƙauye, sai abun yay tasiri a gareta har zuwa yanzun.
        “Bily Please ina gyalenmu ƙalar Ash ɗinan?”.
       “Tab babban aiki, ai inaga gyalennan kam yayi datti, kinsan ranar walima ɗinmuncan shina ɗaura akai mukaita aiki, kuma ba ai wankiba”.
       “Amma dai kin gama dani, yanzu wanne zanyi amfani dashi kenan?”.
    “Ki saka yellow ɗinnan mana, shima zai zauna sosai ALLAH”.
     Kallon kanta tai a mirror, kafin taja gyalen ta jingina da kayan, ganin zai shigane saita fesa masa turare.

    “Woow Autocin Ummi irin wannan ƙyau haka?”.
     Murmushi su Ummukulsoom sukayi saboda tsokanar yaya Attahir ɗin da maman Ahmad, Zaid kam ya kafe Ummu da ido ko ƙyaftawa bayayi, hakanne yasa taƙi kallon inda yake, da tasanma tafiyar da shine da wlhy bata amsa zuwaba, shaf ta manta yau weekend yana gida, kuma koda sun barta a gidan bazai mata daɗiba, dan Ummi da Abba sunje Niger state duba wani yayanta da baida lafiya.
     Koda suka fito sai Yaya Attahir yace su shiga Motar zaid, shi matarsa kawai zai ɗauka, Ahmad kam yana tare dasu Ummi.
    Ko kaɗan Ummu bataso hakanba, amma saita basar kawai, gashi Bily tai saurin shigewa gaba.
         Koda suka fice a gidan duk yanda Zaid yaso Ummukulsoom ta saka baki a hirarsu ƙi tayi, sai taso ma take murmushi, maida dukkan hankalinta tayi ga latsa waya, shi dai Zaid har mamakinta yakeyi, anya batada aljanu kuwa? Yarinya Sam batsan soyayya ba?.
      Oho ko kaɗan Ummukulsoom batasan yanayiba, ita zuwa yanzuma sotake ta leƙa ƙyauyensu taga yaya lafiyar jama’a, dan shekara ɗaya kenan bata jeba kuma duk shekara idan sunzo ƙarshen shekara take samu ta leƙasu koda kwana ɗayane itada Bily, yanzu kuwa kafin ta koma makaranta ya kamata ta leƙa kam ko sati biyu tayo…….
      “Hajiyar tunani saiki fito mun iso”.
     Ajiyar zuciya Ummukulsoom ta sauke kaɗan, kafin ta kalli Zaid dake maganar tsaye ya buɗe mata mota, ita saima abun yasata murmushi, “Yaya zaid kenan saikace wata sarauniya?”.
      “Ai ke Kinmafi ƙarfin sarauniya Babie”.
     Murmushi ta kuma masa, batareda ta bashi amsa ba ta fice daga motar shikuma ya rufe yana shakar daddaɗan ƙamshinta mai narkar dashi.
        
     Sosai Ummukulsoom ke kuma ware idanu tana kallon gidan, ko shekaru nawa zata ɗauka bata zoba bazata mantashi ba, yana nan yanda ta sanshi, sai fenti da aka canja masa, saiko tsarin flowers ɗin gidan, ta haɗiye wani abu mai kama da hasala a maƙoshinta, tareda saurin dannesa da tarin alkairin mai gidan, kodan alfarnar Dad bazataki alfahari da zuwa gidanba.
       Da sallama suka shiga falon da komai na cikinsa ya kasance baƙon ganin Ummukulsoom, dan duk ba wanda ta sani baneba, ko ina ƙal yake da tsafta, a wannan fannin kam tasan Momcy gwanace, batason ƙazanta ko kaɗan, sanyin AC ne kawai ke ratsa falon sai ƙamshin turaren wuta. Tsit gidan babu yawan hayaniya kam yanzun.
      Bily takuma kwaɗa sallama, daga kicin muryar wata dattijuwa ta amsa.
     Idanu Ummukulsoom ta kafe ƙofar kicin ɗin dashi dan taga wazai fito, burinta kawai taga baba halima.
    Ilai kuwa itace, amma ta ƙara manyanta, cike da girmamawa take musu sannu da zuwa.
    Tausayinta ya kama Ummukulsoom, ALLAH sarki rayuwa, wato talaka shidai haka rayuwarsa a mafi yawan lokuta take ƙarewa, ka taso cikin wahala, idan haka ALLAH ya ƙaddara maka saikaga harka girma a cikinta, Baba halima ta cancanci ta huta, amma sam hakan bai samuba, batason bayyana mata kanta kam a halin yanzun, dan a ganinta lokaci bai yiba.
     Itace da kanta ta hau saman benen, dama tun can da ita kaɗaice keda wannan lasisin, saiko wadda suka ɗauka domin musu aikin gyaran saman.
    Babu jimawa saiga Momcy ta sakko cikin kwalliya.
    Ganin su Ummukulsoom ne baƙin yasata rikicewa da musu lale mar habun, “Haba dai ya zaku zauna anan kuma ƴaƴana? Kunga kutaso ku hawo sama dan ALLAH.
       Baki Ummukulsoom taɗan taɓe a kaikaice, kafin tabi bayan su Bily da har sunyi gaba itada maman Ahmad.
      A falon Sama ma komai baƙon Ummu ne, sai kallon falon take tana tuna baya, tamkar batai bauta a cikinsaba, ALLAH sarki rayuwa, ni’imar ALLAH da bance wlhy, hakama ikonsa akan kowa dabanne, karkaga kana shiga haƙƙin ɗan uwanka koda da mummunar maganace ko zagi ka ɗauka ALLAH bazai jarabcekaba, shi buwayine gagara misali, yakan yafe laifin a tsakani sa da bawansa, amma fa baya yafewa tsakanin mutum da mutum, to bakasan ta hanyar da ALLAH zai sakankama wanda ka cutamawa ɗinanba, sannan kaikuma bakasan ta ina zai jarabceka da haƙƙin wanda ka ƙuntatawarba, yau dai gata tazo gidan Momcy ba’a Ummu ƴar aikiba, ba’a ƙasƙantaciyar dasu suke ɗaukaba, sai dai ALLAH kuma ya toshe saninsu da fahimtarsu ta yanda suka gaza ganeta.
    Dan danan aka cika musu gabansu da kayan motsa baki, Hajiya jamila tamkar zata goyasu dan tsabar ɗoki.
    Hakama Buhayyah data fito daga ɗakinta jin hayaniyarsu.
        Suna tsaka da gaisawa kira ya shigo wayar Momcy, ɗagawa tayi cikin murmushi tana faɗin, “Yaya dai Fodio?”.
    Basu san wace amsa daga can ya bataba, sundaiji tace, “Ok to babu matsala bara a kawo musu”.
          Kallon Ummukulsoom tai dake a kujerar farkon shigowa a kaikaice, yarinyar tafi dacewa da Fodio ɗinta, saboda tafi Bily cikar halitta dukda suna mata satar kamanni, taɗanyi gyaran murya da kallon Buhayyah.
    “Buhayya keda diyata kuje ku kaima su yayanku abin motsa baki da lemo”.
     Buhayyah taɗan ɓata fuska, dan itakam ta tsani aikin yaya Amaan, kafin ka gama yakusa cinyeka da harara, amma babu yanda ta iya saita miƙe tana kallon Ummukulsoom dake kusa da ita, Auntyna dake zamuje ko?”.
        Tamkar Ummukulsoom ta danƙara mata zagi haka taji, dan duk tana saurarensu amma tayi kamar bata fahimta, murmushin yaƙe tai a fili tana faɗin, “Babu damu muje”.
       Momcy dake kallon Ummukulsoom cike da birgewa tace, “Yi haƙuri ɗiyata, daga zuwa an saki aiki, yayan nakune sai a hankali, bayason ƴan aiki su masa komai”.
     “Lah babu damuwa Momcy ”. ‘Cewar Ummukulsoom a wani yanayi’.
    Itako Momcy daɗi taji, saboda itadai yarinyar komai nata birgeta yake, akwai jan aji sosai, irin yanda take fatan matar Fodionta ta kasance komai Ummu ta haɗashi.
     Ummukulsoom da Buhayyah kam tuni sun fice, kicin suka nufa suka karɓi Kayan da Jud ya haɗa, Ummu sai kallonsa take, amma sam shi bai ganeta ba, yana nan bai canjaba, hakama wulaƙancin su Buhayyah ga ƴan aiki, dan yanda takema jud ɗin magana dolene ya baka tausayi, saikace wani ƙaninta ko ɗanta, a gadarance take bashi Umarni.
       Koda suka fito Buhayyah sai sukar ƴan aiki takewa Ummukulsoom, amma sam taƙima tanka mata, hakanne ya saka Buhayyah ɗan kallonta, taga Ummukulsoom tayi kicin-kicin da fuska babu alamar sauƙi.
    Buhayyah a ranta ayyanawa take “kin cancanci jan aji wlhy, dan komai kina dashi najan ajin, ni saima naji kin kuma burgeni, inason huɗɗa da masu aji” a zuciyarya taketa surutannan, Ummukulsoom kam tama ɗauke kanta daga gareta tamkar ba a tare suke tafiya ba.
     A ƙofar falon suka tsaya Buhayyah ta  ƙwanƙwasa. Babu jimawa aka buɗe musu suka shiga.
           Shine a kujerar farkon shigowa falon, Ummukulsoom ta danna ma bayansa harara kafin taima falon kallon tsaf, komai shima an canja hatta da fentin sashen, sai dai mayataccen ƙamshinsa da ta sani tun fil azal yana nan nane da sashen, koda sukai sallama Attahir da Zaid sun amsa amma shi ko motsi baiyiba balle ya ɗago ya kallesu, sai aikin latsa waya yakeyi hankalinsa kwance.
      Tsabar iya neman faɗa irin na Ummukulsoom da zata wuce sai ta taka masa ɗan yatsan ƙafarsa ta wuce. Zaid yayma Ummu murmushi tarefa mata signal da ido alamar sannu da aiki.
    Ɗauke kanta tayi kamar bata gansaba, ta ajiye tiren hannunta.
     Buhayyah ce ta fara wucewa Ummukulsoom na binta a baya, batareda taga sanda ya motsaba kawai tajita a ƙasa ya taɗeta.
     “Wayyo Ummina”. Ta faɗa a hankali saboda shigar azaba da ƙashinta ya fuskanta na ƙafa.
      Duk kanta Yaya Attahir da Zaid sukayo suna tambayar lafiya? Hakama Buhayyah, amma gogan naku ko motsi baiyiba balle ya kalleta.
     Attahir ne yaɗansha jinin jikinsa, ya kalla ƙafarsa tareda auna inda Ummukulsoom ta faɗi, tabbas yaji a ransa Ajiwa ne ya aikata tsiyar, amma ya fuske tamkar bai aikataba.
       Sai abun ya ɓatama Attahir rai, a ganinsa mi Ummu tai masa dazai mata wannan muguntar, ransa a ɗan ɓace yace, “Ajiwa wai garin yaya hakan ta faru? Naga a gabanka ta faɗi?”.
    Yiyay tamkar baiji mi Attahir ɗin ya faɗaba, sai da ya mula da kansa sannan ya ɗago manyan idanunsa farare tas ya sauke akan Attahir da shima ya ɓata fuska. Bakinsa yaɗan taɓe tareda maida kallonsa ga Ummukulsoom dake kuma narke murya tana kuka, wanda da gani kasan harda shagwaɓa da sheri ganin Attahir ya nuna fushinsa akai????…………✍????







*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button