NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 30

_NO. 30_*

…………Bakinsa ya kuma taɓewa tareda kauda idanunsa daga kanta.
      Zaid da yakejin kukanta har cikin ransa yay saurin kai hannu ga ƙafarta amma sai carab Amaan ya riƙe hannun.

     Dukansu idanu suka zubama hannun nasu, kowa baki hangame, hatta da Ummukulsoom saida ta tsaya da kukanta tareda hangame baki tana kallon hannunsa dake riƙe da na Zaid, kafin ta maida kallonta ga fuskarsa.
     A tamke take sam babu alamar sauƙi, sannan kuma ya ƙi kallon kowa har Zaid ɗin, yakumaƙi sakin hannunsa.
      Attahir ne yay gyaran murya ganin abin zai canja salo, “Ƙanwata jawo baya kinji inga ƙafar”.
      Matsawa Ummukulsoom tai shirinyi fuskarta ɗauke da mamaki amma sai taji an riƙe ƙafarta mai ciwon.
        Saurin kallonsa tayi, sai ta ga ya saki hannun Zaid ɗin, ƙafar tace yanzu kam a hannunsa……
    Tunaninta baije ƙarsheba ya matsa ƙafar sosai sai da tayi ƙara tareda ƙan ƙame hannunsa ta fashe da kukan gaskiya kam yanzun.
    Ture hannunsa Attahir yayi da sauri yana faɗin, “Wai kai Ajiwa mike damunka ne haka?!”.
        Zaid kam da Buhayyah idanu suka rumtse saboda tausayin Ummu, dolene ka fahimci taji zafi, dan da alama taji ciwo a wajen, matsawar da yay kuma yabama ƙashin wajen damar dai-dai ta.
       Amaan da yasan Attahir ya fusata, kuma komai zai iya faruwa a tsakaninsu sai bai tankaba yama miƙe yabar falon.
      Saurin binsa Attahir yayi, dan ya shirya suyi koma miye, bayason zalinci mara dalili, abinda ya fuskanta kawai Ajiwa ya gane wacece Ummukulsoom shiyyasa yake neman magana, shiko a wannan karon bazai ɗaukaba wlhy, dan jinta yake a ransa tamkar Bily da Zaid.
       Ganin sunbar wajen Zaid da abin duniya ya damesa yakuma yunƙurin kai hannu ga ƙafar Ummukulsoom…….
       Cak ya tsaya daga yunƙurin shiga bedroom ɗinsa, cikin kakkausar murya yace, “Wlhy Zaid idan har ka aikata sai na ɓata maka rai, kubar falon nan kaida Buhayyah”.
      Kasa aikatawar Zaid yayi, dan yasan halin Yaya Amaan farin sani, amma zuciyarsa na mamakin miyasa yake son shiga rayuwarsa shida Ummukulsoom?, ko dai sonta yake shima?.
     Buhayyah kam tuni ta fice dan tasan ƙarshen zancen inma tayi taurin kai, dama darajar su Ummukulsoom dake falonne ya bata damar sakin jikinta.

       “Wai kai mika ɗauki kan kane? Mi kake taƙama da shine a rayuwa?!”.
      Ummukulsoom ta faɗa a matuƙar fusace, dan zuwa yanzu bata shakkar yasan itaɗin wacece, bazata ɗauki wannan rainin hankalinba.
         Tsaƙi yayi ya ƙarasa shigewarsa batare da ya bata amsaba….
      Dukda azabar da ƙafarta ke mata miƙewa tayi ta fice, zuciyarta na wata irin tafasa da kuma kumbura….

           “Ajiwa mikenan kakeyi? Kaga kana neman haddasa raini tsakaninka da yarinyarnan ko”.
       Murmushi Amaan yayi, irin wanda duk tsantsar shakuwarsu da Attahir yakan jima bai ganiba, dukkan hannayensa biyu zube suke a aljihun wandonsa 3quarter, gaban Attahir yazo ya tsaya sunama juna kallan kallo tamkar wasu zakaru, ya lumshe idanunsa ya buɗe akan Attahir dake hararar sa fuska a ɗaure.
      “So kake ka san dalilina? To ba yanzuba, sai dai lallai ka gargaɗeta ta kiyayi shiga lamarina, inba hakaba da hannuna zanta karyata ina ɗorata, inga ƙarshen fitsara”. Yana gama faɗa yaɗanja baya daga gaban Attahir.
     Katsesa Attahir yay da faɗin,
       “Ajiwa ba maganar wasa nake makaba anan,  banga mi yarinyar nan ta makaba, karka bari akanta saɓani ya shiga tsakaninmu”.
       “Attahir karka azamin ciwon kai Please, kaje ka fara bincikarta kafin kazo kanamin surutun banza”.
      Tsaki Attahir yaja tareda hararsa ya fito daga bedroom ɗin.

       A tsakar gida ya iske jama’ar gidan cirko-cirko, ga Ummukulsoom gaban Dad tana hawaye zaune a farar kujera.
    Kallo ɗaya yayma fuskar Dad ya sunkuy da kansa, dan lallai ransa a ɓace yake.
        Momcy dukta rikice, sai tafa hannaye take, tanason nufar sashen Amaan amma tana shakkar Alhaji Mahmud.
     Sashen Amaan Dad ya nufa ransa a matuƙar ɓace.
         Tunda Dad ya shigo falon Amaan da fitowarsa kenan daga bedroom ɗinsa yasha jinin jikinsa, amma kasantuwarsa ɗan gado akan dakiya sai bai nunaba ya hau faɗin, “Dad lafiya kuwa?”.
      Cikin hargowa Dad yace, “Ban saniba, Mi yarinyar can tamaka kaji mata ciwo a ƙafa!?”.
      Kansa ya dafe cike da tsantsar takaici, ɗan abunda ya mata har yakai na a hau kansa irin haka?…..
      “Fodio da kai nake, banason iskanci fa?”.
      Idonsa harya fara canja Cala, da ƙyar ya iya furta “Dad ni minai mata to?”.
        Dad ya yunƙuro zaiyi magana Momcy data shigo tai azamar tararsa da faɗin, “Abban Fodio dan ALLAH kayi haƙuri, mubi a hankali”.
     “Anƙi abi a hankalin kekuma, in banda iskanci da tsabagen zalunci daga zuwan yarinyar gidan ziyara saiya kama cutar da ita, kai wai a rayuwarka bakajin daɗine idan bakai zalunci ba? To wlhy wannan yazama farko da ƙarshe da ko harar banza ka sake mata, shashasha kawai mai baƙar zuciyar tsiya. Ke kuma ki gargaɗi ɗanki ya kiyayi taɓa yarinyarnan, akanta zan iya saɓa masa wlhy”.
    Fuuuuu Dad ya fice yabar musu sashen.

       Kafe ƙofar da Dad ya fice yay da kallo, yakasa koda motsi daga inda yake tsaye, akan wannan yarinyar Dad kemasa waɗannan kausasan kalaman? Bayan kuma itace taja yay mata hakan……..
      Ita kanta Momcy kalamansa sun girgizata, to ita yarinyar wacece ita da har yake tada jijiyar wuya a kanta?.
       “Fodio wacece ita wannan ɗin? Dan na fahimci daga kai har Alhaji kunsanma wacece kenan?”.
      “Momcy ni ban santaba”.
        “To in bakasan wacece itaba miyasa kai wannan gangancin? Miya haɗaka da ita?”.
      Kallonsa ya maido akan Momcy amma ya kasa bata amsa. sanin ransa a ɓace yakene ya saka Momcy kama hannunsa ta kaishi har rukunin kujerun dake falon, ya zauna. Itama zama tayi gefensa, “Fodio kayi wauta, yarinyarnan dama itace nake fatan kaje ku daidaita, gashi tunkan aje ko ina kafara ruguzamin shiri, dan ALLAH Fodio ka rage zuciyarnan taka……
      “To amma Momcy sai kawai na zauna ƙaramar yarinya taitamin rashin tarbiyya.”
      “Wane irin rashin tarbiyya kuma Fodio? kai yaushema ka santa da zakace haka?, irin waɗannan yaranfa abun tattaline, Ko dai ka santa ɗin da gaske kuna ɓoyemin ne?”.
       Idanu ya tsura mata kawai, yana maimaita kalmar tattalin data ambata a zuciyarsa tareda rarrabe ma’anoninta a ransa.

         A tsakar gida kuwa Baba Halima ce ta duba ƙafar Ummukulsoom, dan ta iya gyara, sai taga ashe targaɗene kawai tayi a ɗanyatsa, kuma ya maida ƙatsin lokacin daya matsa ƙafar, magani taje ta ɗakko ta shafa mata, a ranta tana mamakin halin Amaan, shikam yama zarta mahaifinsa murɗaɗɗen hali, ina daɗi daga zuwan yarinya gida kai mata wannan ganganci haka in banda dai ƙarfin hali.
      Bily tayi zuru-zuri, sai tsoron Amaan ɗin ya kuma kamata itakam.
      Ana gama gyarawa Ummukulsoom tace itadai gida zataje gaskiya, Dad bai hanaba yace suje ɗin.
       

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

           *_Birnin Paris_*

      Dur ƙushe yake a gabanta tamkar ɗa mai neman gafarar mahaifiya, ya rame ya lalace matuƙa gaya, tamkar ba Baseer ɗinnan ba ɗan ƙwalisa mai bama mata pepe, babu wannan kwarjinin da cikar haibar da kwanciyar hankali ke samarwa.
      Hawayen dake tsiyaya a fuskarsa wasu na bin wasu ya share, ya kuma gurfana a gabanta yana roƙo, “Dan ALLAH hajiya kimin aikin gafara, wlhy tallahi ƙarfina ya ƙare bazan iya ba, dan ALLAH ki bani dama na sawwaƙe miki na koma ƙasata wajen iyayena da kika nisantani dasu tsahon shekara Biyar, wlhy nayi nadama………”
      “Wlhy bakayi nadama ba Baseer, dan har yanzu baka gama magantuwa ba, baka kai ƙarshen littafin rarrabe shu’umcin maceba…….”
      Muryar da bai zato ba ta katse masa zancensa, a matuƙar rikice ya juyo jikinsa na wani irin ɓari da rawar mazari, cikin tsantsar tashin hankali da gushewar tunani ya furta *“Suhailat!!”* saiya sulale wajen a sume kawai. 

         Suhailat dake tsaye a bakin ƙofa ta tako cikin tsantsar ƙasaita zuwa gaban Baseer dake kwance wanwar a ƙasa, murmushi mai ƙayatarwa tayi kafin ta maida kallonta akan Meenal dake tsaye itama fuskarta ƙawace da lallausan murmushi, hannu suka bama juna cikin kashe idanu……????

           ????????????‍♀️ Tirƙashi, nasan babban burin kowannenku sanin mikuma ya maida Baseer haka bayan barinsa ƙasarsa ta haihuwa????????????‍♀️, to lallai yanzune zaku sani kuwa tamkar yanda kuka matsu da cigiyarsa a kullum.????????


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

             “Yaya Zaid ya naga Yaya Attahir ya nufi hanyar gidan Hajiya yaya kuma?”.
      “Wlhy nima ban saniba Bily, amma bara dai na kirashi a waya naji”.
          Ummukulsoom na kwance cikin kujera a baya tana jinsu, sai dai kuma bata tankaba, dan dama ta daɗe tana son zuwa gidan Hajiya yaya ɗinnan, amma tarasa miyasa Abba kamar yake ƙin son zuwanta? Ƙyaƙyƙyawan zaton da take masane ya sata bata zargi hakan a matsayin komaiba sai ƙyaƙyƙyawan dalili wanda shine kaɗai ya barma kansa sani.
     Tunanin da tatafi ya hanata jin mi wayar Zaid ta ƙunsa, dan haka taci gaba da tunanin shika-shikan rashin mutuncin datake tanadama wannan azzalumin (Amaan) (maganar gaskiya masoyan Ummu kune bakuda gaskiya a wannan gaɓar????, dan kuwa Ummu ce ta takalo faɗan dayafi ƙarfinta).

       Bara nayi ta kaina karnasha suburbuɗa a hannun gayu
⛹????‍♀️⛹????‍♀️⛹????‍♀️⛹????‍♀️⛹????‍♀️⛹????‍♀️????

★★★★★★

          Gidane madai daici ammafa mai tsari tamkar ba tsohuwa ke a cikiba, da taimakon Bily Ummu ke takawa zuwa cikin gidan daya ƙayatar da ita.
          Falo tsaf tamkar bana tsohuwa ba, sai ƙamshi ke tashi na musamman.
      Sallamar da suke rangaɗawa wata dattijuwar murya ta amsa daga wata ƙofa.
      Bily ce cikin ɗaga murya tace, “Tsohuwa mai ran ƙarfa kimazafa kinada manyan baƙi yau a gidannan”.
      Hajiya yaya tsohuwa mai tarin dattako ta fito cikin shigar kamala tana faɗin, “Ja’ira mai ɗan karen ƙaudi, kune baƙin nawa?”.
     Zuwa bily tayi ta rungumeta, Hajiya yaya ta tureta, “Bilkisu kinci garinku, karyani zakiyine?”.
     Bily dake dariya tace, “Waceni da wannan gangancin Abba ya ci ƙaniyata”.
         “A’a kice gidanne du gaba ɗaya, Zaidu lafiya naganka yau rai a ɓace?”.
     Duk kallon Yaya Zaid ɗin sukayi, shiko dai yakasa fara’a tun abinda ya faru gidansu Dad ne kecin ransa, yayma Hajiya yaya murmushin yaƙe kawai.
      Duk wannan abun dake faruwa Ummukulsoom ta fita a hanyyacinta, dankuwa tun fitowar Hajiya yaya ta ƙureta da ido baki sake.
       Attahir ne ya fara lura da halin da Ummukulsoom ke ciki, dan haka ya taɓa Hafsat dake a kusa dashi ya nuna mata Ummu…
     Miƙewa Hafsat tayi ta nufi Ummukulsoom da ɗan hanzari ganin tayi baya zata faɗi saboda tsabagen firgici da take a ciki, wannan ne kuma yaja hankalin sauran har Hajiya yaya da ita sam bama ta lura da Ummukulsoom ba sai yanzun……..


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

             Tunda suka bar gidan sai ya rasa inda zai tsoma kansa yaji daɗi, miyasa ya aikata mata hakan? Anya kuwa ta cancanci hakan duk da itace ta fara aikata masa laifi? Ya rintse idanunsa da ƙarfi tareda tafe kansa, batareda ya shirya suɓutowar maganar dake kan harshensaba yace,
           “Zuciyata bakimin adalci ba, kin jefani a halin da gangar jiki da ƙwaƙwalwa bazasu iya juraba, ni ban shiryaba! Ban shirya ba nace…..!!!”.
    Ya faɗa a matuƙar harmutse yanajin kansa tamkar zai fashe gida biyu, tun daga randa yaji muryarta komai ya fara canjawa a rayuwarsa, abubuwansa masu muhimmanci dake da alaƙa da gangar jikinsa sun kasu gida biyu wajen yin aiki, *ƙwaƙwalwa da Zuciyar sa* duk sun raba tunaninsa tare da nata, wane irin jarabawace wannan ta sartse mai wahalar fiddawa koda da tsinin allurane. Shika ɗai yasan a halin da yake ciki, miskilancin sane kema damuwarsa hijjabi da fahimtar mutane, duk yanda yaso yakiceta ya kasa, kullum lamarin ƙara ruruwa yake da girmama a duniyarsa.
          Wanene zai tunkara? Wazai fahimcesa? Ta yaya zai fiddo abinda ke ransa? Dad ne yay masa katanga ta baƙin ƙarfe akan dukkan maganar data shafi kalmar aurensa………….✍????Kuyi manage Please⛹????‍♀️


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button