NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 31

*_NO. 31_*

……….“Ai ta suma”. ‘cewar Maman Ahmad a matuƙar harmutse, da gudu Zaid ya nufi kicin ɗin Hajiya yaya ya ɗakko ruwa. koda ya buɗe sai Hajiya yaya da itama jikinta ke mazarin rawa saboda ganin fuskar Ummukulsoom ta amsa ta shafa mata a fuska.

    Nannauyan numfashi Ummu ta sauke, kafin ta buɗe ido a hankaki ta saukesu kan hajiya yaya.
    Dukansu numfashi suma suka sauke.
      “Da ana mutuwa a dawo da yau nace mahaifiyata ce ta dawo gareni, duk da a hoto kawai nai mata farin sani ba’a zahiriba. Dan ALLAH yaya Attahir idan mafarki nake ku tadani daga wannan nannauyan barci kafin sauran hankalin da ya rage a ƙwaƙwalwata ya ida tarwatsewa”. 
      Hajiya yaya da har yanzu jikinta ke rawa ta kamo hannun Ummukulsoom cikin nata, idanunta kafe a kan fuskar Ummukulsoom, lallai tanaji a jikinta ko tantama babu wannan yarinyar jininta ce, amma ta yaya ta kasance a cikin family ɗinta bayan babu wani mahaluki daya san inda take tunda ta juyama jiyanta baya, tai wani murmushi mai ciwo, a hankali ƙwallar da suka cika mata ido suka sulalo a dattijuwar fuskarta.
    Hakan sai yakuma saka jikin su Attahir yin sanyi ganin Hajiya yaya na kuka, lallai hakan yana nufin akwai abunda basu saniba kenan.
     Kallon Attahir hajiya yaya tayi, “Attahiru ina kuka samo wannan yarinya?”.
      Numfashi Attahir ya sauke a hankali, kafin ya kalli maman Ahmad da Zaid da Bily yay musu nuni da su fita.
    Harsun yunƙura zasu fice Hajiya yaya ta dakatar dasu, “Kunga ku dawo ku zauna. Kai kuma mushiga ciki”. Tai maganar tana jan hannun Ummu, bin bayansu Attahir yay har bedroom ɗinta.
       Jikin Ummukulsoom yakuma yin sanyi ƙalau, ga ƙafarta na mata zugi dan sai yanzu ma takejin zafin har a zuciyarta.
       A bakin gado hajiya yaya ta zaunar da Ummukulsoom itama ta zauna, Attahir kuma ya zauna a kujerar dake ɗakin mara tudu sosai, an mata itane kawai dan hutawarta.
      “Attahiru ina saurarenka”.
        Guntun murmushi Attahir yayi, kafin yace, “Hajiya yaya da son samune ace Abba yana tare damu, dan nidai shine silar komai, ko dai a kirasu a waya ne?”……
    “Basai an kirani ba gani a kusa”.
     Dukansu ƙofa suka kalla inda Abba ke a tsaye, ya ƙarasa takowa cikin ɗakin, Attahir yay saurin sauka a kujera ya koma ƙasa, itama Ummukulsoom ganin haka sai ta sauka ƙasan.
      Hajiya yaya dake kallon Abba tace, ”Abubakar ina saurarenka”.
     Murmushi Abba yayi, kafin yace, “Hajiya ki gafarceni, ni mai laifine a gareki wajen tone abinda kiketa ƙoƙarin binnewa”.
     Sosai ta kafeshi da idanu, “Abubakar!”.
     “Na’am Hajiya”.
 “Ya akai hakan?”.
“Kiyi haƙuri hajiya, komai na rayuwa yanada sanadi, ni nawa sanadin shine auren Ummukulsoom da Fodio na wajen Alhaji Mahmud abokina. Tun randa Alhaji Mahmud yazomin da zancen ya samawa Fodio matar aure a garin Ɗilau tunanina ya dawo gareki”.
      “Ɗilau Abubakar? Dama acan Usman yayo aure?”.
    “Eh hajiya a canne, bayan munkai kuɗin auren mun dawo nazo na faɗa duniyar tunani, tareda samun ƙwarin gwiwa bisa wasiyyar mahaifina da bai samu damar ƙarasa faɗaba ciwo ya gala baitar dashi,     *(Abubakar mahaifiyarka ƴar wani ƙauyece ɗilau, amma an haramta mata z….)* iya abunda ya faɗamin kenan tari ya sarƙeshi, daga nan kuma harshensa bai sake furta wata kalmaba har ranar barinsa duniya, ban fahimci ƙarshen zancensa ba ko ma’anarsa shiyyasa a koda yaushe nake ɗakko miki hira akan sunan garin, amma sai kikan nunamin ɓacin ranki akan hakan, wannan dalilinne yasani daina miki maganar, sai dai a kullum neman inda zansan garin ɗilau nake, sai a dalilin auren Fodio na sani, ashema kusa take damu. Bayan bikin Fodio ban sake wani yunƙuri akan komaiba, saboda bansan ta inane zan fara ba, amma na kira Attahir akan yay ƙoƙari ya kusanta matarsa da matar Fodio, ƙila kota sanadinta zansan wani abu gameda wasiyyar mahaifina. Ban san fuskar matar Fodio ba, saboda ko a lokacin da tazo gaishemu ranar ɗaurin aurensu fuskarta a rufe take. Babu wani bayani mai gamsarwa dana samu a wajen Attahir kusan watanni shida, sai kirana da yay yake sanarmin saɓani daya shiga tsakanin matar Fodio dashi Fodio ɗin, hakanne yasa nace duk yanda zaiyi yayi tazo gidana ni da kaina saina maidata ga iyayenta, wataƙil ta sanadin haka nima na samu haske a nawa binciken. Wannan shine dalilin dawowar Ummukulsoom gidana, tunda naga yarinyar hankalina saiya kuma tashi, dan tabbas akwai kamanni a tsakaninku, sai mutum ya maida hankali sosai zai fahimci hakan, wannan ne yasa nai duk wani ƙoƙarin ta zauna tare damu domin jifan tsuntsu biyu da dutsi ɗaya, ta samu cikar burinta, nima na samu cikar nawa burin. Zuwan su Bilkisu garin ɗilau rakkiyar Ummu ne ya kuma tabbatar min da akwai ɓoyayyen sirrin da ban saniba game da mahaifiyata, amma gudun ɓacin rankine yasa na hana akawo Ummukulsoom gidannan a tsawon shekarun da tai tare dani, anawa tunanin saina gama gano komai, to gashi kuma ban gama gano komanba Attahir ya kawota”.
         Hawaye sosai Hajiya yaya take sharewa, haka ma Ummukulsoom da duk mamaki ya kamata, itako ashe lallai haukar ƙuruciya na ɗawainiya da ita, dan bata taɓa kawo komai gameda zamanta gidanba, hakama sometimes mutane kance tana kama da Bily, amma bata taɓa gasgata zancenba saboda ita bata ganin kamannin.
         “ALLAH yay maka albarka Abubakar, ba abun kunya yasani ɓoye maka komaiba, bin Umarnin mahaifinane, inason garinmu, inason zuwa cikinsa, inason ahalina dake cikinsa, sai dai wani furuci yay min hijjabi da tsintar kaina a cikinsa”.
     “Sunana Ummukulsoom na yanka”.
     Gaba ɗayansu suka kalli hajaiya yaya da mamaki.
    Murmushi tai musu tareda jinjina kanta, “Ƙwarai da gaske sunana kenan Ummukulsoom, Mu uku mahaifinmu ya haifa a duniya wato malam Ado ba rinji”.
    Da sauri Ummukulsoom ta kalli hajiya yaya jin sunan wanda ta ambata.
    Nanma murmushi Hajiya yaya taima Ummukulsoom ɗin, sannan ta cigaba da faɗin, “Ni ce babba a gidanmu, sai ƙanwata Hindatu, sai autanmu Lirwanu. Muna samun gata a wajen mahaifinmu dan mahaifiyarmu tun a wajen haihuwar Lurwanu ALLAH yay mata rasuwa, kulawar da mahaifinmu ke manace ya saka iyami tsanarmu, wato matar babanmu, a haka muka rayuwa cikin wata bahaguwar rayuwa a hannun Iyami, a wajen baba kawai muke samun sauƙi. Shekarata 12 baba yay shirin aurar dani, dan haka ya bada sadaka ta ga Ɗan-asabe, anyi baikonmu da ɗan-asabe duk da ba sonsa nakeba, amma biyayya ta saka ban musaba.  Bayan baikon mu da sati guda na tafi kiwon dabbobi daji ni da Hindatu kamar yanda muka saba a kowacce damuna, dan anayin ɗaurene, zalincin iyami yasa da ta sai ciyawa gwamma ta sanu kwance dabbobin mu tafi kiwonsu daga safiya har yammaci, randa mukayi gigin dawowa da wuri ta lakaɗa mana duka tace cikin dabbobinta bai ƙoshiba, idan kuma lokacin rani ne bata sakinsu, saidai muje daji muyo musu abinci, hakan ba komai bane face salon ƙuntata mana. A wannan ranar da muma fitane muna tsaka da kiwo sai maciji ya sareni, take a wajen na zube, dan haka hankalin hindatu ya tashi ainun, tashiga kuka da kururuwar neman taimakon wani. Ana haka ALLAH ya kawoshi cikin mota”.
      “Hajiya yaya wake nan?”. Cewar Attahir.
     Murmushi hajiya yaya tayi tana gyara zama, “Attahiru mi kakeci na baka na zuba, ai yanzu zaka sanshi. Ba kowa bane face kakan ku, shine ya taimakeni bai saurari komaiba ya ɗaukeni yasa a mota tare da Hindatu ya nufi Zaria da mu. Ni bamma taɓa zuwa zaria ba sai ranar, ALLAH ya taimaka dafin macijin mai sauƙine, sai aka samu kaina cikin amincin ALLAH, amma dai an kwantar dani a asibitin. Shine ya koma da Hindatu Ɗilau suka sanar da halin da nake a ciki, hankalin baba ya tashi matuƙa, yay ta sakama kakan ku albarka tare da godiya. Amma Iyami gareta ba hakan baneba, ita masifa ma take ina dabbobinta? Sai a sannan kakanku ma yasan abinda yakaimu jeji har wannan lamari ya faru. Gidan maigari baba yakai cigiyar dabbobinta, kaifin yabiyo kakanku su dawo Zaria wajena. Indai taƙaice muku zance shine yayta ɗawainiya da hidimar asibitinmu harna warke, sai dai kuma Ubangiji mai hikimane, dan kuwa shiyya saƙa soyayya mai ƙarfi tsakanina dashi a wannan jiyya, bayan warkewata muka dawo ɗilau, sai ya zamana duk sati saiyazo ɗilau. Hakanne ya tashi hankalin Iyami, dan kuwa ta ɗau alwashin waninmu bazai taɓa samun cigaba ba, yanda bata haihuba a gidan mu da aka haifa sai dai muƙare rayuwarmu a wahala. Ita ta fara fargar da baba wai soyayya nake da Ibrahim. Hankalin baba saiya tashi saboda yana ganin yarigada ya badani, janye waccan maganar kuma tamkar zubar da kimarsa ne, sannan hana Ibrahim ni tamkar butulcine, sai yay yunƙurin datse alaƙar da hanzari, amma kuma sai hakan bata faruba, dan kuwa yana tunkarata danson jin gaskiyar zance na sanya kuka akan nifa lallai Ibrahim nake so, dama kuma banason Ɗan-asabe kowa ma yasan hakan. Da farko Baba kam lallaɓani ya farayi, ganin naƙi saurarensa saiya canja salo saboda zugashin da Iyami keyi. tun anayin abu iya gidanmu harya fito ya fara yawo a garin ɗilau, kowa ya samu abin faɗa. Hakan ya kuma birkita baba ya gaza fahimtar ba laifina bane, zuciyata ce, yagaza fahimtar sheɗancin Iyami. Ibrahim shima yana matuƙar sona sosai, dan kullum cikin zuwa roƙon baba yake amma baba ya baɗe idonsa da toka yaƙi saurarensa. A wani dare sai hindatu ta tadani na rakata banɗaki amma sam naƙi, nace in bazatajeba sai dai tayisa a wando. Ƙyaleni tayi ta fice dukda tanajin tsoro, batafi mintuna uku ba sai gata tadawo, “Yaya, yaya tashi kiga mi Iyami keyi”.
     “Tashi nai zaune da sauri, nace, “Mi Iyamin keyi?”.
     “Ke dai taso ki gani Yaya, dan bayanina bazai gamsar da keba”.
    “Ban musaba na tashi na bita, ta can bayan ban ɗakinmu inda Rumbu yake muka iske iyami tana haƙa rami, laɓewa mukayi ta gama tsaf ta saka wasu layu a ramin, sai da tagama harda yayyafa ruwa ta maida ƙasa ta rufe kafin ta miƙe tana ƴar dariya, “Umma ɗan-asaben ma basamun damar aura zakiyiba balle wani Ibrahim ɗan birni, kamar yanda malam ya sanarmin layunnan na cika kwana goma a ƙasa Ibrahim zaiyi iskanci dake, na tabbata hakan ne zaisa kowa ya tsaneki a ƙauyennan idan kikayi cikin shege, mahaifinki ya tsine miki ya koreki, na gama da babinki, saura Hindatu itama”.
      Gaba ɗayanmu mun tsorata da kalamanta, danni harma na fara hawaye, da ƙyar muka ɗauke numfashi yayinda zata wucemu, a ranar bamuyi barcin sauran darenba daya rage. Washe gari tunda safe muka nufi gidan ƙanwar mahaifiyarmu muka sanar mata abinda mukaji, itama hankalinta ya tashi, dan haka tace mu turo mata Ibrahim idan yazo. Dato muka amsa, cikin amincin ALLAH kuwa washe gari saiga Ibrahim, dayake a lokacin a ɓoye muke haɗuwa, shine na sanar masa da zancen Innarmu. Bai musaba mukaje wajenta. Bayan sunyi gaisuwar mutunci tace, “Bawan ALLAH da gaske kake son ƴata kuwa?”.
      Cike da ladabi Ibrahim yace, “Wlhy Ina sonta Inna, kuma a shirye nake na aureta ko a yanzunnan ne”.
     “To Alhmdllhi, yanzu inaso ka ɗauki Umma kuje garin ɗan-gamau a katsina, idan kunje garin kuyi tambayar gidan Malam Baushi, kuyi masa bayanin komai daya faru, kuce masa nace ya ɗaura muku aure, Ibrahim ga amanar Umma nan, idan kaci ALLAH ya ci taka, karku zo Ɗilau saita haihu”.
    Godiya mukai mata muduka muna kukan jin daɗi, a ranar muka tafi babu wanda yasani har Hindatu, duk yanda Inna tace muyi haka kuwa mukayi, Malam Baushi ya ɗaura mana aure, satinmu ɗaya a can Ibrahim ya ɗaukeni muka wuce legas wajen aikinsa, ban fuskanci matsala a wajen danginsa ba danshi marayane. Ban sake waiwayen garin ɗilau ba, dukda kuwa ina matuƙar kewarsu, sai da na shekara biyar, dan har lokacin ban haihu ba, saida na shekara biyar da wasu watanni nasamu cikin Abubakar, bayan haihuwarsa naso zuwa Ɗilau domin cika alƙawarin inna amma sai wani aiki ya riƙe Ibrahim, dan haka ya bani haƙuri, dan shi burinsa muje tare mu nemi gafarar baba, zamu-zamu tafiya bata yuwuba har na yaye Abubakar, kwatsam kuma saiga wani cikin, ganin haka sai Ibrahim ya lallabani akan nai haƙuri na haihu saimu tafi, ƙilama Baba yafi karɓarmu. Hakance ta faru kuwa, dan saida na haihu tagwaye duk mata sannan muka shirya zuwa ɗilau. Komai ya canja mini daga yanda na sanshi, abubuwa da yawa kuma sun faru, dan ansha tashin hankali bayan nemana da akai aka rasa, a maimakona sai aka ɗaurama Hindatu Aure da ɗan-asabe, baba kuma yace ya barma duniyani, har abada ya cureni cikin ƴaƴansa. Har zuwanmu ɗilau baba na akan bakansa na ƙin karɓata, dankuwa muna fita a mota bai bari nataka koda zauren gidanmu ba yace mu juya, tareda furucin inhar na sake dawowa garin ɗilau ALLAH ya isa bai yafemin ba. 
     Hajiya Yaya ta fashe da kuka mai tsuma rai, wanda yasaka su Ummukulsoom da Attahir harma da Abba kuka suma, da ƙyar Hajiya yaya ta tsagaita taci gaba da faɗin, “Bansan yanda zan fassara muku halin dana shigaba dagani har ibrahim, da ƙyar nasamu wani ya faɗamin inda Hindatu take aure, Lurwanu kuwa na iske ya rasu sanadin zazzaɓi da yayi. Naje gidan Hindatu, muka rungume juna muna kuka, na isketa har tayi haihuwa Uku ita, ƴar da take goyo ma tsakanin haihuwarta da ƴan biyuna kwana ukune, na amshi ƴar saina ganta a langaɓe, hankali tashe na kalli Hindatu da itama take kallona tana kuka.
    “Hindatu miya sametane?”..   
      “Yaya ta rasune yanzunnan, ina kukan mutuwartane ma kika shigo”.
     Sosai hankalina ya tashi nima, na rungume yarinyar a jikina ina hawaye, muna cikin haka saiga ɗan aike daga baba, yace inhar ban zo nabar garinnanba yazo gidan hindatu ya iskeni saiya min abinda ban taɓa tunaniba, kuka na kuma fashewa dashi, na kalli hindatu da itama kukan takeyi.
         “Hindatu dan ALLAH kimin wani taimako kafin nabar garinnan”.
     “Inajinki yaya ki faɗi komiye zan miki”.
    “Hindatu ba kowa yasan ƴarki ta rasuba, dan ALLAH ki bani gawarta, nikuma na baki guda ɗaya cikin ƴan biyu, inason ɗaya a cikinsu ta tashi a garin haihuwata, tunda ni an haramtamin koda zuwa cikinsa, dan ALLAH hindatu ki taimakeni, nasan har abada ba sake haɗuwa zamuyiba”.
    Fashewa tayi da sabon kuka tareda ƙankameni, tace, “Yaya mizai hanani aminta da shawararki, wlhy na yarda, ke kaɗai gareni kaf duniya, gashi kuma ƙaddara ta daɗe da shiga tsakaninmu, mizai sa bazan ji daɗiba idan har kika bar jininki a wajena amatsayin ƴar dana haifa”.
     Nace Na gode hindatu, sauri sauri muka cire kayan jikin Hassana muka maida jikin gawar Ɗahara, na ɗahara muka sakama Hassana, inaji ina gani nataho na baro ƴata hannun ƴar uwata, ko mahaifinta bai saniba, dan baba tozarci bana wasaba ya shigo har gidan Hindatu yanamin dagani har Ibrahim dake mota yana jirana shida Abubakar dake ya yayye. Saida mukazo gida nace masa Hassana ta rasu a madadin gawar Ɗahara ɗiyar Hindatu, damuwar da muke cikice ta kauda damuwar rasuwar Hassana a zuciyarsa, niko inata kewar ɗiyata tunda nasan bata rasuba. Tun daga wannan ranar ban kuma waiwayar ɗilauba, tunma ina kuka harna haƙura, naci gaba da rainon Husaina, bayan shekara biyu Husaina ta rasu saboda ƙyanda da tayi, daga nana Abubakar kaɗai ya rage mana a gabanmu, a legas muka cigaba da rayuwa har Abubakar yakai minzalin aure sannan muka dawo kd, koda muka dawo ban taɓa waiwayen ɗilauba, saboda katangar da Baba yaymin da ita, Har ALLAH yayma Ibrahim rasuwa bayan haihuwar Attahir kuma yanata burin hakan, amma ALLAH yay alƙawarin bazai sake taka ƙasar canba shiyyasa harya rasu bai cika alƙawarinsa na dai-daitani da Baba ba. Wannan shine labarina, inaji a jikina kuma lallai Ummukulsoom tanada alaƙa da ahalina, amma tambayoyin dazan matane kawai zasu bani wannan tabbacin.
      Jikin Hajiya Ummukulsoom ta faɗa ta fashe da kuka, “Hajiya wlhy basai kin tambayeni komaiba, ni ɗin jininki ce, dan kaf sunayen waɗanda kika ambata sun tabbatar min da hakan, Gwaggo hinde kakata ce, itace ta haifi mahaifita Ɗahara……”
     Ɗagota da sauri Hajiya yaya tayi, jikinta har rawa yake tace, “Da gaske kike ƴarnan?”.
     “Wlhy hajiya na tabbatar da hakane kuwa”.
     Fashewa da kuka Hajiya yaya tayi yanzu kam mai ban mamaki da yafi na ko yaushe, tabbas inhar maganar Ummukulsoom gaskiyane to itaɗin jinin ƴartace Hassana data bama Hindatu.
      
     Zaid da Bily dake maƙale a ƙofa suna kuka suma suka kalli juna, cikin kasa-ƙasa da murya maman Ahmad tace, “Ba kallon juna zamu zaunaba, hanyar ɗilau yakamata mu dosa ɗakko Gwaggo hinde”.
     “Maganarki gaskiyane Aunty Hafsat, kumuje kawai, insha ALLAHU daga nan zuwa bayan isha’i na tabbata zamu dawo”.
     A tare suka ɗaga kai tareda juyawa suka fita da hanzari.

      A ɗaki kuwa numfashin Hajiya yaya ne yafara gagarar ƙirjinta, hakane yasaka Abba da Attahir rikicewa, dan tabbas ciwontane ke barazanar tashi.
      Ummukulsoom da batasan komaiba akai tai masifar kuma rikicewa, sai girgiza hajiya yaya take tana kiran sunanta.
    “Attahir maza kira Ummin ku tazo da gaggawa”.
     A rikice Attahir ya amsa da to, tare da zaro wayarsa daga aljihu…………✍????


_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU????._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

????????karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863


*_ƴan Niger kuma_*

_ZAKU BIYA NE DA KATIN;_
*_MTN ko MOOV_*

*Novel 1 Naira 200 = 350fc,*
*Novel 2 Naira 300 = 500fc*
*Novel 3 Naira 350 = 550fc*
*Novel 4 Naira 450 = 750fc*
*Novel 5 Naira 500 = 850fc*

 _TA NUMBER;_
 *+22795166177*   


Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon wani*????????????????????????




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button