WUTSIYAR RAKUMI 34
Cak numfashin Amaan dake tsaye a ƙofar gate ɗin ya nemi ɗaukewa, tsaye suke shida Attahir da wani abokinsu a wajen, da alama wani abun sukeyi, Attahir ne kawai sanye da complet Uniform a jikinsa da ɗayan abokin nasu, Amaan kuwa wandonne kawai sai dark green ɗin t-shert data kamashi sosai.
Attahir da yaga Amaan ya tsirama waje ɗaya ido fuskarsa na kuma tsukewa sai abin ya bashi mamaki, dan haka ya kalli inda ya ke kallo shima.
Ummukulsoom ya gani tsaye da ƙyaƙyƙyawan saurayi tana zabga murmushi waya a hannunta tana dannawa, yayinda saurayin shima yake murmushin hakoransa waje yana kallonta, ta mika masa wayar dake tabbatar da tasace, da alama Number ɗinta ta saka masa.
Attahir ya janye idanunsa daga kansu ya maido kan Amaan da Abokinsu ke tambayar lafiya?, sai dai sam da alama hankalinsa bama ya wajensa.
Taɓasa Attahir yayi, ya lumshe idanunsa ya buɗe batare da ya kalli Attahir ɗinba, zuciyarsa wani irin zallo take tamkar zata fito waje, ga kansa yay masa wani irin masifaffen nauyi, sam baya fahimtar jawabin abokin nasu.
Sarai Ummukulsoom taga su Amaan tun lokacin da zata fito a motar Umar, hakan ne yasata biye masa dan ganin yanda gaba ɗaya hankalin Amaan ya dawo kansu, saboda ta sake ƙular dashi harda ɗagama Umar hannu da zai tada motar, bata bar wajenba sai da taga motarsa ta hau titi sannan ta saita kanta ta tako a hankali cikin nutsuwarta zuwa gate ɗin.
Sai da tazo saitinsu sannan ta kalli inda suke, da Amaan ta fara haɗa ido, amma tsabar wulaƙanci sai catai “yaya Attahir barka da yammaci”.
Murmushi Attahir yayi yana amsata da faɗin “Yauwa autan Ummi, an dawo lafiya?”.
“Lafiya lau yayana”. Ta faɗa tana yin gaba abinta tareda watsama Amaan harara, Abokinsu kuwa yabar wajen tunkan ta ƙaraso.
Ko motsi Amaan kasa yi yayi, dan tabbas ba’a taɓa masa irin wannan rainin ba da Ummukulsoom ta masa yau, shi bama wannanba, Ubanwaye wanda ya sauketa a mota? Dolene ya takama wannan yarinyar birki, inba hakaba wlhy zataja yayta karya ƴaƴan mutane a gabanta….
Yanda yake fidda numfashi da sauri-sauri ya saka Attahir kallonsa, fushi da tsantsar fusata ya hanga a cikin ƙwayar idanunsa, “Ajiwa lafiya kuwa?”.
Ƙin takama Attahir yayi, saima yabar wajen gaba ɗaya.
Attahir yay ƴar dariya yana girgiza kansa, zuwa yanzu kam yagama yarda Ajiwa yagane Ummukulsoom, tsabar miskilanci ne ya hanasa nuna hakan………..✍????
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU????._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
????????karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
*_ƴan Niger kuma_*
_ZAKU BIYA NE DA KATIN;_
*_MTN ko MOOV_*
*Novel 1 Naira 200 = 350fc,*
*Novel 2 Naira 300 = 500fc*
*Novel 3 Naira 350 = 550fc*
*Novel 4 Naira 450 = 750fc*
*Novel 5 Naira 500 = 850fc*
_TA NUMBER;_
*+22795166177*
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon wani*????????????????????????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????