NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 36

*_NO 36_* 


………..Tun da ga randa Amaan yazo gidan shan ruwa basu sake haɗuwa ba, ALLAH dai ya sota wajen da ya sa mata kunu bai tashiba, tunma a daren yabar zafi.

     Yau tana makaranta Baba ya kirata, bayan sun gaisa yake cewa, “Ummukulsoom dama magana nakeson muyi”.
     Nutsuwa ta kumayi sosai, murya a sanyaye dake nuna alamun a gajiye take tace, “To baba ina jinka”.
        “Ummukulsoom baƙya ganin zuwa yanzu ya kamata ki fidda miji kiyi aure kuwa? Tunfa muna ɓoyema mutane akan zamanki babu aure wataran zata bayyana kowa ya sani, niko bana fatan hakan gaskiya, dan maƙiya zasu mana dariya”.
     Idonta ne ya ciko da hawaye, amma ta daure ta haɗiyesu bata bari sun zuboba, ta gyara zamanta tana kuma raunana murya saboda ɗacin da takeji a maƙoshinta har zuciya, “Baba kayi haƙuri, insha ALLAHU zanyi, amma kaga watannine ya ragemin na gama shekara ɗayannan…….”
     Katseta baba yayi da faɗin, “Nasani Ummukulsoom, dan Alhaji Mahmud yaymin bayanin komai, jiya mun daɗe tare dashi akan maganarki, shima kuma ya amince da maganar ki fidda mijin auren, idan san samune dakin kammala shekara ɗayannan sai a kaiki ɗakinki, munyi maganar da Hajiya yaya da Gwaggo hinde da babanki Alhaji Abubakar, kowa ya amince da hakan”.
    Yanzu kam dai kasa riƙe hawayen tayi, suka ziraro bisa kumatunta masu ɗumi, muryarta na rawa tace, “Shikenan baba, insha ALLAHU zanyi ƙokari kodan na saka farin ciki”.
     “Yauwa Ummukulsoom, ALLAH ya albarkaci rayuwarki kinji ko”.
      “Amin ya rabbi baba, nagode”.
      “To masha ALLAH, kukan ya isa haka kinji share hawayen, ALLAH ya baki miji na gari”.
    Murmushi tayi tana share hakawayen, tanason babanta dan shima yana nuna mata ƙauna sosai.
      Bayan sunyi sallama class ta koma, lecture ɗaya ta rage mata, dan haka ana kammalawa tai yunƙurin wuce wa gida jiki a matuƙar sanyaye, dan itakam batasan wazata nuna ba amatsayin abokin rayuwarta.
     Umar yana sonta, itama kuma harga ALLAH bazata ce bai mataba, dan ya haɗu fiye da zaton mai hasashe, sai dai haka kawai batajinsa a zuciya a matsayin miji.
        Zata iya auren yaya Zaid ma, amma sam batajin hakan a ranta, saboda tun fil azal bata ra’ayin yin auren zuminci saboda wani dalili nata.
     “Abdul-Waheed” zuciyarta ta ayyana mata, nannauyan numfashi ta sauke, komai ya haɗa a yanda kowacce mace zatai fatan ya zam mijin urenta, sai dai bai bata damar sanin hallayyarsa ba, a yanda yake mu’amulantar ta kuma sam kamar ba son aure yake mataba, a ganinta kuma halayya itace abinda ma’aurata ya kamata su fara fahimta a rayuwar aurensu kafin maganar ƙyawun fuska ko wani ƙyale-ƙyale ya biyo baya, wannan kuskuren shiyya janyo mafi yawan rikicin aure a wannan zamanin, har ake gaza fahimtar ina aka dosane?……….
     Wayarta dake ring ce ta dawo da ita hayyacinta, ta sauke numfashi tana ƙoƙarin lalubota a cikin bag. Bily ce, dan haka ta ɗaga tana faɗin, “Babie yaya dai?”.
      Daga can Bily tace, “Komai dai-dai, cazan idan baki fito makaranta ba ki jirani nazo sai mu wuce kasuwar muyi gaba ɗaya mu hutu goben kawai”.
    Cike da gajiya ta ce, “Kai Bily, wlhy kin cika matsala, ALLAH na gaji sosai”.
     “Sorry Bestie, ALLAH ki daure kawai muje”.
     “Shikenan, amma ke yanzu kina inane?”.
    “Gani a taxi mana”.
 Yanke wayar Ummu tayi kawai batare da ta ce komaiba, ta samu waje ta zauna zaman jiranta, yayinda maganar baba keci gaba da mata kaikawo a rai.
    Ba tafi zaman minti talatinba saiga Bily ta iso, babu wani ɓata lokaci ta shiga suka tafi.

       Suna cikin kasuwa har 5pm, ga garin yay masifar ɗaurewa da hadari, hakan saiya saka Ummukulsoom ruɗewa, gashi duk taxi ɗin da suka tare saisu ganta da mutane, Ummukulsoom tamkar zatayi kuka, batason ruwannan ya taɓata saboda kanta dake ciwo sosai, ita kanta Bily dukta damu.
     Tafiya suka cigaba dayi a ƙafa suna kuma bincika abin hawan, ga maman Ahmad sai kiransu take, babu wanda ya samu damar ɗagawa, ita kuma acan Attahir nata mata masifa akan tana ganin hadarin miyasa ta barsu suka fita.
        Yayyafin da aka farane ya saka Ummukulsoom ja ta tsaya idonta na cika da ƙwalla, Bily ta kalleta cike da damuwa, ga kaya riƙi-riƙi a hannunsu. 
     “Bestie ya kika tsaya kuma?”.
     “Bily minene amfanin tafiyar tamu, tunda dai harma ruwan ya sakko gara kawai mu tsaya komu samu mafaka”.
       “Ok to mu tsallaka ga wata rumfa can”. Cewar Bily tana kama hannun Ummukulsoom.

         Zaune yake a bayan motar cikin Uniform, kayan sun masa ƙyau sosai, gaba ɗayan hankalinsa nakan lap-top da alama abu mai amfani ya keyi.
     A ɗarare Osin yace, “Sir! Ga wasu da alama suna bukatar taimako”.
     Shiru yay tamkar bazai tanka ba, harma sunɗan gota su Ummu dake ƙoƙarin tsallaka titi ya buɗe baki da ƙyar, “Ka tambayesu idan hanyarmu ɗaya”.
      “Ok sir, thanks you”.
  Bai sake cewa komaiba yaci gaba da abinda yake, Osin ya dawo baya gaban su Bily, kaɗan ya sauke glass ɗin gefensa yay musu nuni da su zo.
    Babu wani batun jan aji Bily tace, “Ummu inaga ALLAH ya kawo mai taimakonmu, saura kuma kice bazamu shiga ba”.
    Hararta kawai Ummu tayi suka nufi motar, Bily ce ta gane Osin, kamar shima da tana matsowa ya shaidata, yay murmushi yana musu nuni da su zagayo su shiga.
      Ummu da batason shiga gaban mota saita tura Bily gaba ita kuma ta buɗe baya ta shiga, Osin na ƙoƙarin nuna mata ta dawo gaba itama amma sam bata luraba.
      Sai da ta rufe motar hancinta ya shaƙo mata ƙamshin turarensa, dukda zuciyarta bata gaskata ba sai da gabanta ya faɗi.
       Shikam duk da yaji an shigo inda yake baiko motsaba, sai ɗago manyan idanunsa da yay a fusace ya zubama Osin harara ta Mirror.
     Osin yasan laifinsa, dan haka yay saurin faɗin, “Sorry sir”.
    Uffan bai ceba ya maida kansa ga lap-top ɗin.
     Bily da taga fuskarsa ta mirror tai saurin dafe baki, “kutt ashe hardashi a motar? Ta faɗa cikin ranta” A fili kuma tace, “Yaa Amaan ina yini”.
      Kamar zai share sai kuma ya ɗago dan yayi mamaki ambatar sunan nashi da tayi. ta Mirror ya kalleta, murya ciki-ciki yace, “Lafiya lau, daga ina kike haka cikin ruwa?”.
      “Yaya kasuwa mukaje ni da Bestie ruwan ya ritsamu saboda mun kasa samun abin hawa”.
        Bai tanka ba, bai kuma kalli gefen da Ummu takeba, dan amsar Bily ta tabbatar masa da itace, dama tun shigowarsu bugun zuciyarsa ya canja salo, musamman da ya shaƙi ƙamshinta.
       Ummu ma gaidashin da bily tayi yasata tabbatar da zarginta akan shiɗinne dai ashe, dan haka taki kallon inda yake, saima ƙokarin duba kayan cikin Handbag ɗinta take taga babu abinda ya jiƙe ko?, ganin komai normal ta ciro wayarta tana dannawa, jitake a ranta da tasan shine bazata shigoba wlhy, hannunsa data kona ranar ta ɗan saci kallo, gabanta ya faɗi, dan ganin wajen harya ɗaye alamar dai ƙunar ta tashi kenan, duk kuma saitaji babu daɗi, dan sam batai masa danta cutar dashi kamar hakaba.
    Ko tari babu wanda yayi tsakanin ita dashi, sai bily da Osin ne keɗan hira har suka shigo cikin Barrack ɗin.
       A ƙofar gidan Attahir Osin ya tsaya.
    Godiya bily tai musu, sai dai Osin ne kawai ya amsa, itakam Ummu uffan bata ce ba.
    Jin Bily ta fita, itama saita buɗe motar zata fita, wani feshin ruwa ya feso mata a fuska saboda ruwa ake tsulawa sosai, saurin dawowa tai baya ta maida murfin ta rufe tana sauke ajiyar zuciya tareda narke fuska kamar zata fasa ihu, musamman data hango Bily da har tana ƙoƙarin shiga gidan, buɗewa tai ta fita da sauri, sanyin ruwan dake jiƙata na shiga kowanne ɓargonta, ko kallon motar bata sake yiba ta shige ciki.
       Kallo ɗaya yayma bayanta ya ɗauke kansa, dan jallabiyar jikinta dukta manne mata a jiki saboda jiƙewa da tayi.
   Ya sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya yana sauke idanunsa inda ta tashi, ɗan kwalin jallabiyarta data zame ta riƙe a hannune ta manta, sai handkherchief.
     Hannu yakai ya ɗaukesu duka yana kallo, ya lumshe idanunsa tareda matsesu a cikin hannunsa, har suka ƙarasa nashi gida yana a haka, saida Abbas ya buɗe masa ƙofar side ɗinsa ya buɗw idanunsa da suka fara canja launi a hankalo, kayansa daya tattare yasa a ƴar jakar gefensa ya fara miƙama Abbas dake tsaye ya buɗe masa Umbrella, sannan shima ya fita, sam shi ba tsoron ruwan yakeba, dan haka yayma abbas nuni daya janye Umbrella ɗin kawai.
     
       Su Ummu kuwa suna shigowa maman Ahmad ta sauke ajiyar zuciya, haka shima Attahir, tambayoyi ya shiga jeho musu a jere sai kace ɗan jarida, sai da sukai masa bayani ne hankalinsa ya kwanta.
     Maman Ahmad kam coffee ta kawo musu mai zafi, godiya sukai mata da sannu, Ummu da gaba daya zuciyarta takuma dagulewa ɗauka tayi ta wuce ɗaki akan zata canja kaya, babu wanda ya hanata ko cemata danmi.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

          A cikin sati ɗaya su Suhailat suka gama binciko Fannah, ita harma tayi aure, amma kasan cewar babban burinta cin uban Baseeru babu musu ta amince da bukatarsu, harma ta fisu ɗaukar zafi akan lamarin.
     Zaune suke a falon Fannah dake aure yanzu haka a Abuja, kowaccensu cikin nutsuwa take cin pizza ɗin gabanta tana ɗora juice, Fannah tace, “Kun gane, bawai na raina shawararku ba, amma sam ku fahimci shifa ɗan halak baya maida bashin gaba da gaba, da soyayya ya yaudaremu, harma ya haɗa da damfara ku a gareku, to muma da ita zamu yaudaresa, yanzu kunga binciken mu ya nuna mana Meenal da ALLAH ya yankama kazar wahalar zama dashi a yanzu tanada shegen kishi, to da wannan kishin nata zamuyi amfani mu tarwatsa shi, abin ƙarin jin daɗi da farin ciki ƴan uwanta basonsa sukeba, shiyyasasuketa zugata tasha magani a ɓoye karta haihu dashi, amma saboda su sakata farin ciki basa nuna tsanarsa a gabanta sai abayan idonta, wannama damace da zamuyi amfani da ita”.
     “Lallai maganarki gaskiyace Fannah, to amma matsalar dai wazatayi soyayyar dashi yanzu?, mudai duk yariga da ya sanmu, rayuwar da mukai dashi ta shakuwa kuma bazai yuwu ace ya gaza ganemu ba”.
       “Hakane kuma Lubna, indai kuma kuna ganin wannan shawarar tayi nima na amince ɗari bisa ɗari, dan kuma wadda zatai soyayya dashi inaga zamu samu, waddama kuwa zatai saurin jan ra’ayinsa”.
     “Wa kenan?” cewar Lubna.
     Murmushi Suhailat tayi tana gyara zama, taɗan kurbi juice ɗin sannan tace, “Yarinyar ƙanwar Mom ɗina Zulfah, yarinyar ta haɗu, sannanfa gogaggace amma bata bariki ba, ina nufin tanada matuƙar wayo sosai”.
    Fannah tace, “Ok to indai hakane Why not musame ta muji”.
     “Wannan mai saukine, dan yanzu hakama tana Abujar nan gidan Aunty Amrah”.
      Babu bata lokaci Suhailat ta dannama Zulfah kira, sunci sa’a kuwa tana hanyar zuwa yawonta wajen shakatawa, dan haka ta canja akalar motarta zuwa inda suke.

     Tunda ta shigo Lubna da Fannah suka tabbatar zata iya, gata ƙyakykyawa kuwa, sai daifa da gani akwai ɗaukar kai, danda da farko ma iyayi zata fara musu, sai da Suhailat tace, “Zanci ƙaniyarki Zulfah, nutsu abu mai muhimmanci yasa muka kiraki”.
     Murmushi tayi cike da basarwa tace, “Sorry Aunty ina saurarenku”.
           A nutse suka zayyane mata komai, tare da nuna mata pictures ɗin Basiru da matarsa Meenal, wanda duk a social network suka samosu, bama wani yawane dasuba, dan Meenal batason ɗora hoton Basiru kar wata ta ƙyasa saboda ɗan banzan kishinta.
      Zulfah ta kalli pictures ɗin ɗaya bayan ɗaya tana wani taɓe baki, a fili tace, “Akwai ƙyau kam, sai dai babu ƙwarjini, lallai zaisan ya haɗu da Zulfy B mai tafiya daidai da zamaninsa, ku kwantar da hankalinku auntys na, indai wannan ƙaramin ƙwaronne wata ɗaya zuwa uku sai yazo gabanku a durƙushe, yanzu dai ina buƙatar mota”.
     “Indai Mota ce ki ɗauki tawa”. Cewar Suhailat ’.
    Murmushi Zulfah tai tana sake kallonsu, “Auntys ba wacce zan hauba, ta kafin alƙalamice wadda zata zama tarko, dan sonake a haɗuwata dashi ta biyu na masa ƙyautarta”.
    Cike da rashin fahimta duk suka kalleta, tai wani far da idanu, “Bazaku taɓa fahimta taba, amma bara na baku satar amsa. Yanzu ba soyayya kawai yake bukata ba, ba kuma kishine kawai zaisa matarsa da danginta fara shakku akansaba, dole sai an ɗorasa a hanyar cin amana, duk da kuwa shi ɗin gwanine wajen iyata, sai dai a yanzu ganin kamar ya hayene yasashi kwantar da kai, to ya kamata mu mu farkar dashi”.
      Basu wani fahimceta ba sosai, amma sanin halinta da Suhailat tayi sai tai saurin cewa, “Babu damuwa za’a nemo miki, babba kuwa”.
      Murmushi tayi tana mikewa, “Hakan yayi, dukkan wani ƙofar raminsa Aunty S ki turamin, zuwa ƙarshen sati idan nagama nazarinsa zan fara aiki a kansa”.
      Da kallo kawai suka bita na mamaki, ƴar ƙarama da ita sai tsaurin ido, gaba ɗaya bazata wuce 24years ba. 


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

         “Bily wlhy ina cikin matsala”. ‘Ummukulsoom dake shirin kwanciya ta faɗa murya a raunane’.
     Tashi Bily tai zaune a tsorace tana kallonta, “Damuwa kuma Ummu, wace iri?”.
       “Humm, Bily ɗazu baba ya kirani ina makaranta, wai lallai saina fidda mijin aure, kuma ina ƙyautata zaton wannan maganarce zata kawo Abba garinnan gobe”.
        “Humm Ummu wannan matsalar tamuce mu duka, dan kuwa hardani a ciki, dan kina makarantane, amma Hajiya yaya itace ta fara kira bayan tafiyarki, na tabbata meeting akai akanmu ni da ke da yaya Zaid”.
    “Wai har shi ma?”. ‘Cewar Ummu tana ƙwalalo idanu waje’.
    “Wlhy kuwa karkiji wasa, ai Hajiya yaya tace, ta kira Number ki bai shigaba ke da yaya Attahir, shinefa ta kira a ta aunty Hafsa”.
       “Na shiga uku Bily ya zanyi? Gara ke kinada Huzaifa a hannu”.
      “Humm wai inada Huzaifa a hannu, kinsan kuwa yaya mukai dashi jiya da daddare?”.
     “A’a ki faɗa ba yaza ai in sani”.
      Cije baki tayi cikin takaici, Ummu wlhy maganar babu daɗin ji, Huzaifa ba sona yake dan ALLAH ba, sha’awata kawai yakeyi, dama yasha min zancen banza ina sharesa, sai jiya ya nunamin asalin wanene shi da manufarsa a kaina, karanta massege ɗinnan kiga”.
    Amsar wayar Ummu tayi ta karanta, gaba ɗaya fuskarta ta nuna ɓacin rai, cike da fusata ta ɗago tana kallon Bily, “Wai da gaske shine ya rubuto?”.
    “Humm Ummu kennan, wlhy shine, ribarmi zanci idan na masa ƙarya, kin riga da kinyi barci a time ɗin, inaga kawai zanba Muhseen dama, dan na lura shikam domin ALLAH yake ƙaunata yanzun”.
        “Dakin birge kuwa Bily wlhy, shawarar da naketa baki kenan tuni amma kikaƙi fahimta ta, saboda son Huzaifa ya lulluɓe ganinki, nifa dama shiyyasa sam bai minba wlhy, amma sai kike ganin kamar kushesa nakeyi”.
      “Ai yanzu kam na gane gaskiya bestie, kuma ko a baya bawai inakin jin maganarki baneba, kawai dai ki ɗauka ƙaddaratace yin soyayya dashi”.
     “Ito hakane kuma, ALLAH ya zaɓa wanda yafi alkairi tsakanin shi da Huzaifan”.
       “To amin aminiya, yanzu ke mikika yanke akan nakin?”.
    ”Ban yanke komaiba Bily, inaga zanma Umar magana”.
    ”Umar kuma? Please dan ALLAH a’a, bawai fa bai cancanta bane, Umar handsome ne sosai, sai dai matsalar gaskiya ya miki yarinta, baifi shekaru uku fa zai iya baki ba wlhy”.
    “Kai bestie bana son sheri, Umar ɗinne baifi shekaru uku ya bani ba? Gaskiya a’a, wannan mazgegen ƙatonne zakice bai ban shekaru fiye da uku ba?, kedai kawai kice bai mikiba, kuma idan ban fiddashi ba bestie wa gareni?”.
    Shiru Bily tai tana tunani, itafa dason samun tane wlhy Ummukulsoom ta koma gidan yaa Amaan, amma sam ta lura su hankalinsu baya akan juna, tarasa miyasa hakan?….
    Kafin tasamu damar bayyana tambayarta a fili saƙo ya shigo wayar Ummukulsoom, kallon wayar sukai su duka, kafin Ummu ta ɗauka jiki a sanyaye, tasan dai bazai wuce A-Waheed ba, ilai kuwa shine, kallon Bily tai da ta tsareta da ido, kafin ta buɗe saƙon.
  
      _Amincin ALLAH ya tabbata a gareki, yau dai zuciya na buƙatar jin motsin ƴar uwarta, kokin bani damar jin sautin muryarki?._
         *_Naki UMA_*

   Sake maimaita saƙon taketa yi, gaba ɗaya ƙwalwar kanta ta gaza ɗaukar komai yanda ya kamata, tsawon watanni Huɗu da fara wannan ƴar wasan ɓuyar tsakaninta dashi, sannan kusan wata uku kenan bama ya a makarantar su, a wani massege daya turo mata yake shaida mata zaiyi tafiya, amma tafiyarsa batada shamaki da ita,  tundaga wannan lokacin bata sake ganinsa ba, saidai kuma babu fashi masseges nashi kullum saisun riski wayarta….. 
      Ring ɗin wayarta ne ya katse mata tunaninta, ta ɗan zabura saikace wadda taga abin tsoro, sai kuma ta ware idanunta akan screen ɗin wayar tana kallon sunansa ɓaro-ɓaro a jiki.
     yankewa tayi ya sake kira, amma har lokacin Ummu ta kasa ɗagawa, ganin ta kusa tsinkewa kuma bata da niyyar ɗagawa sai Bily ta amsa ta ɗaga ta saka mata wayar a kunne tareda sauka a gadon tama fice daga ɗakin, a ranta tanajin haushin wannan Abdul-Waheed ɗin, tanaji a ranta shine zai raba Ummukulsoom da Yaa Amaan, saboda ta kula tana sonshi sosai dukda yana ta faman wasa da hankalinta……..✍????


_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU????._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

????????karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863


*_ƴan Niger kuma_*

_ZAKU BIYA NE DA KATIN;_
*_MTN ko MOOV_*

*Novel 1 Naira 200 = 350fc,*
*Novel 2 Naira 300 = 500fc*
*Novel 3 Naira 350 = 550fc*
*Novel 4 Naira 450 = 750fc*
*Novel 5 Naira 500 = 850fc*

 _TA NUMBER;_
 *+22795166177*   


Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon wani*????????????????????????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button