NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 4

*_WUSHIYAR RAƘUMI….!!_*
*_NO. 4_*

   ………..Kasancewar basuyi fitar wuriba sai gab da magriba suka isa cikin kaduna, koda mota ta ajiyesu a
kawo sai suka hau napep zuwa Tudun wada anguwar su Inna Harira ƙanwar baba.
    Ita dai Ummu babu abinda take sai kallon hanya, dan wannan shine zuwanta na uku da wayonta dai.

        Gidane madaidaici mai jan murfi baba ya tsaya, ya tura ƙofar suka shiga, a soro ya tsaya yace Ummu tashiga sannan.
     Da sallama Ummu tashiga gidan, budurwar dake a tsakar gida tana kwashe kayan shanya ta amsa mata, duhun magriba ta rufa, gashi babu wuta shiyyasa bata fahimci waneneba, tace,
     “Wacece dan ALLAH?”.
     Murmushi Ummu tayi, dan ta fahimci Azizah ce ɗiyar Inna harirah, dukda dai taɗan jima bata gantaba tun bikinsu Azima. Cikin tsokana Ummu tace, “Ƴar yankar kaice”.
     Maganar saita bama Aziza dariya, dan haka ta sagale kayan da tafara kwashewa a igiyar tare da takowa inda Ummu take a hanyar shigowa.
     Wani ihun murna Aziza ta saka tana faɗin “Kan bala’i Ummukulsoom! Tab wlhy badan fuskarki bata canjaba da ban ganeki ba, sannu da zuwa keda wa?”.
     “Nida Baba ne”. ‘Ummu tafaɗa tana nuna zaure da hannu’.
       Inna Harirah data idar da salla ta leƙo tanama Aziza faɗa, “Wai Aziza kanki lafiya kuwa? da mangaribar ALLAH kiringa kira mana bala’i a cikin gida? Keda wace Ummukulsoom ne?”.
      “Yi Haƙuri mama, wlhy daɗine yasani faɗa ban shiryaba, Ummukulsoom fa ta ɗilau, hardama baba buhari”.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});     Da sauri Inna harirah ta ida fitowa daga ɗaki tana gyara ɗaurin zani, “Da gaske ɗiyatace yau agidan? Ina yayan shima?”.
    “Aiko dai itace wlhy mama”.
     Ummu dai dariya taketa musu, yayinda shima baba yay sallama ya shigo.
      Murna sosai takuma kaurewa, dan Inna harira taji daɗin zuwan Ummu, dama kullum cikin yima baba tsogumi take akan rashin barin yaransa zuwa wajemta sosai, mazan sunfi zuwa.
      Alwala baba yayi yatafi masallaci, Ummu ma haka tayi tata agida. 
       Sai da suka nutsu bayan baba ya dawo da malam ɗanjuma baban Aziza sannan aka samu nutsuwar zaman gaisawa da taɗin zuminci. Ummu dai bata iya saka baki sai an sakota, saima Aziza dake  zungurinta idan taji tayi shiru.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

           Ɓangaren Baseer kam Alhmdllh shima yagama jarabawarsa, a yanzu haka satinsu ɗaya kenan, amma yaƙi tafiya ɗilau, wai sai yayi bautar ƙasa (NYSC) ɗinsa sannan yahuta gaba ɗaya kenan.
      Innarsa bataja maganarba, ta shirya taje ɗilau ta sanar musu da yanda sukayi da Baseer, aiko mahaifinsa ya shirya da kansa yabita zaria n, saida yayma Baseer tsiya ta fitar hankali sannan yashirya suka koma ɗilau da baba, babban baƙin cikinsa ma baiyi sallama da Suhailat ba saita waya.
    Abin mamaki tunda Baseer ya dawo ɗilau ya nane a gida baya fita balle kai tunanin zai nemi hanyar gidansu Ummu yaje ganinta. Hakan da iyayensa suka ganine ya sasu zaunar dashi sukai masa bayani gameda aurensa da Ummukulsoom da har an tsaida rana.
    “Baba an tsaida ranafa? Miyasa ba’a bari nadawo anji ta bakinaba? Wlhy ni zanmafa cigaba da karatunane na mastas (masters)”.
      “Kai kasan wani masta basiru, aure dai mun ajiye rana kuma babu fashi, tun watan jiya ma an fara ginin gidanka a faƙon amare”.
      “Inna ban ganeba, ni aka farama gini a garinnan? To na ƙasa kona siminti?”.
     Wane shege kabama kuɗin sayen simintin da za’ai maka ginin bulo da bulo? Basiru wlhy karka kaini wuyafa, bar ganin muna lallaɓaka, kai bazaka dawo cikin hankalinka bane waishin? Wane irin ruɗi duniya da ganga sheɗanne ke buga maka? Banda rashin hankalima inakai ina yarinya ƴar birni ƴar masu kuɗi? Kai kanama ganin iyayenta zasu bakane……?”
      “ALLAH baba zasu bani, naga idan na auri Suhailat kumafa zakuji daɗinnan, dan ɗaukeku zanyi na maida binni.”
     “dalla rufama mutane baki shashasha kawai wanda baisan ciwon kansaba”.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});        Shiru basiru yayi yana ɓata ƙyaƙyƙyawar fuskarsa fara tas.

          A ranar da yamma ya shirya yaje gidan su Ummukulsoom, bawai dan taji daɗiba kodan shi yana ɗokin ganinta, a’a soyake yaje yaja mata dogon gargaɗi akan tace ta fasa aurensa, dan yasan hakanne kawai zaisa iyayensa su barsa, soyakema yakoma zaria gobe bazai iya zaman ƙauyennan ba wlhy.
     Koda Baseru yaje ya aika yaro kiran Ummukulsoom sai yaron yace ai bata nan, jiya suka tafi kaduna itada Baba.
      Shiru Basiru yayi takaici na cinsa, haka yabaro ƙofar gidan yanata wani ɗaɗɗaure fuska shi adole mai aji, ko magana wani yay masa a hanya sai dai ya ɗaga hannu yana wani basarwa. Can yakoma bayan gari tafkin da jama’ar ƙauyen ke ɗibar ruwa, yasamu waje ya zauna yana tunanin mafita, ganin wankin hula zai kaishi dare ya yanke shawarar shiryawa yaje zaria koda yini ɗayane ya gana da abokansa su Areef.
     Da wannan shawarar yadawo gida yana shaidama innarsa ashe Ummu taje kaduna?.
         “Au kaduna taje? Ko shiyyasa ɗazun a gidan raɗin sunan Amina Rashida ke cemin ƴata antafi birni?”.
     “Aiko dai inna, nima duk sainaji babu daɗi daban sametaba, inaga gobe idan ALLAH ya kaimu zanje kaduna na yini da yamma saina dawo?”.
      ”A gaskiya ina bayanka kaje, yanda kusan shekara ɗaya kenan baku haɗuba yakamata kaje, itama zataji daɗi”.
     Kallon Inna yayi a kaikaice yana murmushi kawai dashi kaɗai yasan fassarar kayansa, kafin daga bisani ya amsa mata da “to inna”.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});       Washe gari kam kamar gaske Baseer yay shiri yace musu yaje kaduna, baba harda bashi kuɗin mota, nanko zaria ya yada zango, ko gidan innarsa baijeba yanufi gidansu Najeeb abokinsa.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡ 

        Ummukulsoom taji daɗin zuwanta kaduna sosai, balle ga Aziza da suke kusan sa’anni, komai tare sukeyi abinsu, Baba ma washe gari yabar gidan, dan dama ba’anan yake zamaba idan yazo, yanada masaukinsa saidai ya leƙo su gaisa.
      Kwanan Ummukulsoom tara a gidan ranar Aziza take ce mata gobe zata koma gidan aikinta, iyalan gidan Alhaji Sufiyan sun dawo daga tafiyar da sukayi.
       Ummu dake kwance tana karatun novel ta tashi zaune tareda ajiye buk ɗin, “Ban ganeba Aziza, aikinmi kuma kikeyi?”.
     Murmushi Aziza tayi tana cigaba da gugar kayanta da takeyi da dutsen guga na gawayi, “Ummukulsoom kinsan rayuwa irinta yanzu ba’a zama, ballemu rayuwa ta birni bakamar taku ta karkara ba, nauyi yayma baba yawa shiyyasa bayan munyi candy naga da zaman banza gara ko wani abun naɗanyi, akwai makwafciyarmu tana nema ma yara gidan aiki shinefa namata magana ta samarmin gidan Alhaji Sufyan, da ƙyar baba ya yarda nafara, itama mama saida naita roƙonta wlhy, nakan musu share-share da goge-goge sai kula da yaransu, duk wata dubu goma sha biyar”. 
       Cikin zaro idanu Ummu tace, “Aziza dubu sha biyar fa? A waɗannan ƴan ayyukan kawai?”.
       “Wlhy kuwa Ummu, shiyyasa suma su baba suka barni, kuma ga alkairi da wataran haka kawai za’ai miki, yanzu haka ɗan anko da ƴan abubuwa na kwalliyar ƴa mace basai na takurama su baba suminba, da kuɗina nakeyi”.
       “A to nima kam ba’a barina baya wlhy Aziza, ni ɗinnan da kina gani an saka ranar biki, ga baba nauyi yamasa yawa shima kuma bawani ƙarfine dashiba, kinga insha ALLAH kafin dai na koma gida wlhy nasamu abin taimakonsa”.
     “Hakane wlhy Ummukhoolsum, kuma tundama bikin ansaka da nisa basai kiyi zamankiba har sai lokacin ya matso, kinga ƙya tara ko yayane”.
       Haka sukaita tattauna maganar, Aziza nakuma wayar mata dakai gameda aikin. Daga ƙarshe suka sanarma Inna harira.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});      Shiru Inna harira tayi tana nazarin maganar tasu, dan wannan kam dole ta tuntuɓi yayanta, idan ya amince babu komai sai Ummu ta fara zuwa.
       Da daddare Baba yazo gidan bisaga kiransa da Inna harirah tayi masa a waya, bayan sunyi hirarsu ta zuminci saita zayyano masa zancen aiki da Ummu tace zatayi.
     Da farko dai cayay a’a, saida Inna harira tai masa bayani na gamsuwa sannan ya fahimci maganar, saima ya amince kai tsaye, yace “Harira to babu laifi, yanzune na fahimci zancen naki, idan ita Ummukhoolsum ɗin taga zata iya sai tayi, fatana dai ALLAH ya karesu daga sharrin wasu ƴaƴan manyan na rashin tarbiyya”.
      “To amin yaya, ai lamarinnema yanzu basai ƴaƴan manya ke lalata yaraba, ƴaƴan talakawanma taƙadirane, fatanmu dai ALLAH ya karesu aduk inda suka tsinci kansu”.
     “To Amin ya rabbi harira”.

***********

       Washe gari inna harira da kanta tashiga gidan Rahine taimata bayani a samawa Ummu gidan aiki dan ALLAH, amma na mutanen kirki irin gidan da Aziza ke nata.
       Baki Rahine ta washe tana faɗin, “Wlhy faɗuwa tazo dai-dai da zama, dama maƙwaftan gidansu Alhaji Sufiyan ɗin suna neman mai aiki kuma budurwa kamardai Aziza, kuma suma basuda damuwa, aiko yau ɗinnan ta shirya sainaje na nunata, ALLAH yasa a dace, ina mai tabbatar miki maman Aziza yarinyar zataji daɗin zama gidan Alhaji Mahmud Ajiwa, tsohon sojane mutumin kirki wlhy”.
     Murmushi Inna harirah tayi tana cewa “To Alhamdulillahi, babu damuwa bara na tura miki ita kuwa”.
        “To tayi maza tazo kuwa mutafi, dan ba’a sakaci da irin wanga dama kar wasu su rigamu”.

        Sosai Aziza tai murna dajin gida kusa da kusa zasu ringa aiki, koba komai zasuga juna kullum.
     Itama Ummu taji daɗin hakan, dan haka tafara shiri kamar yanda Inna harira ta sanar mata.

★★★★★★★

      Ummukulsoom na zuwa ta iske har Rahine tagama shirinta itama, dan haka suka fita zuwa gidan aikin.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});        Tunda mai napep ya tsaya Ummukulsoom ta saki baki da hanci da idanu tana kallon katafaren gidan, “Oh ALLAH mai rahama mai jinƙai, kiga gini tamkar baza’a mutuba, saima ka ɗauka ba hannune ya ginaba”.
    Dariya Rahine tayi saboda a fili Ummukulsoom tayi maganar, “Kinga muje ciki, keda zakiyi aiki acikinsa miye na santi tun yanzu?”.
      murmushi Ummu tayi tabi bayan Rahine.
       Sai da suka gaisa da mai gadin soja sannan sukai ciki, Duk tsoro ya kama Ummu ganin soja, arayuwarta tana bala’in tsoron soja da ɗan sanda wlhy, kuma batasan daliliba, itadai suna mata kwarjinine kawai.
        Rahine ta katsema Ummu tunani da faɗin, “Kinga Ummukulsoom zauna a gaban Fulawarnan nashiga na shaidama hajiya zuwanki sannan”.
      Ummukulsoom ta amsa da to.
       Kusan mintuna talatin da shigar Rahine saigata taleƙo ta yafito Ummukulsoom da hannu alamar tazo. Tashi Ummu tayi ta nufeta, dama zaman dukya gundureta saboda sojan mai gadin can da take hangowa.
        Da ƙyar numfashin Ummu ya daidaita saboda ganin daular dake cikin falon da suka shiga, ga wata hamshaƙiyar mace dukda shekaru sunja gareta hakan bai hanata cake gayuba tamar zata biki. Duk zumuɗin Ummu na zuwa gidan aiki sai taji jikinta yayi sanyi, ta zauna a ƙasa tamkar yanda taga Rahine tayi. Muryarta har ƴar rawa take tace, “Hajiya ina yini, mun sameku lafiya”.
       Jitai ba’a amsaba, saita ɗago kai ta kalli hajiyar azatonta bataji baneba. Amma sai tayi karo da idon Hajiya na ƙare mata kallo sama da ƙasa. Kanta ta maida ƙasa ta sunkuyar.
     Cikeda isar masu ƙasaita Hajiya Jamila tace, “Minene sunaki?”.
      Ummu ta haɗiye wani yawu daya daskare a maƙoshinta kafin tace, “Ummukulsoom”.
     Kusan minti biyu kafin hajiya tace, “Ba laifi Rahine, tayi, dan nakula tanada ƴar wayewar kai bakamar kidahumar yarinyar da kika kawo ranarba”.
     Rahine ta washe baki tana faɗin, “Alhmdllhi hajiya, amin afuwa da kawo waccan ɗin, ita wannan ai tayi karatu bakamar waccanba”.
     “Yayi” kawai Hajiya jamila tafaɗa tana jawo handbag ɗinta dake gefenta, ƴan dubu-dubu ta jawo aciki tana miƙama Rahine,
      “Ga wannan dubu talatinne, ashirin kuɗin aikinta, biyar kuma ki ɗauka, biyar ɗin kije da ita a wanke mata kai daduk abinda ya dace, kinsan banason ƙazanta hakama yarana, zuwa gobe sai tazo tafara aikinta ko jibi, dan inaga gobe zan yini gidan bikine?”.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});       “To hajiya ALLAH ya saka  da alkairi, ya ƙara buɗi, kidaɗe kina zamani Uwargida kuma Amarya agidan Alhaji”.
    Ummukulsoom dai najinsu hajiya ko uffan bataceba, saima yunƙurin miƙewa da takeyi.
    Hakanne ya saka suma suka miƙe suka fito, mamaki nacin zuciyar Ummukulsoom, shin tunkanma ta fara aikin har anfara biyanta albashi kenan?.
        Kasa daurewa tayi, bayan sun shiga napep tace, “Baba wai kenan tunma kafin mutum ya fara aiki suke fara biyansa kuɗi?”.
      Dariya Rahine tayi, “Ai Ummukulsoom kaɗan daga halin kirki na Alhaji Mahmud Ajiwa kenan, kinga wannan albashin data baki? To abinda ya bata na tabbata ya ɗara hakan, amma babu komi ko hakama Alhmdllhi, kafin wani lokaci saikiga kin tara arziƙi, kedai kawai ki kwantar da hankalinki, duk abinda suka nuna basaso karkiyi”.
      “Insha ALLAHU baba zan kiyaye, dan wlhy ni yanayin matarma saiya saka jikina sanyi, sainaga kamar tanada wulaƙanci?”.
      “Ummukulsoom kenan, karki saka wannan a ranki, kedai kawai kiyi abinda ya kaiki, idan har baki shiga hurumin taba bakida matsala da halinta insha ALLAH, yarinyar dana kaimusu kwanaki ƙazamace, shiyyasa suka koreta, kuma karki ɗauka ke kaɗaice mai aiki a gidanfa, a’a akwai wasu, sai dai basa bari su shigar musu sashe, kekuma aciki zakiyi musu aiki bakamar sauran ma’aikatanba”.
       “ALLAH sarki, to ALLAH ya bamu sa’a baba Rahine”.
     “Amin ƴarnan”.

Da wannan firar suka ƙarasa gida, sosai inna harira tai farin ciki da har anfara bama Ummukulsoom albashi, nan take takira baba ta shaida masa. Yace ta adana mata kuɗinta shi babu abinda zaiyi dasu.
      A ranar Rahine ta ɗauki Ummukulsoom takaita shagon saloon domin a wanke mata kai daduk abinda ya kamata wanda hajiya bazatayi tsogumiba.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

          A ɓangaren Baseer kuwa shima ya isa zaria, inda suka samu zama shida shaƙiƙan abokansa uku, Najeeb, Areef da Abdull.
     Abdull dake saman mota zaune ya kalli Baseer dake gefensa yace, “My guy wai ina kaje ka maƙalene anata harka babu kai? Lokacifa yayi da zamu afka camp”.
       Cikin takaici Baseer yace, “Bazaka ganeba Abdull, ina cikin tsaka mai wuyane wlhy, nima hankalina duk yana Camp ɗin”.
     “Mike damunkane?” 
Cewar Areef dake cikin mota amma yabuɗe murfin ya zuro ƙafafunsa waje duka, Najeeb na zaune daga sama shima.
     Numfashi Baseer ya sauke yana jan tsaki, “Wato akwai wata yarinya tun muna ƙanana haka nake tsokanarta irin budurwata-budurwa ta ɗinnan, so ayanzu fa shine su dad suka wani dage wai saina aureta, harma sunkama kai kuɗi an tsaida ranar aure”.
     A tare su Najeeb sukace “Aure!!?”.
    Kansa ya ɗaga musu zuciyarsa nakuma harzuƙa.
       Abdull yace, “Haba guy dole kayi baƙi ka rame, to kai yazakayi da Suhailat ne?”.
     “Ai ba ya zaiyi da Suhailat zaka tambayesa ba, cazakai dama yanason yarinyarne amma yake yaudarar Suhailat?”.
      Harara Baseer ya danƙarama Areef mai maganar, “Areef banason iskancifa, a zancena nace muku tun tana ƙarama nake tsokanarta, kuma tana ɗan shan wahalane a gidansu shinefa nake nuna tausayinta, tosukuma su mom nalura sun ɗauka wani sonta nakeyi har yanzu, mafita nazo kubani ba surutan banzaba guys”.
       Dirgowa Najeeb yayi daga saman mota yadawo kusa da Baseer yana dafa cinyarsa.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});      “Bas kawai ka nuna musu kaifa ba sonta kakeba kanada wadda kakeso, ai dai ba aima namiji auren dole naga”.
      “Bazaka ganeba Najeeb, dad ɗina shegen taurin kaine dashi, yanzu dana nuna banayi zaima iya aurota ya ajiyemin kokuma yay fushi dani, adai canja wata shawarar”.
             Tsaki Abdull yayi duk suka kallesa, yace, “Nifa ina takaicin iyaye irinsu dad ɗinnan naka, sai suyita abu kamar basu gama wayewaba, ni shawarata kawai yarinyar zaka samu kaja mata dogon gargaɗi, kokuma mu saceta mu ɓoye, saimuga wadda za’a sakaka ka aura”.
      Kwashewa sukayi da dariya suna tafawa, Baseer yace,
     “Ai matsalar shine batanan tayi tafiya, kuma bansan ainahin inda takeba, kai Areef minene shawararka?”.
     “Ni gaskiya duk shawararku bataiminba, abinda kawai nake gani inhar kanason Suhailat kace tafito kuyi aurenku, ko a gidanka saita cigaba da karatunta, sukuma su momcy idan sunga kadage ga mata kakawo duktaurinsu sai sunyi laushi, kaidai kadage akan ra’ayi ɗaya”.
    Shawarar Areef tayifa, amma gameda dagewa su dad karyayi haka, yabisu ta siyasa kamar yanason aure, sauran shawarar matakin da zaka ɗauka agaba zan faɗa muku”.
      Duk sun amince da shawarar Najeeb ta ƙarshe, dan haka sukabar zancen ahaka.

          Baseer bai koma Ɗilau ba a ranar, saima wajen Suhaulat yaje makaranta sukasha hirarsu har dare, sannan ya tafi gidansu Najeeb ya kwana.
       Da safe ƙanwar Najeeb tazo kawo musu breakfast taga Baseer, rikicewa tayi sosai, dan baƙaramin ɗaukar hankalinta ƙyawun Baseer yayiba, aranta faɗi take dama ana samun indiyawa a cikin hausawa haka?, samun ƙyawawa irin Baseer acikin hausawa sai an tona, itadai ana cewa mutum tara yake bai cika gomaba to zata rantse Baseer yacika cif, dan bataga abin kushewa ko kaɗanba a jikinsa (niko nace tawajen a haline bai cika gomanba ai????).
       Tsaf Baseer yalura da kallon ƙurillah da Nehal kebinsa dashi, shiyyasa yaketa kuma kamewa yana basarwa, yasan ƙyawun da ALLAH yamasa ba ƙaramin kankaro masa mutunci da kima yakeba wajen Al’umma, shiyyasa yake alfahar da ƙyawun nan nasa, dan shine ƙarfin ikonsa”.
     Nehal dai ta zurma kam akan son Baseer, saidai kunya tasata yin kawaici, yayinda ƙasan ranta ta ɗaura aniyar saita mallakesa matsayin mijin aurenta kota halin ƙaƙa………….✍????

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

????????????????????‍♀Ummu kin bani gata uku tazo.????????‍♀⛹‍♀



_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU????._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

????????karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke, abari ya huce shikesa aci lami????⛹‍♀*????????????????????????





*_ALLAH ya gafartama iyayenmu????????????_*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button