NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 3

*_Wutsiyar raqumi_*
_*Billyn abdul*_
*_NO 3_*

   ………..Yau akaima su Ummukulsoom busting amma ko alamar Baseer ɗinta bata ganiba, sai baba ne yazo mata shi
da Inna Laraba, tayi farin ciki da ganinsu tamkar yanda ta saba.
      Baba kasa haƙuri yayi ya tambayeta ina basiru?, dan yasaba duk zuwan da zasuyi anan suke iskeshi ya rigasu zuwa.
    Kan Ummu a ƙasa tace, “Baba bai zoba”.
     Baba yay Murmushi idonsa a kanta, “Karki damu Ummukulsoom, zata iya yuwuwa wani uzurine ya hanashi zuwan, yaron yanada himma, tunda aka kawoki makarantar nan yake ɗawainiya da zuwa dubaki duk bizitin, dukda kuwa shima cikin hidimar nasa karatun yake”.
     Kafin Ummu tace komai Inna laraba ta karɓe da faɗin, “Ai basiru yaron kirkine, ga hankali, banyi zaton zai riƙe alƙawari irin hakaba, musamman yanda naga ya canja yanzu yazama ɗan birni na sosai, ga tsoron zantukan jama’ar ɗilau akan alaƙarsa da Ummu, kowa faɗi yake yafi ƙarfinta yanzu”.
       Dariya Ummu da Baba suka sanya saboda furucin Inna Laraba da tace yazama ɗan birni, furucinta na ƙarshe kuma yasaka zuciyarsu harbuwa, ita kanta Ummu maganar na damunta, tana dannewane kawai dataga babu wani canji daga Baseer ɗin har yanzu..
      Bayan tafiyarsu duk sai Ummukulsoom tashiga damuwa, dan dama a irin wannan lokacin idan sun tafi akan barta da Baseer ɗintane, sukuku tazama gaba ɗaya, daga ƙarshema saitai komawarta hostel, zuciyarta dai namata fatan ALLAH yasa lafiya ta hanashi zuwa, dan ita tafi zargin koma bayajin daɗine.


⚡⚡⚡⚡⚡
       
     Soyayyar Suhaila tai bala’in ɗauke hankalin Baseer ya fara mantawa da wata Ummukulsoom, gidama yaƙi zuwa, ko waya sukayi da iyayensa sai yace karatune ya riƙeshi.
          Soyayya ce mai ƙarfin gaske a tsakaninsu yanzu, abinma saiya baka matuƙar mamaki, zuwa yanzu kam tagama fahimtar shiba ɗan kowa bane, amma hakan baisa taji ta daina sonshiba, dan ƙyawunsa na ɗibarta matuƙa, aganinta shine miji na nunama sa’a, dan kuɗi ba matsalarta bane, zatabi hanyar da zata ginashi ya jiƙe kafin aurensu, yanda ƙawayenta zasuyi respecting nashi 100%.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});         Saima ta samu ƙwarin gwiwar buɗe bakin aljihu tashiga kashe masa kuɗi da masa bajinta tamkar hauka, kai kace itace saurayin shine budurwar, babu ɓata lokaci ta koya masa mota, kaya na ƴan ƙwalisa kam kullum cikin saya masa take, a kwana kaɗan yakuma zama handsome na gaske, ƙyawunsa da taƙamar girman kai takuma bayyana, dan Suhaila har barmasa motarta take wajensa ta kwana, ko an tambayeta a gidan tasan ƙaryar da zata shirma.
     A karatunta sosai yake taimakonta, dukda 100L take, shikuma yana shekarar ƙarshe. 
       Daɗin da Baseer ke samu ga Suhailat yasashi kuma mantawa da Ummukulsoom gaba ɗaya balle alƙawarinsu ko soyayyarta, idanunsa sun rufe Suhailat kawai yake gani, ko yaushe suna nane da juna, sai dai idan ta tafi gida, shima zaka samesu suna charting ko waya.
       Wannan ne yasa har akayi Busting ɗin su Ummukulsoom bai jeba, toshi gaba ɗayama ya manta da lamarinta. 
      Sai bayan busting ɗinne innarsa da yake zaune a wajenta ta matsa masa yaje ganin gida, dan ita lamarin Basiru tsoro yafara bata, gaba ɗaya ya canja, baƙin abubuwa idan ta ganshi dasu ta tambayesa saiyace saya yayi, maƙwafta harsun fara dangantashi da Homo saboda anga ya zama babban yaro dare ɗaya.
       Hankalinta sai ya kuma tashi itada mijinta, dan  sun rasa sana’ar ubanmi yake da yakema kansa hidimar kuɗi, sai daga bayane ta fuskanci mike faruwa shida Suhaila, hakanne yasata shiryawa taje ta zayyanema iyayensa komai gameda halin da yake ciki.
     Hankalinsu yatashi akan Suhaila zata lalata musu yaro, hakkanne yasasu cewa ta turoshi gida.


Humm Baseer, shegiya naira inji ibro⛹‍♀????.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

          Ummukulsoom kam batasan mike faruwaba, tananan maƙale da son Baseer ɗinta, burinta tagama jarawarnan dake gabanta ta ssce ta koma gida suyi aurensu, ko wani takaicin ya isheta data tunoshi saitaji zuciyarta tayi sanyi, farin ciki ya ziyarceta. Babbar damuwarta da tasan bazasu sake zuwa hutu gidaba sai sun kammala gaba ɗaya, fatanta ALLAH yasa ya ziyarceta ta tabbatar da lafiyarsa ƙalau dai itakam.      
         Wannan damuwar datanemi sakama kanta sai taso taɓa karatunta, sai da ƙawarta Hafiza isa ta zaunar da ita taimata nasiha, da nuna mata muhimmancin wannan lokacin da suke ciki, bai kamata suyi wasa da damarsuba akan abinda zaune yake yana jiransu, itako jarabawar ta taƙaitaccen lokacice.
      Wannan bayani yasaka zuciyar Ummu saisaita, ta nutsu waje ɗaya domin fuskantar jarabawar dake gabansu tareda fatan nasara, dan tasan maganar Hafiza gaskiyace, auren Basheer nacan na jiranta, wannan kuwa lokaci kaɗan za’ayi a gama, kuma ya wuce kenan.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

        Lokacin da Baseer yaje gida jama’a da yawa sunsha mamakin canjawar daya kumayi, gashi yanzu yawani ɗaurama kansa girman kai ba kowa yake kulawaba, gashi yazo a dalleliyar motar Suhailat kuma data bashi aro, hakanne yasa magana keta yawo agari Baseer yayi kuɗi yana ƙyamar ƴan garin.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});        Ran iyayensa a ɓace suka shiga masa faɗa akan rayuwar daya ɗaura kansa a yanzu bamai ɓullewa baceba, inashi ina ɗiyan birni ƴar masu kuɗi, ai *WUTSIYAR RAƘUMI TAI NESA DA ƘASA!*, shidama ga matarsa nan na jiransa.
      A razane ya ɗago idanu yana kallon mahaifan nasa, “Baba matata kuma? Yaushe akaimin aure ban saniba?”.
      Harara mahaifiyarsa ta danƙara masa, tareda masa daƙƙuwa, “Basiru kaci gidanku dan ƙaniyarka, koba a ɗaura maka aure da Ummukulsoom ba ai kasan akwai maganarka da ita a ƙasa ko”.
      Taɓɗijan, shifa saima yanzu da suka ambaci sunan Ummu yatuna da itama, yagaji da jan maganar da faɗan da iyayensa suke masa, dan haka yaɗan murmusa yana miƙewa, “To ai indai maganar Ummukulsoom ce kumabar wahal da kanku inna, tananan ko, badai kun ajiye magana da iyayentaba?”.
       “To ina kuma zaka?”.
   “Baba zan zagaya bayine mana”.

        Tunda Basiru yabar wajen sai inna ta riƙe baki da sallalami, baban Talatu anya kuwa yarinyarnan tabar yaronnan hakannan?”.
       “To mizatai masa? Shashancine kawai irin nasa da ƙuruciya, kana ɗan ƙauye irin ɗilau, talaka fitik inakai ina ƴar masu kuɗi ƴar birni? wannan yana ɗaya daga cikin abinda ke tsoratar da irinmu ƴan ƙauye barin yara suyi karatu, dasunje can idonsu ya buɗe saisu kwashi duniya da faɗi, dukda dai bakowa ke koyo banzan halinnan ba na mutanen birni, amma nasan maganinsa ai, ƙwanannan zanje mu tsaida magana da malam Buhari, bazan yarda ya maidani ƙaramin mutunba”.
      “A wlhy ina bayanka baban talatu, gara dai kam a tsaida magana tunda dai dagashi har ita sunkusa kammala karatunma, ai halaccin da waɗannan mutane sukai mana baici ai musu wannan sakayyarba”.
       “To ALLAH dai ya kyauta, ni bara naje nan gonar bakin tafki na ida kai takinnan, garinnan gab yake da saukar ruwan damuna, yanayi nata ƙara canjawa”.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});       “To saika dawo, garikam ai yanata harama”.
        Baseer duk yana jinsu, babu abinda yake ayyanawa a ransa sai tayaya zai yakice wannan banzan auren ya huta, ina mai zankaɗeɗiyar yarinya irin Suhaila, ga kuɗi ga ƙyawu zai yarda a ƙaƙaba masa wata baƙauya wadda iyakarta secondary, shima da ƙyar ta harhaɗa, shifa saima yanzu ya fahimci bason Ummukulsoom yakeba, tausayinta kawai yakeyi dama can, rashin wayewar kaine da sanin menene soyayya ya hanashi fahimta. Amma yanzu kar yake kallon komai, degree fa zai haɗa, abinda kaf ƙauyen ɗilau wani bai taɓa yiba saishi, ai dolene ya kuma jama kansa girma a ƙauyennan, jama’r ciki su ƙara fahimtar *WUTSIYAR RAƘUMI TAI NESA DA ƘASA!* tsakaninshi dasu fa yanzu.Hummm.????????‍♀☹

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

       Su Ummukhoolsum na gab da gama jarabawa aka kai kuɗin aurenta daga gidan su Basiru batareda shi yasan hakanba, sosai Malam Buhari yaji matukar daɗi da farin ciki, yayinda zuciyar matansa kamar tayi bindiga dan baƙin ciki, koda wasa basa fatan Basiru ya auri Ummukulsoom, babban burinsuma tadawo da ciki.
    Koda malam Buhari ya fahimci hassada ƙarara a fuskokinsu baice komaiba sai girgiza kai da nema musu shirya, baisan mi Ummukulsoom ta tare musuba a gidan da a kullum basa ƙaunar cigabanta, saikace wata sa’arsu ko kishiyarsu.
       Ba wai ranar aurenta da Baseer aka tsaidaba, sundai kawo kuɗin gaisuwa domin su tabbatar har yanzufa suna nan, sun ajiye magana bayan dawowar Ummu da kammala karatun Baseer nanda wata biyar sai a tsaida ranar aure kai tsaye.

      Shidai Baseer da baisan hidimar da akeba kwannasa biyu ya tattara ya koma saboda zasu fara exam shima..

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
      Rayuwa ta cigaba da turawa cikin aminci, Yayinda su Ummu keta zana jarabawa, zuciyarta kuma na maƙale dason Baseer ɗinta, saboda son faranta masama taketa ƙoƙarin ganin tayi abun arziƙi.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button