Labarai

Yadda ‘yan sanda suka kama malama Zarah da ta rika saka wa dalibarta ‘yar shekara 4 yatsa a gaba

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta kama malamar makaranta mai shekara 32 da ke saka wa dalibarta ‘yar shekara 4 yatsa a gabanta.

 

Mahaifin yarinyar Hasan Dala ya ce a ranar 11 ga Maris ‘yarsa ta dawo daga makaranta tana kukan cewa gabanta na mata ciwokuma duk lokacin da za ta yi fitsari ta kan ji zafi.

 

“ A lokacin na yi zaton cewa kukan da ‘yata ke yi matsala ce na rashin shan ruwa sai naumarci mahaifiyarta ta rika bata ruwa tana sha.

 

“ Sai dai mahaifiyar ta fada min cewa yarinyar ta ci gaba da kuka a duk lokacin da za ta yi fitsari sannan ta kula da jini a gaban yarinyar.

 

Dala ya ce cikin gaggawa sai muka garzaya asibiti.

 

“ Da muka je babban asibiti sai likita ya bayyana mana cewa yarinyar ta ji rauni a gaban ta ta hanyar neman shigan sa da karfin tsiya.

 

“ Da muka dawo gida sai na ce wa mata ta tambayi yarinyar abinda ya faru da ita.

 

“ Mahaifiyar ta ce yarinyar ta ce malamar ta Aunty Zarah ce a makaranta take saka mata hannu a gabanta sannan ta sakata cikin hijabi tana tilastata sai ta rika tsotson nonuwan ta dole.

 

“ Da na garzaya makarantar domin ganawa da mahukuntar makarantar sai shugaban makarantar ya karya tani ya kuma kin ya bi diddigin abin.

 

“ A dalilin haka ya sa na kai kara ofishin ‘yan sanda.

 

Yan sanda sun kai kara kotu sannan kuma a wasu lokuttan da ake sauaren karar, an tsare wannan malama. Kungiyoyin kare hakkin yara da aka ci zarafinsu a jihar sun baiwa mahaifin wannan yarainyar tabbacin sai sun ga abinda ya ture wa bizu nadi game da wannan magana.

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button