Yadda Zakayi katin Zaben (Voters Card) Da Kanka
Yadda zaku cike Katin zabe
Da farko zaku Fara Bude Gmail address Sai ku Shiga wanann link dake kas
Idan ya bude zai kaiku inda zaku bude profile naku zaku cike bayananku kamar suna, Gmail address, phone number sannan ku kirkiri password naku bayannan zasu Sanar daku sun tura muku da confirmation code ta cikin Gmail address da kuka saka zaku je ku duba zakuga sunyi muki message saiku shiga zai kaiku kuyi login zuwa inda zaku cike bayananku.
A shafin farko zaku ga zabin sabuwar register ko tsohuwa ce kuke so ku sabinta. Saiku zabi Wanda kuke so.
Ga masu yin sabuwar register zasu.
Akwai mataki da zasu bi Wajen yin register.
Na farko zasu cike bayanansu na bio data. Wanda suka hada da cikkyakyan suna, shekaran haihuwa, jinsi, Sana’a, unguwar da mutum yake, kasar da kake da Zama, jaharku ta haihuwa da karamar hukuma, sannan zaku saka number ku ta katin Dan kasa wato NIN.
Sannan akwai Wajen da zaku Dora hotonku zakuga sunyi muku misali yadda ake so fuskar ku ta fito Wajen Dora hoton, zaku Shiga Wajen saiku zabi hoto biyu ku tura su da kansu zasu nuna muku Wanda ya dace ku dauka.
Sannan Sai Wajen da zaku Dora hoton katin Dan kasa Dana local government indigine
Sanann Sai Wajen da zaku zabi polling unit, Wato Wajen da zakuyi zabe,
Sai Kuma ku zabi jahar da inec din dakake, karamar hukuma Wanda anan zakuje su karasa muku apply na katin zaben,
zaku zabi Wajen da zakuje akarasa muku katin zaben, zaku zabi ranar da lokacin Amma Ana bukatar kuje Akan ranar da kuka saka.
Bayan Nan zasu Nuno muku duk bayanan da kuka saka idan Kuna da gyara saiku gyara sannan saikuyi submit Kuna Yi a sama zaku sun nuna muku download/print application slip saiku je ku cire shi kuje inec wato ma’aikatar da za’a karasa muku katin zaben aranar da kuka saka domin su karasa.
Shikenan.
Muna muku fatan nasara