YAR BAIWAH HAUSA NOVEL
Umar kam tun ranarda yakoma gida yahadu da baccin rai yayi alkawarin barin kasar kozai samu sawaba ga jiya sai shirye _shiryen aure sukeyi Alhaji Basheer kawai take jira aje asaka rana a biyawa diyan ta sadakinsu Dan kam harta hada lefe nagani na fada duk ta zauce ji takeyi kamar ma ace gobene saurin auren Dan kuwa Hajiyarsu Salma asiri taketa banka musu itada danta ganin ko anyi ma Umar baya tasiri shiyasa suka maida kambun yakinsu zuwa ga Hajiyarsa ba laifi a gurin su Dan kwalliya ta biya kudin, sabulu hakonsu na gamda cinma Ruwa. Shikan Faruuq BISA yayi ta zuwa umara Dan acewarsa gara yakaiwa Allah kukansa kozai rage zafin ra dadin da zuciyarsa ke masa bada dadewaba ta fito bai fadawa kowaba sai randa zashi yayi musu sallama ya fice yayansa ya ajiyesa airport jirginsu yadaga sai kasa mai tsarki haka ya wanzu ba dare ba rana yana Addu,ar samun Rukayya Allah yasa ita alkhairi CE agaresa Alhmdllh addu,arsa ta karbu Dan kuwa yanxu Rukayya batada wani aiki saina tunanin sa kwata2 wan nan hutun a Raba bata wani yi enjoying dinsaba.
Maman Ussee????
???? ‘YAR BAIWAH ???? 5⃣7⃣
~Maman~ ~Usseey~????
★ Masha Allah Abu yayi kyau Domin An Daura aure Lami lafiya komai yatafi yanda yadace Yayinda Yan Daurin Aure suka nufo Hanyar Dawowa Sokoto Dan Can Ne Bidirin Yake Dayake Daurin Auren. Ne kawai Malam Sa'eed yace azo Gida ayi sauran komai Yabarwa Baban Amarya wato Shugaban Biki Daddy???? Wanda Yayi Alfahari da Hakan,, da Baban Rukayya yamasa.
” A bangaren Amarya kuwa tun Safe aketa shagalin Biki Amarya wanka ,, kawai take Dauka na mutunci Ba karya kam Sosai tayi kyau misalin . Karfe Hudu aka Fara walima Wanda Akayi Nasiha mai Ratsa jiki game da zaman Aure da yanda Hakkin miji yake akan matarsa. sosai Abin ya ratsa Jama,a Sai gab da magrib Aka yi Addu,a Allah yabawa Amarya zaman lafeeya da Samun zuri,a Dayyaba ,,Aka watse tun Kare walima Rukayya da Sajeeda keta Kukan Rabuwa Duk Wanda yagansu sai sun Basa tausayi Saida . mummy Ta nuna Baccin Ranta kamin Suka Hakura Dan Dolene su Rabu dama Sabo akewa kuka.
★ Uwargida kam tun da FAROUQ yayi Fushi ya tafi taketa jin Badadi a Ranta,, Haka yaturo mata Sakon cewa Zai turo Ta Dauki abinda Takeso Yau zasu Tare a Sabon Gidansa Komai ya zuba mata aciki kawai Dai ta tattare abinda takeso Dan By 3:pm Zai turo adauketa ,, Tana kare karanta massege din Ta Fara tattara yan komatsan ta Zuciyarta sai Zafi take mata . Haka Yan uwanta da Danginta suka Zauna tare da Ita bamai Bata shawaran Kirki Duk zuga. Ta kawai Akeyi Wanda Hakan kara Ingiza Zuciyarta kawai yakeyi . Maman ta batazo ba Acewarta sai An gama Biki Zata Zo da Sabon Tuggu Dan Tasamu labarin cewa Salma Nada Juna biyu yanxu sun samu Gidin zama . A gidan Umar Farouq . (ohhh kuji min Mata 'yarta fa ke Auren Farouq din Amma ita Dukiyarsa,, CE kawai A Ranta Allah kashiryar Damu kasa mufi K'arfin Zukatan mu Ameen) Haka suka wuni Har Gurin 3 din kamin Yaturo aka Dauki Salma da Sauran K'awayenta Da yan Uwanta yan Kore masu Rakiya .
★ Ba,a Zarce dasu Ko,ina ba Sai Gidan Farouq Dake Unguwar Guiwa lowcost ,,, Gidane Babba nagani Nafada An kawata gidan Ba karya indan Nace Zan Iya Fayyace muku Yanda tsarin Gidan yake Yazama ,, Waist of Time . ???? Lol . part Biyu ne A gidan sai Garden da Kuma Dan karamin swimming pool ,, da Filn Wasan Ball kusan Irin Ukku Basket Bolly da Kuma Hand Ball. Sai shuke shuke da kuma parking Space . Wanda yake da isowarka ,, Gidan Mutuwar Zaune Salma tayi ta sake Baki tanata Kallon kayyatuwar ,, gidan A Ranta take cewa Ohh All This is myn Wata ,, Zuciya kuma take cewa Ku biyu fah mtseww..... Taja Tsaki Wallahi dai Kishiya batayiba Acid CE Hava ,muna Zaune kalau a Hadani da ,, yar bakin Ciki zaki Ganene inkin Shigo Gidan Wata kawartace tadan bugetah tace .
” ke Ki fito Mana kin wani hakince a Cikin mota ni na matsu naga ,, ya cikin gidan yake Dan gaskiya Salma ur lucky kinga yanda gidan ya Hadu kuwa Sakowa tayi ta Nufi Dayan part din taga A Rubuta kamar Haka “ This Belongs' to RUKAYYAH!!! A Ranta Tace ,,, Ohh Farouq Dan Rainin Hankali ne jifa Ko gidan ban saniba gashi ,, Duk Nama Rasa INA ne Nawa part din Mai gadine ya iso Gun da Take ya ,, Rusuna yace Hajiya ,, Ga makulin Part dinki gaya can Karba tayi bayabo ba Fallasa ta nufi Dayan Part Din sauran Jama,artah suka Rufa mata Baya ,,Ta bude ta Shiga “Ni ma dai Sauri nakeyi na Shiga na ganewa Idona Menene Acikin Gidan Dan gaskiya Ba karya fah ,, Wow„ na Furta A Hankali. Dan A gaskiya ,, Ba,a cewa komai wani Makeken Falone. Na Hango D'auke da Wasu Kayyatattun Kujeru komai Na Falon Black ne da White ,, Kai harma pent din Jikin Bango ,,, Dan Kara min koridor nagani Wanda Zai sadaka da Store da kuma Kitchen daga ka zagaya kuma Ga Dinning nan sai kuma wata yar Hanya ,, Wanda Zata sadaka da can Cikin gidan Dayan bangaren kuma Dakuna ne kusan ,, Guda Hudu a Jere sai Daya kuma A ,, Gefen Wadan nan da Alama Guest Room ne wato D'akin Bak'i . Sai kuma Wata Hanya Daga gefe Can na nufa ,, Wani Katon Falon nagani A gurin ,, Shikuma an masa Kwaliyar Pink komai pink da White color Fantastic na Fada ,, Tare da Zuba Idanuwa na Dan nabasu Abincinsu Shikuma Kofa Biyu ne nagani da Alama Dakin Mai Gidan ne Wata Hanya nabi naga kuma ta sadani da Dinning anan Nan ,, Ne Nafahimci Falon Maigidane Dana Salma Sai aka Sanya Kitchen a Tsakiyarsu dakuma Dinning Area ,, dawowa nayi nashiga Kifarda Naga su Salma sun Bude sun Shiga ,,,Zaune nayi Dana Hango wasu Mayyun Leader sit, Kut???? mai kud'i ya More Wan nan Dukiya haka da aka zuba a Gidan nan Kuryan Room din wani Gadone Hadararre mai Rumfa!
★ Suna Tafe ina binsu a Baya ,, Kowane Room sanda muka Shiga ba karya gaskiya Dakin , mai gidane kawai banmu shigaba Dan a kulle yake Falon suka Dawo nima nasamu Gurin zama ,,, sai Kallonsu nikeyi yayinda my Usseey. Yaga Ana shan Juice kala2 yaje yadauko Daya yafara sha banma lura ba sai Ganin shi nayi yanata zukar lemu ,,, Zare Ido nayi nace Kai ???? Rufa mana Asiri da shegen kwadayi gobe ma Bazan taho tare dakaiba Dan kar ka k'ara Kwasamin ???? lol.
★ Yan Daurin Aure sun ,iso lafeeya yayinda Ango da Abokansa basu Zarce ko,Inaba sai sabon Gidan FAROUQ . Dan anan zasuyi liyafarsu . yana isowa Kota kan Salma baibiba kawai Wuce ta yayi ya Shiga Dakin sa,, kawayenta sai tsokanar sa sukeyi suna Ango kasha Kamshi Murmushi kawai yamusu ya fice abinsa Salma ,,ta bisa a Baya yana Shiga itama ta Shigo Zatayi Magana yadakatar da ita da Hannu Durkushewa tayi ,,tafara mai kuka Abinda Bayaso kenan Dole ya Rarrasheta ,, Harsuka shirya kunsandai Mata da Miji sai Allah ,, Haka ta Daure suka Gaggaisa da fans Dinsa yayinda aka Bata kyata kala2 Kawayenta ke karba suna godiya,, yayinda Bakin Farouq yaki Rufuwa Har Gab da magrib kamin suka watse Dan suje akai Ango gurin Wankisa ????.
★ Shirye2 aka farayi na zuwa wajen Wanke Amarya ,, Wanda ba,a Bata lokaciba ,,, Aka kaita bayan an karene Aka dawo da ita gurin mummy kuzo kuga. Kuka anxo Rokon gafara Haka mummy ma sanda tayi kwallah saboda sabo ,, kakar Amarya sai Baaba sai tsokanar Rukayyah take . haka taje Gurin Daddy dakyar ta Rabu dashi Dan Saida yamata wayo ta Hakura haka suka nufi ,,Gidansu FAROUQ aka damka Amanar Rukayyah a Hannun Hajiyarsa sosai tayaba takuma karba ta sanya Alkhairi Kamin aka wuce da ita Zuwa Gidanta Wato Gidan Ango FAROUQ .
” Salma najin tsayuwar motar kawo Amarya Hankalinta ya matukar tashi ,,Jitakeyi wani. Abu na taso mata kamar Zata mutu . haka ta Daure ta Gimtse har aka Shigo da Rukayyah Lullebe da Mayafi ,, Aka Damkata Hannun Uwargida Sarautar mata Dakyar Salma tayi control din kanta Dan,, jinsu kawai takeyi haka suka karaci Surutunsu ,, suka Ja Rukayyah Zuwa part dinta Wanda komai Dayane Dana Salma saidai ita Kalar na Rukayyah Pupplene da White ba laifi Daddy yakashe mata Kunya Dan itama an zuba mata dukiya wane Diyar wani Shahararren mai Kudi ,, Rukayyah Bata taba Tunanin Zata kasance Haka A Rayuwarta. Ba wan nan wata BAIWAH ce daga Allah Da Addu,ah a Bakinta tashiga har kuryan Dakin ta suka ajeta Saman Bed. Yayinda kowa yaba tsarin gidanta yakeyi wasu kuma Cewa sukeyi Rukayyatu tayi dace mudai Fatanmu Allah yabada Zaman . lafeeya da Zuri,ah Mai Albarka.
~Maman~ ~Usseey~????
“Special Thanks to you my Beloved oneces ,,Bazan taba mantawa dakuba Nagode Sosai da Kwarin Guiwarku a gareni ”
★ Maman Khairy Allah ya Raya mana Ummul-khair.????
★ Ummu -Alkhairi B. B????
★Bintu Tijjani Zaifada ????
★ And my Lovely Aunt Sister Zainab Mai Kano Allah yakawo yan Biyu Ameen????.
Thanks much more Luv u all my Fans Lodi-Lodi????.
???? ‘YAR BAIWAH ????5⃣8⃣
~Maman~ ~Usseey~????
★ Gidan Amarya ya Rage daga Sajeeda sai Afra da Afnan da wasu Fans Dinsu mutun Biyu ne su Biyar kenan. Yayinda Rukayyah ke lullub’e a Mayafi Zuciyarta sai duka takeyi ,, Wai yau itace a gidan Aure gidan Umar Farouq abu kamar Almara .
“Sajeeda tace wai yaushe ne Zasu kawo wan nan Angon ne 10:30 fah Afra tace kin San sai anmasa Huduba kuma kinga Sai sun tsaya Dan Kinga dakwai masu so Su yi masa Naseeha Dan Rike macce Biyu sai jarumi Sajeeda tayi Dariya tace Tab kenan . Yayanku Jarumi ne ko Afnan tace sosaima ,, kinga zai nunawa Sistern ki Jarumta irin tasa Aisha tace kai kudaina Tsoratata mana kufa zolayace daku Safeena tace No way Ai dolema ya Hakura saboda Sabon Shiga CE Sajeeda tace Ohhh kukan Allah yashiryaku kunga kamar naji Tsayuwar mota may be gasu nan sunzo Suka kara feshe ko,ina da Turare kamin suka sami Gu suka zauna Rukayya Hawayene kawai ke zuba a Idan nuwanta Dan yanxu ne yakara tsinkewa lol????.
★ Bayan an kare wankin Ango Gidansu aka nufa Dan Ayi masa,, Hudu ba sosai Alhaji Basheer ya Masa Nasiha mai Shiga jiki yayi Adalci a Tsakanin su karya nuna musu banbanci Kuma ya Rike su Amana,, Ya tsaya tsakani da Allah karya fifita wata akan wata ya kwatanta Adalci . Haka aka kaisa gurin Hajiyarsa Itama dai Fadan tamasa na a Rike Aman da Adalci ,, daga nan aka Daukeshi zuwa gidansa Abokansa sai tsokanar sa sukeyi ,, Shikuma sai Dariya kawai yakeyi yana Wani jin Dadi har suka iso Part din Salma suka nufa dashi ,, Suna Zaune itada Kawayenta daketa zugata da Sallama suka ,, Shigo aka tsaya Akayi jawabin na Salma ta zauna lfy da yar uwarta Kuma Farouq ya kwatanta Adalci ,, Akayi Addu,a Kamin aka Baiwa Salma Kayanta na tande tande ,, Ba yabo ba fallasa tayi masa saida Safe shima ya mata ya lura sosai Bata cikin Kwanciyar Hankali,, amma bayanda ya iya haka Suka Ja Farouq zuwa part din Gimbiya Amarya .
★ Da Sallama suka Shiga yayinda wani Daddad’an kamshi mai sanyaya zuciya ya doki Hancinsu da Sanyi mai Dadi ya Ratsa su har Kuryan Daki inda Rukayyah take suka kai Farouq sai Daukan su Photo akeyi gwanin kyau Haka aka yi Barkwanci da Haka dai suka karasa komai suka D’auki Su Sajeeda Domin kaisu gida ya Rage daga FAROUQ sai RUKAYYAH . What a wonderful Day Shurune ya Ratsa Nadan wani Lokaci Yayinda Farouq yayi gyaran murya yamatso kusa Da Rukayyah ya Bude mayafinya tare dacewa . Amincin Allah ya Tabbata gareki yake ma,abuciyar Kyau. Girgiza mata Kai yayi Dan Ganin Hawaye ,, a Fuskarta Hannu ya sanya yashiga goge mata Fuskarta yayinda ya umurceta data tashi ta Dauro Alwala su nunawa Allah Farin Cikin su Da Zuwan Wan nan Ranar mai Albarka.
” Ba musu tashiga toilet tayi Alwala shima yashiga yayi yajasu jam,in Sallah Raka,a Biyu sukayi kamin ya matso kusa da ita ya Dora . Hannunsa akanta yashiga yi mata Addu,ah da kuma Fatan Samun Zuri,a Tagari . kamin ya je ya Dauko Plate da cup ya dauko Leda Wata gasaasar kaza yazuba a plate din ya Dauko fresh milk ya zuba dakyar ya lallab’a ta ta ci kadan bada yawa ba kamin tayi brush Shikuma ya fita anan ne Rukayyah ta samu ta zauna a saman bed duk sai taji wani iri saboda Bata saba ba . farouq kam Dakinsa dake part din Rukayya yanufa yashiga Toilet ya washa Ruwa kamin yafito ya feshe Jikinsa Da Turare Yana katewa ya nufi Room D’in Rukayyah Zaune ya tarar da ita Yace a,a wai Ke Zama ma kikayi ,sunkuyar da kanta tayi kasa ya matso kusa da ita yace kinga kidai kije ki cire wan nan kayan ko na cire miki su da kaina Rasa mezatace masa tayi sai murza yan yatsun ta takeyi matso wa yayi kusa da ita ya ,, Fara Rike mata Hannu wani Shock ne taji yajata Dakyar ya lallabata tayarda tacire kayanta ya Dauko mata wata Sleeping Dress .Purple colour. Had’ararriya ta Hadufa ba karya gaskiya yaja Hannunta suka fara zagayawa sanda yanuna mata komai dakomai hard Room dinsa saida yakaita ita dai Takasa sakewa Bayan yakare nuna mata komai ya dawo da ita zuwa Room Dinta Upp din. Wuta yayi yakara A,c suka kwanta Yajawota ya Rungumeta can cikin Jikinsa Jikinta ne yafara Rawa Dayaga Haka sai ya Rada mata a kunne just be Free ba Abinda zan. Maki duk da Haka Bata Sake ba Haka yashiga wasa da ita son Ransa Sanda yakusa Wuce gona da iri Rukayya ta Fara masa kuka badan yasoba ya barta A haka sukayi Bacci Wanda zankira da An daiyi maganin Ace Ba,ayi ba Dan Ba Wanda yayi Baccin kirki acikinsu Sai guraren Asuba ya barta yatashi Dan zuwa masallaci ita kuma ta Shiga Toilet wanka tafara yi kamin tayi Sallah ta zauna tafara karatun Al-Qur,ani Mai Girma har gari ya waye.
★Tun ficewarsu Farouq Salma takasa Zaune takasa tsaye da kyar ta iya control din kanta ledarma ko Kallon ta batayiba fuu tashige Room Dinta kawayentane sukaci kazar Banda kukah ba abinda Salma keyi ba irin Zugarda Zuciyarta batayi mata ba O my God yanxu Farouq dina na can tare da wata ko wane karatun yake koya mata oho Ashe haka mata sukeji idan An masu Kishiya da gaskene Ashe Ba,a Bacci haka ta wanxu cikin Tunani Matar tasiri Har Garin Allah ya waye yanda taga Rana haka taga dare . Shigowar Farouq ne ya sanyata ta fara Baccin karya kamar gaske tayar da ita yayi yace taje ,, tayi Sallah Lokaci yayi kamin yashafa cikinta yabata kiss ya wuce mtsewww taja Tsaki Aikin Banxa Bayan ka gama Lalacewa da wata shine zakazo kamin Dadin baki( Hattara mata wallahi muji Tsoron Allah yakamata musan irin abinda zamu gayawa mazajenmu saboda mumuke Neman Aljannah a gunsu Allah yasa mudace Ameen.) Haka ta Daure taje tayi Alwala tayi Sallah ta Shiga wanka bayan ta idar da Sallah tafito tashirya cikin wata Atamfah Dinkin mai kyau tana ta wani cika da batsewa kamar wadda Akayi wa laifin Wani Abin.
” Bayan ya dawo daga masallaci part din Rukayyah ya Nufa ya tarar da ita tana ta karatu murmushi ya sakar mata kamin ita kuma ta Gaidasa ya Amsa ,, yace Yauwa Sarkin tsoro murmushi tayi cike da kunya kamin ta gama ta fito tadan gyara wasu abubuwan Dayake ma komai Normal yake sabo ne kawai dayi Sai Farouq kam Room dinsa ya nufa ya koma Bacci Rukayya ko rasa abinyi tayi taje kawai ta kunnah T.v tashiga Kallo Abinta.
” misalin 8:30Am Afra tashigo gidan D’auke da Kayan Breakfast nasu Da murna Rukayya ta tareta tace sai yanxu Afra tace tab koyanxuma sakone,, yakawo ni kinga Ficewata ma zanyi Dan Banaso Yaya ya Yiman surutu yafara cewa INA masa ,,Sakko tun da safe a gidansa ,, Murmushi tayi ta karbi kayan ta jera a dinning table Afra Bata wani jima ba tafice tace Zata dawo zuwa anjima Rukayyah cigaba tayi da kallonta sai gurin 9. farouq ya fito D’auke da Fara,arsa yasha wankan Boyel milk colour ,, yace yadai my Angel ,, tace lfy Lou Kinci Abinci ne ta girgiza masa kai yace A,a Ba tun dazu aka Aiko Da Abincin ba tace eah INA Jirankane yace OK to zo muje muci tare suka ci Abinci saida Farouq ya Tabatar taci ta koshi kamin ya barta Ta gyara gurin ,, ya umurceta data Dauko mayafinta suje part din Salma ,, Ba musu ta yi yanda yace yayinda yake Gaba tana biye dashi Baya har suka is a Part din Zaune suka tarar da ita Da. Sallama suka Shiga Rukayyah ta gaidata Wanda dakyar ta Amsa Farouq ne yanuna mata guri ta Zauna Shuru ne yadan Gifta kamin FAROUQ yafara magana kamar haka :