Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
Labarai

Wani Mutum Ya Kashe Matarsa Saboda Ta Gina Makaranta Batare Da Sunanshi Ba.

Wani Mutum Ya Kashe Matarsa Saboda Ta Gina Makaranta Batare Da Sunanshi Ba.

 

Wani magidanci a Ogun mai suna Segun Omotosho Ebenezer ya lakaɗawa matarsa ​​Bukola duka har lahira saboda ta ki miƙa masa makarantar da ta gina saboda ta saka sunan ta.

 

A cewar rundunar ƴan sandan jihar Ogun, wanda ake zargin da marigayiyar sun yi ta cece-kuce a kan kadarorin kafin ya lakaɗa mata duka har lahira.

 

A wata sanarwar da ƴan sandan suka fitar a ranar Litinin ɗin da ta gabata sun ce an kama mutumin ne bayan da ya gudu a lokacin da aka tabbatar da cewa shi ne ya kashe ta sandiyar dukan da ta sha a hannunsa.

 

Wanda ake zargin dai bai a sani ba, ashe marigayiyar ta aika da saƙon murya ga ƴan uwanta, inda ta sanar da su cewa mijin nata ya yi amfani da wani makulli ya buga mata a kai yayin da yake tsaka da dukan nata, kuma idan ta mutu to su sani mijin nata ne ya kashe ta.
Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button