YAR BAIWAH HAUSA NOVEL

YAR BAIWAH HAUSA NOVEL

Bismillahi Rahamanir Raheem!!! ???? ‘YAR BAIWAH????
Maman Ussee

Yau yakasance jumma’ah yayinda kowa ke hada hadar zuwa masallaci garin yayi haske gwanin sha’awa kowa lamarin gabansa kawai yake tafe take tana yan wake wakenta dauke da tulu akanta zataje debo ruwa rafi kasancewar yau kasuwar garin nasu so take taci kwalliya Dan zuwa kasuwa Sameera kenan YAr BAiwa ahankali kawarta indo ta lallabo tabayanta tace Keee, hava indo meye haka nihar kin tsoratani wallahi ohh wadda aka kira da indo tayi ???? tace kekuma gaki da tsoro kamar kura ko samira tayi murmushi tace to sai kawai naganki kwatam toya akayi kawalliya naje gdnku banga ki ba eah wllhi Inna ce ta aikeni sayen omo kinga sauri ma nakeyi tace karna Dade to sa himma nima kinga danakai wan nan din nakare sai mun hadu kasuwa ko taimata sallama suka wuce.
Kai tsaye gidansu ta nufa da sallamarta ta aje tulun washh wallahi umma nagaji ke banason shashanci Dan wan nan diban ruwan ne wai kingaji rafin nisa gareshine daxakice wai kin gaji sa himma kiyi wanka kinga ankusa tasowa daga masallaci, kije kasuwar ki yo mana sayayya ta amsa da to tashiga daki ta kwabe kayanta tafito da daurin kirji tashiga bayi tai wanka ta fito tana Shafa mai da hoda nidai gefe nakoma ina kallon ikon Allah anata cika fiska da kwalli da digo digo ohhh dariyace ta kusa subucemin nadai gimtse INA kallon Samira an takarkare ana Shafa Jan ???? takare takoma fannin sa kaya wasu kaya atamfa ce ba laifi kam a wurin samira da ita a ganinta yau Zata goge sosai.
Sameera yarinya ce yar kimanin shekara goma sha Biyu farace ba Sol ba irin chocolate colour din nan Allah yamata baiwar kyau bakinta Dan karami dashi dauke da siraran labba ga hakora farare Sol kanana Jere gwanin sha’awa tanada idanuwa masu kayatarwa irin na mejin bacci sexy eyes ba laifi kam batada jiki kuma baxa asakata layin maras kiba ba masha Allah da ita son kowa kin Wanda yarasa ga tada shaf brain shiyasa ake kiranta da yar Baiwa duk abinda aka fada mata bata mantawa ga hankali uwa uba hakuri batada kiriniya ga basira sai dai kash abu dayane samera batadashi iyayenta talakawane ga samira nason boko kamar me intaga Dan birni cewa take Dan koyamini turaci Allah yayi sameera mai son abu duk abinda tasa kanta to ta rike kenan kuma da an fada mata so daya ya shiga kanta
Umma na fito bani sakon so nake nadawo da wuri so nake naje wurin Dan birni kinsan yau yadawo Ohh kekam da naci kike to Allah Bada Sa’a ungo ki sayo min kayan yaji da sukari kinji tace to innna ta amsa tafito tana tafiyarta a hankali ba abinda ke damunta har takai kasuwa tana sayayarta saiga garbati shida tawagarsa suka tareta ke yar Baiwa sunanda kowa ke kiranta dashi kenan. Tin dazu ina jiranki kin shanyani mekike nufi itadai bata ce komai ba ta sadda kanta kasa tana wasa da yatsunta can sai ga Indo ta isu takallesu ta watsar wai kai wanne irin bawo nekai ana soyayya dolene kunbi kun takurawa yarinya kun hanata sakat duk Inda taje sai kunbita kamar wasu mayu. Ke yarinya ki iya bakinki mtseew indo taja karamin tsaki kukan dai anyi shashashai wllhi ilu na tare da garbati yadaga hannu zai mareta sai iro yace kai Narabaka gidansu basa yafiya wllhi kumuje tunda uwarta tazo indo taja hannun samira suka wuce kekam dai kinji haushi su wadan nan banzayen zaki tsaya suna garaki to indo yakikeso nayi dasu kinsan halin garbati zai iya kullamin sharrin da banjiba bangani to ki tsaya sokonci har a Rena ki in anmiki tsiwa xakiyi kinuna bakya tsoronsu inba haka. Ba kinatare dajin haushi to Inda banxoba fa sai yaya kenan sai ya kuwa illa in rokesu mtseew kinji haushi wllhi yar Baiwa nidai muje kiraka ni nasayowa innata magarya tam muje.
Suna tafe suna tadi abinka da kawaye har sun manta Indo kawar sameerace tun suna yara sa’an ni. Juna ne gidansu ba wani nisa dagidansu sameera indo akwai tsiwa ga iyayi batada hkr kuma bata daikar raini shiyasa ake shankunta ko a cikin gari uwa uba tanada yayu masu shiga mata gidansu duk Wanda ka taba ka tsokalowa kanka basa Barin kota kwana.
Sallamu alaikum inna nadawo xanje gidansu Dan birni akoya min boko to yar Baiwa saikin dawo kardai ki Dade kinji ta amsa da to ta fito da azama zuwa gidansu kabeer duk da tana shakkun Hajiyarsa Dan ta tsaneta hasalima batason yana zuwa gidan baxata manta ranar da takirata da mayya kekam kullun sai kin likewa Dana to ahir dinki sameera bata kawo komai aranta ba ita burinta kawai akoya mata turanci ta iya zata jure duk wani fada na Hajiya matsawar za’ta samu abinda takeso wan nan kenan.
Tana shiga gidan saida gabanta yafadi tadai danne ta Shiva cikin gidan kai tsaye falon Hajiyar ta nufa suna zaune ita da ‘ya’yanta husnah da yusrah sai kamal kanin Kabeer da Sallamarta tashiga su yusrah naganinta suka washe baki suna dariya ohh Yar Baiwa sarkin son karatu har an iso kenan cewar kamal Hajiya Kareema najin an ambaci sunanta ta hade rai kamar bata taba dariya ba Samira na shigowa ta gaida Hajiyar INA wuni lafiya atakaice San nan taja tsaki mtseew da dawowar tashi baza’a barsa ya huta ba kuma zaki wani zo kidamesa haba Hajjiya meye laifinta nine nace tazo ai dalibata ya kk ya kwana biyu hpe dai kinzo dashiri danyau akwai sababin darussa ta murmusa tace eah uncle to shigo ki zauna kamin naci abinci sai mu fara Husnah kuma Ku shirya musamman ma ke yusrah naga bakya maida hankalinki sosai sunka turo baki hva yaya week end nefa yakamata mu huta kai bana son shashanci kutashi maxa Hajiya kareema hararar samira kawai take itadai ta tsani yarinyar nan nacewa ne da ita to dolene saita iya turanci itada take ba yar kowa ba tashin kauye ko ubanme iya turancin zai tsinana mata oho yarinya kamar mayya tabi ta ha nata sakat itada danta inyazo week end said a dare da rana yana tare da shegiyar yariyarnan sai Yarbaiwa cewar Hajiya acikin zuciyarta.
Itadai sameera ta takure gefe jiran fitowar uncle Kabeer kawai take yazo yafara koya mata abinda zata karu tabar gidan yana kamalawa tafito da book rike a hannunsa yace to daliba muje garden ko ta mike su yusrah ma suka biyota suka biyo bayanta suna isa kowa ya zauna a kujera yafara gabatar musu da lesson yayinda yar Baiwa da yayi tambaya take amsawa itada batamada lesson book amma yusrah sai a hankali gara ma Husnah tana Dan ja haka da haka har suka kare kasancewar ba lokaci dayawa ‘Yar Baiwa tai godiya takoma ta ma Hajiya sallama ta wuce zuwa gidansu tana zuwa ta rungume ummanta tana murna take Bata labarin abinda aka koya mata haka rayuwar samera takansance har karshen sati itadai burinta tasamu ilmi Dan ta taimaki mahaifanta!!!

2 be continued
Maman ussee

???? ‘YAR BAIWAH????2⃣

Maman ussee

Rukayya ‘ya CE ga malan sa’idu ita kadai Allah ya azutarsu da ita bayan sunsha wahala matuka kamin su sami haihuwa shekarar su 10 da aure ko batan wata ba’a taba yiba a gidansa kwatsam sai ga cikin Rukayya ansamu karkuso kuga murna a wurin malan sa’idu ya dauki burin duniya yasaka akan cikin nan mai dakinsa har mamaki take duk da itama tana burin taga kwanta a duniya Dan baxata manta ba ko haihuwa akayi idan taje barka ba’a. Bata jariri wai batasan zafin haihuwa ba Dan haka.Baxa a bata ba tasha kuka amma dayake mijinta na matukar kaunarta sai ya lallasheta da kalamai masu dadi yana kwantar mata da hankali yana lurar da ita haihuwa ta Allah ce kuma Allah yana sane dasu karta damar da kanta wata rana suma Allah zai basu nasu rabon haka ne kam gashi hkrinsu yabasu yau Allah yabaiwa salamatu ciki haka sukayita renon cikin har Allah ya ingantashi Rayuwa kenan(mai hakuri mawadaci) malan Sa’idu mutumin garin Raba ne asalin su fatakene sukanje fautaci gari gari anan ne Allah yaha dasa da salame sunana da ake kiranta kenan jinisu ya hadu sosai Dan ita yar dagacin garin Damagara ce kuma duk bako a gidansu yake sauka suke basa masauki anan me Allah ya hadasu har aure ya shiga duk da dagaci. Baisoba a cewar sa bayason ya baiwa.bako yar sa Dan su danginsu auren dangisukeyi haka salame ta dage sai sa’idu aka wanke aka kaita garin raba duk da sun raina da arxikin sa’idu haka suka baro yar uwarsu suka koma damagara haka kuma rayuwarsu takansance itada masoyinta gwanin sha’awa malan sa’idu marayane su biyu mahaifinsu ya haifa malan sa’idu shine babba sai mai bi masa atine wadda bayan haihuwar tane mahaifinsu yarasu duk nauyin gida yadawo akan Maman sa’idu duk da lokacin. Bai wani girma ba sosai atine na karama itama haka dai sukaci gaba da rayuwa yau da dadi gobe da ciyo har Allah ya tashi kafadarsu Atine kuma tayi aure ta auri Habu Wanda shi a birni yake zama da akayi aure yadauki matarsa suka koma can da zama sai dai insunxo ziyara

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Leave a Reply

Back to top button