YAR BAIWAH HAUSA NOVEL

YAR BAIWAH HAUSA NOVEL

Abakin get yayi fakin yayinda su Sajeeda suka nufin classes dinsu shi kuma ya nufi office din malamin makarantar yaga batar da Rukayya a matsayin daliba akayi mata tambayi ba laifi kan Dan ko a can Raba tana zuwa makarantar allo bayan an kamla aka bashi takarda yasa hannu yabiya kudi sai suka CE yakoma da ita gobe sai ta fara zuwa kuma da uniform suka sake fadamai dokokin makaranta yayi musu godiya ya ja Rukayya suka tafi a mai makon subi hanyar gida sai taga sunbi wata hanyar mexatayi in ba kallo ba ido ya samu abinci dai dai wata yar plaza taga Daddy yayi parking yace ta jirasa batasan meyaje yiba bai jimaba sosai taga yadawo da Iedoji biyu a hannusa ya. bude set din baya daba kowa yasa su a ciki sa,ilin da yadawo yatada mota suka nufi hanyar gida,

Mummy suka tarar harta kammala komai na gyaran gida da Inda sukaci abinci sannu da aiki mommy yara ga kaya nasiyowa Rukayya da yadin uniform saiki bada dinki ayimata iri biyu iri. Nasu Sajeeda Dan gobe zata fara zuwa sauran kayan sa wane nixan fita sai nadawo aff ana manta kinsandai makarantar Boko suna jarabawa ne sai nadawo Hutu zan kaita zadai aci gaba da koya musu extra lesson kamin da dawo hutun Dan naga ba wani Hutu mai yawa bane murmushi tayi hadi da yimasa godiya da fatan alkhairi,
Rukayya kuma tana zaune ta kurawa TV Ido ko kyabtawa batayi mummy ta dafata tace muje kitayani gyaran daki sai mu Dora girkin rana Dan su sajeeda sai 4:pm zasu dawo ta fice yayinda Rukayya ta rufa mata. Baya tana nuna mata abubuwa da yakamata ta kula dasu wan nan kenan,

A cikin yan kwanaki n da tayi a gida. Bata fuskantar komai sai farin ciki ga soyayya da yan uwanta ke nuna mata suna debe mata kewa sosai sun shaku da sajeeda inka gansu gwanin sha,awa komai tare sukeyi Dan ko a Islamiya tare suke komai sajeeda itace take koya wa Rukayya wasu Abubuwan da bata gane ba cikin sa,a kuwa da am fada ta rike shikenan malamansu har mamakin irin Baiwar da Allah yayiwa Rukayya suke gashidai bawani dadewa tayi ba amma inka ganta saika rantse ta shekera a cikin islamiyar gida kuma ga lesson ana musu badama tana kawo wuta sosai Daddy yasan bayada haufin inya kaita skull za,a sakata aji daya da Sajeeda dayake ita jss 2 take, Tun tanajin kunyar saka wando da Riga harta saba Dan kuwa yanxu Rukayya ta goge dama can ita kai waye ne da ita batada matsala in basuda lesson itada Sajeeda suke taya mummy aikace aikacen gida dayake anyi Holiday.

Maman ussee???? Ina Alfahari da Ku my fans

???? ‘YAR BAIWAH ????7⃣
Maman Ussee

Haka Rayuwarsu taci gaba da kasancewa gwanin sha,awah har holiday ya kusa karewa yau ya kasance Sunday kowa da kowa na falon gidan anata firar duniya gwanin dadi fuskar kowa cike da annashuwa da anuri Abdallah ne yace Daddy gobe Holiday zai kare kuma kasan kamuna alkawarin zaka mana shopping yau ko Fadil ya amsa eah little bro Mummy tace harda ni kenan za’aje shopping din Daddy yace OK to Ku shirya sai muje tare kunji yes Daddy suka mike Dan shiryawa Rukayya an zama yan gida yanxu kowannen su yafito cikin shiri Rukayya da Sajeeda jalabiyace a jikinsu dark blue sukayi rolling abin yayi kyau fadil da Abdallah kuwa Riga da wandone suka sa mummy itama Doguwar rigace ta shadda taji kwado kai familyn fa sun birgeni haka suka fito suka shiga mota Mummy dasu Sajeeda a Baya fadil da Abdallah a gaba asu zarce ko inaba sai a Zabira shopping mall nan kowa yayi ta zabar abinda yakeso Rukayya dai kasa daukar komai tayi Dan ita kunya takeji Sajeeda CE kedaukar komai Biyu inta dauka saita daukar wa Ruky bayan sun karene sukaje wurin bill akayi bill Daddy yabiya suka sake fitowa kowa sai kallon su yake nusamman Ruky da Sajeeda kamar yan biyu ba karya Allah yayi Halitta Dan ko Sajeeda ba bayaba a fagen kyau, Daddy bai zarce dasu ko,ina ba sai Daddy’s smart anan sukaje suka ci abinci suka zaga gari sosai kamin nan suka dawo gida.

Gab da magrib suka dawo zubewa sukayi a fallo kowa ya gaji Dan yau sunsha yawo sun more sosai gsky bayan su hutane Daddy yaja su Fadil da zuwa masallaci Mummy kuma ta wuce zuwa dakinta yayinda da umurci su Sajeeda dasuje su yi sallah suma kuma su shigar da kayan ciki haka suka kwashi kayan zuwa Inda yakamata su adanasu. Bayan sun idar da Sallar Isha suka fito bayan aka ci gaba da hira can Daddy Yakira sunan Rukayya, Rukayyatu ki shiryafa gobe zaki soma zuwa skull insha Allah saboda haka saiki shirya kinji murmushin jin dadi tayi yayinda da ta CE nagode Daddy Allah yakara girma bakomai ai kidage dai kinji ko to ‘ya ‘ yan Daddy aje ayi bacci saboda a tashi da wuriko kunji yes Daddy af na manta Ga uniform din Ruky can a bed dina Sajeeda jeki kidauko mata gobe sai a shirya da wur wuri kinji tau Daddy bakida wata matsala Rukayya. Nariga nayiwa principal magana interview kawai za a maki su zasu baki komai da komai saboda haka kidage kawai inkiyi kokari za a sakaki class daya da ‘yar uwarki Sajeeda tam ta amsa suka fice dakin su kowa yayi addu’a ya kwanta yayinda ‘YAR BAIWAH take farin ciki sosai mafarkin ta yakusa yazama gaskiya.

Maman Ussee

???? ‘YAR BAIWAH ???? 8⃣
Maman Ussee

Monday morning tun 6 suketa shirye shiryen zuwa skull Sajeeda CE ke nunawa Rukayya yanda zatasa kayan skull din ,kai gsky fa kinyi kyau tawan kinga yanda skull uniform din nan suka karbeki ta kashe mata idon daya Ruky ta kaimata duka ta goce suka fito falor sunata dariya yayinda su Fadil ma su. Shirya tsaf Daddy kawai suke jira bai wani jima ba ya fito sanye da kayan shi dagani shima aiki zaije daya aje yaran, ba bata lokaci Mummy tai musu addu’ a suka fice dukkansu suna daga mata hannu,

Bayan sun shiga mota Daddy ya tuka zuwa skull din dake dai dai Bafarawa east, garin yacika sosai da mutane kasan cewar yau Monday masu zuwa skull na fita yayinda masu zuwa aiki ke kama ga bansu da zuwa aiki kai tsaye daddy cikin makarantar ya danna motarsa wato KEY SCIENCE ACADEMY, bawani bata lokaci Sajeeda dasu Fadil suka nufi assembly yayinda Daddy ya nufi principal office da Rukayya bayan yagabatar da ita a fadamai rules din makaranta ya amince kamin nan aka bashi takarda yasa hannu yayi godiya sosai ya wuce yayinda PC ta kira senior master domin a iyiwa Ruky inter view da Name dinta aka fara ta amsa Rukayyat Sa’eed bayan nan kuma sai aka cigaba da yimata sauran questions tana amsawa yanda yakamata, mintuna kalelan aka bata class yayinda aka kira, class master dinsu ya rubuta name dinta a Register kuma aka umurce shi daya kaita ya gaba tar da ita wa yan class as a new student kai tsaye , Jss 2 blocks ya nufa da Rukayya kamar dai yanda Daddy ya. Bukata cikin sa,a kuwa ajinsu Sajeeda ne bayan shigarsu, student suka mike tsaye,
Good morning sir, morning how r u today, we are All fine sir, OK sit down,
Anan yagabatarda ita yayi kiran register kuma ya umurci class rep data bata set shikenan yafita Dan yagama aikinsa,
Fitarsa keda wuya Sajeeda ta doka uban tsalle ta rungume Rukayya tana murna sosai, Hi kinga Allah ya amshi addu,a na ko so yanxu muna class daya if u did not understand anything just ask me ???? murmushi kawai Ruky tayi hadi da samun set bayan nasu Sajeeda yayinda su Muhibba yan sit dinsu Sajeeda suke tambayar ta dama tasantane eah yar uwatace she’s my sister daga nan kuma aka cigaba da gaggaisa irin na new students da old kundai gane???? uncle me English ne ya shigo da yake ba musulmi bane ya gabatar da lesson dinsa ya kuma basu pappers dinsu na fist term bayan ya kare sai mai science yashigo shima yagabartar da nasa lesson din kamin nan aka buga aje break fast Sajeeda da Rukayya tare suka fito zuwa dinning area anan ne Sajeeda ta ringa nunawa Ruky abubuwa da dama wadanda bata saniba da kuma Inda ake komai da komai haka suka kasance har time dinda aka koma class ba laifi Rukayya ta dage sosai sai sun hada Kansu ita da yar uwarta ba abinda basayi tare har lokacin barin skull din yayi suka shiga skull bus Dan dama ita ke mayardasu gida saidai da safe Daddy ya kawosu su Fadil da Abdallah bangarensu daban kasancewar su a primary suke sunada masu bus din duk da skull din dayace amma kuma Nursery daban primary daban ss da jss ne kawai a hade Sajeeda da Ruky suka shiga tare aka yita sauke wadanda ke kusa yayi da aka zo unguwarsu suma suka sauka sunayiwa sauran yan mates dinsu bye bye sai mun hadu gobe inji su Hibba sajeeda ta amsa da to,
Bayan su shiga gida suka tar rar dasu Fadil da Abdallah har sun dawo kasancewar su 12:30 ake tayar dasu sukuma sai 1:30 suke tashi Daddy. Baidawoba haka suka cire uniform dinsu suka sake wanka kamin nan suka saka uniform dinsu na Islamiya da time yakusa yi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Leave a Reply

Back to top button