YAR BAIWAH HAUSA NOVEL

★ Salma Kinga ga Rukayyah nan Amanace a gurinah kuma a gurin ki Banason Fada,, Kuma Ku zauna lfy da juna Ku mutun ta junanku duk kanku INA sonku shiyasa na zauna tare Daku Rukayyah Ki Baiwa Salma Girman ta karki Rainata kibita Duk abinda takeso indai bamai wahala bane kimata kinsan Junah biyu gareta sai kinyi Hakuri da ita kinji Tace Insha Allah yace Good . Allah yayi maku Albarka yabani Ikon yin Adalci a Tsakaninku Rukayyah tace Amin kamin ya fice ita ma takoma part dinta Dayake Yan Yinin Amarya sun Fara Isowa haka dai Suka kasance Har Rana tayi.
Maman Usseey????
???? ‘YAR BAIWAH ????5⃣9⃣
~Maman~ ~Usseey~????
★ Gab da Azhr Su Sajeeda sukazo sosai Rukayyah taji Dadi suka Zauna sukayi ta tadi sai barkwanci sukeyi gwanin sha,awah sai tsokanar ta sukeyi badai ta kulasu banda murmushi ba,abinda take musu Haka suka zauna sai Dare Suka gyara mata Part dinta tsaf sai Kanshi ko,ina yake yi Basuda matsalar Abinci Dan Daga gidan Hajiya Ake kawo musu ,, Koyanxu Abincin aka kawo su Afra suka Ni Driver Dan Ya ajiyesu gida harda Sajeeda sanda suka ajiyeta a gida suka wuce Warsu gida.
"Rukayyah wani wanka ta Dauka mai Daukar Hankali ta Zauna a sitting Room tana Kallo Abinta Dan Yau bakonta yazo Hankalinta a kwance. Batada wata damuwa phone dinta ne yayi Ring ta Dauka tare da Sallama ,, mummy takirata da wayar Sajeeda tace Yadai 'Yata lafeeya Lou kike ko tayi murmushi tace lfy mummy ba komai yauwa Dama dan na gaya mikine Ki Duba Acikin Jakar da Sajeeda ta kawo miki zakiga ,, Wasu ledar guda biyu Dayar turarene na Humrah a Ciki dayar kuma maganine ki sha da Madara tace tau Insha Allah sun tan taba Hira daga Bisani Kuma suka katse wayar . ta sauke Ajiyar zuciya kamin ta ci gaba da Kallon ta.
★ Farouq Bai dawo gidan ba sai guraren 9:30pm Da shigowarsa bangaren Salma ya nufa Baiganta anan fallo ba ya Shiga Dakin ta kwance yarar da ita Hawaye duk ya Bata mata Fuskarta ,, wurin Gadon ya nufa Ya kira Sunan ta Salma. Bata kallesa ba Tace wai Salma menene yake damunki Kwanan nan duk Kin wani Rame kin Hana kanki sukuni wai menene Nifa ban kara Aure Dan na muzguna mikiba Dan Allah ki cire komai Aranki please hava Kamar wani abu duk kinbi kin Hana kanki sukuni Batadai ce dashi komaiba ya Rugumeta yafara lallashinta ,, dakyar yasamu ta Hakura shiya bata Abinci da kansa ya bata maganinta tasha Dan yaji Jikinta yayi Zafi saida yaga tadan Fara Bacci ,, kamin yatashi ya wuce bangaren Rukayyah .
★ Da sallama yashiga wow” Ya Furta a Hankali saboda wani Daddadan kamshi da Sanyaya zuciya Daya doki Hancinsa Amsa Sallamar sa tayi tare da Gaidasa ya Amsa yace hope dai Bakiyi Fushiba Dan na makara tace No Bakomai Yace OK Kinci Abinci ta girgiza kai yadan Bude idonsa yace tomeyasa Kosai tare dani Batadaice komai ba ta saddan kanta ,, Kasa tana murza yan yatsun ta Matsowa yayi ya Shafa Gefen Fuskarta Yace zan Cire wan nan kunyar Dan. Naga Alama Zata takurani yanufi Room Dinsa saida ya Rage kayan Jikinsa ya yasanya Short Nikkah da Yar Singlet ya fito Kallo Daya tamasa Ta sauke kanta Kasa ,, Hannunta ya Ja suka nufi Dining Dan Cin Abinci Sunayi suna Yar Soyayya Nakuma gefe Inata Kallon Ikon Allah.
” Bayan sun Kammalah kowannensu Dakinsa ya nufa Rukayyah Brush tayi ta watsa Ruwa ta sanya Nightes masu shegen kyau Jajaye ,, ta Bude Tuearenda Mummy ta Aiko mata tashafe Jikinta dashi ko,INA Kamin Ta zauna kusa da Bed Dinta tana Kallon pictures din da Sukayi Dazu itadasu Sajeeda. Farouq ne yashigo Dakin Shima Kayan Jikinsa Ja ne masu Guntun Hannu Zaunawa yayi kusa Da ita Yace mugani ta basa wayar sukaci gaba Da Kallonsu tare Wani yayi Dariya wani kuma yace kai Kukam dai Kun iya Daukan photo to bari nayi mana wani pic din ,, Ya Jata sosai ajikinsa yamasu photo Selpic Kamin ya Dora mata kiss Wanda ya Ba,in kashe mata Jiki ,, Turning Off din Wutar Dakin yayi yafara Yimata wasan ni Da Zafi Zafi Wanda Rukayyah ta Kasa Gane Ko tantace a ina take ,, Ganin Zai wuce Gona da iri yasanya ta CE dashi Bakonta yazo ,, Dakyar ya iya Control din Kansa Amma fah Duk da Haka ,, Tasha Wahala Dan Dakyar Ta lallabasa ya Hakura ,, Amma yadan samu Relief sosai Rugumeta yayi sukaci gaba da Bacci Kulle musu kofa nayi Tare dayimusu Fatan tashi Lafeeya.
★ Sajeeda CE kwance a Room D’insu sai juye juye take saboda tasaba komai tare sukeyi itada Rukayya yaigashi Bata jin motsin kowa Lallai Yaune take jin Rabuwarsu da Rukayyah Dan Abin duk yataru yamata yawa gara Jiya Dakwai mutane to Yau kowa yayi Tafiyarsa Abin ba Dadi A Hankali ta Furta tace I miss You Sister. Allah yabaki zaman lafeeya da Kwanciyar Hankali. Wayarta ta Dauka tashiga whatapp ,,, Dan ta tagewa kanta lokaci da Dare . saida tafara Jin Bacci ta Ajiye wayar Ta kwanta Sai Safe Daddy ya Buga mata kofa ta Tashi tayi Sallah tadanyi Karatun Al-,Qur,ani Sai Karfe 8 Tatashi tashi Kitchen Dan Ta Dora Breakfast ,, A kitchen Mummy ta Tarar da Ita Tace Hoo sannu Yau kinyi Abin kanki Murmushi Sajeeda tayi tace Mummy an tashi lfy tace Lou Yau kin fito Da wuri tace eah Mummy tace Dan kinsan Ba maiyine keda kikeda Son jiki Murmushi Sajeeda tayi kamin suka ci Gaba da Hada komai a Tare Har suka kammala Hada komai Suka jera a Dining ,, Kowa yakoma Dakinsa Sai 10:Am Suka fito sukaci Abinci kamar yanda Suka Saba Kullun ,, Daddy yace Allah Sarki ‘Rukayyahtu ana can mummy tace Ashe Bamu kadai ke Missing dinta ba yace gaskiya Baku kadai bane ,, Yauwa Sajeeda Gobe Ki shirya kifara zuwa skull Ki shirya da wurifa Dan nasan Halinki tace Angama insha Allah yace Good ,, suka ci gaba da cin Abinci bayan sun kare Sajeeda tashiga gyara gurin mummy kuwa Tashiga kitchen Dan Ta Dora Girkin Rana .
★ Da Asuba Farouq yatashi yayinda ya gyarawa Rukayyah Kwanciyar ta Dan Jiya baibarta tayi wani Baccin kirkiba wanka yafara yi ya nufi masallaci Dan Gabatar da Sallah sanda yanufi Part din Salma ya tayar da ita kamar Yanda yayi jiya ,, Bai shigo. Ba sai Da aka kare Sallah Yadawo Room dinsa yanufa ya kwanta.
" Rukayyah kam bata Tashiga sai ,,, Guraren 7:30Am toilet tanufa tafara wanka tayi Brush kamin tafito tashirya tsaf da ita daganinta kaga Amarya yauma kamar jiya gyara ko,ina tayi ta fesa Turare tadawo Ta zauna tana Kallo a Sunnah T.v Kwankwasa kofa taji anayi ta tashi ta Dauko mayafin ta kamin ta bude kofar Driver ne shikadai D'auke da Breakfast yace gashi inji Hajiya tace a Gaidaki Rukayyah ta karba ,, Tace yauwa kace Angode Nima ina gaidata ta Kulle kofar ta jera komai a dinning ta ci gaba da Kallon ta Hankali kwance .
~Maman~ ~Usseey~????
???? ‘YAR BAIWAH ????6⃣0⃣
Maman Usseey????
★ Sai guraren 10:Am Umar Farouq yatashi sai wanka yafara yi Kamin ya shirya tsaf Ya fito ya tarar fa Rukayyah nata Kallo da murmushinsa ya iso gareta tare da Shafa Fuskarta,,, Amarya Bakya laifi ko kin kashe Dan masu gida . tadanyi fari da Ido tace Bama zan kashe kowa ba Yace to muje muci Abinci Dan Nasan Bakici kina jirana ko kai kawai ta Daga masa yaja Hannunta suka nufi Dinning area.
" A tare suka ci Abinci Yana ta tsokanarta bayan sun karene yayi ficewarsa ita kuma tashiga gyara gun dasuka bata Ta wanke Kayanda aka saka musu ,, Abinci a Ciki ta sanyasu cikin basket Dan dama Haka takeyi idan An kawo Na Rana sai ta Bayarda na Safe hakama idan an kawo nadare saita Bayarda . kayan Rana Da Safe sai ta Bayarda na Daren Tadawo ta Zauna ta Rasa Abin yi kawai sai ta kira Abbanta bayan sun gaisa yake Tambaya ta ya Sabon guri Tace lfy Lou Alhamdullah ,, Haka sukata fira yabaiwa Ummanta harda Baaba ma sanda suka gaisa Daga nan Ta katse wayar ta kira Daddy shima Tambayarta yayi ya sabon wuri tace Lfy Lou ya kara yimata Nasiha mai Ratsa zuciya game da Zaman Aure ya Sanya mata Albarka haka tayi ta kiran Yan Uwa da Abokan Arziki Suka gaisa Harsu Afra saida ta kira Tace su Turo mata No din Hajiya bayan Ta kammala wayar ne Ta kirata cike da girmama,, Daga dayan Bangaren aka Amsata sosai Hakan yayiwa Hajiya Dadi ta Tambayeta dafatar Ba Wata matsala tace Bakomai lafeeya Lou yauwa Haka akeso Allah yayi maku Albarka Rukayyah ta Karba da Ameen ta Ajiye wayar Ta Dan kishin gida kadan Batasan Sanda Bacci ya kashe ta ba .
★ Farouq ne Zaune a room Din Salma wadda yakasa Gane ma kanta cikin kwanan nan Yana dai Biyematane Dan Bayaso Yashiga Hakkin Ta Allah yagani Bazai iya jure Rainin Hankali ba Dakyar yasamu ya lallasata taci Abinci saikace Gareta Aka fara Kishiya duk ta fita Hayyacinta Bayan taci sosai ya Bata magani Tasha Shida Kansa ya mata wanka yadawo da ita ,, Room dinta Ya kwantar Kamin ya yi Ficewarsa Dan Amsa kiran da Alhajinsa kemasa.
” Haka Rayuwarsu Takasance a Tsawon Satin nan Har Ranarda Ya Raba masu Girki Ya Kara tarasu Ya Musu Nasiha mai Ratsa jiki Wanda Rukayyah kawai ta Dauka Salma kam Biris tayi Dan Ita yanxu Kwata2 ta canja daga Sanin da Farouq yamata Salma ce Zata Fara yin Girki Wanda Farouq ya CE Duk mai yin Girki to A part Dinta Za,aci Abinci Hakan bakaramin Haushi yayiwa Salma ba Amma ba yanda ta iya Dole ta Hakura Dan tasan Halin FAROUQ Baya canja,, maganar sa ” Shikuma yayi Hakan ne Dan A kara Samun Had’in kai A tsakanin su ,,
” Da Dare Salma ta Rangada Girki Mai Rai da motsi yayinda ta Ci uban make ,,upp kamar ba itaba ajima Anjima ,,ta Duba agogo haka Ta tsara komai sai wani Kisisina takeyi Farouq baidawo ba sai misalin 9 Bangaren Salma ya nufa Da murna ta Taresa Shikuma sai wani Biye mata yakeyi Dan Farouq Mutun ne maison a tarairayesa nan da nan ta Gama dashi Room dinsa suka Nufa ya Rage kayan Jikinsa . Ganin Abin na Salma bamai karewa bane yasa ya dakatar da ita yace Dear sorry kinsan yanxu Bamu kadai bane Jeki ki kira kanwarki muci Abinci Kinga tana Jiranmu badan Taso ba ta Tashi yayinda Shikuma yadawo sitting Room yana jiran Isowar su.
★ Rukayyah na Zaune A Dakinta Bayan ta karasa Sallah Isha Dan yau tayi Wanka karatun Al-Qur,ani mai Girma takeyi Da murya mai Dadi a gurin mai Saurare Salma tashiga Noking din Door Rukayyah bataji ba Dan Dayake karatun ya D’auke mata Hankali Abin ya matukar Tunxura Salma tace Lallaima wan nan Yarinyar dani take Zance murda kofar tayi tajita a Bude Sa kai ,, kawai tayi Mutuwar tsaye tayi Dan Yau itace Rana ta Farko data taba shigowa part din Rukayyah tun Kawota A cikin Zuciyarta tace Tab Wan nan Dukiya da aka zuba mata a gidan nan kamar wata yar Hamshakin mai Kudi A Hankali ta fara Notice din komai Har kitchen sanda tashiga bata Tsinkeba saida Tashiga Room din da take jiyo Saurin Kira,a natashi bako Sallama ta Bude tashiga Zare Ido Tayi dataga Wani Hadararen Royal Bed ,, Da kyar ta Hadiye Yawo Tare da gyaran Murya Rukayya bata Dago ba saida takai Aya ta dago da Murmushi a Fuskarta Lah Aunty Salma kece yau Shigo Zauna mana Yake Salma tayi tace No bazama Zanyi Abinci zaki fito muje muci Rukayyah tace OK ganinan zuwa Barin Room din Salma tayi Tana ta Magana a cikin Ranta lallai wan nan saina Tashi Tsaye yarinya kamar yar Tsana Hmmm Tabdi ,, tayi wucewarta zuwa nata part din Nidai Binta nayi Da Ido INA Kallon Ikon Allah ????.
” Rukayyah Kara Feshe Jikinta tayi da Turare Aoud mai Dan Karen Kanshi kamin ta Dauki mayafinta ta Rufe Jikinta tana tafiyarta Hankali kwance Harta Isa Part Din Salma da Sallama tashiga ,, Part din Fuskarta D’auke da Murmushi Farouq ya Amsa shima murmushin yakeyi Gaidasa tayi tamin ta samu guri tazauna Batare da Bata lokaci Farouq yace muje muci Abincin ko Salma sai Hararan Rukayyah take Ganin irin Kallon da Farouq yake mata A Ranta tace Jarababa yaudai kya kwana ke kadai mayyah kawai( Jama,ah kujimin Salma Da Wani zance oh oh mata Da kishi ) Rukayyah batamasan tanayiba Samun Kujera tayi yazauna Abinta yayinda Salma ta fara zubawa kowa Abinci Tanayi tana Jan Hankalin FAROUQ Wanda Gabaki Daya ya Mutu a gurin Kallon Rukayyah Dakyar yasamu yayi control din Kansa ya kula Salma Bayan sun Kammala cin Abinci suka Dan Taba Hira Sama2 Rukayyah tayi musu Sallama Zata wuce Farouq yace Angel kona Rakaki ne Tace no Kayi zaman ka Badamuwa Salma tace wane irin karakata Halan dazata zo wanine ya Rako ta , no kinsan Yanxu Dare yakara yi kar taji Tsoro Turo baki Salma tayi Yace lallai nida naje kiranta Dazu wani ne ya Rakani Ganin Zata miyarda Zancen wani Abu yasa ya Dauko wata Caftar aka Basar da Zancen.
★ Sosai Salma tayi mamakin Ganin Irin yanda Farouq yaketa Rawar jiki Daya ,, kusanceta Kwata2 Batama yi Tunanin Samun irin Haka daga Garesa ba Baccima Kalilan yayisa Wanda Hakan ba karamin Dadi yayiwa Salma ba a Ranta tace wayasani koya Canye abinsa kamin a shigo karyar Banxa Anxo ana mana wani fankama ashema nafita sai Rawar jiki yakeyi akaina ina Amaryar Haka tata kitsawa Har Bacci ya kwasheta . Rukayyah Baiwar Allah Tun da tadawo part dinta tarasa Abinda kemata Dadi Saboda a kwanan nan tasaba sosai da FAROUQ yaugashi Zata kwanta ita Daya wata Zuciyar kecemata yanxu yana can Yana yiwa matarsa irin yanda yake maki wani Abune taji yataso mata Ganin Tunanin ta zaiyi yawa shaidan zaiyi tasiri akanta yasa Tace “A,uzubillahi minal shaidanirrajim” Ta Basar da Zancen kwanta wa tayi a beda dinta sai juye juye takeyi Ganin Rakasa Bacci yasanya ta Dauro Alwalah tashiga yin Nafillah Sallar dare Dan Neman Samun Zaman lafeeya da Kwanciyar Hankali Yauwa maccen Kwarai Diyar Albarka Saliha acikin mata nagaidaki Macce Tagari.