YAR BAIWAH HAUSA NOVEL

YAR BAIWAH HAUSA NOVEL

Bamai takura musu sai abinda sukaso sukeyi tun suna yara abindai ba,a cewa komai idan kanaso kaga fadan Hajya to taba mata yan biyunta ba abinda sukeso a duniyar nan Wanda Hajiyarsu bata musu(Jan kunne????Hatara iyaye mata mukula sosai da sangarta ‘yayanmu dominsu amanace awanjemu ki???? sani Allah zai tambayeki game da tarbiyar da kika. Baiwa ‘yayanki dolene mu tsawatar musu Dan ance kaso naka duniya ta kishi inkaki naka duniya ta soshi haka zancen yake Allah yasa mugane Ameen)
Alhaji Basheer rikaken Dan kasuwane kuma shahararren mai kudi Wanda ketashen kudi a wan nan zamani duk da dai ba sa,an daddy. Bane kusan Allah mai hadin zumunta. Wata rana ne Alhaji. Basheer yaje Bank dinda daddy ke aiki domin ya cire wasu kudade nashi sai aka samu akasi bai samu yanda yakeso ba kuma gashi tafiya zai yi yarasa mafita shine daddy ya taimakesa yasamu kudin iya adadin abinda yakeso to tun daga ranar yazama duk indai kudi yakeso a bank dinsu Daddy to Daddyn kawai zai nema hartakai ma daddy da kansa ya sha kawoma Alhaji Basheer kudi har gida wan ne yasa sukayi sabo har Alhaji Basheer yakan Dan saka daddy wani abu Wanda yake na sirri kuma ayimasa yanda yakeso batare da ansha wahalaba wan nanne dangantakar Daddy dakuma Alhaji Basheer ,
Bayan sun gaggaisa Ruky da Sajeedama suka gaida shi cikin girmamawa, sosai yaran suka bashi sha,awa ya yaba da hankalinsu sosai har yake tambayarsu ajinsu nawa da skull dinda suke suka bashi amsa kai tsaye ya CE gaskya kunada kokari so keep it up duk Kansu dariya sukayi sukace Insha Allah , Jim kadan sai ga Hajya Kubra manta manta anfito ana wani tako daya bayan daya kamar,batason taka kasa tana wani nuna is a ,daga saman stairs falon ta nufa gurin da su Daddy ke zaune anata labaran duniya shida Alh su mummy kuwa hankalinsu nakan palasma TV dake jikin bango suna kallon news.
Au Alhaji wai baki mukayine,murmushin taikaici yayi, yana mai jinjina hali irin na matarsa , Eah kawai yace mata yaci gaba da abinda ke gabansa .
Sannuku kawai tace dasu takoma warta dama ko sakowarda da tayi taga Alhaji ya matsa mata da kirane shine ta sakko taga meyene gaidata su Sajeeda suka shiga yi a dakile ta amsa tayi ficewarta Alhaji baiji dadin abinda tayi ba ammato ya ya iya.
Wuraren 10:30pm suka yima Alhaji Basheer sallama ya dauki kudi yabasu sukaki karba aikuwa yayi juyin duniya sukaki saida yanuna bacin ransa kamin nan, daddy ya umurcesu dasu karba kishi Sajeeda CE ta amsa Ruky kam ki tayi saboda kunya.
Muje zuwa

Maman Ussee????
Kuyi hkri aiki ne yamin yawa shiyasa but insha Allah gobe zanyi mai yawa nagode sosai masoyanah????

???? YAR BAIWAH ????1⃣3⃣

Maman Ussee

Da isarsu gida kowa, yanufi dakinsa Dan kwantawa, a huta yaukam ba, zancen fira , Ruky da Sajeeda wanka kawai sukayi sai alwala kowacce ta nemi shifida, sai. Bacci

Kashe gari tun safe suka tashi bayan sun kammala ayunkan gida kai, tsaye dakin mummy suka, nufa bayan sun gaidata da. Ne ,
Suka nufi dakin daddyn su, shima sukayi gaidashi, kamin nan sukaje suka ci gaba da sauran yan aikace aikacen gida Dan mummy bata barinsu girki saidai ta nuna musu amma har yau bata sake musu girki ba acewarta su yarana har,
Yanxu baza ta sake musu komai ba, sai nan gaba iya kacinsu shara sai wanke wanke , da sauran Dan abinda , baza,a rasa ba.
Time din break nayi kowa ya halara mummy tayi saving din kowa, aka fara cin abinci , bayan an kammala ne Daddy ya ke tambayar su daya bayan daya koda matsala ne Dan,
Dama haka yakeyiwa kowa. Daga nan duk mai bukatar wani abu saiya fada kowa yace , Bakomai Daddy ya wuce zuwa Bank. Dan yau ba skull ana hutun good Friday ne yaran yau basa zuwa skull , Bayan sun kamala aikinsu sai suka tambayi mummynsu sunaso, ne suje dubo wata yar class dinsu datake, nan unguwarsu . mum tace dasu karsu Dade suyi sauri su dawo , tau suka amsa kamin nan suka dauki hijabs dinsu,
Suka ficce daga gidan , gidansu Hafsat suka nufa nan ne bayan layinsu da sallamar su suka shiga cikin gidan, bayan sun gaida umman Hafsat sai suka shiga dakin Hafsat din, bayan yan gaishe gaishe , suka fara fira irin nasu na yan makaranta, Basu suka dawo ba sai bayan an taso daga salar jumma,a dayake yau Friday ne , kai tsaye gida suka nufa koda sukaje mummy tayi baki bayan sun gaida sar da bakin mummy dakin su suka shiga suka sayi sallah bayan sun kammala, suka fito suka Debi abincinsu suka koma dakin su, sunata wasa da dariya batare da wata damuwaba yan biyun mummy kenan!!!

Maman Ussee????
Note
Dan Allah kuyi hkr wllhi kwana biyu bana jin dadin ne amma yanxu naji sauki zanci gaba dayi muku insha Allah nagode sosai da kulawarku????

???? YAR BAIWAH????1⃣4⃣

Maman Ussee

Safiyar Talata tun safe suka tashi suka fara shirye 2 na zuwa skull, bayan sun kammala da komai da komai Daddynsu yadaukesu yakaisu bayan ya ajiyesu sai ya ficce zuwa wurin, aikinsa Su Abdallah da Fadil ma nasu bangaren suka nufa, yayinda Sajeeda da Rukayya, suma suka wuce, zuwa assembly, ground,
After ankare Assembly duk student’s suka ficce, zuwa classes dinsu Dan daukar darasi, bayan Class master din su Ruky yashigo ya kira register, sai aka fara gabatar musu da lesson din nasu .
Kwanci tashi baya hana zuwa yau har su Sajeeda da Rukayya sun rubuta JSCE lafiya lau murna gurin Daddy da Mummy kamar me, Haka Rayuwarsu taci gaba da kasancewa har lokacin da exams dinsu ya fito Daddy yayi musu alkawarin zai canja musu skull dan ya yaba da kokarin yaran yayinda Alhaji Basheer shima yayi alkawarin zai bada nasa contribution, din idan zasuje gaba Dan shima yaran suna birgesa, more especially
Tarbiyarsu ga girmama nagaba dasu,
Kamin karshe Hutu Daddy yakai Rukayya da Sajeeda Raba domin suyi hutunsu acan , sunsha Hutu kam Dan saida sukayi kusan wata Daya acan ba karamin Dadi hakan yayima Baaba Dan tana matukar son Rukayya , bayan sun dawo, Hutu kuma sai suka dukkufa zuwa Islamiya Dan dama sauran kadan su sauke kuma Daddy yayi musu alkawarin sai sun sauka zai kaisu SS one Dan dama hakan sukeso badan ma sunje Hutu a Raba ba da yanxu sun sauke hakan sukeyi kullun akaci sa,a kuwa Rukayyace ta fara sauka bayan Sati daya Sajeeda ma tasauke Murna da Daddy yayi. Bata misaltuwa kullun saiyayiwa yaran sa addu,a Allah yakara musu basira Alhmdllh Addu,arsa ta karbu Dan kuwa ga sakamakon hakan yagani.
A tare daddy ya hada musu walimar sauka a gida bayan an gabatar musu da wata walimar a makaranta, ba laifi kam an taru bayan an gabatarda yan naseehohi akayi musu addu,a sai yan kayan rabo da akayi bayan an rufe taro da addu,a kowa ya watse,
Daddy ne zaune da yaran sa anata wasa da dariya uhuum Abban yara wai mexai hana ka kokarta ka kai su Iman ne naga can ana karatu sosai ko cewar mummy Daddy ya nisa eah haka ne amma kudin ne , sunyi yawa kuma nafiso nakaisu Inda zasuci gaba da Hadda Dan ,dama nayi shawara zan kaisu, Sultan Abubakar Maccido Islamic college, koya kika gani ,ai Ruky da Sajeeda najin haka su fara murna yeee Thanks much Daddy we love u Daddy Allah yakara budi sukaje suka Rungume Daddyn nasu suna murna ,daga nan kuma aka ci gaba da hirar duniya kamin time din sallar magrib yayi , Dad yaja su Fadil zuwa masallaci yayinda su Sajeeda da Rukukayya suka shiga cikin dakin su domin gabatar da Sallar magri b.
Bayan kwana biyu Daddy yadaukeso sai new skull dinsu dayake akwai masu yin day a ciki akwai kuma masu yin boarding Daddy baya da Ra,ayin barinsu suyi boarding, Day yasaka su bayan ya yayi musu registration, da duk wani abubuwa da yakamata sanda akayi musu interview, aka basu classes saidai ba,a ajesu a class daya ba kamar yanda sukeso , badan ransu yaso ba,haka suka hakura Dan bayanda zasuyi, haka suka zauna a new skull din taso dayake akwai Dan banbanci kadan Dan yanxu sai 4:pm suke tashi dan, skull din hade take da Islamiya Ruky da Sajeeda baruwansu dashiga harkan da banasu ba hakan cema tasa basuyi wasu sabbin kawayewa ba Dan acewarsu kowa ya tsaya matsayin sa Inda Allah ya ajesa , kwana biyu sukayi suna a cikin makaranta akan BAIWAR Ilmin da Allah yayi musu abin sai Wanda yagani Teachers suka fara sonsu duk Inda kaji cikin skull zance Sajeeda da Ruky akeyi Abin yafara bawa wasu student’s din haushi Dan yanxu da wuya ayi wani skull conpotiong ba dasu ba gasu da kyau kamar diyan laraba da yawa ss3 student, sun sha musu gargardi akan wasu malaman, abin har mmki yake baiwa su Ruky Dan su a tsarin su ba soyayya a halin yanxu Dan Daddy baya barinsu ko da wasa balantana ma a skull dayake dokar makaranta CE .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Leave a Reply

Back to top button