YAR BAIWAH HAUSA NOVEL
Maman Ussee????
???? YAR BAIWAH ????1⃣9⃣
Maman Ussee
Sajeeda saida ta fahimci Rukayya tashi dayawa San nan ta daina bata abinci sun Dan taba fira , anata wasa da dariya Daddy ya kalli Rukayya, yadai baby tazu aikin meye kikayi mai wahala ne a gida ko a skull, Dam taji gabanta yafadi runtse ido tayi ta tuno da irin azabar da tasha a gurin su Sister Jameela Budurwar uncle Faruuq, sake bude ido tayi nanda nan mood dinta ya canja, gabaki daya fara,ar ta.
Ta dauke murmushin karfin hali tayi sannan tace bakomai Daddy bayaso ya takura ta duk da ya fahimci dakwai wani Abu amma bayaso yayi forcing, dinta dole saita fada basar da zancen akayi aka dauko wani zancen na daban,
Basubar asibitin ba sai guraren 10:30pm ya dauki su Sajeeda da Abdallah da Fadil zuwa gida yayinda aka bar mummy ta kwana da Rukayya kamin gobe su nemi sallama, Sajeeda ma ba,ason ranta ta tafi ba Dan dai Daddy yace gobe dakwai zuwa skull kuma bai dace Dan Rukayya batada lfy Sajeeda taki zuwa makaranta ba dolene ita taje ,
Bayan sun tafi. Mummy ta dubi yarta tafara yimata nasihohi Dan ta kula da kanta, da abubuwan da duk suka dace uwa ta fadawa yarta wasu Rukayya saidai ta sunkuyar da kanta kasa Dan kunya takeji mummy sai dai tayi murmurshi , Dan tasan Insha Allah irin tarbiyar da suka baiwa yaran su da wuya su fandare inba wani ikon Allah ba kuma tana musu fatan samun kariya da duk wani sharin mai Sharri,
Kashe gari tun safe Sajeeda ta tashi tashirya cikin uniform dinta, tanata jin wani iri Dan ta Riga yasa ba da komai a tare sukeyi da yar uwarta Rukayya sabanin yau da ita kadai takeyin komai sabo kenan turken wawa. Bayan Daddy ya ajiyesu a skull saida yabiya office din principal yayi report, cewa Rukayya batada lfy sai dai next week zata fara shigo wa insha Allah da yake ranar laraba ne abin yafaru gashi kuma yau alhamis da yau da gobe baxata shiga ba Dan assabar da lahadi week end ne sai dai on monday , principal din yace it’s OK badamuwa Allah yabata lfy sai dai on Monday din nan tashigo saboda sun fara texts kar tayi missing Dan nasan yar wajenka she’s very hard working student Daddy yaji dadi sosai ya basa hannu sukayi misabaha kamin nan ya fice daga skull din, zuwa Hospital Dan ya dubo ya jikin na Rukayyatu.
A asibiti kuwa bayan Doctor ya duba ta da safe. Ba wata matsala sai ya rubuta musu sallama kuma ya umurci data sha maganin ta abisa ka,ida kuma cikin lokaci, Daddy kawai dama suke jira yazo su wuce da isuwarsa daukansu kawai yayi bayan yayima Rukayya ya jiki ya kwashesu sai gida daga nan kuma ya ficewarsa zuwa gurin aikinsa,
Faruuq ne yafito daga cikin motarsa kiran Mercedes sanye da Riga da wando na jeans wandon. Baki Riga kuma fara anyi mata rubuta da bakaken harufa an rubuta it’s my Time bai zarce ko,inaba sai admin block yaje yayi sing kamin nan ya wuce staff office ya dauki abinda zai dauka ya nufi class dinda yakeda lesson wato A class SS one A ajin su Rukayya a zuciyarsa muradin ganinta kawai yakeyi Dan tun jiya yakejin faduwar gaba gani yake kamar wani Abu yafaru da ita bayan sun rabu jiya dashigarsa, bayan student sun gama gaidasa Sit dinda take zama ya kalla amma ga mmkin sa ba tanan sake ,daga Kansa yayi ya kalli wurin bayaso ya tambayi yan class dinsu Dan kar suyi suspecting din wani Abu ,haka dai ya daure ya fara lesson din zuciyarsa sai zafi take baiga Angel dinsa ba, wata dubara CE ta fado masa arai dayake jiya books din su, yana hannu sa shine yayi amfani da wan nan damar ya aiki class captain Dan taje staff room ta dauko books din tanan zai San in angel dinsa na nan ko bata nan bayan ta kawo yafara mark yana kiran suna Dan mai littafi yazo yakarbi kayansa , da haka har yakai ga nata yakira name dinta Rukayya Sa,eed shuru ba Wanda ya karba ,saida ya maimata har sau 2 .
Kamin nan yan class dinsu ka CE uncle yau batazoba ,what? Yafada adan razane sai dai a hankali yayi kokarin saita kansa kamin. Nan yace saboda meye batazoba yau muma bamu sani ba suka. Bashi amsa daga baya sukace akwai dai sister dinta a C class sai in ita za,a tambaya cewa kawai yayi suje su kirata member dayace cikin yan Class din taje block dinsu Sajeeda danyin kiranta bayan tazo, uncle Faruuq yakalleta ke INA sister dinki meya hanata zuwa skull yau , uncle batada lafeeya kuma whorse Dan yanxu haka tana asibiti ,Dam Dam Dam yaji gabansa ya fara duka acikin ransa cewa yake to meke damun my angle yazama wajibi naje naganta to amma ta yaya zanje? A wane matsayin? Ganin zai batawa kansa lokacine yasa ya. Baiwa sajeeda book din Rukayya tare dayi mata fatan samun sauki ya tambayi Sajeeda a wane asibiti ne aka kaita specialist kawai tabasa amsa ta juya zuwa class dinsu Dan daukar lesson dinta.
Maman Ussee????
Naga sakonku my fans INA godiya sosai da kulawarku????
???? YAR BAIWAH ????2⃣0⃣
Maman Ussee????
A gurguje ya kammala duk wani abinda yakeyi yaje yadauki excuse, bai zame a ko,inaba sai a specialist hospital, room by room yayita shiga amma komai alamarta baiganiba kamar ya daura hannu aka yayi ihu meyasamu Angel ya akayi bansaniba anya zan iya jure rashin ganinta kodai naje na tambayi sister dinta gidansu, ohh no baxan iyaba banaso ,ta fahimci wani Abu a halin yanxu she’s still young, batasan meye so ba shikadai yaketa sambatunsa , jiyake zuciyarsa kamar zata faso kirjinsa ta fito in bai samu Rukayya ba ohh wai meyake faruwa dani ne young girl tanata wahalad dani abanxa batama San inayiba,
car dinshi ya shiga ya tadata ya bata wuta sosai sai gida haka shima yakejin kansa kamar bashida lfy har mamakin Kansa yakeyi ,wai yarinyarda bata wuce 15 ba take rudashi ,haka yaga mata kala2 amma baitabajin wani fillings akansu. Ba sai ita, ita din daice a cikin zuciyarsa!! A katon Falon gidansu ya zube. Dafe da kansa , ya Dade yana zaune a gurin yanata tunanin ,yanda zai bullo wa lamarin Dafa shi yaji anyi, a hankali ya dago Kansa yayansa yagani yadai Umar lafiya kake kuwa naga kayi zurfi inata sallama bakajiba, Haka dai naganshi kwanan nan bai cika son surutu ba dama shi bai faye magana. Ba amma kwanan, nan abin yayi whorse cewar Hajiyarsu dago Kansu sukayi a tare suka gaida mahaifiyar tasu , cikin girmamawa, cike da kulawa ta amsa ,dama idan kaga fara,ar ta to tana tare da ya’yan tane .
Hajiya Kubrah kenan manyan mata Abubakar ya dubi mahaifiyar sa mum wai yaushe ne su Aleeyu zasu dawo ne sunfa karasa exams dinsu jiyama nayi waya da Usman ba abinda ya tsayar dasu kawai dai shiriritace irin tasu, Hajiya kubrah ta nisa oho sai sun gama hutawa inga zaman London yana musu dadine shiyasa, Amma duk ranarda Alhaji yaganosu kashin su yabushe cewar Abubakar kawai Dan dan sun maida ba a, bakin komai. Ba sun kare exams shine suke tayiwa Abba karya yana tura musu kudi bayan sunsan sun kare Dan kawai rashin kishin kai, kai dakata ra,ayinsune saboda haka ka kyalesu sai ranarda sukaga dama su dawo Kai takura maka akayi dakake karatun, wayene ya matsamaka, baice komaiba dai shi a duniya yana mamakin hali irin na Hajiyarsu kwata2 bata son a takura wa ya’yanta kawai Dan suna da gata Allah dai ya kyauta,
To Mum su Afra fa sai yaushe, kaga Malan banason sa,ido towai Ina ruwanka ne kai kake biyan kudin makarantar ne ko ta aljihunka ake biyan kudin meye naka a ciki ,kabarsu suyi abinda sukeso lokacinsune, Umar Faruuq da yaga surutun nasu kara chaja masa kai kawai zasuyi fita yayi daga falon yanufi sashensu Dan Inda sabo yasa ba dajin irin wan nan dramer din ,tsakanin Hajiya da Abubakar, kawai dai shi Abubakar, din ne da na cewa kullun saiyama Hajiya maganar dawowar, k’annensa Nigeria amma amsa dayace take bashi ,shibazai iya hkra yasa masu ido bane, gani yayi idan yabiyewa Hajiya da Abubakar sai sun kara karamishi wani sabon al,amarin gara yabar musu gurin,
Dakinsa ya nufa kan bed dinsa ya zube zuciyarsa sai bugawa take runtse idonshi yayi yasake budewa ahankali ya furta I LOVE YOU RUKAYYAH.