HEEDAYAH 6

6…….
Kaka ta rike ha6a tana kallon Mumy tace “Lallai ba lafiya, Kar ki yarda, ba mu san irinta ba, kuma ba ma bukatan sani, ba ruwana da jajibe jajibe
gaskiya, to meye kuma na tsinto yarinya kamar wanda nace ma je ka kagani, to ni dai ba ruwana, mu je ayi meeting din gaba daya, ai kin ga ko
shigowa gaisheni ma bai yi ba tunda ya tsinto wata uwar tasa a titi jiya, kuma ace min lafiya qlau, a’a wllh ba lafiya” sosai hankalin Mumy ya
kwanta jin furucin Kaka, Kaka ta mike ta nufi kofa Mumy na biye da ita tana murmushi, Shuraim ya bi su da kallo kafin ya mike shi ma ya fita
parlon. Babban parlor ne me dauke da tsadaddun kujeru ba masu hayaniya ba, Hajiya Amina da kishiyarta Hajiya Hauwa na xaune parlon sai Safiyya,
Nafisa da Aisha ‘ya yan Hajiya Amina, Jamila da Zainab ‘ya yan Hajiya Hauwa su ma na xaune parlon, Khadijah da Rabi’ah duk suna parlon su ma, Abba
na xaune tare da Heedayah da ya xaunar gefensa, Alhaji Umar ma na xaune idonsa a kan tv dake nuna tashar Aljazeera, a tare Hajiya Maryam ta shigo
parlon da kaka da ta tsuke fuska, Abba dai kallon mahaifiyar tasa kawai yake har ta xauna, Shuraim ne ya shigo da sallama ya nemi kusa da Khadijah
ya xauna sannan ya gaida su Hajiya Amina da Baffansa, d’a murmushi ya amsa gaisuwar cousins din nasa mata dake kallonsa gaba daya, Baffa ya rage
volume din TV din yace “Ina Sudais?” Safiyya tace “Bai dawo training ba” Baffa ya gyada kai alamar gamsuwa, Abba na kallon kaka yyi kasa da kai
yace “An tashi lafiya kaka?” Kaka tace “A’a ba ruwana, lafiya lau na tashi” tana magana ne tana kallon Heedayah kasa kasa, Rabi’ah da Khadijah suka
gaisheta su ma, tace “To duk ku tashi ku fita, ko kun ga sa’annin ku a nan, wannan ai ba maganan yara bane, babban magana ce, Yaron kirkin nan
kadai ya cancanci xama a nan, duk ku fita” Hajiya Hauwa tayi murmushi tana kallon Shuraim da ya sunkuyar da kansa, Mikewa su Khadijah suka yi gaba
daya har da su Safiyya suka fita bbu halin ko yi mata kallon banxa, shiru ne ya biyo baya a parlon, Baffa ya bude wajen da addu’a, bayan haka ya
kalli Hajiya Maryam yace “Why did u invite our mother in here?” Ta gyara xama tace “Bcos it’s necessary, she needs to know what’s happening” Bai
kuma cewa komai ba, bayan few seconds ya daura da cewa “Ba wani abu ya tara mu nan ba… jiya da maraice Barrister ya dawo gida da wata baiwar
Allah wanda hakan ya kawo rashin fahimta a can gidansa, ga kuma yarinyar dai xaune kusa da shi….” ya fadi haka yana nuna Heedayah wanda duk kana
ganinta kasan a tsorace take, Ya ci gaba kamar haka “Duba da irin xamanin da muka tsinci kan mu na yanxu a gaskiya hakan ba shawara bace me kyau
it’s risky bringing the little girl home, sai dai me??? Mu duba wannan yarinya, har nawa take gaba daya, duk magidancin kwarai ya ga yarinyar nan
that looks helpless a hanya ba lallai ya iya wuceta bai yi making effort din taimakon ta ba, ko min kankantar taimakon kuwa, sai dai shi barrister
nasan taimakon ya yanko sa da girma ne tunda har gidansa ya kawo wannan baiwar Allah, wanda ba kowa xai yi hakan ba a xamanin nan na yau gaskiya,
ba wai ina nufin hakan da yyi kuskure bane amma in the other way round xa a iya kiransa da kuskure….” Kaka dake ta hararan Baffa ta yi kwafa tana
girgixa kafa, Baffa ya ci gaba “Amma kuma xai iya yiwuwa yaga kawota gidan shine kadai mafita duba da cewa she is unsighted…. Har xuwa lkcn da
Allah xai bayyana iyayenta” Calmly Hajiya Maryam tace “Idan Allah bai bayyana iyayen nata ba fa?” Baffa yace “Wannan kuma baxa a rasa yanda xa ayi
ba in sha Allah, Hajiya kar ki manta one knows not where his or her reward lies, sannan muna da baya, we should always try positioning things in
our shoes” Girgixa kai tayi irin ba mutunci tace “Toh ni ban hanasa riketa ba Doctor, Amma Wallahil Azeem ba ni xan rike masa ita ba,… Ya nemi
inda xai kai ta, ko kuma ya bar ta nan wajen ku ai duk daya ne…” Da sauri Hajiya Amina ta kalleta da wani expression, Kaka ta kyabe baki tace “To
duk kun gama??” Duk aka yi shiru ana kallonta, ta gyara xama tace “Toh maza tun muna mu bakwai ba mu dawo mu takwas ba a parlon nan Amadu ya maida
wnn yarinya inda ya dauko ta, mu ba gantalallu bane, bamu sa6a kwashe kwashe ba a dangi, baxa kuma a fara ta kan d’a na ba….” Shiru ne ya biyo
bayan abinda Kaka tace a parlon, Abba da Baffa sai kallonta suke, Hajiya Maryam taji kamar ta tashi ta rungume kaka don farin ciki, Hajiya Amina
kuwa sai murmushi take kasa kasa, Hajiya Hauwa dai sai kallon Heedayah da ta makale jikin Abba take, Bude kofar aka yi wani matashi ya shigo da
sallama, sanye yake da sport wears, they have many resemblance in common with Shuraim, sai dai ya girme ma Shuraim da shekara daya duk da ba wai
hakan ya nuna bane, bin occupant din parlon yyi da kallo, coz he knew nothing about the meeting, ya kalli kaka da ta tsuke fuska ganinsa tace “Kai
ka ji wani neman fitina gun Mutumin nan ko sudais….” xaunawa yyi gefenta coz yasan she will brief everything a nan take kafin ma ace masa komai a
parlon, ta gyara xama tace “Kanin ubanka dai ya xama abinda ya xama, Wai kaji yarinya ya tsinto ya kawo gida ba dangin iya balle na baba, har yana
ikirarin bbu wanda ya isa ya hanasa abinda yyi niyya bai san magana xai dawo kunne na ba, Toh mu xuba da shi, idan shi ya haifeni ai yanxu kowa xai
sani, kuma nace masa maxa ya mayar da ita kada raina ya bace….” Murya can kasa Sudais yace “Wacce yarinya ce?” Heedayah ta nuna masa rai bace
tace “Gata can kamar mage….” Sudais ya kalli Heedayah da ta makale Abba, sannan ya kalli Abba da Baffansa da suka kasa cewa komai, ya maida
dubansa kan Kaka, lkci daya ya hade rai yace “Toh meye don an taimaki wannan yar yarinyar, ni na ma xata wani babban abu ne ya faru a gidan, ynxu
ba fata ba yau ace Safiyya ko Jamila sun 6ace baki son wani ya taimaka masu kenan? Kika san dalilin da yasa Allah ya rabata da iyayenta?? Ke da
xaki yi fatan Allah ya bayyana su….” Katse sa tayi da sauri tace “Kun ji min fitsararren yaro ko?? to ce maka nayi ban yi addu’ar Allah ya
bayyana iyayen nata bane?? Ni dai ba ruwana ka daina min sharri, dama kwana biyu na fita harkan ka a gidan nan sam baka da mutunci ka rainani….”
Ya mike yace “A’a ni ban rainaki ba kaka ke dai baki son gaskiya, kawai ki bar Abba ya rike yarinyar a ci gaba da neman iyayenta, ynxu idan ya
mayar da ita kika san hannun wanda xata fada, kinsan fa idan ta fada hannun mugaye ke ma kina da kwamasho me girma, sannan kin fi kowa cewa aji
tsoron Allah, kuma ga lamarin da ya kamata mutum ya ji tsoron Allah nan….” Tagumi kaka tayi tace “Kuna dai ganin Aliyu ko?? To ba komai rayuwa ce
ai” Hajiya Maryam dake ta xufa sai kallon Sudais take tana hadiye abu da kyar, Baffa dai ya jinginar da kansa da kujera yana kallon d’an nasa, Abba
kam kansa na kasa shi ma yana saurarensa, Hajiya Amina duk uwar hararan da take xabga ma d’an nata yaki kallon direction dinta, Hajiya Hauwa banda
murmushi bbu abinda take, Sudais na kallon kaka yace “Kawai dai yanxu sbda tsoron Allah ki bari Abba ya nemo iyayenta, kuma ta xauna har sanda
Allah xai bayyana su….” Kaka tace “To ni dai ba ruwana, dama Maryam ce tace bata yadda ba banda haka ni meye nawa?? ai d’a na kowa ne bawa sai me