NOVELSUncategorized

YARIMA FUDHAL 21-25

*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdaucee Jeebour.
21
DARE
9:00PM
Falon Mai Martaba cike yake da mutanan gidan sabida meeting d’in gaggawa da Mai Martaba ya shirya a daran nan.

Gefe guda Mai martaba Sarki Ubaiyd ne kishingid’e bisa kusun, daga wajen kansa Fulani Bingel ce tare da ‘ya’yanta Aunty Sadiya da Aunty Sa’ida mazajensu suka kawosu, sai Yarima Fudhal daga wajen k’afarsa kuma Fulani Sokoto ce tare da ‘ya’yanta ita ma a kusa da ita, Yarima Jaleel da Jalila sai Gimbiya Safiyya .
Mai Martaba ya shafe tsayin lokaci yana bin iyalinnasa da kallo, kafin yayi gyaran murya tare da jero addu’o’i sannan yayi sallama suka amsa ya fara fad’in.
“Ba komai ne yasa ni shirya wannan taron na gaggawa ba sai dalilin faruwar bijirowar wata b’araka daga cikin danginmu, da kuma shirya rushewar martabar danginmu da mutuncin sarautarmu!”.
“Fudhal…!”.
Mai martaba ya kira sunan da kakkausar murya.
Kowa sai da ya dubi Mai Martaba domin yau karo na farko da sukaji ya kira Yarima Fudhal da sunansa sab’anin Magaji da akafi ji yana kiransa da shi tsayin shekaru.
Mai martaba ya cigaba da maganarsa.
“Fudhal kai ne ke shirin ruguza mana komai !, mene haka ka ke shirin aikatawa ?, k’asar wajen da na kai ka tsayin shekaru kayi karatu abin da suka koya maka kenan soyayya da Baiwarka?”.
Yarima Fudhal yayi shiru kansa a k’asa ya kasa iya d’aga kansa bare har ya iya bada amsar tambayar da ake yi masa, mai martaba ya cigaba da fad’in.
“Karka manta kaifa magaji ne a bayana, shin kanason bijirewa umarni nane kome?, ko kuwa ban isa da kai bane?, kar kamance ni Ubaiyd bana magana biyu auren ka da Safiyya tamkar anyi angama ne !”.
Sai lokacin Yarima Fudhal ya d’ago kai ya kalli Mai Martaba kafin ya sake yin k’asa da kansa ya fara magana.
“Bazan gajiya wajen neman afuwarka ba, sai dai ina rok’o agareka Abba ka taimaka kabani zab’in raina nasan hakan tamkar tozarcin Family namu ne amma babu yanda na iya ne tabbas inason Aynu amma da ace ina da damar da zan iya cire soyayyar da na cire ta domin samun yardarku da cika umarninku…!”.
Yayi shiru nad’an wani lokaci yana jira yaji ko Mai martaba zai ce wani abu jin da yayi bai ce komai ba yasa yacigaba da magana.
“Kayi hak’uri Abba !, ni banyi haka domin na bak’anta ranku ba burina kullum bai wuce ganin farin cikin iyayena ba ko da zan rasa raina !, amma Abba ina son yarinyar ne badan komai ba sai domin ta can-canci a so ta, sabida tarbiyarta da kamalarta….sannan!”.
“Kaga ya isa Magaji !, ban kira ka dan intambayeka can-cantar taba ko tarbiyarta na kira ka ne domin in tabbatar maka kome za kayi aure kai da Safiyya da Saima babu fashi sai dai idan sune sukace basa so !, kuma babu kai babu auren wannan Baiwar KO BAYAN RAINA !”.
Yarima Fudhal ya rintse ido sabida yanda yaji zuciyarsa na zafi sosai, har jiyake kamar ransa zai iya barin gan-gan jikinsa a lokacin.
Fulani Bingel ta dubi d’an nata tare da duban Mai Martaba, ta so yin magana amma tasan bazai saurareta ba, tana tausayawa Yarima Fudhal domin tasan halinsa ko kad’an bai iya sanyawa ransa damuwa ba.
Mai Martaba ya sake duban kowa kafin yace.
“Sannan ita kuma yarinyar daga yau tabar aiki a gidan nan, kowa ya tashi ya tafi “.
Wannan hukuncin bak’aramin dad’i yayiwa Fulani Sokoto da Yarima Jaleel ba, musamman uwar gayyar Gimbiya Safiyya gefe guda kuma ga Aunty Sa’ida domin itama tak’i jinin ace Yarima Fudhal yarasa wadda zai lak’ewa sai Baiwarsa tir da wannan al’amarin.
Kowa ya mik’e ya fice ban da Fulani Bingel da Yarima Fudhal ya ya kasa mik’ewa, domin yasan indai yamik’e a wannan lokacin to tabbas sai dai su d’au keshi hakan yasa yayi zamansa yana karanto addu’o’i cikin ransa, Mai Martaba ya dube shi duba na musamman yana fad’in.
“Ka kwantar da hankalinka Magaji kai fa magajina ne, akan wane dalilin zaka bari ka lalata rayuwarka a banza?, ina so ka cire duk wata damuwa dake cikin ranka kayi ayyukan dake gabanka, an kammala ginin Asibitin dana shirya gina maka, na gayyato gwararrun likitocin da zasuyi aiki a cikinsa tare da kai, zuwa nan da sati guda sai ayi bikin bud’eshi ko?”.
“Ehh duk yanda kace Abba, Allah yasaka da alkhairi ya k’ara girma da arzik’i “.
“Amin”.
Fulani Bingel ta amsa tare da cigaba da fad’in .
“Ka k’ara hak’uri kaji ?, komai mai wucewa ne a rayuwa !”.
“Insha Allah”.
Yarima Fudhal ya mik’e yana mai jan k’afafuwansa da sukai masa nauyi tare da bin bango yabar d’akin kai tsaye d’akinsa ya nufa ya shige toilet ya sakarwa kansa ruwan shower mai sanyi domin wai yaji sanyi cikin ransa.
Fulani Bingel ta dubi Mai Martaba bayan fitar Yarima Fudhal tace.
“Da anbi komai a sannu Mai Martaba !, wannan hukuncin kamar yayi tsauri domin ban da Allah babu wanda yasan matar mutum, domin shi al’amarin aure sai anbi a sannu…!”.
“Ki na so ki goyi bayan d’anki ne?”.
“A’a ko kusa kaima ai d’an kane”.
“To bana buk’atar jin wani k’orafi cikin maganar da nayi !”.
“Allah ya huci zuciyarka !”.
***
Ko da Aynu ta koma gida wunin ranar tayi shine sukuku, har zuwa sanda ta dawo daga Islamiyya ta zauna gaban Ummanta tare da d’aukan littafin Hisnul-muslum tana dubawa, Umman ta d’an kalli gefen da Aynu take zaune tace.
“Meye alak’arki da Yarima Fudhal kuma?”.
Aynu ta d’ago da sauri fuskarta cike da murmushin jindad’i domin ansosa mata inda yake mata k’yaik’ayi.
“Umma ba wani abu bane bafa, kawai dai cewa dai yayi wai yana….!”.
Sai kuma tayi shiru domin jin nauyin mahaifiyarta akan maganar da zata fad’a mata.
Umma tayi ‘yar dariya tare da k’arasa mata maganar da take son yi.
“Yana sonki ko?”.
“Ehh”.
“Aynu kenan…!, amma kinsan abin da zan fad’a miki kuwa?”.
“A’a umma”.
“Duk da cewa ba ganinki nake da ido ba, amma ina kallonki ta zuciyata, nasan kina son Yarima Fudhal amma kada ki bari soyayyarsa tayi tasiri aranki da yawa domin mudai iyayanki zab’inmu shine Ya Sayyadi Umar, duk da ba musan yanda Allah zaiyi nasa hukuncin bisa wannan al’amari ba, amma inaso kiyi tunani Yarima yafi k’arfinmu mu iyayenki bare ke Aynu ki tsaya a matsayinki kada ki kai kanki inda Allah bai kai kiba kinji ko?”.
“Ehh Umma insha Allah zan kiyaye !”.
Aynu takai maganar tana mai goge hawayen da ke bin kan fuskarta, tasan tana son Yarima Fudhal amma kuma bazata iya jayayya da umarnin mahaifiyarta ba.
***
Misalin 6:25 na yamma.
Aynu ta dubi Ummanta tana fad’in.
“Umma bari inje wajen Zainab yau duk bamu had’uba sabida banje aiki ba, kuma ina son karb’o wani littafi ne”.
“To amma kinga yamma tayi ankusa sallar maghriba ki dawo da wuri kada Babanki yazo ya tarar bakya nan”.
“To Umma dama ba jinawa zanyi ba, ina karb’owa zan tawo”.
Ta kai maganar tana mai ficewa, ko da ta isa gidansu Zainab Mamanta bata nan sai Zainab d’in zaune tana yankan farce, Aynu tayi sallama ta shiga ta nemi guri kusa da Zainab d’in ta zauna suka fara hira.
“Kinsan kuwa amsar da Mama ta bani dana tambayeta akan maganar nan?”.
Cewar Zainab kenan tana mai duban Aynu, Aynu tace.
“A’a sai kin fad’a”.
Nan Zainab ta kwashe duk yanda sumai ta sanar mata, sosai kayan cikin Aynu suka juya har sai da ta nufi toilet ta fito ta nemi guri ta zauna tayi ta gumi tana fad’in.
“Ko kinsan d’azun nan Umma kemin maganar wai inyi baya-baya da Yarima su zab’insu Yasayyadi Unar ne?”.
Zainab taja ajiyar zuciya tana fad’in.
“Karki damu Aynu muyita addu’a dai koma waye mijinki Allah ne masani kuma shine zai zab’a miki mijin da ya dace da ke, sannan akwai wata magana ma da zan fad’a miki”.
“Ina jinki”.
Aynu ta fad’a ba tare data dubi Zainab ba.
“D’azu Jakadiyya tazo tace a fad’a miki kinbar zuwa aiki sabida Mai Martaba ya bada umarnin kada ki sake zuwa !”.
A firgice Aynu ta d’ago kai ta dubi Zainab.
“Me kika ce?, to mai nayi masa ?”.
“Baki masa komai ba, akan d’ansa Yarima Fudhal yace kibar aiki gidan sabida ya raba ku”.
Aynu tayi ajiyar zuciya tana fad’in.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un !, shikenan ta faru ta k’are”.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy:-Phirdauceey Jeebour.
22
WASHE GARI
“Aynu lafiya kuwa !, yau ba zaki je aikin ba ne?”.
Aynu da ke kwance bisa tabarma ta d’ago kai ta dubi Ummanta ta bud’e baki a hankali zatayi magana suka jiyo ana sallama Umma ta amsa da fad’in.
“Amin wa’alaikissalam Ta Sallah shigo mana?”.
Maman Zainab ta shiga d’akin, Aynu ta mik’e daga kwancen da take ta matsa waje guda domin bawa Maman zee waje ta zauna, Aynu ta gaishe da ita, ta amsa cike da fara’a kafin ta mai da kanta kan Umma tana fad’in.
“Umman Aynu !, Sai mukaji mummunan labari kuma ?”.
“Labarin me fa?”.
Umman Aynu ta jefawa Maman Zee tambaya mai makon amsar daya kamata ta ba ta.
Duban Aynu Maman Zee tayi tare da fad’in.
“A’a kardai kice Aynu bata fad’a miki ba?”.
“Ni Aynu bata gayamin komai ba”.
“Ai Mai Martaba Sarki Ubaiyd yace kada ta kuma zuwa aiki”.
“Subhanallahi !, wani abun tayi musu ne?”.
“A’a kan dai maganar yaronsa Yarima Fudhal da nayi miki magana jiya ne, to Jakadiyya tazo har gidana ta ba da sak’on nima bana gida lokacin Zainab ta samu, amma da Aynu taje gidan Zainab tace ta gaya mata.
Shiru d’akin yayi babu wanda ya sake furta ko kallama d’aya, sai can Umma tabud’e baki tace.
“To Allah ya kyauta daman inata kwab’ar Aynu dayi mata fad’a kancewa ta tsaya iya matsayin da Allah ya ajiye ta, shikenan haka Allah yak’addara babu komai!”.
Aynu dake zaune gefe sai tausayin mahaifiyarta ya kamata domin tasan abin da yake damun Ummanta bai wuce toshewar hanyar samun abincinsu ba yanzu.
“Umma kiyi hak’uri dan Allah…!”.
“A’a Aynu ko kad’an bikimin laifi ba, sai dai ni yakamata inbaki hak’uri, ki cigaba da hak’uri tare da addu’a kan halin matsi da talaucin rayuwar da Allah ya d’ora mana kinji”.
“Hakane komai ai mai wucewa ne Umman Aynu, wannan al’amarin dama sai addu’a”.
Cewar Maman Zee kenan tana mai mik’ewa tsaye ta cigaba da fad’in.
“Ni zan koma, kuyi hak’uri dan Allah”.
“Babu komai fa Ta Sallah karki damu”.
Cewar Umma kenan, Aynu tabi ta da fad’in.
“A gaishemin da Zainab”.
“To zataji insha Allah”.
Maman Zee na fita Baban Aynu yayi sallama cikin d’akin nasu ya nemi guri ya zauna yana fad’in.
“Wacce magana naji kunayi kuma?”.
“Wallahi wai Aynu ce suka kora daga aiki kan wannan yaron”.
“Wanne Yaro kuma?”.
“D’an Sarkin da yace yana sonta mana”.
“Wai Fudhal ko Jaleel”.
“Fudhal d’inne ko Aynu?”.
Umman ta fad’a tana tambayar Aynu, Aynu tayi shiru tare da sauke kanta k’asa, Baba yayi ajiyar zuciya tare da kallon Aynun bai kuma cewa komai ba kan maganar sai tambayar da yayi kan abinci.
“Kuna da abin da zaku dafa yau ne?”.
“Ehh a kwai Baba shinkafar da akayi mana rabonta a gidan Sarki ai bama muci ta ba”.
“To yayi bari infita sai in tawo da kayan miya”.
“To Allah ya kiyaye”.
Suka bishi da addu’a dukansu.
“Umma wai me yasa Baba baya son maganar gidan Sarki ne !, kuma naga bai damu da barin aikin da nayi ba?”.
“Karki soma tambaya akan wannan al’amari ke dai kiyi ta addu’a sosai kinji?, domin dama da k’yar ya amince kike aiki agidan shiyasa yanzu bai damu ba akan barin aikin”.
Aynu ajiyar zuciya tayi kawai tana mai bin Ummanta da kallo kafin ta mik’e ta fita zuwa tsakar gida domin d’ora musu sanwar abinci.
***
“Komai ya rushe Anwar !, wai ya Abba yake so inyi da rayuwata ne?”.
Yarima Fudhal yakai maganar yana mai goge kwallar data fiddo saman idonsa, Anwar ya dafa kafad’arsa yana fad’in.
“Hak’uri tare da addu’a sune abin da ya kamata kayi Yarima”.
“Nasan da wannan amma zuciyata bazata iya d’aukan hukuncin Abba ba!”.
“Na fahimci damuwarka sosai Yarima, dole zuciyarka ta damu sosai akan rabuwa da wacce take muradi, first love bak’aramin abu bane nasan zafin hakan, amma ka kwantar da hankalinka mu nemi mafita mana?”.
Yarima Fudhal yayi ajiyar zuciyar tare da kora sas-sanyan juice d’in dake gabansa ya lumshe ido tare da kwantar da kai kan kujerar da yake kai, yakai kusan mintuna biyar a haka, kafin ya d’ago kai ya dubi Anwar dake zaune har lokacin yana dubansa.
“Mene mafita Anwar?”.
Anwar yayi shiru nad’an lokaci yana juya cofin glass d’in dake gabansa, kafin yad’an d’aga kafad’arsa sama yana mai fad’awa kan kujera ya zauna ya fara magana.
“Mafita d’ayace zuwa biyu, yarinyar itama ai tana sonka sosai ko?”.
“Fad’ema ai b’ata baki ne”.
“Ok mafita kawai ka nemi yardar iyayenta, bayan komai ya kammala sai ka nemi aurenta ba tare da sanin Mai Martaba ba, sannan kada ka bijirewa dukkan nin umarninsa kayi dukkan abin da yace akan auren da yake son yi maka”.
“Kana nufin in durk’usar da kaina gaban Iyayen Aynu !, daga baya intura iyayen k’arya in aureta kake nufi kome?”.
“Yes ! durk’usawa wada ai ba gajiyawa bane, dole fa wannan karon ka ajiye duk kan wani girman kai da izzar mulki da kake tak’ama da shi ! “.
“Taya hakan zai kasance”.
“Ok ka gane ko?, idan har ka samu soyayyar iyayenta suka amince da kai daga baya zamu san yanda zamuyi su yarda su aura maka ita ba tare da sanin mai Martaba ba, bayan lokaci duk ta hanyar da mai martaba ya dace asanar masa sai mu sanar, nasan lokacin dole yayi hak’uri ya karb’i Aynu natsayin surukarsa”.
Yarima Fudhal yayi shiru yana gyad’a kai, kafin yace.
“Babu wata mafitar sai wannan?”.
“A kwai mana dama nace maka hanya biyu ce ai, idan hakan bai yi maka ba, mai zai hana kasa iyayenta su aminta da kai sosai inyaso sai ka sanar dasu matsalarka ka mayar da Aynu makaranta har zuwa nan da wani lokaci sai ka samu sannu a hankali ka shawo kan mai martaba, ba dai talaka ce ba’aso ka aura ba kan lokacin ka mai dasu masu kud’i mana nasan kana da arzik’in da zaka iya hakan nima zan taimaka maka tunda Mai martaba bai tab’a ganinta ba kaga baka da matsala akai”.
Yarima yamik’awa Anwar hannu suka tafa yana fad’in.
” Woww mutumina !, Kai amma shawaran tayi wallahi amma ta biyum zamu d’auka ita ce zata fi tafiya dai-dai ina ganin daga baya ma kawai incanja musu gari ko?”.
“Ehh mana ai duk hakan na cikin tsarin amma kayi komai cikin iya taku fa…?”.
” K’arar fad’uwar abu sukaji daga dai-dai window tare da ganin giftawar inuwar mutum daga jikin labulan da sauri sukayo waje domin ganin waye?, sai dai basu ga kowa ba kasancewar dare ne duk da hasken fitulun farfajiyar wajen hakan bai sa sunga kowa ba.
“Ashe ba kowa ma yanzu haka k’arar wani abu ne daga wani wajen”.
Yarima Fudhal ya girgiza kai yana fad’in.
“A’a tabbas mutum ne, anyi mana lab’e !, to amma waye?”.
“Kada ka zurfafawa kanka tunani Yarima, yanzu haka gizon wani abu muka gani”.
“Mutum ne Anwar ka yarda kawai !”.
“To shikenan koma waye ma tara wata rana”.
Yarima Fudhal ya koma kan kujera ya zauna, Anwar ya dubeshi yana fad’in.
“Ni zan wuce gida sai gobe ma had’u ko?”.
“Ok “.
Abin da yace dashi kenan sukai musabiha ya tafi.
***
Fulani Sokoto ce kushingid’e ta tayar da kai da kusum sai cika take tana batsewa, Baiwarta mai suna Larai tana durk’ushe gefe tana jiran unarninta.
“Kamar dai yanda aka saba Larai ga kud’innan dubu d’ari ki kaiwa Malam sai kuma dubu goma naki kiyi kud’in mota sauran ki rik’e”.
Larai ta washe baki tana mai d’aukan ledar da kud’in yake tare da fad’in.
“Uwar Magajin gobe Allah ya nuna mana cikar wannan burin namu !”.
“Amin, ki kula da kyaufa Larai ban da shirme kinji ko?”.
“Insha Allah komai zai tafi kamar yanda aka tsara”.
Jalila dake zaune gefe sai wani faman yatsine take tana fizgarwa, ta dubi Larai a wulak’ance.
“Sai ki tashi kije ko?”.
Larai ta mik’e da sauri jiki na b’ari, Jakadiyya dake shirin shiga falon jin maganar da suke ya sanya ta tsayawa tana sauraron maganarsu duk da cewa ba yau ne karo na farko data sabajin haka ba, amma yau hankalinta ya tashi sosai domin ba ta san me suke k’ullawa ba, jin da tayi Larai na shirin fitowa yasa ta sanya kai cikin falon tare da sallama har suna d’an bangazar juna da Larai.
Jakadiyya ta durk’usa tana fad’in.
“Gani ranki ya dad’e”.
Kallom wulak’anci Fulani Sokoto ta watsa mata tare da fad’in.
“Yarima Jaleel yana buk’atar sababbin ‘yan aiki !”.
“Amma ranki ya dad’e wata uku kenan da kawo masa wasu”.
“Yace sun tsufa sabbi yake buk’ata !, ko bazai samu ba ne?”.
Fulani tayi maganar cike da tsawa da b’acin rai, Jakadiyya ta durk’usa tana fad’in.
“Aimin afuwa ranki ya dad’e !, angama gobe insha Allah za’a kawosu”.
Fulani Sokoto ta d’an murmusa kad’an .
“Tashi kije”.
Jakadiyya tamik’e ta fice daga falon.
“Bintu…! Bintu…!!”.
Fulani Bingel tahau kiran wata Baiwarta dake cikin d’aki tana gyarawa, sai gata da sauri ta fad’i agabanta tana fad’in.
“Gani ranki ya dad’e na amsa kiran ki !”.
“Je ki kiramin Uwar Soro “.
“Angama ranki ya dad’e”.
Ta mik’e ta fice.
Mintuna kad’an sai gasu a tare sun shigo, Fulani Sokoto ta dubi Bintu tace.
“Je ki waje zan neme ki”.
Ta mik’e ta fice.
“Bamu waje Jalila”.
Jalila tamik’e tana tura baki gaba ta shige d’akinta .
Falon ya rage daga Fulani Sokoto sai Uwar Soro.
“Ya dai Uwar Soro !, kwana biyu babu labari ne?”.
“Fulani kenan kedai kawai fad’i abin da ki ke buk’atar fad’i”.
Fulani Sokoto tayi wani guntun murmushi kafin ta mik’e zaune daga kwancen da take.
“Ina buk’atar takun k’afar Yarima Fudhal !”.
Tofa wata sabuwa !, ya kuke ganin abubuwan zasu kasance ne?.
Mafitar dasu Yarima suka nemawa kansu zatai aiki kuwa?.
Me Fulani Sokoto kuma za tayi da takun k’afar Yarima Fudhal?”.
Wanne abu Fulani Sokoto take shiri aikatawa haka?”.
Sai naji comment naku masoyana
Team
AYNU-FUDHAL
Team
AYNU-JALEEL
Team
AYNU-YA SAYYADI UMAR
Da wanne kuke ganin Aynu ta dace?”.
Ina jiran amsarku
ASHA KARATU LAFIYA.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.
23
Page d’in naki ne Munayshart tare da ‘yan group naki, Allah yabar so da k’auna, ana tare har bada.
Cikin lokaci k’ank’ani Anwar da Saima sun fara sabawa da juna, duk da cewar a b’angaren Saima wani lokacin idan ta tuna da Yarima takanji kamar ta yaudari kanta ne, idan har ta sake ta karb’i soyayyar Anwar ta mance da Yarima, hakan yasa wani lokacin take kakkauce masa, amma sai dai Anwar ya wuce dukkan tunaninta duk yanda taso ta kauce masa bata iyawa sabida salo da iya taku akan tafiyar da al’amarin soyayya na Anwar, shi kanshi yana tak’ama da hakan, shiyasa Yarima bai bawa kowa wannan aikin ba sai shi domin yasan shine kad’ai zai iya.
YAMMANCIN RANAR ALHAMIS.
Yarima ne tsaye k’ofar gidansu Aynu lokaci-lokaci yana duban k’ofar gidan tare da kallon agogon da ke sanye bisa tsintsiyar hannunsa.
Dai dai lokacin da ya sake d’ago kai ya kai dubansa k’ofar gidan ita kuma tana sanyo kai zata fito, wani sanyin dad’i ya ziyarci zuciyar Yarima har yana ji kamar yaje ya rungumeta sai dai yayi ta maza ya dake har ta k’araso zuwa gareshi fuskarta babu yabo babu fallasa sab’aninshi da yake ta faman doka murmushi har fararen hak’oransa na bayyana waje.
Sallama tayi tare da gaishe da shi, ya amsa cike da fara’a kafin shiru ya biyo baya.
Can dai ya katse shirun da fad’in.
“Kiyi hak’uri kinji?, abisa abin da ya faru !”.
“Babu komai”.
Ta bashi amsa, tana d’an basarwa.
“Kina son ki koma karatu?”.
Da sauri Aynu ta d’ago kai baki a washe tana dubansa tare da fad’in.
“Ina so sosai wallahi !”.
“Ok..! Zanyi magana da Babanki sai musan abinyi kafin zuwa lokacin kammalawarki zan san yanda zanyi inshawo kan Mai Martaba ya amince da auren mu !”.
Sosai Aynu taji farin cikin jin wannan maganar, ta d’an risina tare da fad’in.
“Nagode sosai Allah ya k’ara girma da arzik’i…!”.
Yarima Fudhal ya sanya ya tsansa d’aya kan leb’ansa yana fad’in.
“Shishshshsh…! bana buk’atar jin godiya daga gare ki, komai zan iya indai akan ki ne Aynu sabida ke ce mace ta farko dana fara so !, ina jinki sosai cikin raina…!”.
Aynu dubansa tayi cike da murmushi kan fuskarta, take taji son Yarima da k’aunwrsa na k’ara shiga ranta har dai sanda taji yana fad’in.
“Ki gayawa Abbanki nan da kwana biyu zanzo muyi magana kan batunki da karatun da zaki koma !”.
“Da gaske kake ?”.
Yarima Fudhal kai kawai ya gyad’a mata tare da lumshe idanuwansa, sabida yanda Aynu ta wurk’a idonta kafin tayi masa tambayar ne ya sashi jin wani abu tun daga kwanyar kansa zuwa babban yatsansa, da k’yar ya iya bud’e baki ya bata amsa.
“Na tab’a yi miki wasa ne?”.
“A’a”.
Ta bashi amsa tare da mai da kanta k’asa, sabida wani irin kallo da taga yana binta da shi.
“Zo muje mota zan baki sak’o “.
Ya fad’a yana mai kafeta da idanuwa, Aynu ta d’anyi jim kad’an kafin tace.
“To”.
Yayi gaba yana tafiya ta bishi a baya har zuwa bakin layinsu inda yayi parkin motarsa, ya bud’e gidan baya ya d’auko wata k’atuwar farar leda ya mik’a mata, tsayawa tayi tana dubansa ba tare data karb’a.
“Bana son musu kin sani dai”.
Aynu tasa hannu tak’arba tare da fad’in.
“Nagode sosai”.
Dubanta ya sakeyi tare da zira hannu cikin aljihun wandonsa ya zaro kud’i masu yawa ya mik’a mata, kai ta girgiza alamun a’a tana fad’in.
“Kabarshi iya hankama ya isa nagode sosai….!”.
Katse ta yayi da fad’in.
“Wannan ba daga ni ba ne, daga Abbana ne yace a baki hak’k’in ki ne, na aikin da ki kai”.
Aynu tasa hannu takarb’a tana fad’in.
“Ayimin godiya”.
“Ni zan koma ki kulamin da kanki !, sai nan da jibi zan dawo, karki manta da maganarmu”.
“To insha Allah bazan manta ba, kai ma ka kula da kanka”.
Yarima yayi murmushin jindad’i yana mai bin bayanta da kallo har sai da tab’acewa ganinsa, sannan ya tayar da motar ya bar layin gidan ya nufi gidansu Anwar.
***
“Ranki ya dad’e, sai fa mun dage sosai akan Magaji wajen yi masa addu’a, sabida sharrin mak’iya !”.
“Muna nan munayi Jakadiyya, ke dai kina ji da magaji sosai kullum maganarki bata wuce ta sa”.
Jakadiyya tayi ajiyar zuciya kafin ta ce.
“Ai dole indamu da shi Hajiya, shi d’in ai abin so ne ga kowa”.
Fulani Bingel tayi murmushi na jindad’in maganar da Jakadiyya keyi akan Yarima.
Sallama yayi ya shigo tare da neman waje ya zauna, yana mai gaishe da Fulani, ta amsa cike da fara’a tana dubansa, Jakadiyya ta rissina ta gaishe da shi tare da tamik’e tabar d’akin.
“Yanzu zancenka muke sai kuma gaka ka shigo”.
Yarima ya d’ago kai daga daddanna wayar da ya ke tare da duban Mahaifiyartasa.
“Wai kai kullum babu abin da kake jin dad’ine da ya wuce danna waya?”.
“Hajiya kenan…bazaki gane bane”.
Ya bata amsa cike da murmushi, itama murmushin tayi tana fad’in.
“Taya zan gane ba’ayi min bayani ba?, daga ina kake ne haka?”.
Yarima Fudhal ya dubi Mahaifiyartasa shi dai baya yi mata k’arya kuma baya so ya fara yi mata ayau.
“Naje gidansu Aynu, daga nan naje wajen Anwar”.
Fulani Bingel kafe Yarima Fudhal tayi da ido cike da mamaki, domin yau karo na farko tana ganin tirjiya tare da kaucewa umarnin mahaifinsa.
“Kenan baka bar yarinyar ba?”.
Yarima ajiyar zuciya yayi tare da duban Fulani Bingel yana fad’in.
“Kada kimin gurguwar fahimta, ki tayi da addu’a Hajiya, ni kaina na kasa kaucewa abin da zuciyata take so, na rasa yanda zanyi incire yarinyar a raina ne”.
“Karka damu na fahimci damuwar da ka ke ciki, zan tayaka addu’a sosai insha Allahu kaima ka dage da addu’a kaji?”.
“To Hajiya ina nan inayi dama”.
“Amma Hajiya Aynu taban tausayi sosai wallahi duk sai naga ta rame, kawai na yanke shawaran mai da ita makaranta inyaso ki tayani shawo kan Mai Martaba !”.
A jiyar zuciya Fulani tayi tana fad’in.
“Ka san halin Mahaifinku dai al’amarinsa sai dai addu’a Magaji, amma zanyi k’ok’arin ganin na shawo kan nasa”.
“Yauwa Hajiyata !, haka ya kamata ki fad’a ai tun da farko, Allah yak’ara girma”.
“Amin”.
Ya kwanta bisa cinyarta, d’an bugun bayansa tayi tana fad’in.
“Wai kai yaushe zaka girma ne ?, kai da ake shirin yiwa aure !”.
Fudhal yayi dariya yace.
“Ai a gunki bazan girma ba Hajiya, tunda nine auta !,, kinga ai dole kiji dani”.
Fulani ta tureshi tana fad’in.
“Yau dai ka girma agun nawa”.
Yarima ya zauna yana fad’in.
“Wai ina Aunty Sadiyya ta shige ne?, kwana biyu bata zuwa?”.
“Ina zata zo?, tana fama da jikinta, ta kusa haihuwa fa, kai dai kam Allah ya shiryamin kai baka son zumunci ko kad’an tun da ka dawo babu gidan wacce ka taka bare har ka zaga dangi”.
“Ayya Hajiya karki damu zanje ne insha Allah, kinsan tun da nadawo busy nake ne”.
“To naji amma gobe kaje ka dubota”.
“Allah ya kaimu goben lafiya”.
“Amin”.
***
Ya Sayyadi Umar ya durk’usa ya gaishe da Umma, ta amsa cike da fara’a tana fad’in.
“Munata ganin abubuwan alkhairi mungode sosai, Allah k’ara bud’i”.
“Amin, Babu komai Umma, karku damu, Baba baya nan kenan?”.
“Ehh bai shigo ba tukun”.
“A gaishe dashi ni zan koma”.
“Zaiji insha Allah, Allah kiyaye mungode sosai”.
Ya mik’e ya fita, Aynu ta bi bayansa har zuwa k’ofar gida inda ya tsaya yana jiranta.
Dubanta yayi kafin yace.
“Har yanzu kink’i sakin jiki dani !, ko wani abun ke damun ki?”.
“A’a babu komai”.
Tayi maganar kanta ak’asa.
“Ina ganin kamar ya kamata inturo iyayena ayi magana ko?, domin zance babu tsayay-yiyar magana bata da amfani”.
Dammm gaban Aynu ya buga, tuni yanayinta ya sauya har Ya Sayyai Umar yaso fahimtar hakan.
“Yadai ko bakyaso inturo yanzu?”.
“A’a kawai gani nayi zaifi dacewa ka bari ad’an k’ara kwana biyu”.
Ya Sayyadi Umar yayi shiru nad’an wani lokaci kafin yace.
“Babu damuwa !, Allah ya kaimu lokacin ni zan koma ankusa kiran sallah ki gaida Baba idan ya dawo”.
“Zai ji insha Allah”.
Ta fad’a tana mai juyawa ta koma cikin gidan tabarshi nan tsaye.
BAYAM SALLAR MAGHRIBA…!
Baban Aynu ne zaune bisa tabarma yana cin abinci, Umma na daga gefansa, Aynu na waje d’aya a zaune, sai sak’a take tana warwarewa a cikin ranta, tana son sanarwa iyayen nata maganar Yarima Fudhal amma ta kasa tana jin nauyi sosai.
Har Baban nata ya kammala cin abincin ya wanke hannu tare da alwala yana fad’in.
“Zanje masallaci ankusa shiga sallah”.
“Adawo lafiya”.
Suka had’a baki da Ummanta wajen fad’i.
Sai bayan fitarsa Aynu ta matsa wajen Ummanta tana fad’in.
“Umma dama wata magana nake son fad’a miki”.
“To inajinki Aynu”.
Aynu ta d’anyi shiru kafin tace.
“Umma dama…! dama..!! dama !!!”.
“Dama me?, kiyi magana mana Aynu”.
“Dama Yarima ne yace wai…”.
Sai kuma tayi shiru.
“Yace me Aynu?, fad’i ina jinki”.
“Cewa yayi fa wai jibi zai zo wajen Baba suyi magana, wai za biyamin inkoma makaranta !”.
Umma shiru tayi na zuwa wani lokaci, Aynu kuwa ta zuba mata ido tana jiran taji abin da zata ce.
“To Allah ya kaimu !, zan gayawa Baban naki”.
Umma tayi maganar asanyaye, kamar akwai wani abu ak’asan ranta.
Ita dai Aynu bata ce komai ba illa.
“Amin”.
Data furta kawai, acan k’asan ranta kuwa farin ciki ne fal wanda ba zai fad’uba, tamik’e ta d’auro alawala domim gabatar da sallar isha’i.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.
24
*BAYAN KWANA BIYU*
Yarima Fudhal ne tare da Anwar tsaye jikin k’ofar gidansu Aynu, Anwar sai bin gidan yake da kallo Yarima kuwa kansa na bisa screen d’in wayarsa yana dad-dannawa, fitowar Aynu daga cikin gidan shine ya sanyashi mai da wayar cikin aljihun wandonsa yana binta da kallo.
Ta k’araso inda suke tsaye tare da gaishesu tana fad’in.
“Baba yana ciki !, ku shigo mana?”.
Ta juya zuwa cikin gidan suka take mata baya, da sallama suka sanya kai cikin gidan, yaune karo na farkon shigar Yarima gidansu Aynu.
Ummanta na zaune gefe kan kujera da sandarta agefanta, Babanta shima na waje d’aya kan tabarma, sai wata tabarma ba kowa akai ita ce akayiwa su Yarima nuni da su zauna.
Aynu kuwa tuni ta wuce can k’uryar d’aji ta baza kunnuwa, k’asan zuciyarta kuwa cike ya ke da fargaba data rasa dalilin sa.
Zama sukayi tare da gaishe da iyayen Aynu, Yarima ya sake duban Baban nata karo na biyu a zuciyarsa yana tunanin kamar ya tab’a saninsa, sai dai yana so ya tuna amma ya kasa tunawa.
“Aynu ta gayamin kan cewa zaka zo muyi wata magana !, to yanzu gashi Allah ya kawomu, ina jinku mai ke tafe da ku?”.
Baban Aynu ya katse Yarima daga dogon tunanin daya fad’a, Anwar ya gyara zama yana fad’in.
“Baba munzo ne kan maganar ‘yarka Aynu !, Yarima Fudhal ya ganta yana kuma son ta !, sai dai ya yanke hukuncin zai mai da ita makaranta domin cigabanku da rayuwarta kafin zuwan lokacin da iyaye zasu shiga tsakanin maganar !”.
Baban Aynu ya gyad’a kai cike da gamsuwa da maganar Anwar, kafin ya mai da kansa kan Yarima Fudhal yana binsa da kallo cike da nazarin yanayinsa, Baban Aynu yayi murmushi na wani lokaci kafin yace.
“Yaro ya sunanka?”.
“Anwar, shi kuma Yarima Fudhal d’an Sarki Ubaiyd, nasan zaka sanshi ai?”.
“Kwarai kuwa ni nasan Fudhal !, inajin duk cikar garinnan akwai wanda zai kai ni sanin waye Yarima Fudhal?”.
Anwar ya dubi Baban Aynu cike da mamakin jin maganar da yayi, shima kansa Yarima Fudhal kallonsa yake yayin da gefe guda kuma zuciyarsa sai bugun uku-uku take.
Baban Aynu ya cigaba da fad’in.
“Naji duk kan abin da kuka zo dashi sai dai ina mai baku hak’uri abisa maganar da zanyi yanzu”.
Shiru ya biyo baya na wani lokaci, yayin da Anwar da Yarima suke jiran suji abin da zai ce.
“Na riga nayiwa Aynu miji !, kayi hak’uri nagode sosai abisa taimakon da kukayi niyar yi mana !”.
Zuciyar Yarima tsananta bugu tayi lokaci guda yaji kasala da mutuwar jiki sun ziyarce shi, Anwar ya dubi halin da abokin nasa ya shiga, ya mai da kai kan Baban Aynu ya bud’e baki zai yi magana Baban Aynu ya da katar da shi tare da fad’in.
“Kuyi hak’uri kawai !”.
Aynu dake tsaye cikin d’aki tana sauraronsu ta zube k’asa zaune tana share kwallar dake shirin zuba kan fuskarta.
“Baba muna baka hak’uri muma !, amma naga ai bakayi mata baiko da kowa ba, ka taimaka Baba abokina nasonta sosai wallahi !”.
“Nasan da hakan !, amma kusan wani abu guda d’aya ko da ban yiwa Aynu baiko ba, nariga na gama magana bazan canja ba, ko da ace babu wanda nayiwa alk’awarin aurawa Aynu bazan tab’a yarda Aynu ta auri Fudhal ba !”.
Cike da firgici Yarima Fudhal ya d’ago kai ya dubi Baban nata yana fad’in.
“Me yasa Baba ?, kataimaka kada ka yimin yankan k’auna dan Allah kayarda ka bani Aynu!”.
“Sai yanzu kasan da haka Fudhal !, ni nasan ba zan tab’a yi maka yankan k’aunar da ka yimin ba !, shin zaka iya tuna MALAM ABDALLAH, Tsohon malamin makarantar primary mai ritaya ?”.
Yarima Fudhal fiddo ido yayi waje yana duban Baban Aynu take hawaye ya fara zarya bisa fuskarsa, wani abu yaji na fizgar zuciyarsa ya mik’e da sauri ya dubi Anwar ba tare da ya ce komai ba yayi hanyar waje.
Anwar ya biyo shi da sauri yana kiran sunansa amma bai kulashi ba, har ya shiga mota ya zauna ya jingina da kujerar maotar yana mai kwantar da kansa, idanuwansa ya lumshe take hawaye suka fara zarya kan fuskarsa.
Anwar ya k’araso da gudu ganin halin da Yarima ya shiga yasan yashi tsayawa turus yana dubansa, tare da bud’e murfin motar ya shiga mazaunin driver ya zauna, yana mai dafa kafad’ar Yarima.
Yarima ya bud’e ido a hankalin yana duban Anwar tare da bud’e baki yace.
“Shikenan yanzu ya zama dole inbar Aynu !, Anwar rabuwata da Aynu tamkar rabuwa da rayuwata ne, zuciyata zafi Anwar!”.
Tausayin Yarima ya kama Anwar sai yake ji kaman shima zaiyi kukan da k’yar yayi k’arfin halin fad’in.
“Kai ne kab’ata komai ai, mai makon kabari mushawo kansa mu bashi hak’uri sai kawai ka tashi ka fito !”.
Yarima yayi murmushin da yafi kuka ciwo tare da duban Anwar.
“Bazai tab’a hak’ura ba !, ka sani yana son yayi amfani da wannan damar ne kawai wajen d’aukar fansarsa a kai na!”.
“Kamarya kenan!, ban fahimce kaba ?”.
“Malam Abdallah, tsohon malamin makarantar primary ba kowa bane illa mahaifin Aynu !”.
“To amma wani abu ya tab’a had’aku ne?”.
Yarima ya dubi Anwar natsayin lokaci batare da ya bashi amsar tambayar da yake yi masa ba.
“Muje gida Anwar insha magani zuciyata zafi “.
Anwar bai kuma cewa komai ba ya tada mota suka bar layin gidansu Aynu zuwa gida.
***
“Ka da kace min kana son d’aukan fansar abin da yafaru ne tsayin shekaru?”.
“Ko kusa Umman Aynu, bana da burin fansa cikin rai na !, kawai ina son yin amfani sa wannan damar ne wajen mai da Fudhal cikakken mutum domin shi har yanzu bai san waye shi ba?, sabida shi duk da tarin shekarunsa amma bai cika mutum ba !, har yanzu yana matsayin rabin mutum ne !, ina son in nuna masa muhimmancin mutum da darajar da d’an adam yake da shi a wajen Allah da cikin dukkan halittu !, inaso in nuna masa abin da mahaifinsa ya kamata ace ya nuna masa tsayin shekaru amma ya gaza yin hakan !, ka da ki yiwa maganata gurguwar fahimta domin kinfi kowa sanin mai ya faru?, taya zan yarda Aynu tayi aure a gidan da basu san darajar d’an adam ba?”.
“Kina tunanin sarki Ubaiyd zai yarda Fudhal ya auri ‘yar talaka ne?, shima kanshi Fudhal d’in da abu biyu yazo wajena a yanzu, nasan abin da shi kanshi Fudhal d’in bai san nasani ba, haka kawai Fudhal bazai k’ask’antar da kansa a garemu ba !, da a ce ya zomin a cikakken mutum da fuska d’aya da bazan tab’a ta da abin da ya riga da ya wuce tsayin shekaru ba, sai dai ya zomin da fuska biyu ne ba akan gaskiyarsa ya zomin nan ba !, nariga da nasan wannan tun ba yanzu ba, kawai addu’a ce taki cikin wannan al’amari domin bamusan abin da Allah ya riga ya b’oye ba !, sannan kuma kada ki sa damuwar wannan abin da ya faru aranki dan Allah kinji?”.
Umman Aynu kai kawai ta gyad’a tare da fad’in.
“To, Allah ya shige mana gaba”.
“Amin, ni zan fita, sai zuwa anjima zan dawo”.
“Allah kiyaye a dawo lafiya”.
“Amin”.
Yana fita Aynu dake cikin d’aki ta fito da gudu ta fad’a kan cinyar Ummanta tana mai rushewa da kuka mai cin rai.
Ummanta d’an bubbuga bayanta tayi tana fad’in.
“Kiyi hak’uri Aynu ka da kisa abun aranki kinji?, komai zai wuce da yardar Allah”.
Aynu ta d’ago ja jayen idanuwanta ta dubi Ummanta tana fad’in.
“Amma Umma mai ya sa Baba ya yanke hukuncin tauyemin hak’k’ina?, ina son inyi karatu sosai Umma ki fahimtar da Baba mana!”.
“Aynu ki sani ni bani da abin cewa cikin wannan al’amarin ban da addu’a kaman yanda mahaifinki ya fad’a, yanzu babu abin da zai fahimta kome zan fad’a masa, sai dai ina mamakin canjawar Malam lokaci d’aya haka ban sanshi da rik’o ba !, amma koma dai mene nasan akwai wani babban dalilin da ya sanya mahaifinki yanke wannan tsats-tsauran hukuncin kamar yan da ya fad’a?”.
“Amma Umma wanne abu ne ya faru tsayin shekaru haka da yake shirin zamowa silar wargajewar farin ciki na?, ki sanar dani Umma!”.
“Babu abin da zan fad’a miki Aynu !, amma ki sani kada ki k’ullaci Mahaifinki domin shine yayi silar zuwanki duniya yana da ikon da zai yanke ko wanne irin hukunci akan ki…!”.
“Amma Umma…..!”.
“A’a Aynu kada ki sake furta komai akan wannan maganar kinji, kibi umarnin mahaifinki!”.
Umma takatse Aynu daga maganar da take son yi.
Aynu ta mai da kanta kan cinyar Ummanta tana mai goge kwallar dake zuba bisa fuskarta lokaci-lokaci.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.
25
Cikin lokaci k’ank’ani Aynu ta fita haiyacinta sosai ta rame ba ta da walwala ko kad’an, ita kanta bata san tana son Yarima Fudhal sosai haka ba sai da yayi mata nisa, dan ma Zainab a kullum tana k’ok’arin ganin ta d’ebe mata kewa, Babanta kuwa yanzu bai fiye shiga harkarta ba sosai shiyasa abun ya had’u yayi mata yawa, b’angaren Ummanta kuwa kullum lallashi ne nata tana tausayawa rayuwar ‘yarta sosai to amma bata da abin da zatayi da ya wuce add’a.
To shima Yarima Fudhal a nasa b’an garen haka abin ya ke, shi zama a iyacewa abin nasa ya zarce na Aynu domin cikin kwana biyu da faruwar al’amarin sabida sanya damuwa da yayi da yawa a ransa abin har ya kai shi da kwanciya.
Anwar ne zaune gefan katifar da Yarima Fudhal ke kwance yata lallashinsa akan ya daure ya sha ko da ruwan tea ne amma ya yi banza da shi domin ji yake baya sha’awar komai anan cikin duniyar nan.
Turo k’ofa akayi tare da sallama Fulani Bingel ce ta shigo tare da ma’aikatanta su biyu na biye da ita, daga gefe guda kuma Aunty Sadiya ce da tsohon cikinta sai Aunty Sa’ida kuma da ta keta cika tana batsewa.
Suka zauna kusa da shi Anwar ya gaishe da su ya mik’e ya koma falo domin ya basu waje, Fulani ta dafa goshin Yarima tana fad’in.
“Haba Magaji !, jibi yanda duk ka lalace kaman ba kai ba?, ya kake so ka sanya rayuwarka cikin tsaka mai wuya ne?”.
Yarima ya dubi Mahaifiyartasu hawaye nabin gefen idonsa bai damu daya share ba haka kuma bai iya cewa da ita komai ba, tasa hannu ta goge masa tana mai cigaba da fad’in.
“Kayi k’ok’arin cire wa kanka damuwa da yawa haka kaji?, kada ka jawa kanka wani ciwo na daban”.
Sai lokacin Yarima ya saki wani guntun murmushi ta gefan fuskarsa, amma har lokacin bai furta komai ba kamar yanda hawayen bai bar zuba bisa pillown da yake kai ba.
Aunty Sadiya ta nisa tare da fad’in.
“Hajiya al’amarin Magaji sai addu’a wallahi !, amma ka daure dan Allah karage yawan damuwar da kake sanyawa kanka, addu’a ita ce mafita wata rana sai labari!”.
“Mtsww kema dai Aunty Sadiya !, wallahi dan yaga kawai ana lallab’ashi ne, amma kaman Magaji ace sai angaya masa abin da ya dace da wanda ba dace ba, Doctor ne shi fa yafimu sanin abin da damuwar zataje ta jawo masa!”.
Cewar Aunty Sa’ida kenan, tayi maganar cike da fushi da b’acin rai, Yarima ya jawo hannunsa ahankali yana mai kama hannunta yarik’e gam, fuskarsa har lokacin da murmushi samanta, sai kuma jikinta yayi sanyi k’alau ta janye hannun tamik’e ta fice daga d’akin tana goge kwallar data kawo mata domin ya bata tausayi sosai a wannan lokacin.
“Kayi hak’uri Allah ya baka lafiya, zamu cigaba da tausar Mai Martaba insha Allahu komai zai dai-dai ta kaji?”.
Yarima ya gyad’a kai, Fulani ta d’auki kofin tea d’in ta mik’a masa, ya mik’e ya zauna yana mai karb’an kofin ya fara shan tea d’in a hankali.
“Ni zan koma Magaji ka cigaba da hak’uri kaji?”.
“To nagode sosai”.
Ya furta yana mai kallonta, itama shid’in take kallo kafin ta mik’e da k’yar tana takawa tabar d’akin.
Fulani ta bita da kallo kafin ta dawo da kallonta kan Yarima tana fad’in.
“Allah Sarki Sadiya Allah dai ya sauke ta lafiya, cikin nan yana d’an bata wahala sosai, amma sabida k’arfin hali tun da akace mata kana kwance ta tada hankalinta sai tazo ta ganka”.
Yarima yayi murmushi har cikin ransa yana son Yayar tasa, domin itama tana k’aunarsa sosai gata da sanyin rai da hak’uri, kusan ince baki d’aya ita ta d’auko halin Fulani Bingel.
Ajiye kofin yayi ya koma ya kwanta abinsa, Fulani ta lullub’e shi da bargo tana fad’in.
“Ka kwanta ka huta, zuwa anjima zan dawo kaji?”.
Ya gyad’a mata kai ta fice daga d’akin, afalo ta samu Anwar tana fad’in.
“Sannunka da k’ok’ari Anwar mungode sosai Allah yabar zumunci”.
“Amin Hajiya babu komai”.
Ta juya tabar d’akin, shi kuma ya mik’e ya koma wajen Yarima, ya nemi guri ya zauna, Yarima ya mik’e zaune shima yana duban Anwar ba tare da yace komai ba, amma da dukkan alamu so yake yayi magana.
Da k’yar dai ya bud’e baki yana fad’in.
“Kana ta tambayata kan abin da ya had’ani da mahaifin Aynu ko?, zan sanar dakai yanzu insha Allahu!”.
***
Baban Aynu ne zaune bisa tabarma a tsakar gida, gefe guda kuma Umman Aynun ce zaune suna hira, yayin da Aynu keta shige da fice tana aikace-aikacen data saba duk da cewa bata wal-wala amma hakan bai hanata yin abin da ta saba ba acikin gidan.
Baba ya dubi ‘yar tasa ta ba shi tausayi sosai, kiran sunanta yayi tare da fad’in.
“Zo nan Aynu”.
Aynu tazo ta durk’usa tana fad’in.
“Gani Baba”.
“Kin sa kanki a damuwa sosai Aynu !, kada ki d’auki fushi ki d’ora kan mahaifinki Aynu, ban so ki san wannan labari ba amma yau yazama dole infad’a miki, domin ki yanke hukunci da kanki akan barin soyayyar Yarima ko cigaba da son sa!”.
Baban ya d’anyi shiru na wani lokaci kafin ya cigaba da fadin.
SHEKARU GOMA SHA SHIDA DA SUKA WUCE….!
“Ni na kasance haifaf-fan k’asar senegal ne, na taso cikin dangi da abokai tsayin shekaru nayi karatu na duk a can senegal d’in, sanadiyyar barin k’asata kuwa wata annoba ce ta addabi garin da muke ciki, an rasa rayuka sosai a lokacin ciki har da iyayena da ‘yan uwana, kuma lokacin anrasa maganin wannan annoba data saukar mana, hakan ya saka gwannati ta bada jirgi domin d’ebo raguwar mutanan da suka rage a cikin garin zuwa duk k’asar da muke so, domin tsiarar da rayuwarmu, ni dai alokacin na zab’i Nigeria domin nakanji Mahafina yana yawan bada labari akan k’asar wajen kasuwanci saboda yasha zuwa yana komawa domin kasuwancinsa”.
“Nazo Nigeri bani da kowa haka kuma bansan kowa ba, na sauka a gurin dagacin wata unguwa wanda shine mahaifi ga Ummanki ya rik’e ni da amana da gaskiya har dai dana basu labarina da abin da ya kawo ni k’asar nan, kasancewar nayi karatu shine ya samamin aikin koyarwa a makarantar MAI TASA PRIMARY SCHOOL”.
“Cikin ikon Allah suka d’auke ni, da albashin da nake d’auka nake temaka mana muna ci da kanmu kasancewar na samesu suma bawani hali garesu ba sai dai rufin asirin Allah, shima kamar ni yake bashi da kowa sai Ummanki ita kad’aice ‘yarsu, bayan wani lokaci mai tsayi suka yanke hukuncin aura mun ita, bayan aure da shekara guda sukayi gobara da dare duk suka k’one a cikin dak’i, munyi kuka sosai domin munrasa wanda suke uwa da uba a garemu bayansu ba mu da kowa a duniyar nan”.
“Haka mukayi hak’uri muka dan gana, ki sani Aynu ba ke kad’aice ‘yarmu ba, kafin ki akawai Yayanki mai suna Muhammad Shadad !”.
Aynu ta share kwallar dake idonta tana murmushi farin ciki fal ranta taji ance tana da yaya, cike da d’oki ta fara fad’in.
“Ina da Yaya Baba!, Ina yake to?”.
Baba yayi shiru na wani lokaci cike da tausayaa Aynu kafin ya cigaba da fad’in.
“Bayan rasuwar su Malam ashe Ummanki na da ciki, bayan wasu watanni ta haifi d’a namiji, mun raineshi cikin so da k’auna, har zuwa samuwar cikin ki bayan shekaru uku, Shadad na da shekaru uku a duniya aka haifeki, yaron na sonki sosai kamar yanda muke sonku dukanku, domin ku kad’aine kuka zamto duniyarmu”.
“Har lokacin dai ina aikin koyarwa lokacin na sanya Shadad a makarantar primary d’in, tare muke tafiya da shi idan antaso mu dawo tare, har Yayanki ya kai kimanin shekaru biyar a duniya yayin da kike da shekaru biyu ke kuma”.
WATA RANA
“Rana ce da ta zamto silar rugujewar dukkan wani farin cikinmu !, rana ce da ta zamto sanadiyyar zamowarmu haka ayanzu, ranace da ba zamu tab’a mancewa da wanzuwarta a garemu ba har abada !, a ranar antaso daga makaranta kenan ina janye da hannun Shadad a wannan lokaci domin tsallaka titi, a wanna lokacin wata mota ta kawo kai kan titi mu kuma mun riga da mun kai tsakiyar titin kafin inyi wani yunk’uri motar tayi gaba da mu, na fad’i k’asa tayar motar tabi takan k’afata yayin da Shadad akan idona yayi sama ya fad’o k’asa a wannan lokacin ko shurawa baiyi ba yace ga garenku nan!”.
Aynu ido ta fiddo waje cike da hawaye tana fad’in.
“Ya mutu kenan Umma?”.
Umma ta gyad’a mata kai tana mai share kwallar da ke zuba bisa fuskarta itama.
“Naga dai yaron da ke tuk’a motar amma alokacin bansan waye shi ba?, kuma bansan ko d’an gidan waye ba?, jama’ar gurin ne suka d’aukeni zuwa asibiti, yayin da wasu suka nufi gidana domin sanarwa Umman ki, a lokacin wani mutum ya raka Ummanki gidan yaron da yake tuk’a motar ba kowa bane ashe Fudhal ne lokacin baifi shekara goma sha biyar ba a duniya !”.
“Mutumin da ya yiwa Ummanki rakiya zuwa fada kuwa mahaifin Zainab k’awar ki ne !, da zuwansu sun ba da bayanin dukkan abin da ya faru amma kuma sai me ya biyo baya?”.
“Sarki Ubaiyd ya rufe ido yace shi sam d’anshi bai aikata ba yaushema ya iya mota har da zai tuk’a?, yaje yayi wannan d’anyan aiki wai basu dai gani da kyau ba”.
“Ummman ki tayi kuka alokacin ta rok’eshi ko da ba zai yar da d’ansa bane to ya taimaka sai cewa yayi da dai a ce neman taimakon suka zo kai tsaye zai taimaka, amma tunda sun fara neman d’ansa da sharri babu abin da zai yi musu”.
“Haka suka taso suka tawo, ni kuma ina kwance a asibiti ana jiran a kawo kud’in aiki kimanin dubu d’ari domin amin aiki, sai dai a ina zamu samu wannan kud’in ?, mu da bamu ajiye ba bamu bada ajiya ba?”.
“Sai da na kwana uku a kwance ahaka da k’afa a karye tun tana zub da jini ta daina ta kumbura likitoci sunce ba zasu tab’a ni ba sai anbada kud’i, bayan kwana uku kuma a kace ai k’afar ta rub’e sai dai ayanke, haka Ummanki ta sai da gidan mahafinta dubu ashirin, Baban Zainab ya taimaka da dubu goma da ya sai da ragunansa guda biyu ya bayar ta cika takai kud’i dubu talatin aka yanke min k’afata, wannan shine asalin rasa k’afata guda d’aya, kuma shine dalilin rasa aikina da nayi, domin sunce taya mai k’afa d’aya zai iya aikin koyarwa?, tun da aka koreni ban kuma samun wani aiki da zanyi ba duk inda naje sai ace baza’a d’auki wanda ya nakasa ba!”.
“Bayan wannan abu da ya samemu kuma Ummanki ba ta da aiki kullum sai kuka sabida duk sana’ar data kama sai ta lalace, muka shiga k’angin rayuwa gidansu Zainab ne kawai suke temaka mana da abinci kullum har sai da muka shekara biyu a haka, sabida yawan damuwa da Ummanki ta sanyawa ranta ya haifa mata da hawan jini shine yayi sanadiyar rasa idonta sabida rashin mgani da kuma samun abinci mai kyau, lokacin kina da shekaru uku da rabi, nine na dinga kula da ke a wannna lokaci sabida Umman ki bata da idon da zata iya kula dake har zuwa sanda ki ka kai shekaru hud’u na sanya ki makarantar primary har zuwa sanda ki ka kai shekaru goma a duniya cikin rufin a sirin Allah, a lokacin kuma aka tsananta karatun domin duk team ana buk’atar a biya d’ari takwas mu kuwa bamu da ita bare dalilinta, domin fafutukar abin da zamu cima ta ishemu, wannan shine silar barin karatun ki, ki ka dawo zaman gida sai islamiyya, kulawarki ta koma hannuki kafin ki kai shekaru goma sha biyar kin iya komai har sai aikin gidan da komai ya koma hannunki har zuwa yanzu”.
“Wannan shine ta k’ai taccen abin da ya faru ga rayuwarmu baki d’aya, yanzu hukunci ya rage naki na gaya miki ne domin ki daina ganin laifina cikin wannan al’amari”.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button