NOVELSUncategorized

YAR SADAKA 37&38

???????? *’YAR SADAKA..*????????


*STORY & WRITING BY…*
         *BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO…..*
*MMN AMATULLAH**SPECIAL GIFT TO…*
*SIS NAJA’ART…..*3⃣7⃣&3⃣8⃣


Kasa magana daddy yayi Dan baze iya ba daidai wannan lokacin Dan haka ya shige dakinsa Yana murmushi batare da kowa ya Ganshi ba..

Mummy ce tayi qarfin halin cewa,,Kai mashkur Ka Bani amsa mana,,kayi Shiru kana kallona..

Dakyar ya iya bude baki yace” mummy nafa gayamiki faduwa tayi..

Karya kake wallahi idan zaka Fadi gaskiya Ka fada cewar aunty lateefah..

Kinga lateefah rabu dashi,,ke Dan ubanki zonan,mummy ta fada tana kallan nijlah”

Qin zuwa tayi ta zuba mashkur ido,,shiko ya dalla Mata harara tare da yimata kallan Zan kamaki.

Wai ba magana nake Miki ba kin tsareni da Ido,,shegiya mayya me kikaiwa Dana” kunyace takama mashkur Dan haka ya kauda Kai Yana cewa..

Haba mummy me wannan yarinyar zatayimin..

Ka rufemin baki,, ninasan ba lafiya garekaba mashkur,,yo inba mara lafiya ba yama zaka hada Baki da wannan tafada tana Nuna nijlah..

Fakar idan mummy nijlah tayi ta Dan murguda Mata baki,, sedai aduk abinda take akan idon mashkur,,nan yaqara kulewa tare da daukan alwashin koya mata hankali aduk lokacin data sake suka kebe guri daya..

Wai Baka jina?

Cike da kunya yace,,mummy kema kinsan ba haka bane..

To yayane Ubana,,Naga dai a gabanka ta fada..

Hannu mummy tasa ta janyo nijlah tare da zuba Mata rankwashi” tace wai tambayarki nake ba..

Ki Bani amsa mana kinyi Shiru kema kina kallona” cike da tsoro nijlah tafara magana bakinta na rawa” ummmm ummmm dama..
Mashkur yayi saurin bige Mata Baki ta hanyar hanata magana da Ido tare da qif qif ta Mata su….

Yiwa mutane Shiru ko Kai Dana tambayeka Ka Bani amsa,,da zaka hanata magana..

Ina jinki mummy ta fada tana kallan nijlah,,,Dama me??

Bude baki nijlah tayi tana San yin bayani mashkur yace”

Yiwa mutane Shiru”

Bakin nijlah gaba tace” toba tambayana kayiba,,kuma Naga bakace Karna gayaba idan an tambaya cewa kayi nace banasan Zama a gid…

Be Bari ta qarasa ba ya saki tari me rikitarwa,,shiru nijlah tayi tana cewa” sannu kado,,mummy ko haushi ya isheta ganin Yadda suka sata a gaba suna jamata Rai.

Seda nijlah taga mashkur yayi Shiru ya dena tarin tace to mummy in Gaya???

Eh gayamin..

Dama shine ya..

Mashkur yayi saurin katseta”

Wallahi idan naji kin qara cewa uffan anan sai nayi maganinki..

Kama bakinta nijlah tayi tana bashi hakuri” fita anan kafin Saba Miki shashasha mara wayo kawai..

Da gudu nijlah ta fita waje ta zauna tana karkarwa sabida tsabar firgitatan da yayi..

Tana fita mashkur yayi Shiru tare da miqewa tsaye,,zuciyarsa na bugawa da qarfin gaske sabida tsabar bacin Rai,,nan take gumi ya Shiga karyo masa ta ko ina a jikinsa,, iskar ya furzar cike da Jin kunyar mummy yafara satar kallanta..

Dole Ka riqa kallona da gefen Ido Dan wannan abun kunyar da kayi ba qarami bane” auta kana ko da hankali,,ace duk matan garinann Ka Rasa Wanda zatayi tarayya da ita sai wannan,,wallahi Ka Bani kunya..

Gaba daya ya Rasa inda inda zesa kansa,,ya Rasa meyasa mummy take masa haka,,naga dai matatace koma me nayi ba laifi na aikataba yafada cikin zuciyarsa” Amma take yimasa haka akan nijlah…

Suna cikin haka daddy ya fito sabida Jin an fara Kiran salla,,

Yana fitowa ya gansu sunyi cirko cirko dasu kowannesu dauke da tashin hankali musamman Shi mashkur da kunya ta Gama lullubeshi.

Nauyayyar ajiyar zuciya daddy ya safke Yana kallan mashkur,,yace Kai bakaji ana Kiran sallah ba ka zauna kana luguden lebe..

Daddy kama yasan haryar guduwa mashkur yake nema,,nan yayi saurin daukar wayarsa yasa aljihu tare da bin bayan daddy Yana sunne Kai a qasa…

Turus daddy yayi gannin nijlah kwance a qofa tana rawar sanyi,,duk da ba wani sanyi akeba,, tanayine kawai Dan mashkur ya gani ya kuma tausaya masa,,sabida tinda take dashi bata taba ganin bacin ransa irin na yauwa,,ta tabbata Allah ne kawai ze kwaceta.


Sosa Kai mashkur yayi tare da qararo murmushin karya Yana Mata,,yace ke kuma me kikeyi anan,,tashi ki Shiga ciki,,Nima yanzu Zan dawo sai mu tafi gida ko yaqare maganar Yana kallan kwayar idanta..

Daddy najin abinda ya fada ya wuce ya barshi awurin ta..

Kwafa mashkur yayi Shima ya tafi Yana saurin Jin har an tada sallah..

Har suka idar da sallah suka dawo nijlah tana nan zaune a inda suka Barta,,mummy ko da aunty lateefah haushi da takaici be Bari in tashi daga inda suke ba..

Mashkur na zuwa ya kama hannun Nijlah ta miqar da ita tsaye Yana cewa duba kiga Yadda kika bata jikinki,,kodan bakisan ciwan wanki ba..

Shi dai daddy be kulasu ba ya Shiga ciki Yana murmushi” Dan soyayya yake hango soyayyar nijlah a idan mashkur ya tabbata nan gaba suma zasuji dadin Zama da ita..

Daddy na Shiga mashkur ya kama kunnan nijlah da karfin gaske Yana murdawa”

Wayyo wayyo nijlah tafada tanasan kuka..

Dan yatsansa ya Dora akan lips dinta yana cewa”
Idan kika sake naji kukanki saikin yaba Aya zaqinta kuma wallahi kika qara magana saina yanke wannan bakin da bayajin magana ya qare maganar Yana dungurinta…

Tini ta hadiye kukan tana waiwayen inda Zata ga Samu mai ceton ta..
Kigama juyinki anan Baki da me kwatarki a hannuna,,sai kuma yayi kwafa Yana cewa yarinya Saima da dare zakiyi bayani.
Badai nikika watsama kasa a Ido ba?

Idon nijlah taf da hawaye tace Dan Allah kayi hakuri wallahi bazan qara ba..
Kima qara cewar mashkur..

Mashkur Kai mashkur kana inane,,kafasan sauri nake,,zaka zaunar Dani anan..

Daddy gannin wannan yarinyarce” to kadai vita a hankali..

Tashi mu Shiga ciki saura yanzu ma kimin irin abinda kikayi dazu..

Batayi magana ba ta tashi suka Shiga cikin falon..

Daddyne zaune sai mummy dake kusa dashi aunty lateefah na kitchen taje daukowa mummy cup..

Kusa da daddy mashkur ya zauna nijlah ko ta rabe acan gefe tana hawaye..

Fakar idon kowa mashkur yayi yana yiwa nijlah magana ahankali Yadda bame ji sai ita,,yace..
Ke dukanki nayi ko zaki zaki sani gaba kina kukan banza” to wallahi ki Adana kukanki kafin hawayen su qare lokacin zubarsu beyi ba,,kuma ki matsonan yafada Yana Nuna kusa da mummy..

Ba musu nijlah taja gindi tana matsowa” mummy tayi wani irin zabura tare da matsawa tana cewa,,dakata anan kafin ki gogamin karnin Shanu” kema Baki da maraba dasu..

Kai daddy ya girgiza Yana kallan mummy sedai baze iya yimata fada agaban danta da sirikartaba,,Dan haka ya chanza zancen ta haryar cewa”

Mashkur Dama abinda yasa na Kira Bai wuci magana daya zuwa biyu ba,,Abu na farko inasan sanin inda zaka zauna da wannan yarinya,, zaka kaita gidanka dana Gina ma ko zaka Barta a Wanda kuke ciki ala bashi idan anyi daurin auren Ka da Yasmeen saika kaita can,,ko kuma anan gidan zaka zauna da ita?????

Kallan mummy mashkur yayi Yana San cewa a saban gidansa zasu zauna yaga mummy na yimasa Jan kunne akan hakan tare da nunamasa cewa anan kusa da ita zasu zauna..

Dan haka yayi saurin maida hankali ga daddy tare da cewa”

Daddy inaga a tambaya nijlah,,tinda ita Zata zauna akoma inane idan yaso bayan daurin auren sai na hadesu a guri guda Dan gaskiya Bana San raba Iyalina..

Eh hakan yayi kyau cewar daddy Yana kallan nijlah” 

Nijlah daddy ya Kira sunanta…

Tinda nijlah ta safke Kai qasa bata qara dagowa ba Saida taji an Kira sunanta..

Nijlah kinji tambayana ko??

Bakinta na rawa tace” eh Baba naji..

Kaji yar kauyen banza daddy ma bazata iya kiraba sai wani Baba,, tokin Baba da Baba acan ruga nan birni kikazo cewar mummy cikin daga murya…

Ko kadan ran daddy be baci ba Saima murmushi dayayi nijlah ko bata kalli inda mummy ke zaune ba ..

Ki Bani amsa a ina zaki zauna,,nan gidan ko can inda kuke zaune..

Dam gaban nijlah ya bada,,Dan harga Allah idan so samune zatafisu su zauna a gaban mummy Dan ita gwara Mata fada da zagin mummy akan irin matsar da nononta suka sha tare da tsotse Mata Baki da jagula Mata jikin dayayi,,sedai bata da damar gayar hakan sabida tinawa da Jan kunnan daya Mata..

Jin shirun yayi tawa yasa daddy cewa” kinyi Shiru yarinya muna sauraranki..

Mashkur Kam Banda faduwar gaba babu abinda yake ji, so yake ta dago Kai su hada Ido koya Samu damar Tina Mata gargadinsa ita kuma taqi dagowa Saima qara yin qasa dakai take..

Ahankali nijlah ta bude baki jikinta da bakinta Kai komai ma na jikinta rawa yake tace”

Acan din Zan zauna nijlah ta fada cike da tsoro..

Tsaye mummy ta tashi tana cewa” 
Wallahi Baki isaba,,kujimin shegiyar yarinya,, “yar mitsitsiya dake kin iya gulma da kini Bibi”

To anan zaki zauna kinji na gayamiki,, nijlah na karkarwa tace to..

Kallan daddy mashkur yayi daddy ya shafa kanshi Yana cewa Ka kwanta da hankalinka auta,,can din data zaba anan zaki sauna kaji..

Sabida dadi har besan lokacin da murmushi ya subuce masa ba ,,kasa yayi da Kai Yana cewa,,daddy mun gode Allah yaqara girma..

Tashi kuce daddy yafada abinsa. 

Haukane kawai mummy batayi ba,,taso dukan nijlah sedai bazata iya saka hannunta jikin wannan kazamarba,,tana ji tana gani haka suka fita a falon…

Har mota Mashkur ya kaita Yana murmushi,,bayan ya bude mata kofa ta Shiga a zaga ta inda take yayi kissing bakinta Yana cewa”haka nakeso ki Zama mejin magana kinji amaryata”” yanzu dai ki jirani ina zuwa 2 minutes kawai ya ISA..

Yana tafiya nijlah ta Tabe Baki tana cewa ko menene kuma 2 munat oho masa,,shiyasa yasani tafada tana kwantar da kanta jikin kujeran..

Falon mashkur ya koma ya je daf da mummy ya riqe hannunta,,fizgewa tayi tana hararansa,, murmushi yayi Yana cewa haba sweet mom,,kinfasan banasan bacin ranki,,Dan Allah mummy ki saki ranki,,kiso nijlah kamar Yadda kike Sona..

Ka rufemin Baki auta,,kana da kunya kuwa” rufe Ido yayi Yana cewa mummy anjima Zan dawo kinga diyarki tana Kiran waya,, yafada Yana Nuna Mata wayar data fara ringing a hannunsa..

Tuni number Yasmeen ta bayyana,, murmushi mummy tayi tana cewa idan kaje Ka gaisheta.

To yace ta tashi yana dariya,,abinda  mummy bata sani ba kuwa,,shiya tura Yasmeen text massage yace ta kirashi..

Yana zuwa ya Samu nijlah harta fara bacci bayan ya tada mota ya dauka wayar,,
A kunne ya Kara Yana cewa” hello baby..

Uhmn uhmn wai haryanzu Baka zoba inata jiranka” bayan kasan na Gama hada lefen gani kawai zaka zo kayi,,abinda be makaba sai a chanza..

Murmushi yayi me sauti Yana cewa” nasan baby na ta iya Zabe,,karki wani damu nasan kayan sunyi kyau..
Kuka Yasmeen taka tana masa shagwaba,,nan da nan yaji babu abinda yakeso sai ganinta,,tini ya karya akalar motar ta dawo daga hanyar saban gida suwa gidansu Yasmeen…

To to shikenan ki kwantar da hankalinki ina hanya yanzu haka..

Wani tsalle Yasmeen tayi ta katse Kiran tana fadawa cinyar mama..

Seda Mashkur yayi nisa a hanyas ta zuwa gurin yasmeen ya Tina da nijlah dake kwance bacci me nauyi yafara daukanta,,yazo juyawa Amma baze iya ba Dan haka ya tafi da ita a cikin motan….Comment & share
*Momn sultan ce ✍ ✍✍*

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button