NOVELSUncategorized

YAR SADAKA 39&40

???????? *’YAR SADAKA..*????????


*STORY & WRITING BY…*
         *BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO…..*
*MMN AMATULLAH**SPECIAL GIFT TO…*
*SIS NAJA’ART…..*3⃣9⃣&4⃣0⃣


Tafiya yake Yana Jin  farin ciki da annashuwa na qara ziyartar zuciyarsa” tin Yana tafiya anhankali har yaga tafiya bata sauri” gudu ya saki tare da kunna waqar soyayya dadi,,tini ta hade cikin motar da sauti me dadin gaske..
Tafiya yake Yana jinjiga,,kallo daya zaka masa kagane Yana cikin farin ciki..
A Dan firgice nijlah ta Farka sabida Jin iska me zafi tafara kadawa ga qaran kidan dake tashi..
Hannu daya yasa ya tare da,,dayan Yana tuqi dashi,, fuskanshi dauke da murmushi yafara shafa fuskanta Yana cewa”
Keda wa Naga kintashi a firgice”  langwabewa tayi a jikinsa taqi tankasa” kodai azumin magana kika dauka,,nan ma nijlah batayi magana sema kwantar da kanta jikin kujeran mota tayi tana lumshe ido..
Uhmn” kema kin iya muskilanci ko,,turo Dan qaramin bakinta tayi tana girgiza masa Kai..
To meya tasheki adaidai wannan kuma,,har kina firgita?
Ahankali nijlah tace” Nima bansani ba..
Shikenan kirinqa addau idan zaki kwanta bacci”
Cike da sanyin jiki irin na Wanda ya tashi a bacci tace”
Aiba da dare bane,,kuma indai Zan kwanta da dare inayi,,kakama tana tofamin..
Waya gayamiki a bacci dare kawai Ake addu’a?
Shiru tayi Dan ba Wanda ya gayamata,,Niko nace wasu manyan ma basa addua lokacin baccin rana,yakuma kamata mu gyara,,sabida addu’a tana taimaka mana gurin kariya daga sharrin shaidan,,katangar qarfece ga duk wani musulmi…
Kinyi Shiru?
Nima bansani ba,,to shikenan saiki kiyaye,,kinga dai abinda yafaru yanzu..
To nijlah tace tana qoqarin komawa vaccinta.
Kingama munzo inda nakesan zuwa” ki zauna a mota nizan Shiga nan gidan yafada Yana Nuna get gidansu Yasmeen..

A hankali ta daga Kai tana kallan gidan gabanta na faduwa tace” kado nan kuma inane waiku Dama a birni kowa gidansa haka yake da ciyawa” kaga Dana zo da saniyana Aida ta Samu abinci,,ba ruwanmu da kaita jeje kiwo ko???
Hararanta yayi Yana cewa” zaki fara shirmen naki ko,,waya gayamiki abincin dabobine?
To menene Shi,,gashinan wani ya girma wani kanana a qasa,,sai ruwan banza Ake bashi tinda bashi da amfani..
Inji waye ta tambayeta Yana tsareta da Ido..
Gashinan na gani..
To wannan Bana saniya bane,,ado akeyi dashi anan bakuma nasan yawan surutu kinji nagayamiki..
Hannu tasa ta rufe Baki tana girgiza Kai alamar ta dena..

Daga haka yafara qoqarin Kiran Yasmeen a waya..
Yasmeen na kwance a cinyar mama tana zubamata shagwaba wayanta yafara ringing dasauri ta daga mama ta vita da kallo..
Hello baby gani na iso” oyoyo ta fada tana kallan mama”
Ganin zuwa’
No kibarshi Zan shigo da kaina kedai kawai ki budemin qofar Baya”
Ni dai ah ah,,Allah nizan shigo dakai tafada tana katse Kiran.
Gefensa ya duba yaga Yadda nijlah ta hade qiran Sama Dana qasa tare da turo Baki gaba..
Gabansa yaji yayi mugun faduwa da kyar ya iya magana cikin sanyin murya yace”
Ke kuma me aka Miki zaki bata fuska ko duk baccin ne”
Kama zatayi kuka tace” ba Kai bane.
Zafi Ido Mashkur yayi Yana kallanta,,
Nikuma me nayi Naga kece me laifi Amma zaki doramin kodan kinga bamu qarasa gida na hukuntaki ba,shiyasa zakimin rigima?
Turo Baki nijlah tayi tana Jin bacin Rai tare da kishi me zafi tace..
Kuma shikenan saika kawoni nan kana waya da wata qatuwa.
Mamakine ya cika mashkur cikin zuciyarsa yace na Shiga uku kaddai ace yarinyar nan kishina take” a fili ko cewa yayi  ke wai harkinsan wani Abu kishi?
Koda bansani ba ai bazakayi waya da wata a gabana ba.nijlah ta fada tana murguda Baki.
Rasa Yadda zeyi da ita yayi gashi Yasmeen taqi Yadda ya Shiga ciki,,yasani idan yaqi tsayawa su Shiga tare baza’a Samu hiran arziqiba ta riqa yimasa Mita kenan,,to idan kuma ta fito  taga nijlah fa,,Yaya zanyi ya tambaya kansa..
Sai yanzu yake Dana sanin zuwa da nijlah be Ida zancen zuci ba yaji nijlah Na cewa” 
Kaga Ni Idan bazaka kaini gidaba saika budemin nayi wasa acan tafada tana nuna jikin wasu fulawa..

Tsawa ya daka Mata Yana cewa waini sa’ankine zaki riqa magana Dani Yadda kikeso?
Dasauri nijlah tace nadena..

Bangaren Yasmeen ko da sauri ta koma daki ta qara shafe fuskanta da powder ta yasha mayafi ta fito tana tafiya a hankali..
Me aikinsu ta riqa kwala Kira,,dasauri ta fito tana risinawa tace aunty gani.. kingama hada kayan abincin Dana saki,,eh angama suna can falo anshirya komai..

Yasmeen bata qara magana ba ta koma daki ta feshe jikinta da turaruka masu kamshi,,dakin mama ta dawo tana cewa mama Zan shigo dashi..

ke da Baki shigo dashi tin dazu ba,, murmushi Yasmeen tayi tana boye fuska tace mama ina yimasa kwalliya..
Ke dai  Allah ya shiryeki,,Bako kunya kike Bani amsa Yasmeen,,cikin dariya Yasmeen ta fita tana murnar ganin angon nata…
Turus tayi ganinshi cikin mota hannunsa riqe Dana nijlah suna magana’
Wani irin yawu ta hadiye me dacin gaske tana tambayar kanta..
Wacece kuma wannan me kama da ‘ya’yan larabawa,,to kodai ‘ya’yan yayyensane,,Kai ah ah baby be taba zuwa da wani yaro nan ba,,Kai Bama ze Zama sune ba Dan su Bama a qasar suke zaune ba..
To wacece wannan ta sake tambayar kanta” ganin hannunsu sarqe Dana juna yasata saurin qarawa jikin motar tana cewa kambu lallai  yau akwai bala’i,,tana Gama fadar tafara qoqarin bude motar da dukan qarfinta,,Banda rawa babu abinda jikinta yake,duk Wanda yaganta yasan bata cikin nutsuwarta”sosai zuciyarta ke bugawa da qarfin gaske,ta dauka aniya a ranta komai zai faru sedai ya faru Amma yau ko ita ko wannan yarinyar me suffar aljanu..
Wallahi yau Sena Baka mamaki baby ..

A firgice mashkur ya janye hannunsa daga na nijlah ya qaqalo murmushin dole Yana aika Mata,, bude kofan yayi Yana cewa amarya”

Dole kace amarya mana’kaga baby ni duk ba wannan ba,,wacece wannan da har kake riqe Mata hannun ta fada cikin tashin hankali da zafin zuciya tana nufo inda nijlah take..

Dasauri yasa hannu ya tare ta Yana cewa” haba Yasmeen meyasa zafin kishinki yayi yawa” kifa rage ina gayamiki..

Cikin fishi tace dole zakace Kaka sabida kaci amanata Ka yaudareni da soyayayarka,,Amma duk da haka na amince da aurenka shine zaka nunamin Bani kadai kakesoba..
Kidai nutsu Saina gayamiki ko wacece” 
Ka gayamin yanzu indai baso kake zuciyana ta Gama bugawa yanzu ba..
Matsowa yayi kusa da ita sosai had suna jin numfashin juna da bugun zuciyar kowannesu yace”hannunta ya kama cikin masa ya riqe sosai Yana shafawa duk Dan yasamu ta dawo cikin hayyacinta da nutsuwarta,,Amma duk da haka taqi tsayuwa burinta kawai taji kowacece kafin tasan hukuncin dazata yanke akanta..

Cike da tashin hankali yake magana Yana kallan Yadda nijlah ta rikice ta gigice ta kidime tana kankame jikinta hawaye tuni sun wanke Mata fuska Banda karkarwa babu abinda take tana Kiran sunan Allah”

Yace,,pls Yasmeen ki saurareni,,kinfasan da kaunarki na rayu, kuma haryanzu kina cikin zuciya na babu abinda ya chanzaki” to meyasa kike yiwa babynki haka,, wannan yarinyar kanwatace ki nutsu mana..

Ganin taqi nutsuwa sai zufa take yasashi juyawa inda nijlah take zauna yace”
Nijlah ki gayamata koke ba kanwat…. Be iya qarasawa ba sabida ganin nijlah kwance a qasa Yasmeen ta hau kanta tana Duka..

Bane ni zaka yaudara ko an gayama bansan sunan *’yar sadaka* nijlah ba,,zaka ha’inceni” to wallahi yau koni ko wannan tsinanniyar yarinyar,, Dama akan wannan kake wulaqantani…

Kukama nijlah kasawa tayi Banda Ido babu abinda take rabawa” ta ko ina Yasmeen ke dukanta har Saida numfashin nijlah yafara sarqewa..
Duk Yadda mashkur yayi Dan ganin ya kwaci nijlah ya kasa Dan ba ruqon Wasa Yasmeen tayi Mata ba,,tana dukanta tana surutai..
Rasa inda mashkur zesa ransa yayi Banda tashin hankali da firgice babu abinda yake ji” waiwaye ya riqayi koze Samu Wanda ze ceci nijlah ya Rasa,,sabida layin ba mutane indai ba lokacin sallah yayi kaga suna fitowa ba..
Dabarace ta fadowa mashkur yafara kwalama get man Kira Dan Shi kadai ze iya jinsu adaidai wannan lokacin..

Me gadi na zaune jikin get yasa radio a kunannsa Yana sauraran  wani shiri inda yaji labarin governor ganduje ya tsige sarkin Kano Muhammad sinusi ya Dora hannu aka Yana salati,,hakan ne ya hanashi Jin kiranda mashkur ke masa.

Cikin zafin Rai mashkur yayi Kan Yasmeen da Duka ganin Yadda jini ke fita ta Baki ta hanci a jikin nijlah,,Amma Duk da haka yasmeen Bata dena Dukan taba haka Kuma bakinta beyi Shiru ba..
Wallahi Ko Zaka kasheni Saina fara kashe wannan abun tsiyar Idan yaso Sai kayi abinda zakayi..
Yana hawaye yace” shikenan Ai kin kasheta saiki dagata,,kaicona Ni mashkur Dana kasa riqe amanar Dana dauka Yasmeen baki kyautamin ba,,ki dagata Nace kafin nayi qasa qasa dake yanzu..

Ganin yadda hawaye Ke fita a idanshi yasa Yasmeen Tashi Akan nijlah bakinta Na rawa tace”
Baby kuka kake akan Na Daki wannan yarinyar” me Zan gani Ni Yasmeen Sai kuma ta fashe da kuka ta Shiga cikin gida da gudu tana yarfe hannu,,jikin rigarta da hannunta Duka jini ya Bata..
Tana Shiga me Gadi ya yarda radio yayi Kanta yana tambaya,,kallan waje yayi yaga motan mashkur,,dasauri ya fito Yana tambayan yallabai lafiya..

Chak numfashin mashkur ya tsaya ya Dena aiki,fa  gudu yayi kan nijlah Yana kuka saikace qarami n yaro ya tattarota jikinsa Yana jinjigata tare da Kiran sunanta,,jikin Na kyarma ya saketa Yana salati..

Daidai lokacin get man ya qaraso Yana cewa yallabai lafiya” ganin mace kwance Bata numfashi yasa qarasawa Yana matsa hancinta..
Baba ta Mutu Ko,, shikenan Yasmeen kin gama da rayuwana,, nijlah naso ki girma naga yaranmu dake,,naso kema ki dandana rayuwa ta Jin Dadi Sai gashi kin rigamu gidan gaskiya” Sai kuma ya chakumi wayan rigar baba me Gadi Yana cewa,
Dan Allah ka dubamin ita Bata Mutu ba Ko??
Girgiza kai baba me Gadi yayi Dan yariga ya tabbata da mutuwar nijlah sedai Baze Iya gayaba sabida Shima mashkur yaga Hakan..

Baba me gadine yayi qoqarin Tashi Ze ciccibi nijlah yasata a Mota Domin aje ayi jana’izarta.

Mashkur yayi saurin Shan gabansa Yana cewa karka taba ta,,nizan sata a Mota da hannuna,,Allah yajiqanki Nijlah,,wayyo Ni mashkur wannan wacce irin ranace na riska..

Yana kuka yasata a Mota ya nufi hospital da ita,,nan likitoci suka Hau Kan Dan ceto rayuwarta,,seda sukayi kusan 30 minutes akanta kafin Naga daya Daga cikinsu yajamata mayafi ya rufe fuskanta..
Jikinsu a sanyaye suka fito.

DA gudu mashkur yayi kansu Yana cewa likita Yaya Bata Mutu ba Ko?
Shafa kansa dr yayi Yana cewa kayi hakuri mashkur…


Be Bari yaqaraji ba ya fizge hannunsa ya Shiga Dakin,,direct Kan gadon da nijlah Ke kwance yace ya Bude ta..

Wani ihu ya saki ganin hancinta da kunnata rufe da adduga,, haryanzu jini bai Dena zuba ba..

Salati ta kurma Yana neman daidaita nutsuwarsa,,sedai be samu damar Hakan ba yayi Baya luuuuuuuu……
Idan kuka qara comments irin Na jiya,Bazan qara posting ba Sai Bayan Sallah Idan Allah yasa muna da raban gani..Dan Allah ku riqa sharing danayi posting,,banaso ana damuna Akan Na turo,,abin dayawa Idan Na biyeku Bazan Samu lokacin kaina ba..*Momn sultan ce*✍✍✍✍

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button