Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
Labarai

Yaro mai aikin birkilanci yana kuka ya koma makaranta, bidiyon sa ya dauki hankula

Kamorudeen, karamin yaron nan wanda bidiyon sa yana aikin birkilanci yana kuka, ya karade yanar gizo ya koma makaranta.

5430248

Wannan labarin mai dadin saurare dai wani mai suna Lukman Samsudeen ya sanya shi a manhajar TikTok. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Labarin Kamorudeen ya bazu ne bayan bayyanar bidiyon sa yana kuka yana aikin birkilanci.

Bayyanar bidiyon sa ya sosa zukatan mutane da dama a yanar gizo

Bidiyon ya sosa zukatan mutane sosai inda aka rika tambayoyin ko ina iyayen sa suke da kuma meyasa yake aikin karfi yana dan karamin yaro da shi.

Nan da nan sai ta bayyana cewa mahaifin sa ya rasu sannan yana ganin mahaifiyar sa ne sau daya kawai a shekara a cikin watan Disamba.

Kamorudeen ya samu gagarumin tallafi

Labarin sa ya karade shafukan sada zumunta inda mutane da dama suka bayar da tallafi ga yaron wanda yanzu haka ya koma makaranta.

A cikin sabon bidiyon da Lukman ya sanya a TikTok, yaron yayi kyau sosai cikin kayan makarantar sa da kuma sauran sabbin kayan sanyawa da aka siya masa.

user36783072399emmson ya rubuta:

Allah ya albarkaci duk wanda yake da hannu wurin taimakawa yaron nan ya samu rayuwar mai kyau.

@THE MASK ya rubuta:

Wow na ga wannan yaron yau a wata wallafa.

@Emmanuel Jnr ya rubuta:

Ka kyauta sosai dan’uwa

@user1637599248315 ya rubuta:

Allah abin godiya.

@hannahflorence216 ta rubuta:

Ina matukar taya ka farin ciki.

Kalli bidiyon a nan

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button