Labaran Kannywood

Yau shekara 8 da rasuwar Marigayi Rabilu Musa Ibro,ga cikakken tarihin jarumin

A yau ne marigayi Rabilu Musa (Dan Ibro) ke cika shekara takwas da rasuwa. ????

Da me za ku iya tuna dan wasan, kuma wane fim dinsa ne kuka fi so?

An haifi marigayi Rabilu Musa Ibro a shekarar 1971. Ya yi karatun Firamare dinsa a Danlasan da ke cikin karamar hukumar Warawa. Sannan kuma ya yi Sakandare a Kwalejin horon malamai ta Wudil (Teachers College). Daga nan ne ya shiga aikin gidan Yari (Prison Service) a shekarar 1991. Ya yi shekara takwas Ya na aikin Gandiroba inda ya kai matakin insfekto, daga nan ne ya bari ya cigaba da sana’ar wasan kwaikwayo.

 

Rabilu Musa Ibro ya fara sana’ar Fim a tun ya na aji uku na makarantar sakandare. Ya na da Mata da Yara hudu ko uku akwai : Jamila, Kubra, Auta.

Daga cikin ‘yayansa akwai: Akwai Faisal, Jawahid, Lawiza, Abdul-Mummuni, Sannan akwai Asma’u, Annabe, Sa’adiyya, Akwai wani yaro kuma da ya Haifa ya sa sunan mai gidansa wato Baba Yaro.

Kafin rasuwarsa ya bayyana Bashir Bala Ciroki a matsayin dan wasan Hausan da ya fi burge shi.

Da aka tambayi Rabilu Musa Ibro dan wasan santimental da ya fi burge shi sai yace “ Adamu Usher, ba zan manta ba lokacin rasuwar Kulu da Yautai, tun daga farkon rasuwar mu na tare da su.” In ji Ibro

Daga cikin dubunnan finafinansa Ibro ya bayyana cewa ya fi son wadannan fina finai “Akwai Kauran Mata, Kowa Ya Debo Da Zafi, da kuma Mai Dawa.

Ibro ya bayyana ya fi son tuwon dawa a bangaren abincin sa, fannin sutura kuma sai yace “Na fi son yadi wanda zan shekara da shi ina gurzawa, ba in sa shadda ba kwana biyu in ga tana kodewa.

Da aka tambayi Marigayi Ibro a lokacin ya na raye me ya fi bakanta masa rai a kan harkar sana’arsa sai yace“ Ni abinda yake bata mani rai kawai a wannan sana’a bai wuce rashin hadin kan ‘yan wasa ba.

Rabilu Musa Ibro Ya amsa kiran mahallicinsa ya na da shekaru 43, a duniya. Marigayin ya rasu ne a ranar 10 ga watan Disamba, 2014. Allah ya kyautata makwanci.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button