YAZEED 21 – 25
*YAZEED*
❤❤❤❤❤
© Na
Hapsat Musa
(Hapsy baby)
PERFECT WRITES FORUM
P.W.F
21_25
Jumallah bata kallon Gabanta jitayi tayi Karo da mutum
Wani kyakyawan Mari taji Afuskarta Tass!!!
Dafe Kunci tayi taga waye wannan.
Dasauri Dady yamatso wajen Yazeed cukin Fushi yace
“Yazeed meya haka zaka fallama yarinya Mari”Kamo Hannu Jumallah kawai yayi Suka nufi cikin Gida Jumallah
Kaka dake fitowa daga cikin D’aki Dasauri tace ” Ummaru!!!!
Yace “Na’am Inna”
Tace “Kaine ko idanuwana ke Mani Gizo Ummaru”
Yace “Nine Bawani ba”
D’akin da Baban Jumallah yake tashige
Tabarshi tsaye
Cikin sanyi jiki yabita
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Yazeed kam kakakabe rigar shi yayi inda jumallah tafadomashi sai yatsina yake kamar yataba kashi Ayman da Mimi kuma waje Suka tsaya
Itakam dama Jumallah tuni ta ruga Kiran Malam lawali
Dady yabi Kaka jikin sanyi jiki
Yabita Ganin Mutum yayi kwance Dasauri ya isa wajen
Wadda yagani cikin wannnan Halin ne yafirgita tashi
Amadu!!!!
Dasauri yakaraso wajenshi
Yasunguna Kusadashi
Amadu cikin wani Hali yajuyo wajen yayanshi
Yabude Idanuwanshi Ahankali Ganin wadda ke kusadashi. Yace “Kaine Yaya Ummaru ko Idanuwana Suka Fara yimani Gizo da ganinka”
Tamke Hannunshi yayi yace “Nine Amadu gani gareka Kanena kayafeman ga cikin wannan Halin Amma na wofatar daku kayafeman don Allah”
Kaka tace “Ummaru ji Halin da Kanenka yake ciki Amma kayi watsi damu kan Duniya kaicoka”
Dady Hawaye yaji sunzobamashi
Yace “Kiyafeman Inna don Allah”
“Tashi kashigo Dasu”
Dady mikewa ya fito yayi masu Mimi jagora Yazeed kam kamar yashigo wajen Kashi yayi musu Suka shiga Da’ki
Kaka Kafin su shigo wata tabarma tashimfida masu Duk ta yayage
Mimi da Ayman Suka zauna Amma Yazeed kamar ya Dora jikinshi bisa Wuta
Dady kusada da Kanenshi yakoma Amadu rike Hannushi yayi “yaya Umarru nagode Allah dayahada dakai Kafin nakoma ga Ubangiji na.”
Jumallah ce tashigo rike da kwaryar Rubutu sai Haki take domin Gudu Tasha dasauri tadurkusu gaban Kaka
“Kaka Ga Rubutun”
Dady ne Ya Amsa
“Jumallah Ga Kawunki nan Allah yakawoshi Gareni yau”
Hannu Jumallah Yakama da Kaka yace “Yaya Ummaru ga Amanar Jumallah nabaka ga ta mahaifiyata nan don Allah ka kulaman dasu Yaya
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Kar kamanta Alkwalin da mukayi dakai tunkafin mukai Haka nidakai”
Dady yace “Amadu bazaka Mutu ba Har Wannan Alkawalin damukai sai yacika”
Juyowa yayi “Yazeed Ayman taso kuga Kawunku”
Ayman isa tayi Shima Yazeed yamtsa
Baba yace “Yazeedu ne yagirma Haka Kasan Rabon danaganshi tunda yatafi Kasar Turawa Karatu”
Kaka Kam da jumallah sunyi shiru Ruwan da akawomusu ma sun kasa sha
Baba yajuyo wajen Jumallah yace “Muneera”!! dasauri Kaka da Jumallah Suka Dago Fuska Domin bai taba Kiranta da wannan sunanba yace ” Ga Kawunki nan zai Kula Dake Tamkar ni Kinji Ko Baba
“Baba Kadaina fadin haka zaka tashi”
Yajuyo wajen Kaka yace “Inna kiyafeman Zan Mutu Ina farin ciki Yau nahadu da dan uwana yajuyo. Wajen Yazeed “Dana Allah yayi Maka Albarka”
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Kaka tace “Amadu kadaina Fadin Haka Murmushi yayi kawai yace ” Bani Ruwa nasha Ruwa akabashi yasha
Kama Hannu Dady yayi ya tamke Kamar za’a rabasu yace “Yaya kar kamanta da Alkawalin mu”
Mimi kam da yazeed sai Aymana sunyi shiru Kamar Babu su wajen Bareama Yazeed jiyake Kamar Bisa qaya yake.
“Jumallah tashi kigyara Musu wannan D’aki ” dasauri tamike tafito D’akin Dama Babu kura ciki tabarma ce ta shimfida
Tadawo “kaka nagama Mimi mikewa tayi itada Ayman sai Yazeed Suka tafi Akabar Dady da Kaka cikin D’akin
” Inna kiyafeman nasan nayi Kuskure Don Allah kiyafeman bandamu danazo naga lafiyar Ku ba sai dai nayi Aike Inna kiyafeman “
Fashewa yayi dakuka
“Na yafemaka Ummaru”
“Nagode innata”
Jumallah kuma wuri tasamu tazauna kowaye wannan daga natakashi bangani zai mareni shafa inda Yazeed ya mareta tayi
Gakuma fuskarshi babu Far’raa ko kokadan
Sai yatsina Fuska yake…..
Salatin da Kaka taji tanayi yasa mikewa Zumbur tanufi D’akin da mahaifinta yake dasauri…