NOVELSUncategorized

KWARATA RETURN 2

        *KWARATA RETURN…*
      _{{Kalu bale gareku matan aure}}_
Rubutawa…
            *JAMILA MUSA…*


       *SAI NA AURI D ‘ K**ASMA’U ZAYYAN* {{ Asmeenat Xeyyan }}???? —— 2        Palon ƙasa cike yake da duk wani ma’aikaci dake gidan mace ko namiji gaba ɗayansu hallare suke zaune a ƙasa amma shi mai gidan baya wurin. Duk yadda akayi zaibar ƙasar ne , duk lokacin da akayi irin wannan zaman zaiyi tafiya ne , idan zaije Abuja ko ina ne ba’a haɗuwa sai zai tafi yabar nigeria. Ina ganin haka banma yadda na sauko ba na nufi ɗakinshi.

Da sallama na shiga ya amsa yana gyara ma Papi riga , kusa dashi naje na tsaya ba tare da na sake magana ba , shima baimin magana ba yaci gaba da abinda yakeyi , bayan ya gama yace ma Papi yaje ya jirashi wurin Ashiru yana zuwa , saida ya taɓoni yana murmushi yace kayyalni nayi cau….? Murmushi nayi nima tare da cewa kayi kyau , na ƙarasa maganar ina kallon Dikko dake ta wani haɗe rai , Papi yana fita na ƙara matsawa kusa dashi nace ina kuma zakaje ne ? Rai a riƙe kuma bai kalleni ba yace inda kika aikeni…..

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
     A ɗan tsorace na taɓashi da hannuna na dama ina kallon fuskarshi , da yanayin tsoro nace yanzu kuma meya faru kake fushi ? Ba komai ya faɗa a taƙaice yana matsawa daga kusa dani , ƙara matsawa nayi inda ya matsa jikin madubi yana tattara wasu takaddu , baimin magana ba saida ya ajiye makullin ɗaki a gabana , girgiza kai nayi alamar a , a , to minene ? Cikin rawar murya nace zanji babu daɗi ne idan ka tafi , da gaske ? Ey , kin tabbata ? Na tabbatar da haka , ai bazan daɗe ba ya ƙarasa maganar yana ɗaukar takkadun ya matsa gaban gado ya ajiye sannan ya nufi wurin weldrop , ƙara binshi nayi na fara kuka , har yanzu yaƙi ya kalleni , amma a tausashe yace kinsan ni bana san wannan kuka²n ko ? Yayi maganar yana miƙomin hannunshi. Riƙe hannun nashi nayi shi kuma ya riƙe tare da shigar dani jikinshi. A kasalance yace yi shiru An matana.

      Cikin kuka nace to me yasa zaka tafi ne ? Yi haƙuri ai zan dawo in Allah ya yadda , kwantar da kaina nayi saman ƙirjinshi naci gaba da kuka , bai sake magana ba kuma bai ɗagani daga jikinshi ba , yadai cire hannunshi daga kaina ne tun lokacin daya shigo dani jikinshi. Kenan bai rumgumeta ba , saidai a ranshi yaji babu daɗi tanayin kuka , a zahirance kuwa ya nuna ko oho da yanayin ma idan tai mishi ɗanyen kai zai zaneta ba abinda ya dameshi , Allah ya sani yana san An mata kuma yana tausayinta amma ta rainashi iya raini dan ko gaban waye idan ta tashi mishi rashin kunya sai taje inda take so hankalinta zai kwanta , kuma ita rayuwa ba’ayinta haka wannan dalilin yasa shi yaja mata layi ya kuma tsare gida yanzu yasan tsoronshi ya fara hawa zuciyarta. Gashi yanzun ma taji tsoronshi shi yasa ta firgita dashi take mishi magana a tsorace , naso na tambayeshi abinda yasa zaiyi tafi bai faɗamin ba , kuma ince mishi kenan da banga ma’aikata a palo ba saidai inji labari baya nan , tou ya wani haɗe rai cikin rashin mutunci , sauka nayi daga jikinshi bayan nasha kukana harna gode Allah duk na ɓata mishi rigar jikinshi da hawaye , ina sauka ya cire kayan ya canja wasu.

       Bayan ya gama ya ɗauki abinda zai ɗauka da wayoyinshi danshi bayayin tafiya da kayan sakawa shi kaɗai ɗinshi yake tafiya saidai ɗan abinda ba’a rasa ba , da ya tashi fita yayi bankwana dani kamar yadda ya saba , ya sumbaceni tare da shafa gefen fuskanta , ya riƙe haɓata yana ɗagota dan mu kalli juna , na kalli cikin idonshi yayi murmushi mai tattare da tsantsar so sannan ya ƙara shafa fuskata ya kama kumatuna da yatsu biyu kamar anayi ma yaro wasa yanamin wani irin kallo , ajiyar zuciya nayi tare da sauke idona wani wuri daban na daina kallonshi , wasa yayi da tafin hannunshi a gefen fuskata { kumatuna }sannan ya fita daga ɗakin ba tare da yayi magana ba. Yana fita na fashe da wani irin kuka mai kama zuciya , yana jin kukan Sultana har a ranshi amma ya daskare yai tafiyarshi…….

      Wani irin ihu nayi tare da buga wayata da bango ta watse lokacin da naga kuɗi sun shigo a cikin asusun bankina , kuɗin banza kuɗin wofi ko an faɗa mishi kuɗi nake so ne wai….? Nayi kuka׳ , bana san Dikko yanamin nisa nafi so ya zauna gida muyi ta faɗa…. Duk taron mutanen dake palo suka ɗinguma dan rakiya bayan Dikko ya bulalesu da manyan kuɗi , su Ashiru kaf dasu aka tafi hada Papi.

       Sai azahar nabar ɗakin Dikko bayan nayi sallah kuma banje makarantar ba , a ɗakina na haɗa wayata data fashe na kira Mai gilashi , babu wani ɓayata lokaci ta ɗauka , bayan gaisuwa nace ko kirana bakya iyayi kinga kwana biyu bana zuwa makaranta , ai kyace ita wannan lafiya….? Daga haka nayi shiru danjin amsar da zata bani , wata irin dariya nayi sosai dan wata irin ƙatotuwar batsa data sako , jin ina dariya yasa tace bana san iskanci fa sai anjima , ah jira Mai gilashi zaki zo gidana ? Keni fa na faɗa miki bana iya zuwa gidanki , babu munafurci tsakanin ni da kuma ke , D ‘ K ka haɗa hanya dashi ya maka rashin mutunci ina kuma kazo gidanshi….? Gaskiya ni bana iya zuwa gidan D ‘ K , baya nan fa , kizo dan Allah , kashe waya Mai gilashi tayi tare da ƙurawa wuri ɗaya ido…..

         A bayyane tace gidan D ‘ K , hmmm….

      Kyakkyawan murmushi ta hasko yayin da aka gurfanar da ita a gabanshi , da wannan kallon rainin wayan nashi da yake ma mutane ya kalli Mai gilashi , cike da duniyanci ya ke wani murza bakinshi yana cin cingom cikin salonshi mai ɗaukar hankali , kuma shi bawai dan ya burge wani ko wata ba yakeyi , a , a ra’ayinshi ne yake ci , sai yakeyin abun cikin yanayi mai motsa ma mata hankali , dan ita mace abu ƙalilan yake ɗaukar mata hankali tare da tayar mata dashi , yana da kyakkyawan baki ne , ga gemun daya ajiye kamu ɗaya. Kuma gemun yayi matuƙar martaba mishi kyakkyawar fuskarshi gashin gemun ɗan gazar² kuma gazar ɗin mai ladabi da sheƙi dan ko bai gyarashi ba baya wani duƙunƙune wa ɗin nan yayi kalar ƙazanta ko rashi kyau. Yana da kyakkyawan gashin gemu mai burgewa , sai kuma kyau ya haɗu da gyara , kuma shi gemun nan fa ba dan wata ya ajiye ba. Shima kwalliya yayi ma matarshi An mata dan ya riƙa burgeta tunda yaga gemun yana burgeta dan tana yawanyin wasa dashi idan suna tare. Shi yasa yabar mata dan tayi farin ciki. Ita kuma taunar cingom inshi baiwai taunar hauka yake mishi ba , baya buɗe bakin motsawa yakeyi cikin natsuwa sai salon ya bada wani irin sirrintaccen sirri mai ɗaukar hankalin mace da sa mace taji ya burgeta kuma ta kasa daina kallonshi , kawai dai zataji sha’awar yadda yakeyi , cikin sakata irin tasu ta rigimamin yara yace kece kike san gani na ido² ko ? Ya ƙarasa maganar yana murmushin mugunta , yadda yayi maganar ne yasa ya bata sha’awa dan haka itama mai gilashi tayi murmushi tare da sauke kanta ƙasa tayi shiru.

    Murmushi Dikko ya sakeyi a karo na biyu ya ɗauka robar ruwan dake gefenshi yasha , turo leɓonshi na ƙasa yayi kaɗan tare da riƙe shi da leɓonshi na sama yana mata wani irin ƙazantacen kallo , saida taji cikinta ya juya lokaci guda jikinta ya nuna taji tsoro. Ɗan karkace kanshi yayi shima kaɗan da alamar kowa ya fita , da sauri ta fara juye² tabi mutane da kallo har suka gama fita , ya akayi ne…? Ya tambayi Mai gilashi , cikin rawar murya tace yi haƙuri ranka ya daɗe ,  a , a , kuka ta farayi tana ci gaba da cewa kayi haƙuri dan girman Allah , gyara zamanshi yayi cike da mugunta yana cewa har kin gama gani na ne ? Ya ƙarasa maganar yana mata kallon ɗage , shiru tayi shi kuma yace tou kin fasa ɗaukar hoton dani ne…? Tuba nake ranka ya daɗe , zo nan ? Yayi maganar yana nunawa da hannunshi ta matso gabanshi , matsawa Sa’adatu tayi tana ci gaba da kuka , tashshi { yaji } ya ɗauko cikin wata “yar ƙaramar roba ya watsa mata a ido…. 

     A firgice Mai gilashi ta goge zubar data tsatstsafo mata a fuska ta goge idonta dake ɗigar da zufar hawayen azaba dan tuno azabar da Dikko ya gana mata kamar yanzu ne yake zuba mata yajin , wanda ba kowa ne yaja mata ba sai Sharifa , kuma itace wacce Dikko yayi ma liƙi , kuma Sharifa karuwa ce ta gaban mota amma musulmin karuwanci takeyi , murmushi ɓacin rai Mai gilashi tayi tare da ɗaukar wayarta ta fara kiran Sultana….

Ina kallon kiranta yana shigowa yana fita nima nayi fushi. Murmushi Mai gilashi tayi tare da turama Sultana text , Allah ya huci zuciyarki uwar gidan D ‘ K kuma Amarya , daga kanki idan dai kuɗin da D ‘ K zai biya da sunan sadaki ne dan ya auri wata mace , tou ina miki albishir daya ƙare. Kina ciki muna waje , a gida kika san Dikko a waje mune zamu baki labarin ko waye D ‘ K , kizo makaranta idan Allah ya kaimu gobe akwai labari.

     Maƙiyi zai iya mutuwa amma har abadan duniya gaba baza’a daina ba , kamar yadda na faɗa muku karuwanci shine abinda mai gilashi ta zaɓa , to shine cinikinta kuma karuwanci shine sana’arta , Sharifa ƙawar mai gilashi ce ta hannun dama kuma ƙawancen an haɗashi a bariki ne. Sharifa tana alfahari da Dikko da kuma gwamna , ko taɓota mutum yayi sai ta fara burga a waya Yaya D ‘ K kaza² alhalin kuma ko number wayar Dikko bata dashi a (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); wancan lokacin. Gwamna Yayan Mom inta ne , munyi waya da Yaya D ‘ K yana saudiyya ko yanzu yabar Madina ya tafi Makka , yaje London ko yana America kullum shine ƙaryar Sharifa idan aka zauna a mutane. Kiran sunan Dikko da takeyi yasa ake santa dan su a ganinsu zata jasu suje wurin Dikko yayi danbe dasu ya basu manyan kuɗaɗe , dan da harkar mata Dikko ya nufa da tunin duniya ya lalace dan zina ƙarshen rashin kunya ce. Kuma ba ƙaramin ɓarar da mutunci daraja da kuma martaɓar ɗan adam take ba , sun ɗauka Dikkon ɗan tsakiyar fili ne ashe ɗan bayan fage ne basu sani ba , suna mishi kallo go ashe back ne basu sani ba , yadda suka fassarashi kuma suka kalleshi haka yake amma iskanci shi da duniyanci da duk wata tasharshi shidai An matarshi kawai yake mawa , kafin ita Sa’adatu tasan Dikko sunanshi ta faraji da rashin kunyarshi.

    Sharifa tayi alƙawari wa su Sa’adatu idan Dikko ya dawo nigeria zasuje wurinshi , ita kuma Sharifa ganin Sa’adatu tana san ƙureta yasa ta fara neman faɗa da ita , amma Sa’adatu ta liƙe taƙi zuciya tana dai manne bayan kuma ita Sa’adatun tayi bincike ance mata Dikko yana nan baije ko ina ba , ana haka ne akayi rasuwa can ahalin Maman su Dady , ƙanwar Kakar Dikko ta wurin uwa data aifi Dady , dake ba’a abu dan Allah ƙwai da kwarkwata ƙannen Dady da “ya “yansu suka je ranar addu’ar 3 , anje kara wa Dady , shi kuma Dikko dama baya shiga hurumin kowa tunda ko family meeting da sukeyi shi baya zuwa ba abinda ya dameshi da sabgar kowa daga doki sai mota sai kuma bugun zuciyarshi An mata da tazo daga baya ta hana ma zuciyarshi hutawa da soyayyar ta , a wurin ta’aziyar ne Sharifa ta ratso dubun mutane ta isa wurin Dikko tace mishi dan Allah ya tsaya suyi solfie , idan sunce shi ɗan uwansu ne sai ace ƙarya sukeyi , yadda tayi sakin layin ne sai abun yasashi yayi murmushi Sharifa ta ɗauki solfie kenan yana cikin yanayin farin ciki , wannan hoto fa shine ta maƙale mishi take ta yaɗawa a kafafen sadarwa na yanar gizo. Face buk , Instagram , whatsapp d p inta shine kullum , wannan hoto shine status inta ba dare ba rana , da ƙawaye suka fara mata gori mai hoto ɗaya , sai ta shiga familynsu ta samo hotunan Dikko irin wanda “yan uwanshi ke sassakawa masu numbobinsu suke samu , nan fa tazo taci gaba da kafawa , kuma itace tasa Mom inta ta sama mata number Dikko a wurin Aunty Bilki abiyar zaman Momy kenan , Maman Sharifa kuwa ta faɗa ma Aunty Bilki tana san Sharifa ta auri Dikko bata ɓoye mata komai ba saboda su biyun nan aminan juna ne kuma aminci ake na ƙuryar ɗaki. Gashi kuma Momy bata shiri dasu saboda ta rainasu rainin har na wuce misali , dake taga kishiyarta zata shiga damuwa yasa ta miƙe itama sai anyi auren nan dan Momy ta ƙuntata tunda tasan bata sansu , tana so ayi auren kodan Momy ta gune , da kuma buƙatar ta na daban tunda ba Al ‘ Ameen , tana so Sharifa ta shigo. Ta nan ne ma kaɗai zata rufe littafin rayuwar Dikko , tayi waje da Momy ta fasa gidan dan Dikko shine ƙaryar Momy da ma duk wanda uwarshi bata gdan.

    Itace ta miƙe da gaske tasa Dady yasa Dikko ya auri Sharifa dan tasan Dikko baya tsallake maganarshi , su kuma maza basa gane makircin mata da irin “yar nehun nan , sai akayi ma Dady nehu haɗe da bariki shi kuma ya fahimci hakan abune mai kyau da kuma ƙara martabar zumincin su ,  shine fa Dady ya tura Dikko yaje wasan ya kuma ƙara da cewa ya riƙa zuwa zance akan lokaci dan su samu fahimtar juna , banda fushi ɗaure fuska kar yayi duka ya zama mai haƙuri da sakin rai idan yaje , Momy kuwa tace masa bata so , amma sai yace ta kwantar da hankali shi bazai riƙa zuwa zance ba , tace ita ba ma zancen ba auren nan ne gaba ɗaya bata sanshi kuma baya yinshi , dan jakanci fa shine ita kuma Sharifar take zuwa wurin Dikko , ko zai kai ƙarfe nawa bai tafi gida ba zata zauna dashi tana mishi fira , da lafazin su dai irin na “yan bariki har akayi mata liƙi , wanda kuma duk karatun Aunty Bilki ne dan itama sai jawo Dikko jikinta take danma shi Allah yasa mishi wani irin hali haka na kamar dai yanajin tsoron mutune , kuma baida sakin jiki dasu , kana iya zama dashi yau kuyi fira yafa sanka amma idan ya ganka gobe ya nuna shi baima taɓa saninka ba kwata² a rayuwa , kai ta mishi bayanin ka yace shifa bai wani gane ka ba , kuma zaiyi wahala ka bashi abu yaci ko yasha ko kuma ya saki baki kamar sakarai yaita maka surutu ko yawan murmushi , wallahi Allah akan Sultana kawai Dikko ya faracin abunda ya fito daga hannun mace a waje kuma daga kanta ya daina , shi kanshi ya natsu yayi nazari tunda yake bai taɓa ganin macen data bashi wahala kamar An mata ba , kuma shima babu macen da tasha wahalarshi a duniya sai An mata , yana santa soyayyar da tunda yake bai taɓa ma kowa irinta ba sai ita , akan An mata ya fara mafarkin mace , kuma itace farkon macen daya bi ya wuce , itace mace ta farko data mareshi ta zageshi taja mishi gemu yayi murmushi bayan ta gama , itace macen data kashe mishi dokin daya fi ƙauna wanda har yanzu idan ya tunoshi sai yaji babu daɗi saboda san da yake ma dokin , itace macen data maida rungumarshi ba,a bakin komai ba , yana san Sultana fiye da yadda tunanin mai tunani baya iya hasasowa amma bata kunya ko kaɗan haka kuma ta rainashi sai babban iskancin data koya yanzu na raba shinfiɗa dashi , ya ƙyaleta ya kuma zuba mata ido bawai dan baya san su kasance taren ba a , a saboda cikin da take dashi ya ƙyaleta dan idan ya riƙeta da fushi tou fa lallai za’ayi ɓarna. Yana addu’a ta sauka lafiya zataci ƙaniyarta idan ya riƙeta a ɗaki…..

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
    Sa’adatu kuwa wani abokin barikinta ne ya haɗata da Yazeed , Yazeed shine ya kaita wurin Dikko bayan ya biye allonta shima { danbe }, daya faɗa mata ranar da zusu wurin Dikko shine take faɗa zatayi hoto da Dikko idan suka haɗu. Kuma tayi mishi shirin hana bacci , yau duk wasu musu ƙaryar suna tare da Dikko suma zasu je wurinshi kuma zatayo hoto dashi , Sharifa ce ta bawa Dikko labarin zuwan Sa’adatu wai akwai wata karuwa tana faɗa a gari zata zo tayi mishi fyaɗe , abun ya bashi dariya amma baiyi ba a gaban Sharifa saida ta tafi , yaso yaba Sultana labari amma daya koma gidan tai² mishi ɗanyar ƙwalwa , shi yana so ko abu ya faru dashi , ko ya gani , ko yaji yana so ya riƙa faɗa mata suyi farin ciki tare amma ita kwalwarta tana kallon ƙasa , ita kuwa mai gilashi tayi alƙawarin miƙewa tsaye da ƙarfinta da barikinta da tasharta sai ta rama abinda Sharifa tayi mata dan raba tarayyarta da Dikko kamar yadda ita Sharifa ta zuge wani mai san ita Sa’adatu ya fasa aurenta tou itama ta lashi bala’en hana aurenta da Dikko ko da kuwa hakan zai zamar mata silar barinta duniya , wannan kenan.

     Kamar wasu mayu haka suke ta yayam² suna cin shawarmar da Yazeed yasa aka basu , Jiddah ma data zo yanzu an bata nata kasafin itama ɗayar mayyar ta lashe. Bayan ta gama ci ne tace ma Yazeed wurinshi tazo fa , babu wani damuwa yace ina saurarenki yayi maganar yana bata umarni da hannunshi tayi magana , kasan dai komai yana buƙatar sirri ba , cikin matan ne wata tayi katsalandi cewa ba buƙatar sirri a wurin nan malama faɗi abinda ya kawoki basai kun wani tashi ba , ke bake a maganar nan dan haka tsamewa mutane baki , Jiddah ta faɗa. Idan naƙi kuma ? Sai jikinki yayi tsami , umarni karuwar ta bayar cewa jikin Jiddah ya tsamama yanzun nan. Dakatar dasu Yazeed yayi ta hanyar miƙewa yacewa Jiddah suje , a motar Jiddah sukayi masauki dukansu.

       A hankali ya turo ƙofar ɗakin kamar ɓaron tsakar dare a barikin sojoji , ƙiyyyyy ƙofar tayi ƙarar buɗeta a yayin daya fara tura ƙofar dan shiga cikin ɗakin. A tunanin shi tayi bacci amma da mamakinshi sai ya ganta zaune gefen katifa tana ta shafa wayarta mai tambarin apple a bayanta. Cike da ladabi ya takure daga bayan ƙyaure ya durƙusa cikin biyayya sannan ya matsa gaba kaɗan ya ajiye mata ledar daya shigo da ita da kuɗi cewa ranki ya daɗe gashi. Hankalinta yana saman wayarta tace masa nawa ne ? Cikin rawar jiki yace dubu biyar ne… ! Bakaji me nace maka ba ? Kiyi haƙuri dan girman Allah wallahi har rance na nema a daren nan ban samu ba , shiru tayi ta manta ma da yana cikin ɗakin taci gaba da sabgar gabanta a waya……

         Yazeed barka da dare , barka dai matar mai gida , kanta taji yayi mata wani irin gingime cikin izza da nuna ita wata shegiya ce tace , am Ya Yazeed meya haɗaka da Ya D ‘ K , shiru yayi na wani lokaci sannan hawaye ya gangaro mishi daga idonshi yace , hmmm dare ake bi a samu suna , inko ba’sha dare ba asha rana , idan kikayi duba mutum biyun nan basa sabgoginsu da rana ko safiya , daren nan dai shine suke bi su nema kuma sun biɗa sun samu , kiyi tunani duk ɓarowa sai dare yayi yake fita dan haura katangu , masu nema wurin ubangiji idan dare yayi su lokacin garinsu ya waye , zasu kasance ne a saman abinda sallah suna Allah ka yafe mana ka bamu׳ , shin ko kinsan dalilin yasa D ‘ K yake huɗɗonshi cikin dare ne…..?

       Kai kunnamin hasken can kaji , jikinshi yana ƙyarma ya tashi duk ya haɗa uwar zufa kamar manomin da ruwan damina ya ɗauke a lokacin da gero ya fara bininiy , duhu yabi ya lalubo makunnin fitila dan tunin duniya ta ajiye wayarta haka ne yaba duhu damar gauraye kaf ilahirin girman ɗakin , a kiɗime ya kalli Sa’adatu bayan haske yazo , cike da tasha tasu irin ta “yan tasha ta buɗe jikinta gaba ɗaya , idonta na dama ta kashe mishi cikin salon jan hankali , ha… Ya sauke ajiyar zuciya. Wasu wurare ta nuna masa a jikinta tare da bashi damar zuwa kusa da ita , tafiya yayi kusa da ita ya durƙusa ƙasa ƙiƙi² ya hunce ita kuma ta bashi damar tattaɓa jikinta itama tana tayashi da shashshafa mishi wasu mahimman wurare a jikinshi dan tabbatar mishi da martar cewa shima namiji ne. Kaɗan ta ɗan lulashi saman network saida ya tafi ya kusa cinma nasara tace dubu biyar ya ƙare , dan haka ta saukeshi daga saman katifarta ta mayar da kayanta sai ya kawo cikon dubu biyar zai shiga gabatar da wasan danbe…… Wani irin gurnani yayi tare sake nufa inda Sa’adatu take yana wani irin huci kamar an jiƙa mahaukaci a lokacin sanyi , dakatar dashi tayi ta hanyar cewa idan ka haumin katifa saina yaga mutuncin ka , ni nafika ƙaryar rashin kunya iskanci tasha da kuma lalacewa , tattara gashin kanta tayi cewa bani kazar inci…… Ta ƙarasa maganar tana ɗaga mishi gira. Kamar wani gele haka ya miƙo mata , yagar kazar ta farayi saida ta cika bakinta da ita sannan tace tou yi sauri kaje ka samo cikon kuɗin ka kawo ni kuma na ɗoraka a saman lambar girma tayi maganar tana murmushi tare dakai hannunta ta nuna mishi tsakiyar filin wasan danbe…… Bashi da yadda zaiyi dole ya maida kayanshi ya fita daga ɗakin dan yasan tashar Ade mai gilashi ta girmin tunaninshi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
      Gyara zama Jiddah tayi ta kalli Yazeed sosai sannan ta tambayeshi kamar yadda ya tambayeta itama tace me kuwa yasa yake huɗɗonshi cikin dare……. ? Yazeed yace shine abinda nake so na sani tun farko kenan dan duk yadda akayi nasarar rayuwarshi a cikin dare take , kinga D ‘ K baya waya da rana saida daddare idan kika cire wasu ƙalilin mutane wanda su wayarsu ma daban ya fitar musu , uwa uba matarshi sai Ashiru danni tunda Ashiru ya wulaƙanta ni ya korani daga company ya kawo Abbakar bana samun layin da nake kiranshi dashi da rana ko safe duk dai lokacin dana so nayi magana dashi. Jiddah tace nima yanzu ko na kira saima acemin number ma babu ita a duniya saida na sameshi a layin da kowa yake samunshi , idan kuma na saka number a wani waya shima dai baya tafiya wai meya ɗauki mutane ne…. ? Jiddah tace koma meya ɗaukemu zamuji mu kuma gani idan na koma gidanshi.

       Wani irin kallon raini Yazeed yayi mata mai nuni da tama samu warwarewar tunani , ita kuma tana ci gaba da cewa manta da wannan damuwar kaji abinda ya kawoni wurinka , inajin ki ya faɗa bai sake kallonta ba , hoton Sharifa ta nuna mishi tana ce masa kasanta ne ? Kallon hoton yayi sosai sannan ya miƙawa Jiddah yace ya akayi ne ? Yaya D ‘ K yayi mata liƙi kuma aurenta zaiyi , kai tsaye Yazeed yace wallahi D ‘ K bazai aureta ba , ke kina wasa da Dikko ko ? Tou D ‘ K mashaune shi ɓadda musulmi , shi kanshi tsoron kanshi yakeyi kuma bai yadda da kanshi ba , ita wannan yarinya da kike magana yanzu haka tana wurinshi Abuja taje mishi rakiya zaiyi tafiya. Jiddah tace zai aureta , Yazeed yace bazai aureta ba , haka sukayi ta maimaitawa kusan sau goma , shi Yazeed yace Dikko bazai auri Sharifa ba , Jiddah tace zai aureta , daga ƙarshe dai suka rabu a haka kowa yana cewa zaka gani , shima yace mata zaki gani…..

       A wahalce ta ajiye kwalbar cikin maye tace wallahi saina auri D ‘ K , wata irin dariya Amisty tayi tare da cewa Dikkon ne zai auri “yar shaye² ? Cikin maye tayi magana cewa tsaya kisha kallo…… Dariya Amisty ta sakeyi tare da cewa me kuwa zan kalla saidai inga yadda zakici ubaki , murya a lalace da maye Hafsa ta nuna Amisty da ɗan yatsa tana rufe ido da yanayin buguwa murmushi ɗauke a fuskarta tace kema kina layin “yan hassada ko……? Tayi dariya. Tou dama malam ya faɗamin “yan hassada zasu fito ɗaya bayan ɗaya ngode ma Malam daya nunamin ke Kaka , ashe haka kike hassadata ban sani ba ? Gaki nan Malam ya zaƙulomin , buɗe tafin hannunta tayi tare da nuna ma Amisty tace me kika gani ne ? Wata irin ƙatuwar ƙuna ce a tafin hannunta , bayan ta tabbatar Amisty ta kalla ta naɗe hannun da tsumma kamar yadda yake farko cewa malam yace wannan ƙunar sai a gidan D ‘ K zai warke , ta ƙarasa maganar tana dariya irin ta mashaya……

        Da massara ya isa Abuja shi yasa tunda ya shiga ciki bai fito ba yana kwance a gado jikinshi har ƙyarma yakeyi , saida yayi sallah isha’e yasha magani ya koma bargo. Ba tare daya juya bayanshi ba yace Papi tashi ka kawomin wayata ana kirana , sauka yayi ya ɗauko wayar ya kawo mishi , samin a kunne na yayi maganar yana kallon Papi , yadda yaga anayi idan za’a ɗauki wayar yayi tare da ɗorawa a saman kunnen Dikko shi kuma ya fara magana , bayan gaisuwa yace (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); wallahi banajin daɗi ne Momy , magana tayi sannan yace a , a , shiru ya sakeyi bayan wani lokaci yace gaskiya ban sani ba. Ey Papi Momy zatayi magana dakai , cire wayar yayi daga wurin Dikko ya kara a kunenshi yana magana da tsantsamar muryarshi , kusa da Dikko ya ajiye wayar bayan ya gama ya koma ya kwanta gabanshi , yana mishi sannu , cikin yanayin damuwa yace Papi kaga Momy bata kirani ba ko ? Ta kiyaka Yaya , a , a Momyn goruba , ɗaukar wayar yayi yana cewa bari a kirawota Yaya , 

Tsareshi da ido Dikko yayi , saida ya yagaji da shirmenshi ya ajiye wayar ya fara bacci tunda bai iya kira ba , saida ya tabbatar Papi yayi bacci yayi mishi addu’a tare da gyara mishi kwanciyarshi shi kuma ya fara kiran Sultana , amma tsabar iskanci taƙi ta ɗauki wayar , ya kira harya gaji ya haƙura wanda bai ɗauki waya ba taya zaiyi lokacin duba wani saƙon banza can….

     Tunani daban² a ranshi na sabon iskancin da An mata ta koyo , amma yayi alƙawari bazai sake kiranta ba taje can ta ƙari rashin wayanta. Yau sai 12:23am ya cire wayarshi daga jirgi , yana buɗewa kiran Yusra yana shigowa da bazai ɗauka ba amma sai yaji tausayinta har wane tsawon lokaci ta ɗauka tana ta kiranshi sai yanzu ta samu kuma bata gaji ta daina kiranshi ba haka batayi bacci ba. Yasan dan dai kawai tayi mishi sannu da hanya ne wacce ma baa matarshi ba ta damu dashi da san sanin halin da yake ciki , shidai bai faɗa mata ba amma yasan kila taje g r a ance mata yayi tafiya ne , ɗauka yayi tare da kara wayar a kunnenshi yayi sallama.

Ajiyar zuciya Yusra ta sauke cikin kissa sannan ta amsa sallammar da mairainiyar murya , ya gda ? Ya tambayeta , bata ansashi ba taci gaba da watso kalamai na matan waje cikin rashin kunya tana kambamashi da zugashi tare da turashi wata madakatar da bai isa zuwa ba , murmushi yayi kaɗan kuma mara sauti ya kalli Papi dake bacci ya riƙe mishi wuya da hannu ɗaya , shiru yayi yaƙi magana ita kuma taci gaba tunda ai tasan yana jinta , duk kiran dake shigowa bai ɗauka ba kuma bai tsinke kiran Yusra ba haka kuma baiyi magana ba yana dai kallon Papi , itace ta gaji ta sauka a layi.

      Kiran Hafsa shima ya ansa saidai ita bata doguwar tafiya dan bata da irin kalaman da yake so , duk da yanajin haushin Jiddah yana ɗaukar kiranta , itama Mardiyya tayi nata kuma duk sun hura mishi kanshi yanajin yakai wani baban shege , Sharifa kuwa ai suna tare amma ba’a ɗaki ɗaya ba. Yau ko namiji ɗaya baiyi magana dashi a waya ba saidai a cht , tunda ya buɗa wani saƙo ya haɗe leɓunanshi tare da riƙe na ƙasan ta ciki da haƙori ya kura ma hoton wata kyakkyawar yarinya ido , ɗayar wayarshi ya ɗauka ya kawo hoton Sultana a bayyane yace akwai tazara har yanzu….. Ajiye waccan wayar yayi yaci gaba da kallon hotunan Sultana yana murmushi wani kuma yayi dariya yace An mata rigima Allah ya saukeki lafiya jarumata…….

    A dajin data gama tsibbunta a wurin ta kira Dikko tayi magana dashi kamar yadda mushiriki ya faɗa cewa idan ta gama ta kirashi kuma zai ɗauka idan harya ɗauka a lokacin ruwa da iska baya hana Dikko ya aureta sai sunyi aure ,

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
       Ɗan madaidaicin gidane a nan cikin anguwar kwaɗo duk yara²n mata ne suka taru suna ta gulmar mazajensu………. Har 12:39am gidan cike yake wai ana fira , wasu mazajen su matafiya ne basa nan , wasu kuma suna da abokan zama mazansu suna gidan abokiyar zamansu , ita kuma mamallakiyar gidan mijinta yana can majalisa.

     Jakar mace da ita , duk sauran mata sun gyaro gidansu sun gogo ɗakunansu sun saka turaren wuta sunsha wankansu sun taho gidan ballagazar mace fira , ita kuma daƙiƙiyar ta kora mijinta waje ƙawaye sunfi miji dai. Bursunai² da ita sai wari takeyi ba wanka bare wanke ido , wacce batayi haka ba wace fikra gareta na sanin rayuwar duniya….? Tou hausawa dai sunce wanda maciji ya sara idan yaga igiya guduwa yakeyi , masu iya magana kuwa cewa sukayi wanda aka mara yayi hankali yafi wanda aka haifa dashi. Ɗaki daya ne tsal a gidan , nan kicin yake bedroom da toilet , palon nan da kujerunta sunyi daƙa² kalar tashin zuciya , kwanukan da sukaci abinci da wanda aka zuzzubar duk ba’a ɗauke ba , tunda sun ɓata palon kuma wai sai suka koma ƙuryar ɗaki ana fira ,

    1 saura mijinta ya shigo gida , a palo ya ajiye ledar biredi daya shigo da ita da ɗan naman daya riƙo musu ya fara tattara kwanukan dake palon , jin buruntu a palo yasa ita mai gidan tace Hadiza leƙa kiga waye , ita Hadiza data tashi fita sai ta cire hijabi ta gyara ɗaurin kallabi tayi palo…..

       A palo , da sauri ta isa wurin mijin Halimatu tana riƙe tsintsiyar dake hannunshi cike da makirci irin namu na mata tace haba “yar laɓai ai wannan aikin ba naka bane ba , a gafarcemu tayi maganar tana murmushi mai tattare da ɗaukar hankali , shima riƙe tsintsinyar yayi yana cewa ta bari kawai zai share ya faɗa yana murmushi , suma na bedroom sunaji amma Halima bata fito ba sai kuma Zainab ta fito aka baro Fadila da Halimatu matar gidan kenan a bedroom. Ita kuma Hadiza tana riƙe da tsintsiyar suna jayayya da mijin Halimatu akan bazai saki ba zai share…

    Itama Zainab tana isowa ta riƙe tsintsiya haba ranka ya daɗe ina za’ayi wannan abun kunya ka rufa mana asiri mu share , daga cikin bedroom kuma Halimatu tayi dariya tana cema Fadila ai dake bashi da matsala shine zai share bazai basu ba , a palo kuma Hadiza sai cewa takeyi ya bada tsintsiya , ganin dai sun dameshi yasa ya haƙura ya bata tsintsiyar kuma idan sun gama shine ai rakasu gida ,…….

       Idan namiji bashi da matsala (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); kece kike koya mishi ya zama mai matsala , idan namiji bai iya yawon majalisa ba kece kike koya mishi , Halimatu da mijinta auren soyayya sukayi , mijinta bashi da kuɗi amma yana da rufin asiri kasancewarshi ƙaramin ma’aikacin gwamnati , sauran matan nan dana lissafo su 3 , ɗayan su huɗu ne a wurin mijinta , bata yini gidanta kuma batacin abincin gidanta kuɗin cefanenta da komai nata take aikashi wa iyayenta tunda ta samu na mijin ballagar mace iyayenta suna buƙata tunda ta wadata saita wadatasu da kasonta na gidan miji. Kullum da ita ake majalisa amma idan mijinta yazo gidanta zata zauna ta kula dashi ta bashi duk irin kulawar da yake buƙata asha soyayya sai ya tafi taci gaba da zuwa kuma shi baisan tana wannan iskancin rashin zama gida ba.

      Ita kuma ɗaya mijinta driver ne , idan ya tafi sai yayi wata biyu bashi nan , itama a gidan jakar mace take ci tana sha tayi wanka da wanki itama kuɗin da mijinta yake bata idan zai tafi sai ta shiga adashe tunda an samu na mijin daƙiƙiyar mace , ɗayar kuma mijinta gadi yakeyi a asibiti shi dama baya bayar da wani kuɗi saida idan an samu albashi ya ɗan sissiyo abinda ya sawwaƙa daga ita har mijinta a gidan mijin wawiyar mace suke ci suke sha , itace Hadiza , Halimatu kuwa matar gida ba , mijinta yana aiki a C B N ubangidanshi ya cusashi da satifiket ƙaramin ma’aikaci ne amma dogon buri yasashi yakeyin digiri karatun asabar da lahadi , { part – time } ya kusa gamawa ubangidan nashi yake san ganin ya tashi daga ƙaramin ma’aikaci ya zama babba.

Sai 4 saura na sauka a abin sallah , kuma sai a lokacin naje inda wayata take , bayan na ɗauketa ne naga miss calls inshi 7 , data na buɗe nasan yana online , baya online ya daɗe ma da sauka amma ya turo min hotonshi shida Papi suna kwance a saman gado , wai suna gaisheni kuma in sa Allah a raina in daina fushi. Su basuda zuciya kamar yadda nake mishi gori suna gaisheni. Murmushi nayi tare dabin hoton da kallon , ko ina zaije da Papi ? Oho……! Bakuyi kyau ba shine abinda na tura mishi nima na sauka.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
      Yau na samu damar zuwa makaranta , kuma Mai gilashi ta bani labarin Sharifa ta tsoratani sosai akanta ta firgitani , na gigice na tsorata , ta ƙara da cewa idan ina maido hankalina jikina tou in tashi daga wannan asararren baccin da nakeyi , ta nunamin hotunan Sharifa ita da Dikko wanda koni da nake aurenshi ban taɓayin irinsu ba , bawai riƙeta yakeyi ba ko taɓata ba dan shi baya da ɗabi’ar taɓe²n mata kawai dai anyi hotunan cikin takon so. Hotunanshi shida Yusra , abindai yamin babu daɗi , raina ya ɓaci matuƙa , amma dake ina da ɗanyen kai kamar yadda Dikko yace sai nayi ma abun bahaguwar fahimta akan yadda ita Sa’adatu ta fahimtar dani , maimakon nabi abun a sannu naji yadda sirrin abun yake saina fara kiran wayar Dikko , wayar a kashe take ma wacce baya rufemana ita kwata² duk lokacin da mune muka kirashi zamuji shi…. Haka na haukace cikin aji naci gaba da turawa Dikko saƙon zagi na kirashi da mayaudari munafuki ɗan iska , Farisa taci gaba da zugani ina ta ɓarke²n zagi kamar mahaukaciya tana cewa ai wannan ma nuna miki yakeyi tsaron gida ya barki , ya barki gadi matar tana waje ya tafi da ita ke kuma an barki tsaron gida , haka taita tunomin lokacin da yayi mata liƙi na ida ƙwacewa gaba ɗaya na warware kamar falfela , duk yadda Sa’adatu taso ta fahimtar dani naƙi saurarenta saida na gaji dan kaina na tsaya , bayan wani lokaci kuma na tura masa cewa tunda dai kai ka lalace ka zama karuwa saina fitar da cikin nan. Duk haka bai isa ba na farakiran wayar Ashiru , shima nashi a kashe yake , shima na tura mishi saƙo cewa Allah ya isa tsakanina dakai har kaga ana cin amana bazaka faɗamin ba , munafukai “yan partyn amarya…..

      Umar na kira shima na zage tatas kuma nace masa munafuki da kilbibin faɗi ba’a (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); tambayeka bane ka iya faɗa , dake shi Dikkon tsoronshi kakeji shine baka faɗamin ba yana tare da “yan mata , shima dai na tata mishi ɗan ƙaramin haukata na kashe waya. Wannan duk ya zama zargi da wani tunani daban irin namu na mata , duk lokacin da akace miki mijinki yana can yana kaza ko yayi kaza ko kaza yake aikatawa karki kuskura ki yanke hukunci akan abinda baki da tabbaci akanshi , zargi baida kyau haka kuma yanke hukunci cikin fushi yake haifar da ɗa mara ido , domin ita zuciya kamar iska haka take halbawa hawa take da sauka , ƙoƙari ake ana danneta ba’a biye mata haka kuma ba’a bata abinda take so domin za’ayi nadama da dana sani idan ta kwanta…..

      Har aka tashi makaranta ban sake magana ba , haka na koma gida jikina suku² duk abin duniya ya dameni na rasa ina zansa raina , sai yanzu na fara tunanin hukuncin da zai biyo , dariyar shi na tuno da yake cemin ki daina ganin kwana biyu na zuba miki ido ina nan yadda kika sanni ban canja ba halina yana nan yadda kika sanshi. Me zai faru idan Dikko yaga texses in nan ? Me zaice ? Ya zaiyi ? Ni kuma ya zaimin ? Me zai faru………….??? Zuciyata tace duk abinda ya faru sai me ? 

    Jikin madubi na matsa na kalli kyakkyar fuskata da idanuwa na masu burgewa zararan giraren idona da suka ƙara fitomin da kyan idanuwa na , girata yadda tayi wata kyakkyawar ziririyar saƙa su biyun suka haɗe suka ɗanyo ƙasa , dogon hancina na kalla da kyakkyawan bakina , murmushi nayi tare da maida idona saman goshina. Lallausan gashi ya kwanta luf abun gwanin burgewa , ida cire kallabin kaina nayi nabi gashin kaina mai (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); cikar kyau da ɗaukar ido irin na cikakkin fulanin asali da kallo , dirina na kalla ga haskakakkar fatata komai yaji ga hutu ya tabbata a gareni , zuciya tace kallarki Sultana ɗanyar yarinya dake kin cika ta ko ina komai ya zauna kalar burgewa , shekarunki ma yanzu suke tafiya dan zuwa 20 , me zakiyi da Dikko wanda yaƙi yadda ma ya faɗa miki shekarunshi saboda yawansu , gashi nan ma harya fara squeezing , Allah ma yasa yayi fushin kiga yadda zakici wuta a garin nan , ga kuɗinki a account ga mota ga tsadaddun suruta masu yawan gaske. Sarka “yan kunne zobe ɗan hannu duk na zinari kala² , idan kika fita zaki ci gaba An mata da hannuna na nuna da bakina yadda jirgi ke tashi sama , dariya nayi tare dayin rawa a jikin madubi dan mafitar dana samu , kai zanci uwar² uwayen masu wuta , ashe ma hauka yasa nayi aure a Katsina ? Ai ban taɓa lura da haka naɗu ba sai yau , ana ta faɗamin ban ɗauki abin serious sai yanzu na ƙarasa ina wasa da kyawawan idanuwana………

       Rawa naci gaba dayi ashe dai na haɗu da yawa shi yasa shima kanshi Dikkon yake cemin An mata , gani da tsawo dai² kuma ni ba ƙatuwa ba. Kai gaskiya inada siga da kuma launin burgewa gani kuma yarinya , Sultana yanzu lokac 
*JAMILA MUSA…*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button