NOVELSUncategorized

YAZEED 21 – 25

          *YAZEED*
          ❤❤❤❤❤
                ©    Na
               Hapsat Musa
                  (Hapsy baby)

PERFECT WRITES FORUM

P.W.F


21_25

Jumallah bata kallon Gabanta jitayi tayi Karo da mutum 
Wani kyakyawan Mari taji Afuskarta Tass!!!
Dafe Kunci tayi taga waye wannan.
Dasauri  Dady yamatso wajen Yazeed cukin Fushi yace
“Yazeed  meya haka zaka fallama yarinya Mari”Kamo Hannu Jumallah kawai yayi Suka nufi cikin Gida  Jumallah 
Kaka dake fitowa daga cikin D’aki  Dasauri tace ” Ummaru!!!!
Yace “Na’am Inna”
Tace  “Kaine ko idanuwana ke Mani Gizo Ummaru”
Yace “Nine Bawani ba”
  D’akin da Baban Jumallah yake tashige
Tabarshi tsaye  
Cikin sanyi jiki yabita 
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Yazeed kam kakakabe rigar shi yayi inda jumallah tafadomashi sai yatsina yake kamar yataba kashi Ayman da Mimi kuma waje Suka tsaya
Itakam dama Jumallah tuni ta ruga Kiran Malam lawali
Dady yabi Kaka jikin sanyi jiki
 Yabita Ganin Mutum yayi kwance Dasauri ya isa wajen
Wadda yagani cikin wannnan Halin ne yafirgita tashi
Amadu!!!!
 Dasauri yakaraso wajenshi 
Yasunguna Kusadashi
Amadu cikin wani Hali yajuyo wajen yayanshi 
Yabude Idanuwanshi Ahankali Ganin wadda  ke kusadashi. Yace “Kaine Yaya Ummaru ko Idanuwana Suka Fara yimani Gizo da ganinka”
Tamke Hannunshi yayi yace “Nine Amadu gani gareka Kanena kayafeman ga cikin wannan Halin Amma na wofatar daku kayafeman don Allah”

Kaka tace “Ummaru ji Halin da Kanenka yake ciki Amma kayi watsi damu kan Duniya kaicoka”

 Dady  Hawaye yaji sunzobamashi
Yace “Kiyafeman  Inna don Allah”

“Tashi kashigo Dasu”
Dady mikewa ya fito yayi masu  Mimi jagora  Yazeed kam   kamar yashigo wajen Kashi yayi musu Suka shiga Da’ki
Kaka Kafin su shigo wata tabarma tashimfida masu Duk ta yayage 
Mimi da Ayman Suka zauna Amma Yazeed kamar ya Dora jikinshi bisa Wuta
Dady kusada da Kanenshi yakoma Amadu  rike Hannushi yayi “yaya Umarru  nagode Allah dayahada dakai  Kafin nakoma ga Ubangiji na.”

Jumallah ce tashigo rike da kwaryar Rubutu sai Haki take  domin Gudu Tasha dasauri tadurkusu gaban Kaka
“Kaka Ga Rubutun”
Dady ne Ya  Amsa 
“Jumallah Ga Kawunki nan Allah yakawoshi Gareni yau”
Hannu Jumallah Yakama da Kaka yace “Yaya Ummaru ga Amanar Jumallah nabaka ga ta mahaifiyata   nan  don Allah ka kulaman dasu Yaya
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Kar kamanta Alkwalin da mukayi dakai tunkafin mukai Haka  nidakai”

Dady yace “Amadu bazaka Mutu ba Har Wannan Alkawalin damukai sai yacika”

Juyowa yayi “Yazeed Ayman taso kuga Kawunku”
Ayman isa tayi Shima Yazeed yamtsa 
Baba yace “Yazeedu  ne yagirma Haka Kasan Rabon danaganshi tunda yatafi Kasar Turawa Karatu”

Kaka Kam da jumallah sunyi  shiru Ruwan da akawomusu ma sun kasa sha

Baba yajuyo wajen Jumallah yace “Muneera”!! dasauri Kaka da Jumallah Suka Dago Fuska  Domin bai  taba Kiranta da wannan sunanba yace ” Ga Kawunki nan zai Kula Dake Tamkar ni Kinji Ko Baba 

“Baba Kadaina fadin haka zaka tashi”
Yajuyo wajen Kaka yace “Inna kiyafeman Zan Mutu Ina farin ciki Yau nahadu da dan uwana yajuyo. Wajen  Yazeed “Dana Allah yayi  Maka Albarka”
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Kaka tace “Amadu kadaina Fadin Haka Murmushi yayi kawai yace ” Bani Ruwa nasha  Ruwa akabashi yasha
Kama Hannu Dady yayi ya tamke Kamar za’a rabasu  yace “Yaya kar kamanta da Alkawalin mu”

Mimi kam da yazeed sai Aymana sunyi shiru Kamar Babu su wajen  Bareama Yazeed jiyake Kamar Bisa qaya yake.

“Jumallah tashi kigyara Musu wannan D’aki ”  dasauri tamike tafito D’akin Dama Babu kura ciki tabarma ce ta shimfida 
Tadawo “kaka nagama Mimi mikewa tayi itada Ayman sai Yazeed Suka tafi Akabar Dady da Kaka cikin D’akin 

” Inna kiyafeman nasan nayi Kuskure Don Allah kiyafeman  bandamu danazo naga lafiyar Ku ba sai dai nayi Aike Inna kiyafeman “
Fashewa yayi dakuka 
“Na yafemaka Ummaru”
“Nagode innata”

Jumallah kuma wuri tasamu tazauna kowaye wannan daga natakashi bangani zai mareni shafa inda Yazeed ya mareta tayi  
Gakuma fuskarshi babu Far’raa ko kokadan
Sai yatsina Fuska yake…..

Salatin da Kaka taji tanayi yasa mikewa Zumbur tanufi D’akin da mahaifinta yake  dasauri…

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button