Labarai

Ɓatagari sun yanka mai juna-biyu domin cire ɗan cikinta

Ɓatagari sun yanka mai juna-biyu domin cire ɗan cikinta

 

Hukumomi a Mexico sun ce wata mai juna biyu ta rasa ranta bayan da wasu ɓata-gari suka farke cikinta suka sace ɗan-tayi.

 

Wata sanarwa daga ofishin mai shari’a na jihar Veracruz ta bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ɗauke da jariri.

 

A ranar Litinin ne aka gurfanar da waɗanda ake zargin, mace da namiji bisa zargin su da laifin garkuwa da mutune da kuma kisan mace.

 

Wani daga cikin masu gudanar da binciken ya shaida wa kamfanin dillancin labaru na AFP cewa ana zargin mutanen biyu sun aikata laifin ne saboda daya daga cikin maharan ta gaza samun ciki..

 

‘Yan uwan wadda aka kashen sun ce an yaudare ta ne ta shafin sada zumunta inda aka yi alkawarin yi mata kyautar kayan jarirai.

 

Wannan ne karo na uku da aka samu irin wannan kisa a cikin shekarun da suka gabata.

 

An kiyasata cewa an kashe mata 1,000, bisa dalilai masu nasaba da jinsi, a kasar ta Mexico cikin shekara ta 2021.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button