NOVELSUncategorized

WA ZAI FURTA 23

???? *WA ZAI FURTA?*????
              2⃣3⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri’a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.**KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki…… beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

????????????????????  *RUKAYYA  BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*????????????.

        ***************
*ABUJA NIGERIA*

…… Falon ya dauki surutai kowa sai fara’a yakeyi da murna.
 Alhaji Hassan ya kalli daddy ya ce, ranka ya dade Ina neman afuwa amma Zan yi tambaya….
 Cike da fara’a ya ce bisimillah Alhaji…. bisimillah kowa ma na jinka….
   Akan daurin auren nan ne, a gaskiya kaina ya daure ban taba ganin irin wannan ba, mun zo neman Aure ne ba Sanya baiko ba, Jin magana ya kawo mu, amma kwatsam ka karbi Kaya da kudi a matsayin kayan Aure da sadaki dan Allah me yasa ka yanke wannan hukunci Kuma ka saka sharadin baka son yaran su sani….
  Ya Kara fadada murmushi kafin ya Fara magana Yana kallon Alhaji Muhammad tambuwal, kaga maganar ka ta fito na wata kila su bukaci dogon bayani ko?
 Duk sukayi Yar dariya ya maida kallonsa ga Alhaji Hassan ya na magana cikin natsuwa:
  Abinda ke faruwa a gaskiya rawar Kan Anwar yayi yawa, tun asalin tura Bilkisu karatu dutsinma na kaita tare da masu tsaronta ba tare da ta sani ba, na baza securities sosai akan sanar Dani duk wani movement dinta.
  Lokacin da suka Fara takun saka ita da Anwar na Sanya aka mun bincike akansa, Ashe babu Wanda ma yasan yaron shine *Bushara*, shaidar da ya samu ya sanya ban dauki mataki akansa ba saboda naji cewa yana da halin ko in kula, gadara, Yana Kuma da son addini.
  Bayan mun Kai Mata ziyara na hadu dashi sai naga fuskar yaron kamar na Sansa, kwatsam kuwa taron da kamfaninsa yayi a Lagos nagan Shi a daily trust.
 Boye boyen daya ringa yi ma Bilkisu yasa na bashi dama amma a gaskiya zafin sa yayi yawa daga baya muka gane kishi ne. Yana da rawar Kai musamman idan Yana tare da ita, ga kuruciya, ga giyar so da giyar kudi kunga komai zai iya faruwa, Shi yasa na yanke shawarar kawai mu daura masu Aure yanda komin ya Kai hannu ya taba ta Yanzu hankalin mu bazai tashi ba matar sa ce.
    Dalilin da yasa bana so a fada masu shine, matukar ya ji matar sa ce Yanzu tabbas bazai barta anan gidan ba, kuma a gaskiya bamu shirya aurar da ita Yanzu ba abun yazo Mana kwatsam Babu yanda zamuyi…
Na biyu, wallahi sai ya Mata ciki Kota halin Kaka duk da ba haramun bane Amma ga al’ada irin tamu ta hausawa hakan zaifi dacewa idan ta tare a gidan sa kuma gashi wuri daya suke karatu….. Zahiri, inji Alhaji Hassan.
 Yawwah, to Shi yasa na ce mu kyalesu har sai sun gama makaranta sannan tunda saura shekara daya….. Amma wani hanzari ba gudu ba Alhaji Muhammad ya fada…duk aka mayar da hankali wurinsa..
  A sanar da yarinyar domin ta san cewa akwai hukuncin Aure akanta, kasan yaran Yanzu kuma tabbas Kun San cewa shaidanu Yanzu zasuyi ta kunno Kai.
  A fada Mata sannan a ja Mata kunne a sanar da ita implication na fadawa Alhaji Hamzan ita abun zai ba ruwa…… Kuma fa. Kowa yafada Yana girgiza Kai.
  Kenan idan mun fahimceku Anwar din kawai za’a boye mawa?
  Haka ya kamata gaskiya daddy ya fada.
  Masha Allah hakan yayi Amma dole mu sanar da Hajiya na tabbatar baza ta Bari ya sani ba zahiri….. Hakan Yana da kyau. Duk suka fada lokaci guda.
   Nan aka kasa komai aka Basu nasu aka masu Sha Tara ta arziki suka tafi suna Murna……
  Tafe suke suna al’ajabin dattakon wadannan mutane, abun ya matukar birgesu Alhaji Hassan yasha alwashin shima zai ma yarsa irin wannan gatan da tsare mutunci.
   Tana kwance yau duk ta tashi tana Jin jikinta wani iri babu kwari, ga kasala ga yawan faduwar gaba, tayi lamoo wayar ta tayi Kara.
  Tayi shiru don tasan shine kawai zuciyar ta a yau najin haushin sa kadan….ga naci ya dunga Kira ba arziki ta daga…
Hello ..ta fada a hankali.
  Ke yunwa nakeji kiyi mun faten dankalin nan da kikayi mun last week.
  Kamar ta kurma ihu Shi duniya baida wata damuwa sai ta abinci?
  Kinji? Ya fada da karfi.
Naji..
Ya danyi kasa da murya Zan Sami gasassar kaza?
 Lokacin ne ta danyi murmushi, ka lissafo kawai abinda za a maka Yanzu zaka Fara Zan Sami kaza?? Sai ka lissafo goma.
 Ya kyalkyace da dariya sai meat pie da Dan yam balls Amma kada ki cika mun yaji irin wancen kinji ko?
Naji sai me?
Yayi murmushi sai kiyi kwalliya sosai kisa gyale Banda wannan Dan iskan zanzo don bama zai San fita ta ba.
Ta ce hmmm.
Ya naji kin yi la’asar ko an Fara fargaba ne?
Ta galla ma wayar harara fargabar meye?
Ya Kara dariya ya ce wallahi basan an mako mun harara.
Tayi murmushi hmm Kai dai ka sani…. Kema kin sani kilibabba Anwar na kalbinki amma kina wani sharewa irin ba sosai din nan ba….. Ta kyalkyace da dariya kaiii Anwar Allah ya shirya ka… Hubby zaki ce bagidajiya. Ke wallahi kina Abu kamar wata Yar kauyen kumus…. Tayi murmushi kawai.
 Yayi kasa da murya kidan canza mun suna Mana sweetheart……. Kai wallahi Zan ajiye wayar Nan …ya Kara kyalkyacewa da dariya yace ya hakuri nayi shiru.
Ta zumbure baki.
Yaushe Zamu fita yawo cikin gari?
Ana wannan Corona virus din zaka fita yawo?
Ke ban son unnecessary excuse…. Cutar ce unnecessary??? 
Ya ja guntun tsoki…. Ko *Amigo* muje please…… Anwar kana so asanya ni a labarai ko?
 Yayi murmushi to muje ShopRite nasan kinfi son can.
  Ki bari anjima Zan baki labarin abinda ya faru ranar da na ganki a ShopRite din na buya…. Ta zaro ido ka ganni?
Yayi dariya eh, 
Fada mun Yanzu,
Ki Bari sai nazo,
Yanzu nake so .
Yayi murmushi. Kin tuna ranar da Kika tarar da securities a bakin kofa kikayi ta fada a Baki wuri??
Ta zaro ido ba munyi waya lokacin ba, Ina kallon ki ai nine a wurin….. Innalillahi.
Ranar ne na biyoki har gida naga address dinki…. Na shiga uku.
Kin fita uku….ya fada Yana dariya.
  Yau Zan baki labarai kala kala idan nazo kinji ko?
Tohm, ta fada a hankali.
 Sai nazo ko?
Okay.
Ta latse…..
  Daddy bai Sami damar shiga gida ba sai biyar saura.
 Suna falon sama ita da mommy ya shigo… Ta Mike daddy oyoyo… Bilkisu meye kike dahuwa Kuma naji gidan duk ya hargitse da kamshi?
Mommy tayi karaf tana dariya…. Aikin Anwar ne.
  Yayi murmushi da alama kin gaji uwaki wurin kula da miji ……. Maganar ta makale. Yayi saurin canza Babi da kallon mommy muje na ganki ya juya zuwa daki.
  Suna shiga ta kalleshi har an daura?
Eh, Amma fa sun kawo shawara..
    Ta me fa?
  Ya zauna Baki gado, sun ce a sanar da Bilkisun Kuma I reason with them, kin ga yarinya ce karama kada ta je tana janyo ma kanta bala’i ba tare da tasan akwai sharadin Aure a kanta ba Kinga mu Allah zai Kama da laifin rashin sanar da ita tunda Bata sani ba….. Zata firgice gara ayi shiru.
Ba wani firgici kar ki nuna kin sani Ni Zan Mata magana da kaina…. Me zai hana ka mayar da ita nan gwagwalada ta karasa ….. Biyota zaiyi, wallahi Anwar bazai yarda ba.
 Shikenan, Yanzu goben zamu tafi sokoton?
Eh, ke zakiyi gaba Zan biyoki bayan kwana biyu tare da Bilkisun.
Shikenan Allah ya tabbatar Mana da alkhairi……ammeeenn.
 Bisa bike yazo yau, karar yasa ta fito da sauri ta leka ta taga daidai Yana cire helmet.
  Kananan Kaya ne jikin sa, ya ajiye helmet din ya saka facing cap…. Mommy zo kiga Anwar yau a bike yazo…. Ta yi murmushi, daga race ya wuto nan din ko?
  Race Kuma?
Eh, kin manta da marece idan mun fita muna haduwa dasu da yawa yaran ministers, president da su Anwar din?
Wai sune?, Hada Shi kenan?…. Gashi Kinga   alama.!.
Zata Kara magana ta ce kije tun kafin ya nemeki ta Haye sama abinta.
    Yana tsaye bakin kofar ta karaso, bazaka shigo daga ciki ba kayi tsaye?
  Ta juya ciki ya biyo bayanta kin yi wa mommy magana Zan daukeki muje yawo?
 Ta mishi banza har suka zauna bisa dining.
Kinji?
Ta ce a’a bazamu fita mu biyu ba….. Saboda kada na gudu dake?
  Ta Dan kalleshi, Yanzu fa wannan maganar na iya haddasa matsala…kinji?
Kaci abincin Mana….. Ya janyo plate gabansa zanci amma kibani amsa.
  Tayi shiru,
Ko na tamabayeta da kaina?
  Ta kalleshi da sauri, yayi murmushi Allah kuwa…. Ya kamata kana da kawaici fa…. Akanki fa bani da Shi gara ma ki sani….
    Zamu je?
Kaiii Wai Kai me yasa ka fiye naci?
Saboda na turo da maganar neman auren ki.
  Ka bari sai Nan gaba….
Family na sunji dadin zuwa gidan nan fa, suna ta mun addu’a da murnar na dace da Mata in shaa Allah….
Ta ce hmm.
Yayi dariya Allah kuwa, an karamta su mood din su ya kasa boye hakan Amma sun dawo da wasu Kaya da goro Wai namu ne Haka akeyi?
Kai ni ban sani ba…… Ya kyalkyace da dariya ke wannan kunyar fa dole ki ajiye ta gefe kinji…. Ta galla mishi harara. Ya Kara yin dariya…..wannan hararar bansan lokacin da za a daina ta ba ko kuwa salon kallon love din naki ne Haka…… Sai kawai tayi murmushi tare da doka guntun tsoki….Kai dai ka sani….kema kin sani. Duk sukayi dariya.
   Hajiya na son ganinki duk ta rikice na aika Mata da hotunan ki Wai Bata yarda ba zakuyi video call….. Ina ka Sami hotuna na?
  A wayar ki na dauka lokacin Dana tafi da ita kin tuna????
Ta galla mishi harara tun lokacin abinda ke ranka kenan???
Ya kyalkyace da dariya meye ke Raina?
Tayi mishi banza.
Ya Dan gyara Zama ya lunkuma yamball baki kin San fa tun ranar da Kika raba kudin da hahilin nan ya baki class zuciyata ta bani na Sami matar Aure….ta Kara galla mishi harara.
Ya yi murmushi me yasa Wai ranar bakiyi gardama ba Kika bani kudin?
Ta ce hmm.
Anya ba tun tsiwar farko kin kamu da so na …..ta dauki robar ruwa ta Mike kawai ya taso bowl din yamball din a hannu da sauri Yana dariya zo ki daukon meat pie din idan kin gaji da table din….. Nima fa nafi son Zama kasa….. Ya zauna bisa carpet ya Mike kafa.
  Ta dauko ita ma ta zauna dan nesa dashi kadan suna kallon juna…. Ya kalleta yace kamar irin Amarya da angon Nan ko?
Ta galla mishi harara. Yayi murmushi, Dan matso Nan kin mun nisa gaskiya… Ta Dan matsa kadan kada taja kuma ya kamota.
Ina son wannan rigar ina Kika siye ta?
Mommy ta siyo mun Dubai…okkay.
Me yasa bazakiyi mun kwalliya da wadanda na kawo Miki ba ko kina Jin kunya?
Tayi murmushi kawai.
Dan Allah ki saka,
Waye telan ki?
Mace ce,can cikin Area 8 ne shagon yake.
Ki debo kayan da Zaki Kai dinki gobe idan mun fita mu biya kinji ko?…..
Nifa bazan bika ba..
Ya kalleta dalili??
Tayi shiru.
Kina Jin nauyin tambayar mommy ko?
Tayi shiru.
Shikenan, Yanzu Zaki iya magana da Hajiya?
Ta danyi kasa da Kai tana murmushi nidai ka jira ba yau ba…
Ya kura Mata ido Anya ba sauri zanyi a daura Mana Aure ba?
 Ta dago da karfi… Ya maida bayansa jikin kujera ya Dan kwanta…. Yes, saboda kunyarki tayi yawa gaskiya gara kawai na kawar da ita da wuri don Zaki ringa takurani.
Yar tsiwar ma an daina mun sai uwar harara …….Kai zaka karasa mun karatun?
  Waya fada miki Aure na Hana karatu?
Ta harareshi Yanzu ma kana neman kisan Kai Ina ga da Aure Kuma???
Yayi murmushi ko Yanzu ma nikaf Zan siya Miki masu yawa ba shegen da zai Kuma ganin wannan beauty face din ba…. Ta zaro ido nikaf?????
 Kwarai kuwa.
Ta zumburo Baki…
Ya danyi dariya ya tashi zaune ko kin fi son kullum ana tashin hankali????
  Tayi shiru yaga kamar ranta ya baci.
Ya Kira sunanta a hankali….. Kinji haushi ko?
  Ai wannan tsananin ke bana so, kana abu kamar Wanda bai yarda Dani ba kullum…
Yayi murmushi, wallahi na yarda dake…. To me yasa kake da takura?
Saboda *Ina son ki*
Ta kalleshi da sauri.. watau duk lokacin da yake cewa saboda ..yayi shiru abinda baya son fada kenan?
 Kin gane ai Yanzu ko?
Ta Dan harareshi kawai. Ya kyalkyace da dariya yace *Bilkisu H. Bushara*…….. Ta Kara galla mishi harara.
   Sai goma da Rabi yabar gidan.
   Tana shiga ta tarar da daddy falon Yana kallon News.
  Ta wuce sum, sum, sum….. Zo nan Bilkisu.
Cikin Jin kunya ta karaso ta zauna kasa kusa da kafafun sa.
  Anwar din ya tafi?
Eh,
Da alama zaiyi kula sosai ko?
Tayi shiru tana sunne Kai.
Sai dai Shi din ya fiye damuwa ko?
Ta Kara yin shiru tana murmushi.
Ya Aiko da iyayensa kamar yanda na umurta hakan ya nuna tabbas sonki yakeyi da gaskiya.
  Amma kina ganin zaman ku makaranta Yanzu a Haka bazai takura ki ba yayi affecting karatun ki ba Bilkisu?
 Nima Ina tunanin haka daddy, saboda Yana da rigima sosai….. Na sani.
Ko muyi wata shawara nida ke bazaki fadawa mommy ba?
Eh, daddy. Ta fada da sauri.
  Kinga tashin hankalin baya shakkar kowa kada yaje wata Rana ba fata akeyi ba yayi aika aika…..ko ?
Ta daga Kai.
Ko in sa iyayensa su dawo na daura Miki Aure dashi cikin sirri ba tare da ya sani ba?
Ta zaro ido cikin firgici zatayi magana yace jira kiji dabarata…….
Bazamu yarda ya sani ba, dalili kuwa shine irin damukar da yake Miki tabbas Yanzu zai Kara sake salo Kinga hakan akwai haramci Amma idan akwai Aure ko hannun ki ya taba ga Allah babu laifi iyaka kici gaba da nuna mishi Baki so har a Samu ku Gama… Kin gane ai ko?
 Ta daga Kai.
Koda wasa kada ki fadawa kowa kinji ko?
Ta ce toh, Yanzu mubi wannan shawarar tayi ko?
Ta daga Kai yawwa,to ungo ya Mika Mata kudi…sadakin ki ne dazun kafin su tafi an riga an daura Miki…… Kudin suka Fadi sai kyarma kyaf,kyaf,kyaf….. Ya Bata labarin duk yanda akayi sannan yaci gaba da lallashinta har ta daina zubda hawaye.
  Amatsayin sa na uba na gari ya fada Mata sharuddan Aure don ta kiyaye………
 Tana shiga daki ta fada Kan gado ta rushe da wani irin Kuka Mai tsima Rai.
   Anwar kuwa na shawo kwana ya haska sadeeq can nesa bisa wani dakali da alama waya ce yakeyi.
  Ko gida bai shiga ba masu gadi suka bude gate da sauri securities suka fito….
Ya sauka yace su shiga dashi ciki ya koma Yana sando a hankali ya nufi gurin da ya hasko sadeeq….
Zaune yake ya bada baya Yana waya.
    Ya daga hannu zai bashi tsoro sai kawai yaji Yana cewa…… Wallahi tallahi baba an daura mishi Aure yau.. ya koma ya tsaya tare da rungume hannu.
…. Hajiya ke fada mun Amma basa son Anwar din ya sani….. Gabansa ya bada dammmmm….
Yaci gaba da cewa, wallahi kudin neman aure suka Kai shine mahaifin yarinyar kawai yace sun Isa shaida Aure aka daura… Wallahi kuwa.
Amin amin…
Eh, bana tunanin yarinyar ta sani gaskiya.
A yanda aka ce mahaifin yarinyar ne yace lallai sai an daura auren saboda rawar Kan Anwar yayi yawa….. Eh sai dai mun dawo din. Amma Dan Allah baba kada ka fada ma kowa babu Wanda yasan hakan.
 Amin ya Rabbi.
Ya Mike ….juyowar da zaiyi suka hada ido da Anwar din cikin want irin yanayi ya razana ya firgita yayi baya da sauri ……….????✍????


*MAMAN ABDALLAH* ????????????

Assalamu alaikum. Ina Kara godiya ga masoya, Kuma Ina Kara bada hakuri Dan Allah masu kirana a waya a ringa mun chat saboda Kiran Yana hanani typing da wasu ayyuka. Duk wacce ta Aiko da sako Zan gani Zan kuma bada amsa ko amun voice idan bayanin nada tsawo Zan tura Mata hotunan magungunan da bayanan su.
Na gode Ina maku fatan alkhairi.????????

Alawiyya???????????? Aiko da 24 yau an Sami daya as usual????????????????‍♀????????‍♀ *Uwa Mai bada mama, I love you Mom ( Maryam adamu tikau maman amannas)*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button