NOVELSUncategorized

DIYAM 52

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Fifty Two : A Little Game

Inna ta fara sharar hawaye, ita dama kwana biyun nan komai sai kaga ta fara hawaye. “Allah ya ji kan baffan ku. Babu abinda bai gaya min ba sai kace yasan abinda zai faru bayan
babu shi. Abinda na wulakanta shine yanzu gatana ni da yayana, wadanda kuma na daukaka fiye da komai sune muka zama abin wulakanta wa a gurin su.” Sai Asma’u ta tashi ta koma kusa da ita tana rarrashinta, Sadauki ya mike tsaye yana kallona yace “ki kira shi yau. Gobe ki gaya min yadda kuka yi dashi”. Na gyada kaina sai ya juya ya fice. 

Ina kallonsu suka gama kukansu amma ni ko hawaye banji a idona ba, maybe ko kukan ya kare ne oho, nidai abu daya da na sani shine baxan koma gidan Saghir ba and that’s final. 

Sai yamma na samu courage din kiransa. Bugu daya ya dauka yace “ha! Finally. Kin shirya inzo mu tafi?” Na lumshe ido na na bude, ina bitar abinda Sadauki yace min nace “ba wannan dalilin da yasa na kira ka ba. Na kira ne in tabbatar maka da abinda na gayawa Hajiya sanda tazo. Aure na dakai ya kare Saghir. Ba zan koma gidan ka ba saboda rabuwa a tsakanin mu tafi alkhairi akan zaman. Ina neman ka sawwake min. Ka kawo ko kuma ka aiko min da takarda ta nan da kwana uku in kuma ba haka I will have no other choice than in kai karar ka alkali ya raba auren mu” ya yi shiru amma nasan bai ajiye ba, sai yace “are you threatening me Diyam?” Nace “ba threat bane ba, option ne na baka kamar yadda nima Allah ya bani option na ko in hakura in zauna da kai ko kuma in kai karar ka in baka kudin yin wani auren kai kuma ka sawake min” yace “ohh, abinda ya tsara miki kenan ko? Abinda yace ki gaya min kenan? To ki bude kunnen ki kiji sosai nima nawa sakon zuwa gurinsa. Kice masa nace bazan sake ki dinba, idan akwai abinda yafi court ya kai ni can. Amma kafin ku tafi court din bara in fara gaya muku abinda zai fari a can din. Muna zuwa zan zayyana wa alkalin cewa shi wanda ya taimaka miki kika kawo karar tawa tsohon manemin ki ne, na kama ku na hana ku harka shine kuka yi deciding kawo kara ta saboda in sakar masa ke. How about that?” Nace “kai kanka da kake fadar maganar kasan cewa ba gaskiya bane ba. Kuma duk inda alkali yake ai mutum ne mai ilimi wanda zai zai saurari kowa. Ni fa ƴa ce Saghir ba baiwa ba, tunda nace bana sonka set me free please” yace “in nayi haka Diyam ai na bashi abinda yake so kenan, na baku abinda kuke so. Ni kuma nayi alkawarin tunda kuka making fool of me for years sai na dauki fansa. Plus wulakancin da yasa police suka yi min. So here is another message to him. Tell him nace I want my job back, I am kind of out of money yanzu. In ba haka ba kuma zan fara spreading rumors a cikin ma’aikatan sa, and this time around I won’t be drunk yadda zanyi passing clear message har su fahimci wanene real Mr Abatcha, suma su fara boye matansu. Kuma harda gishiri zan kara wa maganar” ya karashe maganar yana dariya. 

Na cire wayar daga kunne na saboda yadda maganganun sa da dariyar sa suke kara huta ga already wutar da take ci a kirjina. Shin anya kuwa Saghir yana tsoron Allah? Shi karya bata yi masa wuya. Sanda ya dake ni a gida ya nuna yana zargina da Sadauki banji haushin sa ba kamar wanda naji akan maganganun da ya fada ranar nan akaina a gaban Sadauki, it shows cewa abinda yayi din ma bashi da remorse akan sa tunda har fada yake yi proudly a gaban third party. Yanzu kuma maganganun sa sun nuna min cewa ba wai ya mayar dani bane ba saboda yana son aurena ba, ya mayar dani ne to get back at Sadauki. Am not a toy, am a person with zuciya a kirjinta da kuma jini a jikinta. Am not going back.

Da dare na gwada wayar Sadauki dan in gaya masa abinda Saghir yace amma naji har yanzu bata shiga. Haushi ya ishe ni na ajiye ta kawai. Amma sai na gayawa Inna duk abinda Saghir yace akan maganar Sadauki. Ta juya kai tace “wannan yaron baya kyautawa. Shi bai san hukuncin wanda yayi wa wani irin wannan sharrin ba? In kotun za’a je fa shine a kasa dan bashi da wata shaida” sai kuma tace “ni bana son zuwa kotun nan wallahi, zuciyata bata so, yan’uwan mu ne mutanen nan, so nake ayi sulhu a tsakani ba sai kowa yaji ba. Ba ga Suwaiba nan ba an bashi, kuma yana da wata matar a gida me yake nema kuma. In kudin yake so sai a bashi shima in dai za’a rabu lafiya. Ni kotun ce bana so, kuma bana so ya bata wa yaron nan suna a gurin mutanen da suke ganin girmansa”.

Nima kuma bana son court din, amma kuma bana son komawa gidan Saghir kuma bana son in watsawa Sadauki kasa a ido ince bazan je ba. Dan haka ranar sai naki bacci na kwana ina gayawa Allah. Kuma na tabbatar ya jini kuma na yarda da cewa zaiyi hukuncin da ya dace.

Washegari da safe Asma’u ta tafi school ni kuma na koma na kwanta in danyi bacci sai naji karar wayata. Na dauka ina kallon number din Sadauki. Sai na jujjuya wayar a hannuna dan in tabbatar da cewa tawa ce bata Asma’u ba. Sai data kusa katsewa sannan na dauka da sallama na gaishe shi yace “ya kuka yi?” Sai da bashi labarin duk abinda Saghir ya fada. Sai kawai naji yayi dariya, yace “that man is so predictable. Ya fadi exactly abinda nake so ya fada. Tell him, na tsorata na tuba nace yayi hakuri kar ya zubar min da mutunci a gurin mutane, kice nace ya dawo ya cigaba da aikinsa ai dama ni ban kore shi ba shine ya daina zuwa. Sannan kice masa kema kin hakura ba kya son zuwa court dashi dan haka zaki koma gidan sa amma kina so please ya baki wata biyu saboda kina so ki shirya sosai” nayi saurin cewa “bazan koma ba” yace “I know. But just tell him that” nace “saboda me?” Yayi shiru sannan yace “do you trust me?” Nayi shiru nima ina lissafa lamarin sannan nace “yes, amma ina bukatar bayani” yace “okay, let me break it down for you. Bana son ke ko Inna ku shiga court dashi saboda kamar yadda Inna ta fada yan uwanku ne babu yadda zakuyi dasu. Sannan kuma ko an kaishi court din karshe kawai raba auren za’ayi and to get even that sai anyi ta faman cecekuce ana saka ki kina bayar da labari kina kara maimaita wa. I don’t want to put you through that emotional trauma. You have had enough of your share of emotions. Still kuma in nace zamuyi sueing dinsa for abinda ya fada a kunnena yayi, ba lallai ya samu wani sentence mai kyau ba saboda a lokacin da yayi din akwai aure a tsakanin ku dan haka iyayenki za’a jawo cikin case din for marrying you off that young. Bana son insa Inna cikin wannan maganar. So option dina shine ya zama tsakani na dashi ne kawai ku kuna gefe. And I promise you ba zaki koma ba but for that I need you to call him ki gaya masa abinda nace”.

Nace “okay, zan gaya masa” yace “thank you. But please kar ki gayawa Inna. Let it be our little secret”.

Ban gayawa Inna din ba kuma ban kira Saghir ba sai washegari. Ji nayi bana son kiran nasa dan haka sai na tura masa text message na fada masa abinda Sadauki yace in fada. Sai kuwa gashi nan ya kira ni na dauka da kyar, yace “it wasn’t so hard now was it? Dama nasan zamewa zaiyi ya barki. Ai mutane irin su babu abinda suke so irin su gyara public picture dinsu, ina komawa kuma zanyi requesting karin albashi kuma sai inga in zaiyi denying” yayi ta maganganun sa ni dai bance komai ba har ya gama sannan yace “and you? Mai zakiyi da wata biyu?” Nace “shiryawa nake so inyi sosai” yace “wacce irin shiryawa kuma? Ba kayanki kawai zaki zuba a akwati ba?” Nace “ina so in shirya emotionally, bayan abubuwan da ka fada ranar nan a gaban Sadauki ai you should be greatful da nace zan dawo din ma” sai na katse wayar kamar nayi fushi na kashe ta ma gaba daya.

Daga nan komai ya lafa a bangaren mu. Two weeks after that Sadauki yazo yayi wa inna sallama yace zaiyi tafiya zuwa Canada. Yana shigowa Subay’a ta zagayo ta dawo bayan kujerar da nake zaune. Muka gaishe shi ya amsa sai ya mika mata hannu “Subis come here” sai ta makale. Yayi dariya yace “inna na kawo karar Subay’a, bata gaishe ni” Inna tace “ke! Ba zaki zo ki gaishe shi ba?” Still taki zuwa, zanyi mata fada yace in rabu da ita, yayi wa Inna bayani “dama family na na Maiduguri kusan duk suna Canada, zan danje in yi musu kwana biyu. In naje zan kira ku da number din da za ku same ni da ita should in case ko wani abun zai tashi” Sai Inna ta nuna irin bata ji dadin tafiyar tasa ba, Asma’u harda matsar kwalla yace “ko wata daya fa ba zanyi ba. Just hutawa nake so inyi saboda ina aiyuka da yawa a nan”. 

Yana fita Subay’a ta zagayo cinyata tace “Mommy bana son mutumin nan” Inna ta kwade ta da muhuci tace “kar in sake jin kince ba kya sonsa, kuma in na sake ganin yazo kin ki gaishe shi ni dake ne. Babanki ne shi, tunda yayan babarki ne”.

Sai bayan tafiyar sa Inna ta tambayeni “wai ya kuke ciki ne maganar Saghir? Ni baki ce min komai ba” nace “na gaya masa abinda Sadauki yace in fada masa, shi kuma yace ba zai sake ni din  ba sai dai aje court din. Shi kuma Sadauki yace vaya son muje court dasu” inna tace “nima bana so, to amma ai ba zaki yi ta zama da aure aka ba. Dole dai cikin biyu za’ayi daga. Bara ya dawo daga canadan muji”.

Sati daya da tafiyar Sadauki muka je gidan Mama gabaki dayan mu. Anan ne muke samun labarin ashe rigima ake tayi a sharada tsakanin Alhaji Babba da kawu Isa. Kawu Isa yayi wa Saghir huce haushi na da suwaiba, har Saghir ya karba ya an fara shirye shirye sai kuma yaxo yace ya fasa ni zai mayar sai kawu Isa ya nuna cewa ba’a kyautawa yarinyar ba, amma as usual, Alhaji Babba ya goyi bayan dansa. 

Mama tace “ni tsoro nake ma Allah yasa bai lalata musu yarinya ba, dan labaran da muke ji basu da dadi”.

Bayan dawowar mune nayi bakuwa. Fauziyya. Ni ban san ma tasan gidan mu ba sai yau. Na karbe ta sosai muka shiga daki nayi serving dinta abinci da drinks. Sannan tace “muna ta jira kuma har yanzu shiru” nayi dariya kawai, sai tace “ko sai za’a koma sabon gida sannan zaki dawo?” Nace “sabon gida kuma?” Tace “eh mana, ko bai gaya miki ba ya siya mana sabon gida? Sai ta fara yi min bayanin girma da kyan gidan “kowa da part dinshi, part din kowa yayi girman gidan da muke ciki. Yayi order komai na gidan next week za’a kawo su” sai ta nuna min key din mota “kinga ya siya min mota, kema ina jin kina komawa za’a siya miki taki. Shima ya sake wata” na gyara zama ina nazarin ta nace “why are you here Fauziyya?” Tace “ziyara na kawo miki mana. Kuma in gaya miki alkhairin da ya samu mijin mu dan in kwadaita miki komawa gidan. Hausawa sunce the devil you know is better than the angel you don’t know. Na zauna dake lafiya, gwara ko dawo akan a kawo min wata wadda ban sani ba”.

Bayan tafiyar ta na zauna tunani. Kudi? Lokaci daya? Saghir? Ina ya samu kudi? And I remembered lokacin daya samu aiki yazo yake bani labari yace “financial secretary aka ce miki. Ni nake kula da duk harkokin shige da ficen kudi a companyn”.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button