NOVELSUncategorized

DIYAM 51

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Fifty One : The Will

A jikin kofar na zame na zauna ina jin zuciyata tana wani irin bugawa, ji nake yi kamar zan mutu, kaina yayi wani irin zafi kuma hawaye ya tsaya a ido na. Ban taba tunanin it’s possible ka tsani mutum kamar yadda naji na tsani Saghir a lokacin ba. Na fara
girgiza kaina ina cewa “no no no” kamar mahaukaciya. I can’t even imagine komawa gidan Saghir a matsayin mijina, I can’t imagine him touching me again. I would rather die. Ina jiyo maganganu a palo kamar muryar inna amma bana gane me take cewa, sai naji ta taba kofar amma da yake ina jikin kofar sai ta kasa bude wa sai naji tana kiran Asma’u. Sai kuma naji ana knocking kofar. Da kyar na bude idona na matsa daga jikin kofar sai suka bude suka shigo su biyu sannan Subay’a ta shigo itama tana kallo na sai naga Asma’u tayi sauri ta dauke ta sun sake fita.

Inna ta durkusa gabana tana taba wuyana tana magana a hankali amma ni bana jin ma me take cewa. Sai kuma naga ta kama ni ta mayar dani kan gado ta kwantar dani ta juya na riko rigarta sannan cikin muryar da naji kamar ba tawa ba nace “Inna bazan koma ba. In na koma mutuwa zanyi” ta juyo tana kallona sai ta zauna tace “komawa ina?” Sai kawai na bita da kallo, wato Saghir saboda bai daraja ta ba bai ma gaya mata cewa ya mayar dani ba? Sai ta gane me nake nufi tace “cewa yayi ya mayar dake?” Ban iya bata amsa ba sai kuka, sai ta mike tsaye “wannan wanne irin abu ne? Wanne irin ya mayar dake kuma? Suzo nan su kare mana cin mutumci sannan kuma ya mayar dake bayan babu wani mataki da aka dauka? To babu inda zaki koma. Yanzu fa Hafsa take bani labarin wai kawun ku Isa ya bashi Suwaiba” Suwaiba yar kawu Isa ce itama kuma kusan set din mu ce, mun dan girme ta kadan. Lokacin muna yara ita da Rumaisa ne suke crushing on hamma Saghir, murja tana yawan gayamin cewa har yanzu suwaiba tana son Saghir amma ni ban taba ko saka abin a raina ba. 

Inna tace “wato su suna can suna kokarin yi masa huce haushi shine shi kuma zai zo nan yace ya mayar dake? To ku biyu yake so ya hada a gida daya ko kuma ya yake so ayi? Ai indai kinga kin koma gidansa to ki tabbatar an zauna ne an hada ku anyi muku fada kowa an bashi laifin sa bawai kullum ace kece da laifi ba” tayi ta fadanta ni dai ina jinta kawai. Amma ni a raina nasan ko anyi mana fadan bana jin zan iya sake zama da Saghir, not after what he did today, not after what he said a gaban Sadauki.

Tuni da Sadauki da nayi sai naji wata irin fargaba ta shige ni. Tsoro nake ji sosai, tsoron abinda Sadauki zai iya yi akan furucin da Saghir yayi a gaban sa. Ina tsoron zuciyar Sadauki, ina tsoron zafin sa, ina tsoron rashin tafiyar sa, considering abinda yaji da kuma yanayin da ya fita a ciki, bansan hukuncin da zai dauka ba. Sai na samu kaina dayi masa addu’ar Allah ya taushi zuciyarsa Allah ya hane shi ga aikata abinda zaizo yayi nadama. 

Sai magrib na tashi. Nayi alwala nayi sallah nayi kuka sosai a cikin sujjada ta na roki Allah ya kawo haske a cikin al’amura na. A lokacin ne Asma’u suka dawo ita da Subay’a. Subay’a ta taho gurina da gudu ta fada jikina tana kallona tace “Mommy kin daina kukan? Dazu naga kina kuka” nace mata “na daina subis” sai tayi dariya tace “Daddy ya tafi ko? Dama cewa yayi zai kawo ni gurinki in kwana biyu sai mu koma gidan mu tare” bance komai da akan wannan sai tace “Mommy kullum sai nayi kuka nace da Hajiya ta kawo ni gurinki ita kuma taki. Mommy dan Allah ni kar a mayar dani can gidan gwara in zauna a gurin ko kuma mj koma gidan Daddy na tare” sai na daga ta nace taje tayo alwala tayi sallah. 

Na lura ta rame, ta fada sosai tayi baki. Kamar ba’a kula da tsaftarta sosai sannan idonta ya nuna alamar damuwa. Sai na yanke wata shawarar, bawai ni kadai ce bazan koma gidan Saghir ba har da Subay’a ma ba zata koma ba, tazo kenan. 

Da dare ina jin Inna tana cewa Asma’u ta kira mata Sadauki, kamar tasan ina son in tabbayda lafiyar sa. Asma’u ta kira switched off, a raina nace nasan za’a rina, amma ban furta komai ba nayi shiru kawai. Nan fa hankalin Inna ya tashi tace “wai me ya faru ne mai zafi a tsakanin su? Ni sam banji dadin yadda naga Sadauki ba tunda kuma ya fita hankalina yana kansa wallahi” ta juyo tana kallona tace “me Saghir din ya gaya masa me zafi haka?” Na sunkuyar da kaina kawai, ni ba zan iya gaya mata kalaman Saghir ba. Jin nayi shiru sai tayi ajjiyar zuciya tace “Allah ya kyauta”.

Washegari babu kunya babu tsoron Allah sai ga Aunty Fatima nan da Hajiya Yalwati da kanwar Hajiya Babba wai Alhaji Babba ya turo su su gaya wa Inna cewa Saghir ya mayar dani, a gaya min in shirya sai mu saka rana ni da Saghir din sai yazo ya dauke ni. Ni kawai kallon su na tsaya ina yi cike da mamaki. Inna tace “yanzu Fatima har da ke? Har dake za’a ci amanar marigayi dan bashi da rai?” Aunty Fatima tace “me akayi Amina? Yanzu mayar da auren shine cin amana?” Inna tace “ba mayar da aure ne cin amana ba, rashin kulawa da nuna son kai shine cin amana” sai ta lissafa musu dukkan laifuffukan Saghir wanda ni na gaya mata tace “ni ba wai goyon bayan Diyam nake yi ba ko kuma bana so ta koma dakinta ba, a’a, so nake a zaunar da Saghir shima ta fadi laifin Diyam din sai a hada su kowa ayi masa fada a bashi laifin sa. A ja masa kunne akan dukanta dan ni abinda yafi komai daga min hankali kenan” sai Aunty Fatima ta nuna itama bata ji dadin abin ba tace “ni duk fa bansan wannan ba, ni cemin sukayi Diyam tana kula Sadauki shi kuma Saghir yaji haushi ya saketa. Kema yadda muke dake ai kamata yayi duk abinda ya faru ki kira ni ki gaya min. Da Diyam da Saghir duk yayana ne ai”. Amma ita kanwar Hajiya sai ta kama fada, ita wai lallai nayi wa Saghir sharri “babu wani shayeshaye da yake yi balle neman mata” sukayi ta bugawa da inna har tayi zuciya ta tashi ta tafi Aunty Fatima ma ta tafi sai Hajiya Yalwati ta zauna tace sai anjima zata taho. Daga jin haka nasan tsegumi ta zauna yi. 

Tace “wallahi Amina karki mayar da yarinyar nan. Yaron nan fa bawai gyaruwa yayi ba. To yaron da baiji kan iyayensa ba ina zaiji kan wani. Shaye shayen nan fa munsan yanayi amma sai a rufe ido ace bayayi. Neman matan nan kuwa yinsa yake yi kamar babu gobe. Ita kanta Fatima da take wannan maganar rannan a gaba na naji tanayiwa Minal yarta fadan kar ta kuma kula shi. Dama Suwaiba ce tasa kuma yanzu sunce sun bashi dan haka ku rabu dasu, in dai abinda Diyam ta fadi gaskiya ne in ya auri Suwaiban ai zasu gani” Inna tace “za kuwa su gani. Ai ni zanso ayi auren nan ma ko dan gaskiya ta bayyana” Hajiya Yalwati tace “gaskiya kam zata bayyana. Tun yanzu ba gashi nan muna gani yana zuwa yana daukan ta a mota ba? Ahau, lokaci kadai muke jira”.

Har tana shirin tafiya kuma sai cewa tayi “ni Diyam kuma ta wani zubin banji dadin tahowar nan taki ba. Dama ke ce mai dan saka shi yana dan kawo mana abinci gidan. Yanzu kuwa shiru. Rannan har ya fara zancen aurar dasu murja yanzu kuwa yadda yake a rikicen nan nasan ba lallai ne yayi ba”. Inna ta dauki yan kudade ta bata tace ta siyawa yara sabulu.

Da dare sai ga wayar Saghir. Na kalli wayar kawai na dauke kai. Yayi ta kira sai na saka a silent sai ya turo min message “ki shirya. Rana ita yau zan zo mu tafi”. Sai na kashe wayar gaba-daya na ajiye.

Washegari wai dan rashin kunya sai ga Hajiya Babba da kanta. Ina ganin ta nayi wa Asma’u text. “Ki dauki Subay’a ku bar gidan nan, sai na kira ki zaku dawo”. Ina kallon su suka fice. Tazo ta saka inna a gaba “yanzu ya za’ayi ace kince ba zata koma gidan taba? Yanzu zumuncin kenan? Koma menene ya faru a tsakanin su shi ya hakura ita me yasa ba zata hakura ba?” Inna tace “tace ba zata koma ba. Ni kuma baxan matsa mata ba, matsantawar da nayi mata a wancan karon ma da ace zan iya dawo da hannun agogo baya da banyi ba”. 

Sai ta kama hannuna ta jani daki muka zauna a bakin gado tace “yanzu Diyam ke kinsan halin Saghir. Kinsan cewa ya chanja sosai saboda ke kuma ya chanja din. Yanzu da kika barshi Diyam Saghir duk ya koma yadda yake da koma fiye da haka. Me yasa ba zaki je ki karasa abinda kika fara ba? Ko dan saboda Subay’a” nace “Hajiya Saghir fa ba wai chanzawa yayi ba. Indai har da gaske ya chanza bai kamata ya koma ruwa ba dan bana tare da shi. Hakan yana nufin saboda ni ya chanza kenan ba wai saboda kansa ya chanza ba. To yanzu kuma in mutuwa nayi fa?” Tace “a hankali ai yake gyaruwar, in kin koma zai cigaba da gyaruwa ne” nace “Hajiya tun farko ba kwa ganin kamar akwai son zuciya da zalunci a cikin dora mim alhakin gyaran Saghir? Ku da kuka haife shi baku gyara shi ba tun yana danyensa ta yaya zaku bani shi bayan ya bushe kuma ku saka ran in kare rayuwata gurin gyaransa?” Tace “saboda munsan zaki iya. Kin fara kuma zaki iya karasawa” na girgiza kaina nace “bazan koma ba Hajiya” tace “saboda me?” Nace “saboda bana son shi Hajiya” sai ta tsaya tana kallona. Sai na tuno da ranar da Saghir yazo gaban inna yace baya son aure na. Hajiya tace “ba kya son sa fa kika ce min Diyam. Yanzu har idonki yayi budewar da zaki kalle ni kice ba kya son Saghir? Koma dai menene Saghir din nan, koma da gaske ne maganganun da kike fada still Saghir dai danuwan ki ne kuma duk kin da kike masa ba zaki taba cire jinin ki daga nasa ba. Mijinki ne kuma, tunda dai yace ya mayar dake Sannan uban yarki ne, ba zaki taba chanja mata uba ba” nace “Allah zai raya ta ko ba a gidan sa ba” sai ta mike da fushi ta fita, ina jinta tana cewa da Inna ina Subay’a zata tafi da ita, sai inna tace “Diyam tace Subay’a ba zata koma ba. Zata rike yarta” nan tayi ta bala’i “wallahi bata isa ba, ita tace ba zata koma ba sannan yar tasa ma ta hana shi?

Da dare inna ta kuma saka Asma’u ta gwada number din Sadauki but still bata shiga. Inna ta kalleni tace “ke baki san inda yake zaune ba?” Na girgiza kai nace “ban sani ba Inna. Sai dai office dinsa na sani” Asma’u tace “ni dai nasan kamar a hotel yake zaune. Amma bansan wanne hotel din ba” Inna tace “to ko Asma’u zan tura office din nasa gobe ta gani? Ni duk zuciyata bata min dadi wallahi”.

Washegari Asma’u tana dawowa daga school sai gashi ya kirata. Tace “Inna ga hamma yana kira” Inna tace “to kiyi sauri ki dauka mana kar ta katse kuma? Alhamdulillahi” Asma’u ta dauka tana gaishe shi sai naga ta kalleni tace “tana nan” sai kuma ta mike zata fita, Inna tace “ina kuma zaki je?” Sai Asma’u ta daga mata hannu ta fita kawai. 

Shiru shiru, ni dai ina zaune a kan kujera staring into nothingness har Asma’u ta dawo after like two hours. Ta zauna tace da Inna “yace ince miki yana lafiya kuma gobe zai shigo” Inna tace “shikenan? Duk wannan dadewar kuna waya shikenan abinda yace?” Asma’u tace “tambayoyi yayi ta yi min kawai. Akan Adda. Yanayin zamanta a gidan Saghir” Inna tace “ke kuma me kika ce masa?” Asma’u tace “everything. Duk abinda na sani na gaya masa sai dai kuma wanda ban sani ba. Abinda na fahimta shine duk shekarun nan shi ya dauka Adda lafiya take zaune a gidan mijinta” na dauke kai ina lissafin wanne ne abinda Asma’u ta sani wanne ne kuma wanda bata sani ba?

Washegari da safe muna breakfast yazo. Fuskarsa babu annuri ko digo a cikinta ya gaishe da Inna muma muka gaishe shi. Ya kalli Subay’a yace da inna “an dauko tane?” Inna tace “tunda uban ya kawo ta Diyam tace ba zata koma ba” yace “good. Ba zata koma ba. Ita ma kuma Diyam din ba zata koma ba sai dai in har ita ce take son komawar” ya juyo ya kalle ni yace “kina son komawa gidan Saghir?” Na sunkuyar da kaina ina girgiza kaina da sauri, yace “good. Then ki dauki wayarki ki kira shi. Ki gaya masa ba kya sonsa ba zaki koma gidansa ba. In yana son rabuwa ta arziki to ya kawo miki takardar ki within the next three days, in kuma ba haka ba kice masa zaki kaishi kara in yaso alkali ya raba ku”.

Ya juyo yana kallon Inna yace “Baffa uba ne a gurina. Dan yadda nake jinsa a zuciyata har yafi yadda nake jin shi kansa wanda ya haife ni saboda Baffa ya bani abinda shi din bai bani ba. Baffa ya bani soyayya, ya bani kulawa, ya bani tarbiyya. And he used his last breath a duniya to tell me in kula daku, and that’s what I have been trying to do, and that’s what I will continue to do sai inda karfi na ya kare”.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button