BA DON SHIBA 102
Page 1⃣0⃣2⃣
LAST PAGE
Tsaki yaja me cike da takaici ganin,har yanxu drivern bai karaso ba gaba daya ya rasa inda zai sa kanshi babbab burin shi shine yaje yaga jiddah.
yana cikin,wannan,tunanin sai ga drivern ya karaso bai tsaya jin ta bakin sa ya shige motar tafiya sassauka sukayi sai gasu sun shigo cikin unguwar ganin yayi drivern na nufar hanyar gidan su da sauri ya katseshi tare da fadin banan zamuyi ba kwatqnce ya rinka mai sai gasu a kofar gidan su Jiddah.
Wani farin ciki ne ya lullubeshi ji yake tamkar yau ammai,bushara da gidan aljannah.
shiru kofar gidan,ba kowa har zai shiga ciki sai kuma yaga wata tsaleliyar mota tayi parking a kofar gidan fasa shiga cikin,gidan yayi dan yasan daya daga cikin en iskan yaran nan ne..
tunanin shi ya tsaya cak ganin wata kyakkyawar budurwa ta fito daga cikin motar jikin ta sanye da wasu irin kaya wqnda ko a wadanda ba musulmai ba sai cikakken mara kunya zai sa su.
shima wanda ya sauke ta ya fito tare da riko hannun ta yana fadain”baby yanxun a gida zaki kwqna pls ki bani 2daz mana saboda ke na tsallakr duk abinda nakeyi nazo amma kwqna 1 kika min.
cike da yauki ta fara magana kamar bata so uhmm nifa a hakan ina ganin nayi maka kokari amma ka raina shikenan sai kuma next tym yanxu zan shige.
shiru yayi bai kara magana kudi ya dauko wanda basan iyakar su ya zuba mata a jaka kamo hannun ta yayi ya kai,mata kiss sannan ya shige mota sao da ta ga ya wuce ta jiyo domim shiga.
Abinda tayi arba dasji ne lokaci daya yasa jakar ta faduwq duk kudin ciki suka zube jikin ta ya fara sai,hawaye kamar an bude famfo.
tun da fara zuciyar shi ke bashi wqni abu amma ya karyata hakan sai da ta waigo ya tabbatar da zargin da zuciyarshi ke gaya mishi.
duk da ta canxa amma hakan bai hana shi gane tq a kallo daya.
ita kam tunda ta tsugunna a wajen take kuka bata taba tsammanin AMMAR zai dawo a wannan lokacin ba.
karasowa yayi inda take ya tsugunna ya kamo habar ta abin mamaki shima kukan yake kamar ba Ammar da ta sani jarumin namiji ba.
A kasan zuciyar sa ji yakeyi kamar zata fashe wai Jiddah ce ta koma haka.
da sauri,ya mike ya shige mota dan idan ya cigaba zama anan zuciyar shi zata iya tarwatsewa.
Mikewq tayi ta shige gidah tana kuka mai cin rai.
A bangaren AMMAR kuwa duk wani abu da Abban shi ya tanada na dawowar sa babu wqnda ya kalla kuma ya tambeye shi yace ba komae.
Nura ya kira a waya cikin 5mnt sao gashi ya iso yanayin da yaga Ammar abin ya tada mai hankali idan yayi jaa duk jiyoyin kanshi sun tashi kallo daya zaka masa kasan yana cikin tashin hankali.
Tambayar nura yaui akan halin da yaga jiddah a ciki tun yaushe hakan ya soma faruwa.
tass Nura ya labarta masa komae.
Tabbasa akwai wani abu a kasa bayin kanta bane ya tabbata akwai sa hannun inna asabe a ciki.
Gidan maman salaha yace nura ya rakashi.
da murnar tq ta tarbeshi tare da kawo masu ruwq da drinks.
Itama tqmbaya ya mata akan jiddah nan ta kwashe komai ta fada masa.
tausayin jiddah da kuma soyayyar ta suka dawo mai sabuwq filll.
cikin bacin rai ya fara,magana”nayi alkawarin dui inda magani yake sai na nemo shi sai jiddah ta dawo kamar daa har sai tafi daa insha allah.
cikin hanxari maman salaha ke bashi labafin wani mai magani,da ya shahara wajen karya sihiri.
cikin murna yake tambayar ta wani gari yake.
ai ba nisa a zaria yake unguwar ban xaxxau.
hamdala yayi sannan ya mike suka mata sallama.
gisan su jiddah suka nufa bai tsaya neman ixini ba ya shige gidan kamar daga sama inna asqbe ta ganshi cikin kaduwa ta mike ta shige daki.
dakin jiddah ya nufa kwance ya sameta tana aikin kuka kanta duk ya yamutse idon yayi jaa.
karasa yayi kusa da ita ya zauna sannam ya fara lallashin ta.
sai,da ta yi,shiru sannan yace ta hada kayanta zata je gidan maman salaha.
ba abinda ya bari ta dauka dan yaga duk kayan bana arziki hijabi ne guda daya ta saka sannan suka fita.
inna asabe na kallon su ta window qmma ba halin magana.
tasan tunda wqnnan tsinannen yaron ya dawo tofaj komai nata sai ya lalace.
hijab ta zara sai gidan,muguwar kawar tq ta fada mata duk abinda ke faruwq.
basu tsaya bata tym suka nufi gidan boka na kan tudu.
fada mata yake tayi sakaci domin kuwa idan har yaron nan yana nan tofahh aikin bazai ciba.
wqni kullin magani ya bata sannan yace a tabbatar yaci maganin to bakin shi zai kulle ita kuma jiddah a tabbatar ta taka tofahh sai tayi yawo tsirara.
kudin suka bashi suja fito suna murnar mota suka shiga suna kara firan mugun abunsu.
basu ankara ba sai ji,sukayi drivern yana salati cikin kaduwa suka kalli gaban motar.
wata tanka ce ta nufo su gadan gadan mutane ma sai salati suke takan su wannan motar tabi.
a take muguwar kawar inna asabe ta mutu.
ita kam ana cirotq a motar a sume aka samera kafafuwqn ta duk cixge driven ma a sume yake asibito a kayi dasu ita kuma gawar aka sa a mutuware.
A gidan maman salaha ta kwana washe gari da sanyin safiya ammar ya iso suma sun gama shiryawa ita sao jiddah bata san inda zaa je binsu,kawai take.
sun isa lafiya inda malamin yana kallon aJiddah yasan meke faruwa da ita.
tana hada ido dashi ta hade rai.
daki ya shiga ya dakko wani abu ba tayi xato ba ci tayi kawai an watsa mata abu,mai radadi a jiki.
ihu tayi wanda duk sai da gidan ya amsa.
cigaba yayi da zuba mata ruwan yana kuma karanto addu’a yana tofah mata.
wani abu ya dauko ya turo mata a hanci birgima ta farayi tana ihuu ammar tana kuma fuxgefuxge ammar malam ta kira ya riketa sannan yasa wata igiya ya daure mata kafa da hannaye.
sannan ya cigaba da zuba mata wannan ruwan addu’an.
sai suka ji wahala sannan suka fara magana wai turo su akayi su sata yawon karuwan ci amma sunyi alkawarin zasu fita ya dena kona su haka.
sai daya kara galabaitar dasu sannan suka fada masa wadda tayi aikin.
wqnnan abun ya kara turq mata a hanci a take ta rinka jero atisshawa.
bacci ne ya dauke ta a take.
hamdala sukayi gaba daya sannan malam ya basu wasu magunguna wani a shafa wani kuma a tayi wqnka.
sai da tq kwashe 2hr tana bacci sannan ta farka da salati a bakin ta.
kallon su take daya bayan daya idon ta ne sauka a kan ammar mamaki ne ya kamata to yaushe ya dawo.
tunanin ta ya katse sanda,maman salaha ta riko ta ta mikar da ita tsaye.
gidan maman salaha suka nufa sai tym,take tambayar ta meya faru taga ammar yaushe ya dawo.
bata fada mata sai ruwan wanka ta hada mata sannan ta xuba maganin a ciki.
tana fitowq ta bata oil ta shafa sannan ta kwanta.
inna asabe ana can asibiti sanda ta farka taga kafafunta duk babu su sumewa tayi gashi an kira yaranta duk ba wanda yazo.
da kwatancen data musu aka kawo ta har gida a lokacin ne tayi kuka kamar ranta zai fita gata kwance ga rabi kwance indo kuma ra tafi yawon ta haladi kam dama sai tayi sato bata ganshi ba asiya ce kawai mai taimakonta.
rayuwa ta juya mata baya ji take dama mutuw tayi ta huta.
farkawar jiddah daga bacci ya dadae da shigowar ammr gidan.
tunani takeyi na rayuwar da ta yi a baya gani take kamar a mafarki.
sai da taci abinci sannan ammar da,maman salaha suka mayar mata da abinda ya faru ashe ba,mafarki bane kuka takeyi sosai wanda hakan ke kona zuciyar Aammar da kuma kara jin tsanar inna asabe a ransa.
dakyar suka lallashe ta yi shiru sannan ya fada musu halin da inna asabe ke ciki.