NAFEESAT 1-END

NAFEESAT Page 31 to 40

    *MONDAY*                 *12:30pm.*

                Ya gama shirin sa na zuwa Office, yana sanye cikin wandon jeans blue, sai baƙar riga me gajeren hannu da ya sake fito da hasken skin ɗin sa sosai ya kuma ƙara masa kyau ainun, kwantaccen baƙin gashin sa sai shaining yake yi zuwa siririn sajen sa, babu abinda yake tashi ajikin sa sai sassanyan ƙamshi me tsananin daɗi ga duk wanda ya shiga hancin sa

Wrest watch yake ɗaura wa a tsintsiyan hannun sa me haske sosai da yalwan gashi, fuskarsa babu alamun fara’a ko kaɗan, har ya gama sakawa kafin ya zauna gefen gado ya soma saka Combat ɗin sa da ya kasance Blue Colour da igiyan sa suka kasance baƙi, bayan ya gama saka wa sai ya miƙe ya ɗau briafcase ɗin sa ya fito cikin ɗakin yana rufe wa

Babu kowa cikin parlour’n, sai ya nufi ɗakin Hajiya yayi Nocking yana jiran izni

Hajiya dake zaune kan gado wanda fitowar ta kenan daga Toilet ta ba da iznin shigo wa

Tura ƙofan yayi yana motsa bakin sa idanun sa a kan ta

Kamar yanda itama ta zuba masa idanu tana kallon sa

Takowa yayi a hankali har zuwa gaban ta kafin ya zauna gefen gadon, shiru yayi yana murza hannun jakan dake riƙe cikin fararen tafin hannun sa

Tsawon mintuna biyu Hajiya tana jiran taji yayi magana amma sai taga be da alaman yi, hakan yasa tace, “har ka shirya my son?”

Gyaɗa mata kai yayi yana kallon ta

She smiled and said, “God bless you and good luck.”

“Ameen”. Yafaɗa a hankali wanda a laɓɓan sa ta fahimci abinda yace

Miƙe wa yayi ya taka ya fice cikin ɗakin yana duba agogon hannun sa.

        Yana fita wajen motan sa ya buɗe ya shiga ya zauna sannan ya rufe, tada motan yayi yaja ya nufi bakin Gate

Tun daga nesa da me gadi ya hango zuwan sa ya miƙe da sauri ya buɗe masa Gate ɗin, yana fita ya ƙara Speed, cikin mintuna ƙalilan ya’isa haraban Hospital ɗin

Ɓude ƙofan yayi ya ziro ƙafafun sa a hankali sannan ya fito ya rufe, ya juya ya soma tafiya cikin taƙama da izza wanda zaka san a jinin sa ne.

               Shakira da Ayush dake tsaye jikin motan Shakiran, Ayush tana faɗa mata yanda suka yi da Baffa sai idanun ta ya faɗa kan Usman dake doso cikin asibitin, baki buɗe take bin shi da kallo

Hakan yasa itama Shakira ta mayar da hankalin ta inda Ayush ɗin take kallo, nan ta hangi Usman har ya shige

Ajiyan zuciyan da Ayush ta saki me ƙarfi ya saka Shakira take kallon ta cike da mamakin ta

“Lafiyan ki kuwa?” Ta tsinkayi muryan Shakiran da ta sake dawo da ita hayyacin ta

“Hmm ba lafiya ba, wane ne wannan Handsome Guy ɗin da naga kamar yana kama da Familyn ku?” Ayush tayi maganar tana tsare Shakira da idanu

Taɓe baki ita kuma tayi tace, “Yaya Usman ne”.

“Kaiii amma wlh ya haɗu, Ni zan iya ce miki ban taɓa ganin mutumin da ya tafi da imani na a second ɗaya ba irin wannan, kai wlh ban taɓa ganin wanda komi nashi ya dace dashi ba sai wannan guy ɗin, Kai Amma wlh ban taɓa..”

“Ke dallah ya isa mana, meye haka kike zuba min hauka? ko dai hankalin ki ya gushe ne?” Shakira ta katse ta tana kallon ta cike da takaici

“Wlh baza ki gane bane, amma wlh yayi Ni dai ya gama dani”.

Shakira tace, “to shikenan yanzu kenan baki yi da Yaya na sai wannan ko? Ko kin manta alƙawarin da ki kai min?”.

Murmushin yaƙe Ayush ta saki tace, “laa I don’t mean that. I’m just saying my opinion on this, but I’m not saying I’m better than Baffa, I like Baff..” Sai kuma tayi shiru ganin zata saki layi

Shakira da hankalin ta ma ba ya ga Ayush ɗin, tana kallon Fadila da tazo wuce su tayi saurin kwaɗa mata kira

Fadila dake tafiya waya a kunnen ta tajuya ta kallo su, sai kuma ta soma takowa wajen su har a lokacin tana ci gaba da wayan ta, sai da tazo dai-dai gun su sannan ta kashe wayan tana ɗago kai ta kalle su

Shakira murmushi tayi tace, “manyan gari wai ke idan ba an neme ki bane ba kya neman mu ko?”

Guntun murmushi kawai Fadila ta saki ba tare da tace komi ba illa gyara zaman jakan ta da take yi

“Yanzu muka gama magana da mutumiyar ki a kan ki ma”. Shakira ta sake faɗan hakan still tana Murmushi

Kallon ta Fadila tayi da rashin fahimta kafin tace, “who?”

Shakira tace, “Ɗahira, ai ita nake nufi, kullum kuma idan na ganta sai na ce ta gaishe min da ke, Allah yasa tana faɗa miki don nasan halin ta ba wai son ki take yi ba?”

Numfashi Fadila taja sannan tayi murmushi tace, “haka ne.. to Ni zan tafi kin ga nayi late yau ban shigo da wuri ba”. Sai kuma ta ɗan ɗago wayan ta tana duba time kafin ta juya ta tafi ba tare da ta sake furta komi ba

Daga Ayush da tun zuwan Fadilan take kallon ta har Shakira bin bayan ta da kallo suka yi har ta ɓace ma ganin su

Tsaki ne ya biyo bayan shirun nasu

Ayush ta kalle ta da mamaki tace, “mene ne ƙawata?”

Sai da Shakira tayi ƙwafa kafin ta buɗe motan tace, “Allah Fadila tana baƙanta min rai idan nayi mata maganar Ɗahira take nuna halin ko in kula wanda Ni ba hakan nake so ba”.

Dariya Ayush tayi duk da bata fahimci me take nufi ba, ta nufi ɗayan side ɗin ta buɗe ta shiga, itama Shakiran shiga tayi ta rufe ƙofan tare da jan motan suka bar haraban Hospital ɗin.

           ⚫⚫⚫

               Kai tsaye hawa na uku ya wuce inda a nan ne office ɗin sa yake, Office ɗin na kallon na Ɗahira ne

Buɗe wa yayi ya shiga ya rufe, kallon ko ina yake yi da idanu fuskar sa babu fara’a, ko kaɗan ba ya farin ciki da kasancewar sa a nan ɗin, jin sa kawai yake yi cikin takura kuma hakan ne ya ƙara ɓata masa rai sosai

Duk da office ɗin yana da girma, ga shi ya haɗu tako ina amma shi be burge shi ba ko kaɗan tunda ko kwatan nashi na ƙasan Turkey be yi ba

A hankali ya soma takawa ya nufi kan kujeran ya zauna yana kwantar da kansa jikin kujeran, ya lumshe idanun sa yana jujjuya wa cikin kujeran, numfashi kawai yake sauke wa ba tare da ya motsa ba tsawon lokaci, sai da wayan sa ta soma ringing ne sannan ya buɗe idanun sa yana ɗago kai yabi wayan da kallo a inda ya’ajiye saman table, ganin sunan Dady na yawo a screan ɗin wayan hakan yasa shi sanya hannu ya ɗauka ya kanga a kunne bayan yayi peacking call ɗin, shiru yayi yana sauraron sa kafin ya buɗe baki a hankali yace, “Eh na zo”.

Kallon files ɗin gaban sa yayi, sannan ya yamutsa fuska yace, “ok”.

Sai ya cire wayan a kunnen sa yana ajiye wa, ya sake maida kansa jikin kujeran ya rufe idanun sa

Bayan mintuna biyar ya jiyo Nocking, iznin shigowa ya bayar ba tare da ya motsa ba

Ɗaya daga cikin staff’s ɗin asibitin ne ta shigo, ta gaishe sa but ko amsa ta be yi ba, kamar ma be san da wanzuwar ta ba

“Dr Noor told me to bring this to you.”

Hannu ya nuna mata alamun ta ajiye a table

Don haka babu musu tayi yanda yace mata sannan ta juya ta fice

A ƙalla ya ɗau tsawon mintuna goma kafin ya buɗe idanun sa ya ɗago kai yana kallon files ɗin gaban sa, numfashi yaja me ƙarfi sannan kuma ya ɗaura kansa saman table ya sake rufe idanun sa be da alaman yin abinda ya kawo sa.

         ⚫⚫⚫

         Hannun yarinyan ta riƙe tana kallon ta cike da tsantsan tausayi, wai yarinya ƙarama kamar wannan ace an yi mata Fyaɗe, kee duniya ina zaki damu ne? Mene mutane suke nema a kan ƙaramar yarinyan da bata fi shekara biyar ba?

Numfashi taja tana sanya hannun ta kan yarinyan ta soma shafa mata gashi, ko kaɗan yarinyan ba ta motsi, ba ma zaka san tana da numfashi ba sai idan ka ƙura mata idanu sosai zaka ga tana fitar dashi ɗai-ɗai ta cikin Oxgyen ɗin da aka sanya mata

1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button