NAFEESAT 1-END

NAFEESAT Page 31 to 40

“This is the first and last time you would do such a thing to me again, domin Ni ba abokin wasan ki bane, idan ba haka ba uhmmm”.

Sai ya ci je leɓen sa na ƙasa yana sakin kanta, ya juya ya danna Numban Liftern yaci gaba da tafiya, yana kai su downstairs ya buɗe ya fice.

      Ɗahira dake durƙushe a ƙasa tana ta shashsheƙan kuka, ko motsin kirki ta kasa yi sabida baƙin ciki da ƙuncin da ya cika ta, ji take yi tamkar ana tsaga magudanan jinin ta ana ƙara rura wutan tsanar da take yi masa

“Shin ta ya ma zata iya bari wani ƙaton banza ya zauna yana mata irin cin mutuncin nan? Kamar ta? Me ta tare masa ne?”

Ta jima a haka kafin ta share hawayen ta tare da gyarawa eyeglasess ɗin ta zaman sa, ta miƙe ta buɗe Liftern ta fice, a hankali ta taka har gaban motan ta tabuɗe ta shige, ja tayi tabar Hospital ɗin.

      Tuƙin take yi amma hawaye na kwaranya a kyakkyawar face ɗin ta, maganganun Usman ne ke dawo mata kwanya, a haka har ta kai gida tayi parcking motan, sai dai ta kasa fitowa sai ma sake fashe wa da tayi da sabon kuka, sosai ranta ke suya da abinda yayi mata, ta rasa meyasa tarasa ƙwarin gwiwan da zata iya mayar masa da martani, alhanin tayi wa kanta alƙawarin baza ta sake barin sa yaci mata mutunci ba, ko kaɗan baza ta iya jure wa ba, shiyasa abinda yayi mata yanzu yayi mugun ɓata mata rai

Kifa kanta tayi saman sitiyarin motan tana rufe idanun ta ruf, tunanin abinda zata yi masa ta huce take yi, but ta kasa, don haka ta ɗago kanta ta share fuskarta tare da gyarawa ta fito daga motan, rufewa tayi ta wuce Part ɗin su.

        A ranan sukuku ta wuni ta kasa taɓuka komi, duk idan ta saki jikin ta sai ta tuna abinda ya faru ɗazu, sai kuma gaba ɗaya ta rasa fara’an ta

Aunty Amarya da ta kula da yanayin ƴarta, tayi mata magana, but Ɗahira ce mata tayi, “babu komi”. Dole ta ƙyale ta don ta san halin ta akwai zurfin ciki wani lokacin.

      Washe gari tana tashi daga barci ta kunna wayan ta, ta soma cin karo da saƙon masoyin ta, yawanci duk complain yake mata a kan rashin reply ɗin ta, kasancewar tunda ta dawo daga aiki ta kashe wayan bata sake kunna wa ba

Murmushi kaɗai tayi ta ajiye wayan ta shige Toilet, sai da tayi wanka kafin ta dawo ta mayar masa da reply ɗin, sannan ta shirya cikin doguwar riga abaya fara me kwalliyan stone da ratsin ja, ta yane kanta da gyalen sannan ta fito

Ɗakin Aunty Amarya ta shiga, tayi mata sallama zata tafi, har ta kai bakin ƙofa ta kira ta tana tambayan ta “taci abinci?”

Dayake Ɗahira ba me yawan yin ƙarya bace don bata saba ba, sai tace mata “a’a but zata ci idan taje can”.

Hararan ta Aunty Amarya tayi tace, “yi maza je kici abinci kar in saɓa miki”

Dole ba don ta so ba ta’amsa mata da “to”. Sannan ta fice

Kan dainning ta wuce ta zauna ta soma haɗa tea, shi ne kaɗai abinda zata iya saka wa a bakin ta don ba daɗin jikin ta take ji ba, ga kanta dake ta faman sara mata sakamakon kukan da tasha jiya.

        Fadila ne ta fito itama ta zauna akan dainning ɗin ta hau haɗa abun karin ta, sai da ta gama sannan ta kalli inda Ɗahira take a karo na biyu tun zuwan ta wajen, tun jiya ta kula da yanayin ta kamar tana cikin damuwa, sai dai kuma miskilanci ya hana ta tambayan ta, yanzun ma ganin Ɗahiran ta tafi tunani ta kasa shan tea ɗin ne ta kalle ta tace, “Sister, are you all right? What’s wrong with you?”

Ɗago idanuwan ta tayi ta kalli Fadilan kafin ta kau da kai tana sauke numfashi a hankali, ɗaukan tea Cup ɗin tayi tana bata amsa da faɗin, “nothing, I am thinking something”.

Fadila bata sake magana ba duk da kuwa bata gamsu ko kaɗan da amsar ta ba, sai ma ci gaba da tayi da yin breakfast ɗin ta.

      Miƙe wa Ɗahira tayi tare da ɗaukan jakanta tayi hanyan fice wa, a Steps ta haɗu da Baffa zai yo Part ɗin su, sai ya tsaya yana kallon ta, yayinda itama ɗin ta tsira masa idanu, kafin kuma ta ɗauke nata ganin yanda yake mata kallon ƙurilla, ɗan dai-dai ta fuskarta tayi tana sakin murmushi tace, “Good morning my brother”.

Be amsa ta ba illa jeho mata tambaya da yayi, “What is wrong with you, my dear? What happened to your swollen eyes?”

Har a time ɗin murmushin fuskarta be gushe ba tace, “Yaya babu komi.. it’s just that I’m not feeling well”

“Shi ne kika yi kuka?” Ya sake jeho mata tambayar

Shiru tayi tana sauke kanta ƙasa

Sake matsowa kusa da ita yayi yana bin ta da kallo, sosai suka yi kusanci da juna, hakan yasa har suna jin hucin junan su

Da sauri ta ɗago kanta ta zuba masa manyan idanuwan ta, sai tayi saurin ja da baya gaban ta na matsanancin faɗuwa da ganin wasu abubuwa cikin idanun sa, wanda ta kasa fassara su illa saka ta a matsanancin faɗuwar gaba da suka yi, saurin runtse idon ta tayi saboda yanda ƙirjin ta ke sake bugawa sosai, ƙarar sahun takalman da taji yasa ta buɗe ido a lokaci ɗaya

Gaba ɗayan su daga ita har Baffa suka bi Usman da kallo, wanda yake dumfaro wajen su shima idon sa a kansu fuska a turɓune

Ɗahira ɗauke kai tayi daga kallon sa, tana mayar da idanun ta gefe

Lokacin har Usman ɗin ya iso wajen suna gaisa wa da Baffa, iyakan gaisuwa ya haɗa su ya wuce ya nufi hanyar Part ɗin Kaka

Idanu Baffa ya aza kan Ɗahira yace, “meyasa kike son min ƙarya ƙanwata? Kin san duk halin da kika shiga dole ne na gane? Sabida kin kasance mace me fara’a, wanda ba komi ne yake ɓata mata rai ba, kin kasance me juriya me ɓoye baƙin cikin ki ga maƙiya, why kike son nuna gazawan ki?”

Itama idanun ta da suka cika taf da hawaye ta mayar kansa

Ganin ƙwalla cikin idanun ta sai hankalin Baffa yayi mugun tashi, nan da nan ya rikice da tambayar ta yana saka hannu ya riƙo mata hannayen ta

Bata yi yunƙurin hana sa ba, illa lumshe idanu da tayi tana matse bakin ta, buɗe idon tayi cikin rawan baki tace, “How can you tell you what is wrong with me? What have I done? How can Yaya Usman hate me? Meyasa yake son muzguna ma rayuwa ta? Shin na taɓa yin masa laifi ne a rashin sani?” Taƙarishe maganar cike da ɗacin zuciya hawayen na silalo mata daga kuncin ta

Sake damƙe hannayen ta yayi cikin nasa, cike da sanyin murya yace, “Ƙanwata ki dena saka damuwa a kan abinda Usman yake miki, babu abinda kika yi masa, kawai Allah ne be haɗa jinin ku ba, amma insha Allahu wata-rana sai yayi alfahri dake a rayuwan sa, tabbas watarana komi zai wuce my dear, ki saka wannan a ranki zaki ce na faɗa miki, duk inda akwai jini dole ne akwai ƙauna, ke ɗin ƴar uwan sa ce, dole zai so ki kuma zai yi nadamar hakan, Plz ƙanwa ta wannan ya dena ɗaga miki hankali, I’m not happy to see you in this situation. wlh ina ji kamar zan mutu duk sanda na ganki a damuwa, ko kaɗan ba na jin daɗi”.

Murmushi ta saki hawayen ta na sake silalo wa, cikin farin ciki tace, “haƙiƙa shiyasa nake sake alfahari da kai yaya, wlh billahi kai kaɗai ka ishe Ni a matsayin Yaya, ina son ka yayana ina matuƙar son ka fiye da yanda kake so na! insha Allahu kuma bazan sake damuwa da ko wani abu da ya nuna min ba, domin kai kaɗai ka ishe ni”.

Murmushi sosai Baffa yake yi sakamakon jin zantukan ta, tsaban farin cikin jin kalman so a wajen ta, be san sanda ya janyo ta ya rungume ta ba; duk da kuwa ba yau ya soma jin hakan a wajen ta ba

Sosai Ɗahira ta zaro ido da ganin abinda be taɓa faruwa da ita ba, tayi saurin jan jikin ta tana matsawa da sauri

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button